MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 35

MUSAYAR ZUCIYA 
CHAPTER 35
Shirin zuwa Sumaila kauyen sani suke farin ciki ya cika zuciyar INdo harta kasa boyewa, kallonta yayi bayan ta rufo dakinta ta juyo gashi cikinta ya fito yace. 
“Cutie koma daki gaskiya mun fasa zuwa.” 
Kirjin INdo ya shiga bugawa hankalinta duk yayi mugun tashi ta kallesa dan san tabbatar da maganarsa. Gani tayi yana dariya hakan yasa ta yin kansa zata dokesa yayi saurin guduwa cikin shagwabar da ta farayi wadda yanzu take neman zame mata jiki tace. 
“Ka tayar min da hankali Allah ya dawo damu lafiya sai na rama.” 
Fitowa suka yi suka shiga mota Sadeeq ya dauki hanya, wannan karan cikin hira suke kai daka gansu kasan masoyane sabanin lokacin da akace ya kaita garinsu ya dinga kumbura tamkar wanda aka sanyawa yeast. Cikin kwanciyar hankali suka shiga garin sumaila, suna zuwa kan kwanar da zasu shiga kauyen sani sadeeq ya kalleta yana murmushi yace. 
“Cutie ga barkono da gyada bazaki siya bane?!” 
Juyawa tayi tana kallon gurin kafin tace. “Eh wallahi kuwa, dan Allah kaje ka siyo min kwano daya-daya.” “Ke wasa nake miki ni.”
Ya fada yana tafiya, kallonsa tayi shima ya kalleta tare da daga mata girarsa. Hannunsa yasa ya janyo nata yana matsawa ta lumshe idanuwa tana shafar cikinta da dayan hannunta. 
A kofar gidan su yayi parking, gidan yana nan yadda yake tun lokacin da Abubakar ya gyara musu katangar su ya maida ita ta bulo sabanin da datake na kasa. INdo ta kallesa tare da Kama hannunsa tace. 
“Wait for me, naje na sanar ma Inna zaka shigo ku gaisa.” 
“Hmm lalle wariyar launin fata, meyasa ni bazan shiga direct ba sai an wani yi min iso? Ban yadda ba tare zamu shiga kema ai idan mukaje gidan Mama wani sa’inma kina rigani shiga.” 
“Hehehehe lallaima, toh ai ni macece zan iya shiga direct, kaifa sabida su Mubasheer na zuwa su shiga kai tsaye kasa duk muke kulle gidajen sai an buga munji ko waye sannan mu bud’e.” 
“Toh aini har yanzu saurayi ne, su kuma su Inna sun tsufa toh meye a ciki.” 
“Kai My super glue, wallahi Innata ba tsohowa bace rayuwa ce kawai ta maida su haka amma ka bari na kammala karatuna sannan cinikin zobo ya kankama zaka sha mamakin Inna da baba wallahi. Kuma kasan dai ai abban ku dasu Mama sun girme su lnnata.” 
“Kaiii cutie..?!” “Yanzu dai bazaka barni in shiga ba.“ 
Tayi maganar tana turo baki,janta yayi kasan cewar tinted glass ne yasa ba’a ganinsu. Sadeeq ya shafo cikinta tare da cewa. 
“Yau dai ina zata ga kokarina, but dan Allah cutie karki bari ta ankara harsai nazo mun 
gaisa na fito, wallahi kuma sai naji inajin kunya.” 
“Kunya kuma? Hahahah tab ai aikin gama ya riga ya gama, yanzu wannan abun taya yaya za’aiyi ya boyu? Dama hijabi ne ko duguwar riga shine zan iya danyin dabara amma ai yanzu kuwa ka makaro hakan nan zan shiga Inna ta gani kuma ka shiga ku gaisa da ita.” 
Sadeeq ya turo bakinsa tare da dafe kuncinsa yana kallonta yace. “Toh ya zanyi? Dole na shigo tunda an banike.” . 
