MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 22

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 22
Harkasa INdo ta tsugunna tana gaida shi idanta akan fuskarsa tace, “Abba ina wuni?” 
Ya zura wayar cikin aljihunsa yana kallonta ya amsa. “Lafiya lau Aisha tashi kishiga daga ciki.” “Toh adawo lafiya.” Tafada tana mikewa ta nufi cikin gidan, tana shiga sallama tayi tana kiran Haleema kamar yadda takeyi idan suka zo gurin da zasu hadu. Haleema dake zaune a falo tajiyo lNdo na nemanta da sauri ta mike ta shige dakin su dan bata son su hadu a cikin wannan yanayin. Mata tagani a zaune a falo wasu sunzo wasu kuma na shigowa Mama 3 gefe gurin kujera ta takure Umma kuma a bakin kofa INdo ta dinga binsu da kallo kafin ta karasa kusa da Fateeman Sadeeq ta zauna itama ta takure tana gaida su, suka amsa mata a sanyaye. Juyawa tayi tana lekan fuskar Fateema wadda take faman hawaye a dai-dai fuskar tata tace. 
“Kai amaryar malam menene kike kuka? Ko malam Sadeeq ne,dan nasan shi sarai tun a makarantar mu meh yayi miki..?!” Zame jikinta tayi daga na lNdo tajuya tana kallon Mama sai taga itama ta dauke kai Fateema ta rasa yadda zatayi gashi lNdon ta takura mata akan sanjin abinda takewa kuka,mutane dake shigowa ne ya kara sanya lNdo cikin wasi-wasi kuma da sun shigo zasu samu guri su zauna a cigaba da zaman shiru sai kuma kallonta da akeyi. Mama ce tayi karfin halin yin magana tana kallon su fateema tace. 
“Fateema jata kushiga cikin daki mana.” Hakan akayi kuwa suka shiga ciki nan INdo taga Haleema a makure jikin gado sai shashekar kuka takeyi, cikin sauri ta karasa wajanta dayake Allah ya hada jininsu da ita ta janyo ta da sauri cike da damuwa da nuna kulawa tace. “Haleema Hali dubu kyakyawa, me kikema kuka kema?!” Rungumeta Haleema tayi yayin da INdo tayi shiru tana rike da ita, ita lNdo ba komai yake sanyata saurin kuka ba har sai abin yakai makura sannan batada tsoro musamman a fagen magana kafin Haleema tayi magana Mama tashigo dakin Fateema na zaune fuskarta cikin hijjab Mama ta riko lNdo ita kumajinta ajikin Mama yasa tayi murmushi sai taji tamkar 
Abubukar dinne ya rikota. 
A bakin gado ta zaunar da ita can suka jiyo muryar Wata tsohowa makociyar su ta shigo tana fadin. 
“Allahu akubar Garbati ankai sa’i, dazu-dazun nan yana futowa daga gidannan ya leka zaurena muka gaisa yace min zai tafi birnin taraiya, Allah sarki kungani ya bani yaci inci goro Allah yajikanka Garba..” Ta karasa maganar tana nuna musu naira dari biyar d’in daya bata, a cikin daki lNdo ta 
kalli Mama tana zaro ido tace. 
“Mama waye Garba a gidannan da ya mutu?!” Cikin dakiya Mama ta karasa wajan wardrobe tana cewa. “Anan gidan yake Aisha zakiji ko waye.” Farin hijjab ta zaro tare da mikawa lNdo shi tana cewa. “Ciro mayafin Aisha a ajiye shi.” 
Kamar yadda Mama tace haka tayi tasanya hijjab din Mama zumbulele sannan Mama tace ta zauna karta fito. Suna zaune zugum sai ta dakko wayarta numbern sa ta kira cikin sa’a aka dauka cikin zumudinta tace mai. “Salama alaikum my key kaje ko kakusa zuwa..?!” Taji ance “Sorry hajiya me wayar yanzu haka Allah yayi mai rasuwa.” Da mamaki tace “Rasuwa kuma? Toma waikai waye ma tukunna?! Kashewa akayi INdo ta zaro ido tana kallon wayar tare da furta. “Rainin hankali toh ko faduwa wayar tayi wani ya sace shine zaice min haka. Aniyarka ta 
bika mugu Garabo.“ 
Ta fada su kuma Haleema dasu Fateema da wasu da suka shigo dakin suka bita da kallo. Hawwa ce ta shigo tana kuka sosai saida tazo falo ta kuma barkewa da wani kukan tana shasheka tace. 
“Allah sarki Yaya Habu yanzu ya gama min waya Mama kinga kiran da yayi min yace gobe insa aje a dakko min Humairansa… Tazo muyi hira da daddare a maida ita baya son ta zauna it….” 
Ta kasa karasawa sai kuka, INdo ceta fito fululum cikin hijjabjin muryarta ta karasa kusa da Hawwa ai Hawwa na ganinta ta janyota jikinta kukan ya tsananta amma bakin be fasa magana ba. 
“Aunty Humairah kinyi rashi Allah yajikan Yaya Habu yaso kuyi long life a tare sai gashi Allah ya daukesa ya barki….”
Muryar Mama ce ta katsewa Hawwa kukan da takeyi cikin fada tace. Amma dai ban taba sanin bakida hankali ba sai yau Hawwa,  wane irin hauka ne daga shigowarki sai kace ba gidan musulmai kika shigo ba. Toh kin gaya mata kinji dadi Tun zuwanta kowa ya kasa gaya mata saike wawuya kawai…” Da sauri Hawwa ta kalli lNdo sai taga ta kura mata ido fuskarta a murtuke tun daga nan kuma sai bakin mutane ya fara budewa aka fara zance mutuwar kunnuwan lNdo suka dinga jiyo mata ai yana tafiya har ya wuce Kaduna Allah yayi masa rasuwa. 
Sosai hankalin Hawwa ya tashi ganin yadda INdo ta kafeta da ido hakan ya bata tsoro tayi saurin matsawa baya lNdo ta bita cikin tashin hankali Hawwa tace. “Aunty Humairah Lafiya? Please wannan kallon fa..?!” 
A hankali lNdo tasa hannu ta rungume Hawwa cikin rawar murya tace. “Yaya Hawwa kema sokike Yaya Abubakar ya mutu? Yanzu na buga mai waya wani ya dauka yace min me wayar ya mutu ashe kema sokike ya mutu? ‘Dazu ni narakasu mota suka shiga shida malam Sadeeq amma meyasa kike son yayanki ya mutu? Kinga yana sona dayawa dazu fa har cemin yayi yana son duk wani mesona kuma zai sani a makarantar abuja…” “Kiyi hakuri aunty Humairah nima inason Yaya Habu amma Allah yafimu sonshi shi yasa 
yayi hatsari…” Hawwa ta fada tana kuma sakin kuka, da sauri INdo ta hankada Hawwa baya iya karfinta jikake gam..! ta bugu da kujera cikin kukan bakin cikin maganarta yasa INdo cewa. 
Daga yin bikin mu shine zaki mana addu’ar ya mutu sabida bakya sonmu, toh insha Allahu sai Isyaku ya riga dacta mijina mutuwa fatanki ya biki, ance miki Garba ne ya mutu shine zaki zo kice Yaya Abubakar ne dan bak’in ciki…” Umma ce tayi saurin toshewa lNdo baki cikin rufewar ido ta fara tureta domin ta baya ta rikota ta kuma toshe mata. Cikin kwantarda murya Umma kishiyar Maman su Sadeeq take mata magana a hankali. “Kinga Aisha kiyi shiru kinga mutane sun fara cika gidan yi hakuri taho muje ki zauna kinji ‘yar albarka.” 
Tana nishi Umma taja ta still bata dena yiwa Hawwa kallon banza ba duk kuwa da cewar ta girmeta nesa ba kusa ba amma cewar Abubakar dinta ya mutu shine ya darsa wata kazamar kiyayya a zuciyar INdo. Fateema ce ta fito idanunta jawurta kama hannunta suka koma cikin dakin Mama, suna 
zama amma sai mita INdo takeyi Mama ta shigo ta kalleta tare da cewa. “Aisha kidinga hakuri kinji k0?” INdo tace “Toh Mama ki gaya mata bana son wasan mutuwa.” “Toh zan gaya mata tashi muje ki wanke fuskarki da sabulu.” Babu musu ta mike suka shiga bathroom saida ta gama wankewa sannan Mama ta kamo hannunta suka wuce, dakin Abba suka shiga yana zaune yayi shiru yana bude likkafani gefe turare ne a kusa dashi suka shiga bayan Mama tayi sallama. Sake gaisawa suka yi da INdo sannan Abba ya kalleta tsawon lokaci ya kasa cewa komai, can dai ya nisa yace. “Aisha ke musulmace k0?!” 
‘Dan murmushi tayi alamar kunya tana sunkuyar dakai tace, 
“Eh Abba.” 
“Alhamdulillahi ina son sanar dake Abubakar dai Allah ne ya bani shi, nina raineshi tundaga zanin goyo har girmansa da temakon Allah, bayan ya girma ya mallaki hankalinsa shida dan uwansa suka dauke min duk wani nauyi nasu dana kannansu, kafin ya aureki ya nemi auran wata yarinya Allah ya kadarta beyi ba sai dake, toh Allahn daya baki Abubakar 
Aisha ya karbi abinsa domin yanzu haka suna hanya za’a kawo gawarsa ina son ki daur….” 
Bekarasa ba yaji ta fashe da kuka, kusa dashi ta rarrafo tare da riko Hannunsa tana jijigawa tana fadin. “Abba… Abba wallahi ba dacta bane, ba shine ya mutu ba shi yatafi abuja kila dai malam 
Sadeeq ne, dan Allah Abba karku ce haka wallahi yace zai dawo ya tafi dani can garun…” 
Mama Abba ya kalla alamar tazo ta zanye ta, tana zuwa INdo ta juya kanta tare da riko hannunta itama tana cigaba da magana tana basu rabarin abinda yace zai yi mata nan gaba sai kawai itama Maman ta fashe da kuka Abba ya fara mata fada amma ina ta kasa yin shiru bare ta bawa lNdon. “Kutashi kuje yanzu suna hanya zasu kawo shi, karku sake kubarta tafita ko’ina kinajl’na…?” Mama ta kada kai tare dajan hannun lNdo suka shiga gidan sai ihu take mutane na 
kallonta cikin tsananin tausayawa. 
Tana shiga ciki ta zube akasa jikinta sai rawa yakeyi aka rufa a kanta kowa sai nemar mata 
dauki yake ta zame jikinta daga na wata mata tana kallon Matan tace. “Sani zantafi.” Umma ta rikota itada Fateema ta fara tirje musu dama lNdo yaya lafiyar kura, dacta ne yasanta ya kuma san yadda zai biyo mata gashi babushi dan haka abin nata ya kuma yawa. Kullesu akayi a daki babu me fitowa suna jiyo kukanta har aka dawo daga dakko gawar 
Abubakar, dakinsu aka kaishi Sadeeq tamkar wani zararre fuskarsa fal hawaye idanunsa 
sunyi luhu-luhu tamkar kurji ya fito ya shiga cikin gida yana neman Mama. Da kyar ya iya 
tambayarta zani ta mike ta bude dakin, suka shiga. Gaidashi mutanan dakin suke suna mai gaisuwa, yana furta “Alhamdulillah.” INdo tayi zumbar ta mike daga rukon da Zulaihat tayi mata, lokacin Mama ta mika mai zannin ya karva kawai yaji lNdo ta makaleshi katakam tamkar ba rikon mace ba tana kuka tana 
cewa. “Dacta ka dawoko? Nasan dama bazaka barni ba dan Allah da manzansa kace min Malam Sadeeq ne ya mutu ba kaiba, wallahi kaga zanyi kwalliyar da kace irinta dazu, mu koma gidanmu nan kana da makiya ciki harda Abba duk fatan mutuwa suke ma…” “Aisha sakar ni please.” Sadeeq ya fad’a yana banbareta daga jikinsa amma tamkar mutum biyu ne suka rikesa, ya rasa dalilin dayasa takeja masa mugayan alkaba’i tun suna makaranta nanfa su Mama 
suka karasa suna nuna mata bashi bane amma taki sakinsa cewa take. “Duk inda zahi zan bihi wata kila akwai masu bibiyarsa basa sonshi toni ina sonsa.” 
Janta yayi ganin ta makale suka karasa bakin gado ya zauna tare da nunawa Fateema alamar tazo ta zauna kusa dashi. Tana zuwa lNdo ta kare shi alamar karta tabashi Fateema ta toshe baki kuka na shirin kwace mata, haskilowa kawai takeyi tasan da shi ya rasu kila 
da tuni itace a cikin wannan yanayin da lNdo take ciki. Kabeer ne ya shigo ya karbi zanin domin sam INdo taki sakin Sadeeq, Mama kuwa so take ta banbareta domin tasan hankan ba dacewa bane kuma
lNdo tashiga cikin takaba hakan yasa ta fara sanya ta cikin dokokin da musulinci ya tanadarwa ga duk macen da mijinta ya 
rasu… 

😥😥

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE