MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 19
MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 19
Suna cikin dakin su kowanne yana kokarin karasa hada ragowar kayanshi a cikin trolley domin da daddre idan zasu tafi gidajen su kowa ya tafi da abinsa,Abubakar sai murmushi yake yi Sadeeq na kallonsa amma be tambayesa ba domin yasan dole ya gaya mai tunda abin da alama na farin cikin sune. Jin yayi shiru yasa Sadeeq yin gyaran murya Abubakar ya sake yin dariya ya ganosa shima sarai hakan yasa shi kin gaya masa sayya wanashi tukunna, Sadeeq ya sake daukar towel yana yarfewa amma still Abubakar yayi shiru ganin haka yasa Sadeeq yin magana da cewa. “Kai twinnie kasani a gaba sai faman smiling face kakeyi, kagaya min muyi tare mana. “Oh sorry ai bansan kana son jiba, kawai tunani nakeyi naga tunda aka haifemu har muka girma bamu taba raba daki ba indai muna cikin garin nan, amma sai gashi twinnie kana cikin garin kano Ina ciki amma mata sunsa zamu rabu muje mu kwana kusa dasu.”
Shima Sadeeq murmushin yayi yana kokarin zuge zip din trolley din, shi kansa haskilo hakan yake yana hangosa da Zarahn shi abar kaunarsa. Dukjinsu sukeyi tamkar wasu sababbi a cikin duniyar sunajin wani nishadi Abubakar yana hango yadda zasu kwashe a daran yau shida INdo ya kuma yin wani murmushin har yana fitar da sauti Sadeeq ya kuma kallonsa tare da mikewa yana cewa. “Amma dai ba abinda ka gaya min kadai kesaka wannan farin cikin ba dan abin naka yayi over..?!”
“Ina tunanin yadda zamuyi rayuwa ne da Humairah, ina ganin kamar bazan iya barinta anan ba kafin a gama gyara min gidan danake acan, twinnie advice me please.”
Mamaki Sadeeq yake ganin wai lNdo Abubakar yake yiwa wannan sambatun tun kafinma suyi rayuwar aure ya kuma fahimtarta. Jan trolley dinsa yayi yakaita saitin kofa sannan ya dawo yana kokarin cire singlet din jiginsa zai shiga wanka dan sai anfara daura nasa
auran sannan zasu wuce ayi nashi yace. “Toh mezai hana idan kagama 2weeeks din naka kutafl tare saita zauna a gidan haka tana ciki ana gyarawa ai tasaba da rayuwa a irin wannan yanayi bazata damu ba.” Wani banzan kallo Abubakar yayi mai kamar yasan hakan zata faru yaki kallonsa saima saurin shigewa toilet dayayi yana murmushi ciki-ciki. Kwafa Abubakar yayi tare da zuge tashi trolley din sannan ya kira lNdo a waya ringing biyu ta dauka yaji muryarta a dashe tana gaidashi yayi dariya yana cewa. “Kai babyna tun yanzu.?!” Tayi dariya murya a dashe tace “Tun jiya da yamma.” Yace “Nikam banajinki amma tunda naji kadan bari na kyaleki inyi wanka kafin gobe kizo kiyi min..” Kit.. Yaji ta kashe wayar dama yasan za’arina yayi dariya tare da ajiye wayar ya gama kimtsa komai nashi shima Sadeeq yana fitowa ya shiga kafin ya fito har abokansu sunfara zuwa. Karfe 11:00am suka fito cikin shiga iri daya hatta aikin babbar rigar da agogonan su
takalminsu da huluna duk iri d’aya ne sai faman kamshi suke zubawa lokacin gidan yacika da mutane, sai suka fara gaggaisawa
gidan su Fateema bakunan su kaf yaki rufuwa kai daka gansu kasan suna cikin farin ciki.
Shadaya da rabi dai-dai dubban mutane suka shaida auran Sadeeq Salman Harun da Fateema Idris yahaya. Sadeeq murna kamar zuciyarsa zata fito sai gaisawa suke da mutane wanda yawance basu gane waye angon ba yanzun sabida kowa akayiwa murna saiya amsa. Bayan sun shiga gidan su Amaryar sun gaisa da iyaye amarya ta fito cikin makeup tayi masifar yin kyau cikin farin les riga dazani tazo ita kanta kasa gane waye nata tayi saida aka ce za’ayi musu photo su biyu sannan aka musu su uku itace a tsakiya, ana gamawa suka fita. Bayan an koma gida mutane sunci abinci sukuma suka kumayin wanka suka sa wasu fararan kayan wanda suma babbar rigace kalar surfanine ba irin wanda suka cire ba nan ma sunyi masifar yin kyau Abubakar yayi ma INdo text message cewar gashi nan zasu taho. Motoci ne reras sunfi ashirin aka tafi Sumaila kauyen Sani unguwa kuwa unguwar su lNdo akayi parking motocin, ana gayawa su lndo jikinta ya fara rawa hankalinta ya tashi tsoro ya fara shigarta suna zaune a gidan Rukayya ta kule cikin uwar dakinta tayi shiru domin su Uwani su Rukayya duk suna bata labarin Abubakar nata kiran wayarta tana gani taki dauka shi kuma befasa kiranta ba. Sai dasu baffajo na saye suka shigo zauran gidan sukace a fito musu da ita sannan ta fita jikinta ya kuma yin sanyi. Hannayenta suka kama sanye take cikin shadda maroon color sai hijjab datasa fuskarta tasha kwalliya kaida kagani kasan amarya ce su Baffajo suka wuce da ita wajan masu daurin auran Abubakar na zaune aka zaunar da ita a kusa dashi ga uban maza waliyin amarya ya tambaye ta. “Aisha kina son Abubakar wanda za’a d’aura muku aure yanzu..?!”Kan lNdo a kasa jikinta sai uban rawa yakeyi Abubakar hankalinsa yayi mugun tashi ganin tayi shiru, ana kokarin sake tambayarta ta daga Kai alamar Eh sai a sannan ya sauke wata uwar ajiyar Zuciya yana dafe kirji shima wakilinsa ya tambayesa. “Abubakar kana son lNdo zaka aureta da yardarka ba takurama akayi bako..?!” Yace “Eh uncle.” Sannan akayi kabbara aka fara addu’ar daurin aure a gurin aka damkawa lNdo kudin sadakinta naira dubu tamanin lakadan kowa ya shaida sannan su Baffajo suka shiga da ita cikin gida, fuskarta kunshe da murmushi ganin yadda Abubakar dinta ya tsure taji ta kara sonsa cikin zuciyarta.
Shigowa ango yayi da abokansa cikin gidan aka fara hotuna wasu sun tsaya sun shiga cikin
matan yayln da wasu abokan da girman kai yayi musu yawa sukaja baya cewar mutanen basuyi musu ba wata ma mata tukin tuwo sukeyi suka saki dan ayi hutonan dasu, hatta Sadeeq buya ya dingayi a bayan Abubakar. Shikuwa babu ruwansa duk Matar data matso zai matsa suyi tare za’ayi musu shida INdo yayi kokarin cafko hannunta ta cikin babbar rigarsa, da sauri ta kallesa cikin sa’a akayi musu hotuna sai hakan ya bada style zata yi magana yayi saurin sakin mata yana dariya Sadeeq yazo akayi musu su uku sannan suka tafi sam an hanashi amaryar su kebe har suka kammala komai aka bar motocin da zasu tafi da amarya sukuma su Sadeeq suka wuce. Duk zaman dasu Abubakar sukayi a garin an hanasu ganin amarya sunyi magiyar sunyi duk iya yinsu amma mutanan bikin nan suka hana. Sai bayan la’asar an shirya amarya za’a tafi sannan Abubakar suka tafi yabar abokansa da zasu dakko su duk da yasha wulakanci wai yaja zasu dakko ‘yan kauye a motarsu. INdo na lullube su Inna nayi mata fad’a idanta har’wayau hawayen sunki zuwa sai Innace keyi dan tama kasa tsayawa sosai tayi mata fada sai faman cewa takeyi. “Tabi mijinta tayi zaman aure.” Sune kawai kalaman Inna, haka ma malam Hamza shima abinda yace mata kenan sai kuma nuni dayayi mata da yadda Inna takeyi mai biyayya. ‘Yan uwa duk sunyi mata fada ana kokarin fita da ita saiga malamarsu ta islamiya malam Hansa’u tazo yi mata Allah yasanya alkhairi ta jata daki suka zauna ta Fara mata nasiha.
“Toh Aisha yau dai gashi Allah ya kawo ranar da kika koma karkashin wani ba iyayanki ba, yanzu ya koma shine uwar shine kuma uba shine danginki. Aisha kiyi biyayya yin biyayya ga mijinki shine zaki samu aljanna, karki manta da karatun da ake koya muku duk abinda mijinki yace kiyi toh kiyi indai be sabawa addininki ba, ke ko cewa yayi Aisha ga wuta fad’a karkiji dar kifada din kawai, Aisha kibi aure karki yiwa mijinki rashin kunya k0 gaddama ko kiyi musu dashi yin hakan Allah zaiyi fushi dake fushin Allah kuwa babban hadarine akan kowanne halitta. Allah ya bada zaman lafiya Aisha ya kade muku a cikin auranku ya baku zuri’a masu albarka tashi muje akaiki gidanki mai tarin ni’ima da albarka..”
Sai a lokacin INdo ta fara kuka tsoro ya kuma shigarta har aka shigar da ita jibgegiyar motar abokin Abubakar dayazo daga Abuja. Su uku suka shiga sai driver da friend dinshi a kusa dashi, ana gama cika motocin suka dauki hanya shikenan INdo tabar kauyen Sani saidai tazo da ziyara Allah ya dagata. Gudu suka dingayi kafin wasu awanni sun karasa kofar gidan su ango lokacin duhu yafara yi. Bayan an kaita su Mama sunyi farin cikin shigowarta zuri’arsu sunyi mata nasiha aka sake dinguma aka kai INdo gidan Abubakar masoyinta farin cikinta abin alfaharinta, fuskarta a lullube aka shigar da ita cikin d’akinta. Ita kuwa Fateema saida akayi sallar isha’i sannan aka kaita gidansu Sadeeq itama su Mama sukayi farin cikin shigowarta cikin su sannan aka wuce da ita gidan Sadeeq farin cikinta abin kaunarta, ta riga ta tsara musu yadda zasu gudanar da rayuwar auransu abinku da ‘yar boko wayayya. Masu kawo INdon kauye sai da suka kwana Abubakar yace abarsu sabida dare yayi kuma
duk masu motocin sun tafi wai bazasu koma wannan kauyan ba yadai sha iskancin abokai wanda hakan besa yaji kaunar lNdo ta ragu koda da kwayar zarra ba. Sadeeq suka raka gidansa aka yi musu nasiha shida amaryar sannan Abubakar suna kokarin fita yace ma Fateema dake lullube cikin mayafi”Ke..! Sauran kibawa twinnie dina wahala ko kiyi mai rowa.” Tana jinsa taki cewa komai har suka fita Abubakar ya kalli Sadeeq tare da cewa. “Kai twinnie wallahi kabi yarinyar mutane a hankali, nasanka sarai a mafarki ma kana wuce ka’ida bare kuma yau gaka ga mace mallakinka. Idan ka kirani da safe ba zuwa zanyi ba ah toh…”Hannu Sadeeq ya bashi suka tafa suna dariya kana suka rungumi juna Sadeeq yace.
twinnie har gobefa kai saurayi ne sorry to you wallahi but zaka iya sato Aishan ku koma wani dakin fa.” “Nop karka damu zan hakura harsu tafi ai daga yau ne gobe zan samo musu mota ta maidasu.”
Kamar karsu rabu haka sukeji amma babu yadda zasu yi yana fita ya rufe gidan ya koma ciki. A hankali ya zauna kusa da ita tare da yaye mayafin kanta cikin kunnanta yasanya bakinsa yace.
“Amarya muje kiyi alwala muyi sallah.” A kunyace ta mike ya kama hannunta ya kaita har bedroom dinsa cikin toilet sannan ya fito ya shimfida musu sallaya ya ajiye mata sabon hijjab, tana fitowa shima ya shiga yayi alwalan sannan yazo yajasu sallah suka yi raka’a biya ya dafa kanta yayi mata addu‘a sannan ya kalleta yace. “Nasan akwai yinwa a cikin nan tashi muje na baki kici bana son kwana dayinwa.” Ya fad’a yana shafa mata ciki, Fateema cike dajin kunya ta mike yayi saurin rikota tare da jantajikinsa suka nufl parlor. Kajine gasassu sunsha kayan hadi da lemuka da fresh milk suka zauna yafara bata, a yangance suka gama ci sannan ya wanke hannunsa yajata suka shiga dakinsa. Kayan bacci yasa hannu ya dakko wata shegiyar rigar mata ta bacci ya mika mata yace tasa, ta daga rigar nan ta ganta ‘yar firit Fateema aka dinga raba idanuwa ta kasa tashi tasa yayi murmushi tare da cewa. “Bari nazo na temaka miki.” Ya mike daka bakin gadon tana ganin haka tayi wufta shige toilet yayi murmushi yana lasar lebbansa. Fitowa tayi bayan tasawo sai kuma ta nadejikinta da mayafl kamar tasa lafaya ta kwanta a kunyace, shi kuma yayi musu light of kafin kuce me naji kici-kicin su kila kokarin kwance mata yake yi nidai kasancewar bansan komai game da harkar ba yasa nayi ban kwana dan dakin badai duhu ba yau su Sadeeq za’a angon ce na fita zuwa gurin Abubakar.) …..
Hmm koya zata kaya da indo oho muje zuwa