Tana dariya ta bude k’ofar yaran unguwar da suka zo gurin suka dinga kallon lNdo wasu na cewa itace wasu kuma suna cewa ai kanwar Inna ce dan ga kama nan. Gidan ta shige tana dariya jin abinda suke fada, tana zuwa tsab ta ajiye cewa itace ‘yar fari ta danne Inna dake sharce gurin da tayi wanke-wanke. 
“Oh ni Maryamu waike yaushe ne zaki san kin girma ‘yar nan.?!” 
Inna ta fada tana janye jikinta daga na INdo. Dariya kawai ita kuma takeyi tare da kallon Innar tana cewa. “Kai Inna Oyo-yo fa mukayi, nayi missing dinku wallahi Inna dake da baba tunda aka kaini bakujeba sai su dan rainin hankalinnan Sagiru…” 
“Ga INdo… Ga INdo, yeeeeee sannunku da zuwa.” 
Nafeesah ta fada tana rungume lNdo, murmushi tayi cikin nuna wayewa da kuma zaman birni tare da nuna zaman teburin class ta kamo hannunta tace. 
“Su Feenah ‘yan mata daga ina haka..?!” Ta fad’a tanajan hannunta suka nufi cikin d’akin Inna. 
“Kinga Feenah dauki tabarmar baba ki shimda anan sabida Malam Sadeeq zai shigo su gaisa da Inna.” 
Sabuwar tabarmar malam Hamza aka shimfida sannan INdo ta ciro dari biyarta bawa Nafeesah cikin kasa kasa da murya tace. 
“Mazaki siyo min lemon roba da ruwa zanba shi yasha.” 
Karbar kudin Nafeesah tayi sannan ta fita da saurinta, sai da ta kuma tsayawa wajan 
Sadeeq yana tsokanarta kafin ta wuce zuwa shagon da zata iya samowa mijin yayar tata 
lemo da ruwan jarka. “Sannun ku da zuwa, ke daya kika zo k0 hardashi me gidan naki?!” 
“Inna tare muke dashi zai shigo ku gaisa ma, wai ina baba?!” 
“Malam yana can gurin sana’arsa, bari wani ya shigo sai yaje ya kirasa ku gaisa.” 
lNdo dake bakin gadon Inna na karfe tace “toh.”. ‘Dan kuma gyara dakin tayi sannan ta share shi ta ciro turare a handbag dinta ta fesawa dakin da kan tabarmar da Sadeeq zai sauna sannan tace. 
“Inna bari nace ya shigo ko? Karya ga an barshi a mota shi daya.” 
“Toh kice ya shigo barina saka mayafi na nima.” 
Fita tayi suka yi karo da kawarta Uwani da Sahura da alama sunji labarin zuwanta. “Ahhhh kaga su hajiya INdo amaryar Malam Sadeeq oh harda su abinga.” 
Sahura ta fada tana daga mayafin jikin lNdo, kaf dinsu sunyi wani bululumu dasu Uwani ma harda tsohon ciki kai idan ka gansu bazaka ce kawayanta bane sabida tsabar yadda kalar wayewar ta bambanta. 
“Kai sahura kina nan da gulmarki, ku shiga ciki ina zuwa.” ‘ 
Ta fada tare da dukan bayan Uwani ganin yadda ta rik’e habarta tana kallonta. Cikin gidan suka shiga ita kuma ta shiga motar Sadeeq wanda ke jingine jikin kujera ya sanya hularsa a fuska yana kuma zagaye kwantaccen quarter million din fuskarsa. 
Jin an bude kofar motar ne yasa shi cire hularsa ya kalleta, zama tayi tana kallonsa da 
murmushi a fuskarta yace “Uhmmm wato anzo gida harma kin manta tare muka zo k0?” Hannunsa ta kamo cikin nata cikin kalar jimami tace
“Ni na isa, tunda na shiga mafa koda Inna bamu gaisa ba kuma babu kowa duk basa nan amma ni banajin zan iya mantaka a yanzu domin ka zama ni na zama kai kadena sawa ranka cewar duk inda zan shiga wai Zan manta dakai no, idan nayi haka toh Zan iya 
mantawa da kaina nima.” 
Sadeeq ya lumshe idanuwa tare da jan hannunta murya a shake cikin wani irin salo yace. 
“Kina nufin kenan munyi ‘MUSAYAR ZUCIYA’ dani dake a yanzu? Ba kamarda ba yadda kike nuna min cewar zuciyarki ta twinnie ce shi kadai yanzu zaki iya mallaka min ita…?!” 
“Sosai ma kuwa na baka ita ina fatan ka riketa amana. Anan aka daura mana aure dan 
haka anan na kuma baka amanar kaina da duk abinda ya shafeni.” 
“Na karba cutie Allah kuma ya bani ikon rikewa gam-gam, a baya ma ’lllar Zuciya’ ce tasa nake ganin kamar anyi min ba dai-dai ba amma a yanzu…” 
Yakai bakinsa kan hannunta ya sumbace shi yana kashe mata idanuwa tayi saurin kawar da kai tana dariya. Nafeesa ta hango hakan yasa INdo fitowa da sauri. Amsar aikenta tayi ta shiga ciki Nafeesah kuma ta tsaya a gurinsa suka dinga hira har su Shehu suka dawo suma suka gaida shi. Cikin gida kuma INdo ta gama jerawa Sadeeq abin tarba dan inna ta gama dafa wake da shinkafa Allah sarki harda yanka mai lawashin albasa kuma duk INdo bata hana ba domin ta haka ne zata iya kuma tabbatarda kaunarda yake cewa yana mata dan marigayi baya kyan-kyamin duk abinda zata bashi bare yanzu tasan kanta tasan me takeyi ta kuma san waye mijinta. “Lallai INdo wai duk malam Sadeeq din kikewa wannan tanadin?!” 
Uwani ta tambaya tana tabe baki, gani take kamar INdo ta zurma da yawa duk miji akewa wannan hidimar. 
“Toh Uwani bakin ciki kikeyi ko me? Ina zan samu kifi kuma dan yana son wake da shinkafa da kifi ko dafaffen kwai.” 
“Tab lallai INdo Hamza, toh kila dai yana baki kema ba irin muba da sai dai komai kayiwa 
kanka.” “Kwaji dashi gulmammu, Inna bari naje nace ya shigo.” 
Tana fada ta kuma fita tace ya shigo. Jerawa suka yi shida Nafeesah yana kallon INdo daga baya. Gaskiya ikon Allah baya karewa a duniya ko kana menene sai ya nuna ikonsa akanka yau shine da INdo harda kunshin cikinsa a jikinta “Allah astagfurullah.” 
Ya fada cikin ransa tare da shiga gidan yana sallama, su Sahura da Uwani suka amsa bakinsu a washe yayin da Inna ke tsaye kanta a kasa sam bata iya kallonsu tun zamanin Abubakar. Cikin daki Nafeesah ta shigar dashi ya zauna yana sosa keya yana shafa wuya. 
Daga bakin kofa Inna ta tsugunna suka gaisa da Sadeeq sannan su Uwani ma suka sake gaidashi duk da cewar sun gaidashi a cikin mota INdo ta kallesu tare da makewa Sahura hannu ganin yadda take leken sadeeq tana wangale baki. “Ke dallah can malama kina da miji kina kallon mijin wasu haba.” “Kai INdo bana san herri.” 
Tashi Inna tayi ta shiga rumfar malam Hamza bayan ta tura Nafeesah tace ta kirasa. Kallonsu tayi tace. 
“Zan shiga daga ciki, karku ce na barku anan.” 
“Lallai ma INdo toh ba abinci zaici ba? Toh ki zauna muyi shira mana kafin ya gama.” 
Uwani ta fada tana hararta cikin jin haushin yadda take wani nan-nan da malam Sadeeq 
sai kace su basuda mijin. “Toh kuje ku gama muna nan hajiya INdo.” “Toh hajiya Sahura.” 
Itama ta fada tare da shiga cikin dakin. Kallonta yayi ta zauna kusa dashi tare da dakko Coca-Cola ta bude mai cikin halin damuwa tace. 
“Kayi hakuri kasha a haka da bakin jarkar, nan gidan bamu da kofuna kaji my super glue ka daure.” “lNdo Aisha ta zaria medan kallabi..!” 
Ya fada tare da matsawa kusa da ita. Lekawa yayi kofa aikuwa karaf suka hada ido dasu Sahura da Uwani suna lekowa yayi dariya tare da Kai bakinsa saitin kunnen INdo yace. 
“Gaskiya daliban nan nawa gulmammu ne, sai leken mu suke kamar a gidan zoo.” 
Itama dariya tayi cikin hillata da shagalta yaci wake da shinkafar nan dan sai da suka cinye ta cikin kwanon silbarda Inna ta kawo musu. Suma su Sahura da suka kasa suka tsare aka zuba musu sukaci lokacin malam Hamza ya shigo fuskarsa kunshe da fara’a Sadeeq yayi saurin tura kwanon gaban INdo da ragowar lemonsa da ledar yajin ya matse sai wani danne dannen waya yake shi a dole beci da yawa ba. 
INdo kuwa banda dariya babu abinda takeyi mai amma still ya matse su Uwani na jiyo ta sai mamakin abinda yasa ta dariyar suke yi. “Sadeequ ashe kunzo? Sannunku da zuwa. Ah kaga uwata an zama manya.” 
Sadeeq ya fara motsi yana gyarawa malam Hamza guri dan ya shigo. Gaida shi suka yi sannan yayi ta sanyawa Sadeeq da marigayi albarka ganin yadda INdo ta canza tamkar ba ‘yarsu ba. 
Tare da malam Hamza Sadeeq suka fita ita kuma lNdo ta koma tsakar gida gurin su sahura Inna ma taje ta zauna. Suna zaune Rukayya ta shigo murna ba’a magana sabida ganin INdo da ciki, nan fa suka shiga hira baji ba gani amma duk da haka zuciyar INdo bata manta da Sadeeq a mota ba. Nafeesah ya dauka suka shiga cikin garin har sai bayan sallan la‘asar 
sannan ya dawo dansu tafi. 
“Gaskiya Inna zan baki kudi a hannunki a samu dan Allah a gyara bandakin nan, habba wallahi za’a iya daukar larura tunda aka haifeni a haka yake. Ga dubu sha biyar nan ita kadaice a hannuna nasan kila malam Sadeeq zai bawa baba ma wasu amma idan be bayar bama dan Allah Inna a fara da wannan kudin ko buhu d’aya ne na siminti a siyo a malale kasan bandakin can kosu Sagiru ne da Shehu sai suyi ai sun iya.” 
Kwallah Inna ta share tare da yin godiya sam bata taba tsammanin akwai ranarda ‘ya’yanta zasu yi mata wani abunba ganin itama ba tayi wa nata komai sabida rashi gashi ance sai kanayi za’ayi maka. 
“Inna ya kike kuka? Karki bari na tafi haka dan bazan yafewa kaina ba bayan na barki cikin kuka
Murmushi Inna tayi tare da cewa. 
“Allah nakewa godiya ‘yar nan domin ban taba zata zanga irin wannan ranar ba musamman akanki, sai gashi Allah ya shirya minke ya kuma azurtaki gashi har kina tallafa mana da abinda kike dashi, Allah yayi muku albarka dukanku.” 
“Amin Inna ta, karki damu dana gama karatu na kware insha Allah zanyi kudi duk gidan 
nan sai an gyarasa.” “Toh Allah ya yassare miki.” ‘ 
“Feenah dan Allah idan ya koma kwara state zan cewa Sagiru ya kawoki mu zauna tare ko bakya so?!” 
“Ke! Ina so mana ai wallahi kin more gidan miji INdo.” 
Mtwww “Ban hanaki cemin INdo ba gatsal? Ki kirani yayya Aisha ko Yaya INdo karki sake cemin wani INdo mara kunya.” 
Kallonta Nafeesa tayi tana tabe baki kafin ta kada kai tabar dakin. Har zaure Inna ta raka ta tana yi musu fatan alkhairi bayan Sadeeq yazo sunyi sallama. Dubu daya ta karba gurin Sadeeq ta bawa su Sahura su raba d’ari biyar-biyar suka dinga godiya suna karajinjina arzikin da INdo ta samu sannan ta shiga mota suka tafi cike da farin ciki. 
Kwanaki biyar yayi bayan sunje kauyan Sani sannan suka daga suka tafi kwara state da Fateema bayan yayi yayi da lNdo ta bishi taki sabida karatunta. Yana taflya da kwana biyu tasa Sagiru ya kawo Nafeesa duk ranar school d’inta zasu je tare ta zauna a barandar ajinsu INdo idan sun tashi su koma gida ta koya mata abinda ta iya itama hakan ya kara bud’e brain d’inta ga cikinta yana ta girma cikin kwanciyar hankali. 
Duk wata Sadeeq suke dawowa kuma INdo bata nuna damuwarta duk da bata son tafiyarsa amma bata son nuna mai dan karya kansile mata karatunta, gashi dama ya sanyata a makarantar dare ta islamiya ta matan aure anan unguwarsu hakan yasa ta kuma zama busy tana kuma wayewa ta fannoni da yawa a cikin rayuwarta. 
Cikinta har ya shiga 10months bata haihu ba sai dai yayi girma har bata iya zuwa ko‘ina. Ranarwata laraba cikin dare ta farka lokacin Sadeeq na makale da ita duk da girman cikin 
jikinta hakan baya hanashi nanikarta. Kallonsa tayi tana faman rintsa ido cnkin wani irin 
mugun riko yaji ta rike mai hannu hakan yasa shi saurin farkawa. 
“Cutie what happen?” Shiru sai cizon lips d’inta takeyi tana matse idanuwa ya mik’e tsaye ya sakko yace. 
“Cutie kodai haihuwa ce? Bari nazo muje asibiti.” 
A gigice ya sanya jallabiya ya zari mukulli yayi parking lot. Motar ya fitar da ita shiru garin babu kowa ya kuma komawa gidan da kyar ya kimtsata ya fito da ita mota lokacin makocinsa ya leko sabida yaji karar mota. Ganin halin da ake ciki ne yasa shi taso matarsa ta bisu zuwa asibitin. 
Duk ya rude ya bugawa Fateema ya gaya mata itama hankalinta ya tashi gashi babu abin hawa bare tabisu gata mace. Ganin abun yayi yawa ne yasa suka kira Sadeeq din ciki INdo tana ta kuka ya rike hannunta zuciyarsa na bugawa da karfi da karfi tace
“Dama a makaranta malama tace idan mace zata haihu kafarta daya a duniya daya kuma a kabari. Malam Sadeeq kayi hakuri nasan nima yau dacta zan…” 
Sadeeq yayi saurin rufe mata baki yana kada kai, da karfi ta fide kanta tajuyar da kai tana ci gaba da magana. 
“Sai na fada din ka bari in gaya maka mana, dacta zanbi nima yau amma dan Allah tunda ance namiji zan haifa dan Allah koda na tafi malam Sadeeq ka sawa dan suna Abubakar Sadeeq kar kuma a Sauya mai suna dan Allah.” 
Jikin sadeeq ya dinga rawa gumi gaba daya ya gama jikasa, tana gama yin magana kawai nurse din dake gurin tasa hannun zureren jariri ya santalo kan hannun nurse din lNdo na kwance tayi shiru yayin da Sadeeq ya bude baki yana kallon fuskarta gumi na diga akan hannunta na jikin fuskarsa…. 
Hmm 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE