MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 3

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 3
Da sauri ta fito ta biyo bayan sa amma ko kyallin sa bata hango ba,ta ciza lebanta tare da ficewa daga gidan gaba d‘aya.Gidan su Maryam k’awarta ta wuce tana wak’ar ta da d’an tsallen wasa hankalinta kwance.malam Sadeeq dake k’ofar gida ya bita da kallon takaici ganin yadda tayi fururu ba wanka,sam bata kula dashi ba sai faman wak’a take tana cewa. “Indo Aisha…ta zariya mai d’an kallabi…” 
Har tayi kwana sai tayo baya ganin shi da tayi, shi kuwa yana ganin zata dawo yayi sauri zai koma cikin gida be kai ga k’arasa juya wa ba yaji tace. “Wil dam malam. (Well done sir)..” K’in kallon ta yayi yana danna wayar sa domin service yake nema.Ya gane abinda take son cewa so take ta gaida shi, ko me ya kawo well done a tsayuwar da yayi.dan haka Murya k’asa k’asa ya amsa mata,lndo ta washe mai baki tare da matsawa kusa da shi yayi saurin daka mata tsawa ganin yadda take shige mai.kallon sa tayi cikin mamaki ido waje ta kuma binsa da kallo kafin tace. 
“Malam Sadeeq baka gane ni bane?lndo ce fa ta makarantar gwamnati ta nan unguwar d’an Awaisu. Ka gane ni? Nan tsefawa fa gwamman sakandare sukul.” Tsefawa government secondary school). “Ke! Naji me zan miki ne..?!”Ya fad’a cikin k’ufula domin ta kai shi bango. lta ma share shi tayi da masifartashi da yake mata domin tana son yi mai tambaya wadda take son jin amsar su daga bakin sa dan haka masifar shi ba za ta d’aga mata hankali ba. kusa da k’afar sa ta k’ara sa haushin ta ya kuma zuwar mai wuya, tsoran sa d’aya kar ‘yan kauyan suyi mai muguwar fahimta sai kauce mata yake amma ta kasa ganewa ya kuma had’e rai amma ko ajikin ta tace. “Malam tsakanin ka da Allah gaskiya da gaskiya zaka gaya min, shin ku ‘yan biyu ne, k0 kuwa dai ni kake bawa tsoro sabida ina kwaikwayon ka a aji…?!” Wata uwar harara ya narka mata dan yaga alamar kamar zata kawo mai rai ni shi kuma bezo garin dan su raina shi ba, wato ma k’arya yake mata shine zata zo ta k’ure sa dan tsabar ba ta da kunya. Fuskar sa a murtuke ya kalleta yace, “You’re very stupid.” Tana dariya cikin nishad’i tace, “Sanki u malam Sadeeq, (thank you) wallahi shi yasa kake birge ni sabida ka iya turanci mai kyau da dad’i. Amma dan Allah malam ka d’an fassaramin abinda ka fad’a da hausa he 
nima in rik’e gurin na iya sosai…” “Zaki bar gurin nan ko sai na ballaki… mara kunya fitsararriya kawai..” Ya fad’a cikin d’aure fuska. tayi baya-baya tana kallansa tare da kama habarta tace, “Kai malam! masifa, daga tambaya sai cibi ya zama k’ari shi kuma k’ari ya zama k’ababa. na tafi kuma ba zanje makaranta ba ehe, sai ayi kuli-kulin tara sisi dani..” Ta yi maganar tana taflya da baya da baya har ta shige lungun gidan su Maryam. tsaki yayi 
ya koma cikin gida yayi kudurin sai ya gyarawa ‘yan makarantar zama. kowa tayi wa dan ba taje makaranta ba oho  yara sai rashin kunya basu san komai ba dak’ik’ai zai nuna musu shima bashi da mutunci. Ranar haka ya wuni yana kunci jefI-jefl yakan yi tsaki har dare yayi ko fita baiyiba sabida takaicin Indo da sanya idon ‘yan gari domin fita dubu shiga dubu sai sun kalle shi gashi ya tsani saka ido cikin lamuran sa. 
Washe gari da yaje makaranta lndo bata je ba yaga ashe da gaske take yi, still wata washe garin tayi nan ma babu labarin Indo sai ranarjuma’a yana tsaye wajan black board yana koyarwa kawai yaji ana magana a taga,juyawa yayi sai yaga babu kowa domin da taga alamarzai ganta sai tayi saurin yin k‘asa, dan haka ya cigaba da abinda yake yi. Can ya kuma jiyo kus-kus yayi a hankali ya kalli gurin caraf suka had’a ido da Indo tana cillowa Sa’ade wani abu a leda, dariya ta sakar masa ya k‘arasa bakin tagar yana kallonta. Sanye take cikin house wear hannunta rik’e da faranti an jera kallik‘ak‘au da yajin masau da alama shi ta cillawa Sa’ade ya had’e girar sa tare da cewa. “Zo nan..!” 
Ita yake kallo amma sai tajuya wai ko zata ga wanda yake kira amma sai taga babu kowa sai ita, da mai baki tayi tare da d’an matsawa kad‘an ba sosai ba tace. 
Gani malam.” “Jeki zaga yo ta k‘ofa.” 
Ya fad’a, Indo ta tsuke fuska tare da cewa. 
“Malam ai ba zuwa nayi ba yau d’in ma tallah nake yiwa mak’ociyar mu. Kasan idan na siyar mata mawa zata bani?” 
Yayi mata banza ganin ita yake kallo yasa ta juyawa ta dafe abubuwan cikin farantin ta ruga da gudu dan ba zata yadda :aje ya hana ta ,,,,,,,
Kai ya girgiza tare da komawa ya ci gaba da yin aikinsa kuma a kwanaki biyun alhamdulillahi suna ganewa, tamkar dama Indom ce ke hana su rashin fahimta. Yana gamawa ya fita ya koma ofls haka ya dinga ci gaba da koyar musu har aka kusa fara jarabawa wadda daga ita zasu wucej.s 2 amma Indo bata sake zuwa ba shima har ya manta da ita har ya Saba ma idan yana kiran suna ya samata absent. 
Ana gobe za’a fara jarabawa Indo ta dawo makaranta. washe gari aka fara musu sai da suka yi jarabawa hud’u sannan a ta biyar d‘in zasu yi English language wato subject d’in malam 
sadeeq. Kasan cewar tun da aka tara beje aJIn ba saI yau da za’a yI tashl jarabawar kuma dole sai yabi aji-aji ya kuma yi musu bayani sannan. Tare da Abubakar suka shiga domin lokacin yazo abinsu gwanin ban sha’awa, zasu gaida su Sadeeq ya hana dan karsu yi hayaniya, can k’arshen aji INdo take duk’ufa sai satar amsa take yi cikin littafln Ayuba mati sabida ita bata da ma littafin bare tayi karatu. Tsayawa Sadeeq yayi a gaban allo domin shi bema san ta samu damar zuwa ba ya fara musu bayani. Malamin dake tsare su yana zaune a kujera Abubakar yana tsaye ya hango wata ko d’agowa ba ta yi hakan yasa shi k’arasawa gurin da take ya lek’a yaga meke faruwa sai yaga ta bud’e littafi sai kwafa take yi har ta kusan cika shaf‘ln farko. Taji an fad’a dai-dai kunnan ta. tsoro da razana yasa ta sakin tusa bum ba tare da ta shiryawa hakan ba ‘yan aji suka kwashe da dariya ita kuma ta zaro ido ta fara rantsen rantsen kare kai. 
“Malam wallahi tallahi….” Da sauri ya kifawa bakin na ta mari tayi saurin toshewa da hannun ta. matsawa yayi tare da nuna mata hanya yace. “Fito waje kafln na yayy-yaga ki a gurin nan barauniyar amsa.” “Wallahi mal…” Zata tsaya yi mai gaddama ya yi saurin fin ciko ta tare da tura ta gaban ajin tayi taga-taga zata fad’a kan tebur Allah ya temake ta tayi saurin sanya hannu. Kwal-kwal idanunta suka kawo ruwa zata yi kuka Abubakar ya k’arasa gurin yace. “Shanye shi, idan kika bari hawaye suka fito sai na zane ki barauniyar amsa.” Maida hawayen tayi tana nan tsaye har Sadeeq ya gama yi musu bayani sannan ya kalli Abubakar yace, “Twinnie bar yarinyar nan k0 tayi ba dubawa zan yi ba sabida ta yaye kanta ba zuwa take yi ba tayi degree yanzu sai zuwa tallah.” “Ohhh! No-wonder ashe dak’ik‘iya ce, amma baki yi halin asalin me sunan ba shame on you.. Kawo wannan ta hannun taki da kika sato amsar, ki d’akko sabuwar pepper kizo nan ina jiranki.” 
Taflya tayi tana gunguni tare da murgud’a musu baki, sabuwar takarda ta d’akko tare da biro taje ya nuna mata gaban allo yace. 
Zauna kiyi anan.” Kallon gurin tayi sannan ta turo baki kai da kagani kasan zai yi fitsara tace. “Toh malam ai babu abin d’orawa kuma yagewa takardar zata yi” 
Ba tare da ya kalleta ba dama Sadeeq ya flta yace, “ki d’ora akan cinyar ki kiyi.” “Amma malam ai…” Wata uwar harara daya yi mata ne yasa ta had’iye sauran maganar, zama tayi tana zumbura 
mai baki yace. “ldan kika sake kira na da malam sai na fasa miki baki.” Bata sake kula shi ba ganin yafl malam Sadeeq zafl da saurin kai duka, har kowa ya gama ya amma INdo tana zaune a gurin sai raba ido take yi gashi bata rubuta komai ba sai jagwalgwalo take. Ganin bata da niyar kawowa ne yasa Abubakar k’arasawa wajan tayi saurin cukwaikuye takardar ya mik’a mata hannun alamar ta bashi amma taki, “baza ki kawo ba mara kunya?” Baki ta kuma murgud’a mai aikuwa ya sanya k’afarsa ya doke shi da takalmin sa. INdo ta kurma wani uban ihu tare da fad’uwa k’asa tana ihu tana birgima. Sunkuya wa Abubakaryayi ya d’auki takardar ya sanya cikin sauran tare da bawa invigilator d’in, ko takanta be kuma bi ba sai ma tsallake ta da yayi yabar gurin. Ihu ta kuma saki tana shure-shure har daddaud’an pant dinta ake gani sabida wandon makarantar ya yage d’alibai suka zagaye ta ana bata hakuri da kuma masu yi mata dariya amma bata fasa shure-shuren ba shima malamin yayi taflyar Sa dan yasan INdo sarai hakan yasa be kulata ba. “Allah ya isa ban yafe ba mugaye kawai anyi satar amsar, shi dama ba malamin muba yazo 
yana cin zalin mutane…” “Hahaha INdo me tusa bum…” Uba Aminu ya fad’a yana nuna ta yana dariya, ai kamar jira take yi ta mik’e tare da cakumar sa suka fara fad’a. K’arfi ba d’aya ba shi namiji ya dinga gwarata da allo jikake k’um…k’um amma tak’i sakinsa sabida tsabar jaraba, can akaji Uba ya rushe da wani irin ihu mai had‘e da kuka. “Kai..kai…kai! Lfya meya faru haka.?.|” 
Malam Zubairu daya zo wucewa yaji ihu ya tsaya yana tambaya. “Malam fad’a suke yi.” “Waye da waye?!” “INdo da Uba.” 
Ihu Uba yake yana hawaye gashi ya rik’e gaban sa, malam Zubairu ya kallesu ganin INdo na rik’e kugu yasa shi cewa “ku biyo ni ofls yanzun nan.” Abokan Uba suka kamashi suka kaishi k’ofar staff room, ita kuwa tahowa tayi tana bugun cinya alamar bala’in be k’are ba taje ta tsaya malam Zubairu yakai takaddu ya ajiye sannan ya flto dan jin kanun zance, be fara bawa INdo damar magana ba yace Uba ya fara yi uba amma ya kasa sai shasshek’a yake yi da kuka. “Ke kuma gaya min gaskiyar abinda ya faru.” Dai-dai lokacin Sadeeq da Abubakar suka shigo cikin staff room, tsayawa suka yi Abubakar na waya ta fara baya ni. “Tonona yake yi shine muka fara fad’a.” Sai kuma aka yi yaya..? Sai kace mu biyo ka.” Kai Uba me yasa ka toneta gashi ta saka kuka..?!” “Malam cizo na tayi a anan.” Ya fad’a yana nuna gurin, duk wad’anda ke gurin suka zaro ido Abubakar dake waya ya zare ta daga kunnansa yana kallon lNdo cikin tsananin mamaki yace. 
“Ke mayya ce? Baki da hankali?ke wace irin yarinya ce ne da kika fitini kowa ne? 
Stupid,nonsense, what a fool wawuya kawai, mai wasa da maza karya..” 
Haushin maganar sa da kuma turancin da yake yi bata jinsa yasa ta fara murgud’a baki tana motsa labbanta alamar magana take yi, da sauri Abubakar yayi kanta zai hambare ta Sadeeq ya rik’osa yana kad‘a masa kai alamar karyayi yayin da zuciyar Abubakar d’in ke tafasa yanajin wani tururi cikin ransa dan yaki jinin rashin kunya da k’in gaskiya. A hankali Sadeeq ya dafa kirjinsa yana kallon INdo wadda ta makure jikin karfe tana jiran jin saukar duka yace… 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE