MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 2

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 2
Bayan an tashi daga makaranta, su Indo ta k’ofar gidan da su Sadeeq suke suka biyo. lek’en su suka din ga yi su dai sunajin hayaniya da guje-gujen yara amma basu kula ba sai can Indo da Maryam Ali suka kuma kutsa kai suka shiga suna lek’a tagar wani d‘aki karaf suka hango Abubakar zaune a bakin katifa yana danna laptop wanda daga shi sai 3quarter da singlet sam beyi tunanin cewar ana lek’an su ba sai da yaji motsin yayi yawa sannan ya d’aga kai yana kallon gurin. Mamaki da al’ajabi yasa shi saurin mik’ewa tsaye su kuma suka zaro mai idanuwa kamar had’in baki su sam basu gane waye aciki ba kasan cewar kamannin iri d‘aya ne. Suna k‘ok’arin guduwa suka ga Sadeeq tsaye a bayan su ya rufe k’ofar gidan yajin gina a jikin ta yana watsa musu wani mugun kallo. can Abubakar ma ya flto fuskar nan a murtuke. “Wayyo Allah dan girman Allah dan annabi Muhammad s.a.w idan kuna kaunar iyayanku kuyi mana hak’uri.” 
Cewar Indo tana faman tafa hannuwa alamun rok’o,itama Maryam tsugunnawa tayi tana magiya, “Dan Allah kuyi hakuri wallahi lndo ce tace muzo mugani ko aljanu ne ku, amma wallahi ni banyi niyar shigowa ba.” “Shhhhhhhhhhhhh..!” 
Abubakar yayi musu bayan ya d’ora yatsan shi d’aya akan Lip’s d’in shi suka had’a idanuwa da Sadeeq suka fara matsowa gurin su yayin da jikin su Indo ya hau rawa kamar an saka musu shock ai kuwa suka fara kurma musu ihu. Kan kace mene har unguwar ta cika da mutane sai bugan gidan ake amma sunk’i bud’ewa, yaran da suka taho tare da su Indo ne suka yiwa sauran mutanen gurin bayani kan cewar ai su Indo ne suka shiga wai sai sun kallesu. wani dattijo ya kuma buga gidan jin su indo na ihu yayi magana da d’an k’arfl yace, 
Ku kuwa bayin Allah dan Allah kuyi hakuri ku bud’e su fito ba dan halin su ba.” 
Sai da Abubakar yasa su kamun kunne wajan mintina goma sannan Sadeeq yaje ya bud’e su indo suka kwasa da gudu suka bar gidan,hatta wad’an da suke mak’otaka dashi Sadeeq d’in sai da suka tambaya waye Sadeeq a cikin su yace… “Gani nan baba Al-hassan.” Wanda aka Kira da Baba alhassan yace, “Ikon Allah toh ai kud’in ne dole ku zama abin kallon jama‘a sabida ba kasafai ake samun samarin matasa maza ‘yan biyu masu matukar kama dajuna ba. koni da Al»husain d’ina kafin ya rasu ana iya gane mu amma ku babu wata alama da zata sa a gane ku dole yara suzo kallan ku.” Murmushi Sadeeq yayi tare da shafa k’eya yayin da Abubakar ya kalle su sai kuma ya juya tare da komawa cikin d’aki yana tausayin d’an uwan shi akan wannan aikin nashi daya zoyi duk babu sa’a, ba‘a makarantar ba ba kuma a garin ba duk babu sauk’i haukan garin yayi yawa. 
Abubakar da Sadeeq ‘yan blyu ne wad’an da ba zaka taba Iya banbance Hassan k0 Husaini ba muddin suna tare sabida tsabar kamannin da suka yi. Hatta taflyar su, dariyar su, yana yin maganar su sai d’abi’un su ne kawai idan ka zauna dasu zaka iya tabbatar da cewar sun ban-banta danajuna. Engineer Alhaji Salmanu Haruna shine mahaifin su, yana da arzik’in shi dai-dai misali Matan shi na aure guda biyu ne Mama A’i itace uwar gida kuma mahaifiyar su Abubakar da Sadeeq sune yaran Alhaji Salmanu na farko sai kannan su da suke uwa d’aya su biyar Hawwa, Halima, Hamza,Amina sai Khalifa sai ta biyun Umma Fatu tana da yara uku Khaleel, Mubasshir da Rukayya. Gabaki d’ayan zuriar sun taso cikin tarbiya da ilimin boko dana addini dan Alhaji Salmanu tsayayyan mai gida ne da yake tsaye akan matan shi da yaran shi. Wannan kenan.. lndo Aisha d’iya ce a wajan Hamza mai gyaran radio da Inna Mero sai kannanta guda uku Sagiru, Shehu sai Nafeesa. Malam Hamza ya dad’e yana gyaran radio dan da sana’ar yayi aure harya hayayyafa duk da suna matukar shan wahala dan wata rana ma basa samun na abinci sai dai su kwanta haka. lndo yarinya ce k’azama ainun domin wanka ma sai juma’a jum’a take yi,shima se an tilastata agaba bayan haka kuma gagarumar fitinanniya ce ga d‘an karan tonan fad’a da shiga fad’an da bana ta ba,tana da son wasa hakan yasa koda aka bud’e musu wata primary aka sanyata bata kwaso komai ba sai k’arin fitina da rashin kunya a haka harta zana jarabawar fita daga primary ta wuce secondary yanzu tana aji d’aya ko sunanta da kyartake iya rubutawa shima a karkace cikin rashin tsari, kuma kusan duk haka ajin yake monita ne kawai mai iya rubata sunan shi complete sannan ya rubuta na wasu suma ba duka ba. Gidan su na k’asa ne d’an k’arami wanda shi da kanshi Malam Hamza shi ya gina abunshi yayi d’akuna uku da makewayi katangar tasu gajeriya ce domin idan kai dogo ne to hak‘ika idan kana tsaye sai an hangoka hakan yasa duk shirgin da suka kwaso suk’e iya cillashi ko su watsa shi ba tare da sanin koda mutum a wajan ba dan ansha fad‘a dasu da mutanen unguwa amma sun kasa denawa har anyi shiru an zuba musu ido. Da gudun tsiya ta shiga gida tana sauke wani uban nishi Inna ta kalleta tare da cewa, 
“Ke kuma laflya kuwa kika shigo gida bako sallama ‘yar nan..?!” Inna ta fad’a kasan cewar bata iya fad’in sunan Indo sabida ‘yar ta ce ta farko kuma sunan surikar ta ne wato mahaiflyar malam Hamza. cire daddauhar hijjab d’in Indo tayi me tashin hamamin wari tare da cillar dashi a tsakiyar gidan su tace, “Wato inna akwai abubuwan kallo idan mutanen cikin birni suka zo nan wai…!”Tah fad’a tana zaro idanuwa, kallonta inna tayi cike da takaici ta rasa gane kan Indo tunda aka kawo malam Sadeeq kullum taje makaranta ta dawo da saban labarin da zata bata 
akan shi dan haka tasan tatsuniyar gizo bata wuce ta kok’i inna tace, “Allah shi kyauta miki ‘yar nan, tunda aka kaiki makarantar nan ban tab’ajin kinzo kina yin karatu ba yadda nima zanji dad’i ba sai dai tunda aka kawo sabon malamin ku toh babu ranar da zakije baki dawo da sabon labari akan shi ba sai kace shi aka ce kije ki koyo..” “Kai inna ana baki kina k’in k’arba.” “Eh ba zan k’arba ba bana so ki rik’e kayan ki.” Indo ta kuma gyara zama tare da bugun kanta da alama kwarkwata ce tayi motsi,cikin son bada labarin tace, 
“Aikuwa inna sai na baki labarin nan dan kuwa wallahi har suma nayi aka samin ruwa na farfad’o.” Jin abinda ta fad’a ne yasa inna zaro ido tana dafe k‘irji tace, “Na shiga uku ni Maryama meya faru dake ‘yar nan?!” A take Indo ta kwashe labari tun daga wanda ta sani har wanda d’alibai ‘yan uwanta suka gaya mata ta k’arashe zan cen da fad’in lokacin da suka shiga gidan su shine fa ana bud’e musu ta shigo gida da gudu. “Ikon Allah kenan, toh ke dai babu ruwanki dasu..ah to karkije wata rana ki basu haushi suyi miki aika-aika su cuceki Allah ya tsare ba fata ba” “Toh inna ai na fisu iya gudu wallahi.” “Yi min shiru wawiya kawai an ce miki wannan muguntar ta gudu ce, ke dai babu ruwanki dasu na gaya miki.” Da haka suka dinga magana inna na son fahimtarda ita sai dai kunya da kawaici yasa ta kasa sai faman kwana-kwana take yi. Ita kuma wadda ake wa dama ba wani fahimta ne da ita ba  dan haka bata fuskanci Inda maganar inna ta dosa ba. “Other half gaskiya ya kamata ka nemi transfer daga wannan gajarabal d‘in makarantar, ah wannan school da kauyan ai sai kaima su maida kai kamar su dan wallahi rayuwa a irin wannan gurin tsab zasu canza ka su saka maka hobby d’inka.” 
Kai twinnie God forbid wallahi sai dai ni na canza musu, ni sam basa yi min haka kawai zuwanka ne yasa dan sun ganmu mu biyu shashanci sai kace akan mu aka fara zuwa duniya mutum biyu iri d’aya…” 
Abubakarya kuma kallon Sadeeq shi tausayin shima yake dan ya san kawai yana zaune a garin ne ba dan yana jin dad’i ba,tabe baki yayi tare da d’aukar laptop d’in shi ya koma cikin bedroom ya k’agara gari ya waye ya bar garin dan jin shi yake yi tamkar akan k’aya. Mik’ewa Sadeeq yayi tare da d’aukar mukullin motar Abbakar d’in, flta yayi ba tare daya sanar mai ba yayi waje. Can cikin gari ya tafi wani restaurant ya shiga inda yake zuwa cin abinci yayi musu order mai rai da lafiya sannan ya siyo musu drink‘s masu sanyi ya dawo gidan lokacin ya tarar da Abbakar d’in ma bacci yake kasan cewar sun kunna inji akwai iskar fanka. kallon shi yayi sannan ya fito ya dawo parlor ya fara rubuta lesson plan har wajan la’asar sannan Abubakar ya farka yana fitowa yagan shi zaune gaban shi duk takardu ne da littattafai kawai ya kalleshi yace, 
“Wai twinnie haryaushe ne ka koma haka? duk ka takurawa kanka ya kamata ka sauya makaranta dan kafi karfin koyar da irin wad’an nan school d’in.” Sadeeq ya numfasa tare da cewa, Meye abin fin k’arf‘i twinnie ? a gani na tunda teaching nake sha’awa ai be kamata nayi korafl ba.” Da sauri Abubakar yace, 
“Ba anan ya dace da kai ba twinnie kamata yayi yanzu ace kana wata university d’in kana bada lecture’s dan kafi can-canta da dacewa acan, amma nan wallahi tsaf zasu nakasa maka ilimin da kakeji dashi ya kamata ka duba magana ta.” Kallonsa yayi harya shige cikin d’aki sannan ya sauke idanun shi, dama tun ba yau ba tun suna k’anana suke da ban-bancin ra‘ayi wajan zab’ar samun gurin aiki sai dai shi Abubakar ya cika burin shi yayin da shi kuma Sadeeq be samu zama pilot ba sai aikin koyarwa a university of sokoto amma yak’i tafiya sai ya tafi ya samu a wani secondary school itama d’in a kauye, sai gashi sam baya jin dad’in ta. Abubakar ne ya dawo ya zauna tare da janyo take away d’aya ya fara cin abincin shi, Sadeeq ya kalle shi tare da ture takardun gaban shi yace, “Twinnie wai ya zancen Ummi kuwa ka kuma komawa kun dai-dai ta ko?!” Abubakar yayi murmushi tare da ajiye spoon d’in hannun shi yace, “Bari kawai twinnie ban koma ba sai aikowa gida da mahaiflnta yayi wai ance angan mu a tsaye toh idan na shirya na fito. kaji fa? ni ai Ummi bata cika quality’s d’in da nake da burin matata ta kasan ce ba dan haka nace a’a ban shirya ba ko ya ka gani?!” 
Dariya Sadeeq yayi sannan yace, 
“Kai ma ka tsaya ruwan ido meye aibun Ummi tsakani da Allah, yarinyar nan fa yanzu 5.5 1 zata shiga kuma gata kyakyawa to meye ya rage maka.?”Gayu, twinnie ka san ina son mace ‘yar gayu mai aji wadda koni idan ina mata magana sai taga dama zata amsa ni amma fa Ummi kana magana kafin kakai k’arshe ta mayar maka, no gaskiya akwai wata dai a cikin hospital din mu da suka zo sanin makamar aiki naga kuma kamar type d’ina ce sai dai ba zan iya mata magana ba karma ta rainani.“ Rai ni kuma Abbakar? toh kenan idan kayi auran ma bashi da amfani tun da dole sai wani abun raini ya shiga tsakanin ka da matar ka..” Kasan kuwa wani sa’in inajintsoron yin aure, sabida wani sa’in sai naga ba shi da amfani.””lkon Allah.” 
Cewar Sadeeq yana yi mai kallon mamaki yayin da Abubakar d’in ya mik’e yayi waje yana son ya samu almajirin da zai wanke musu toilet d’in su. Yana fita ya samu wasu yara zaune suna wasa ya kira wanda suka had’a ido da shi. yana zuwa yaron befl 10 years ba Abubakar ya kalleshi yace. ‘ “Kai whats your name?!” 
Yaron ya kura mai idanuwa kunnuwan shi sai bud’ewa suke dan beji abinda yace ba nan ya fara kwakular hanci har lokacin idanun shi na kan na Abubakar ganin kamar be gane ba yasa shi cewa, “Ya sunan ka?!” Ya washare baki hak’oran nan yalaye kamar yasha d’orawa kafin yace, “Suna na Sagiru Hamza.”  Abubakar ya d’auke kai tare da kallon sauran yara, gaba d’aya kaf cikin su babu na zaba har garama Sagirun dan haka ya kalle shi yace. “Zaka iya wanke mana toilet?!” 
Da sauri Sagiru ya d’aga kai duk kuwa da cewar be gane abinda ake nufl da toilet din ba amma yaji ance wankewa yasan koma me ye zai iya wanke shi tatass. “Toh shiga muje.” Abubakar ya fad’a yana komawa ciki, Sagiru ya juyo tare da yiwa sauran abokan nashi gwalo. “Yauwa Sagir kaga ga klin da hypo shi zaka d’auka ka wanke shi sosai.” Ganin inda ya nuna ne yasa Sagiru tabbatar da cewa ban d’aki ake son ya wanke, Abubakar na gama nuna mai ya koma cikin d’aki shi kuma Sagirya shiga yana wankewa.sai da ya kammala tasss sannan Abubakar ya fito ya bashi naira d’ari biyu ai kuwa ya dinga murna sannan ya tafi gida da gudun sa yana murna tare da burin ramuwar abinda INDO tayi mai lokacin da tana da kud‘in ta naira 50 ta dinga siyan awara tana hana su. 
Sagirya shiga gidan da gudu yana k’iran ta da k’arfi, da gudu ta fito daga ban d’aki hannunta rik’e da buta tana fltowa tayi wurgi da ita tana gyara kullin pant d’inta wanda yayi mata yawa sabida bud’ewar da yayi gashi kamar rai shi kad’ai gareta ta k’arasa kusa da Sagiru tana raba idanuwa. 
“Wai kai dalla meye kake ta kwad’a min kira ne?!” Be yi magana ba sai kud’in daya nuna mata yana tsalle, da sauri ta ware idanuwa cikin tsananin mamaki sannan tace, “Kai Sagiru a ina ka sato ko kuma waye ya baka kud’i har d’ari biyu haka…?!” “Yarinya wankin ban d’aki nayi shine aka bani ita lada.” “Ikon Allah a wane massalaci ne haka?!” Sagir yace, 
“Ba’a matsallaci bane a gidan malamin ku wannan mesa glass d’in nan.” “Tab d’ijam! toh Sagiru nawa zaka bani a ciki?!” Wani banzan kallo yayi mata tayi kallar tausayi tare da cewa. “Dan Allah kabani ko naira hamsin ce kaji kanina wallahi nima wata rana idan na samo zan baka.” “Uhh-umm yarinya ba zan bayar ba.” Cewar Sagir yana danna kud’in a cikin aljihun shi, ganin haka yasa ta cewa, “Toh kuwa yaro dama Inna tana ta neman kud’in da za’a siyo daddawa da kuka sai kazo ka bayar tun da ai kaima da kai za’a ci tuwan.” Ke wallahi ba zan bayar ba, ke rannan ba da naira goma a hannunki ba Inna tace ki kawo a siyo manja da ita ba amma kikak’i sai yanzu dan kud’in ba naki bane ba zaki ce na bayar a siyo kuka toh ba zan ba da ba.” 
Ganin bashi da niyar bata k0 sisi yasa ta fara kwad’awa Inna kira, yanajin haka shi kuma ya zura da gudu yayi waje nan ya barta sai faman masifa take tamkar kud’in nata ne… 
Hmm su INDO manya

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE