MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 39 THEND

MUSAYAR ZUCIYA 





CHAPTER 39 THEND





Tun a cikin mota suke yin fada kasa kasa yadda ba kowa ne zai gane ba bare aji. lNdo mita kawai take masa sabida tsabar ta gaji da zama bata taba yin tafiya irin me nisan haka ba gashi tun a cikin motarta fara ganin ban-bancin kano da inda za suje domin duk cikin motar yare ne basufi su shida bane hausawa kuma suma ba wai zaune suke a guri daya ba kowa yana kan kujerarsa. Wani yare dake kusa dasu yana ta kallon Ayman ya zuro hannunsa yana shafar kanshi tare da tambayar INdo ya sunan dan cikin yarbanci kirjin lNdo ya dinga bugawajin bata gane abinda yake nufi ba, sai kallon mutumin take shi kuma yana faman kuma tambayarta. Kallon Sadeeq tayi kawai taga yayi tamkar baya jinsu yana karanta jarida tasa hannu ta zunguro shi ya kalleta sannan ta kawar da kai tare da cewa. “Ana maka magana fah.” Kallonta yayi yana kumshe da dariyar sa kafin ya kalli bayeraben sai taji ya gaya masa sunan Ayman bayeraben ya jinjina kai bakinsa a washe ya cewa Sadeeq yaron yana da kyau Sadeeq yayi dariya duk babu abinda INdo taji a cikin maganar gashi sai dariya bayeranen yake hakan ya sake kona mata rai domin abinda take gudu ne yake shirin faruwa wato a dinga magana bata san me ake cewa ba. Sun tsaya anyi sallah anci abinci an rage mara sannan suka kuma daukar hanya ran INdo ba karamin baci yayi ba har suka karasa garin cikin tsakiyar dare. Duk da tayi bacci a mota ammaji take tamkar bata taba yin bacci a rayuwarta ba, ko wanka bata yi ba dakyar ya samu tayi sallan magrib da isha’i tabi lafiyar gado. 
Da kyar Sadeeq ya samu ta farka karfe takwas tayi sallah dan tunda ta kwanta ba tayi juyi ba, ko kukan Ayman bataji sai dai shi ya farka ya ciro bra ya bashi yasha.. idan ya saki kuma sai ya mayar mata sam bata sani ba sai da tazo suna gaisawa yake bata labari suka dinga dariya. Fita Sadeeq yayi ita kuma ta shiga taga yadda gidan yake bayan ta goya Ayman. Bejima ba ya dawo hannunsa rike da leda yaje kitchen ya juye musu abincin daya siyo musu suka tafi falo. 
“Wannan kuma bakin abun menene haka.” “Amala ce da miyar ayayo da dadi kuma cutie ci kiji.” 
Zama tayi suka faraci tana sawa abaki ta dinga yatsina fuska daga karshe ta matsa ta hadiye ta cikin bakinta da kyar. Sadeeq ya kalleta cikin mamaki yace. 
“Cutie ya haka? Ba kya ci ne?” “Gaskiya bana ci wallahi wannan abu a sams min wani.” 
Shimaji yayi sam ba zai iya ci ba duk kuwa da son amala da yake yi. Kallonsa tayi tana goge hannu cikin shagwaɓe fuska tace. 
“Kuma ni yunwa nakeji wallahi kamar inci babu, ko cinyeka nayi ji nake bazan koshi bama gashi da Ayman ya farka zaice zai sha kuma babu komai a ciki wallahi dukya tsetse.” 
“Kai cutie wai ba komai a ciki, toh duk meye wannan abun a ciki?!” Yayi magana yana kallonta da mamaki, ta kuma narkewa cikin nuna jin yunwa sosai tace. 
“Shikenan tunda baka yadda ba,zoka tsotsa kaji idsn akwai murmushi kawai yayi ni dai ka samo min abinci.” 
Tashi yayi da sauri tun yanzu yaga ban-banci tsakanin su da Fateema domin duk abinda ya siyo ko bata taba ciba toh zata ci amma ita common amala tace wai ba dadi. Tunani ya dinga yi yana neman abinda zai siyo mata gasu da shegen tsadar abubuwa daya rasa yadda zai yi kawai sai yaje gurin wata kawarsa cinyere da take dafamai abu idan bezo da Fateema ba yasa ta dafa mai indomie da ruwan tea ya kai ma INdo, harda su murmushi tayi mai sabida ganin abinda zata iya ci. Kadan yaci kasan cewar bata damesa ba ita kuwa taci sosai kad’an ta bari tasha tea sannan walwalarta ta dawo taje kuma ta dinga narke mai tana takura mai. 
Satinsu d’aya da zuwa garin babu inda lNdo take zuwa ko leke batayi , aranar kuma ya fara fita gurin aikinsa yana tafiya ita kuma tana gyaran gidan sai ga wasu ‘yan mata kowacce da ‘yar bingilar riga da mini skirt suka shigo. 
Madam excuse us,can we come in please?” 
lNdo ta bisu da kallo ita kuwa me ya hada ta da arna da har suke neman shigo mata gida? Ganin tayi shiru ne yasa daya daga cikin su tace. “We are friends of your husband,can you let us in..Mrs sadeeq?!” “Me..? For what‘ reason??” “Don’t get us wrong Mrs sadeeq,we are friends of sadeeq ,we just came by to see his newly born baby” 
Shi kuma ya rasa da suwa zai yi kawance sai da mata dan rainin hankali, toh baxata bada 
dan su ganshi ba bama su da kunya basu santa ba kawai zasu wani zo kilama karya suke salon su sace mata dah ne. 
“Madam please…” “Eyyah am sorry he is sleeping.” 
Ta fada tana dari-dari kar su gano cewar ‘yar koyo ce a cikin yaren turancin. Suka ce zasu dawo anjima ko gobe, suna fita ta kulle gidan bata bude ba sai da ya dawo ya buga mata waya taje ta bud’e. 
“Ya aka yine cutie wallahi yanzu kin fiye rigima kamar ma karuwa take yi. Sam kamar baki haihuba yanzu kuma meye ya faru ko yaro nane ya tasoki ne..?!” 
Yana rike da hannunta suka shiga falon ta kuma hade rai ya juyo da ita suna kallon juna yace. 
“Gaya min menene k0 kina nufln dadewa nayi ban dawo ba?!“ 
Zaunar dashi tayi taje ta kawo masa ruwa yasha kad’an sabida baya tare da kishi dan kartayi zargin wani abun ne yasa shi yasha. Zama tayi Ayman na kan kujera yana bacci ta kwantar da kanta a cinyarsa yana jan hancinta tace. 
“Bayan ka fitane wasu mata arnaye gunduma-gunduma suka shigo su hudu ko wacce da wani banzan skirt, wai dan son maidani wata sakarai suke ce min sunzo ganin Ayman ne wai ka gaya musu kanada d’ah.” 
“Ohh su Juliet ne da blessing sauran ne dai ban gane k0 suwaye ba. Toh kin basu sun ganshi k0?” 
“Kut in basu kuma..?! Wai kaima ka dauka har yanzu bani da hankali ne? Kawai ban san suba baka yi min bayanin su ba zan d’auki dana na basu, lallai da hankalina wallahi yanzu ba dah bane.” 
Kallonta yake shi yanzu baya ganin wani aibunta komai tayi sai yaji zuciyarsa ta aminta da abun koda kuwa yana son yi mata gyara. Hannunta ya riko ya sumbata sannan ya fara shafar fuskarta yace. 
“Cutie su Juliet makotan mune wannan benan na jikin mu shine gidan su, please ki bari kuyi mutunci musulunci be hana ba suna da kirki basuda matsala suna ganin girmani sosai.” 
“Lallai in rasa da wadan da zanyi kawance sai da arna wallahi ba ruwa na bazan yi ba sam. 
Shafa kanta yayi lallai ashe akwai gwarmai domin idan yazo da Fateema suna zuwa kuma bata kyarar su hakan yasa suka saba ita kuma ko me ta d’auki Christians oho mata. Share zancen yayi ya dagata tare da janta suka shiga kitchen dan yaga alamar har lokacin haushin bakin basu barta ba. 
“Cutien Sadeeq da Ayman a dafa min wannan abun.” 
Yafada yana ciro wani magani a cikin aljihunsa, tana tsaye tasa shi ya dakko tukunya tace ya tari ruwa a sink ta kunna gas ya zuba maganin yana dariya k’asa-k’asa dan dama yasan lNdon sa tun a tsefawa ‘yar rigima ce dan haka yanzu in tayi abin bazai damesa ba
sosai kuma tafishi gaskiya tunda bata sansu ba tayi hankali da ta hanasu dan za‘a iya zuwa a damfareta hakan kuma da tayi ta nuna mai ba da kowa zata dinga yadda ba kamar yadda wasu suke ganin hakan cinyewa ne sai kuma an cucesu suzo suna kuka. Harya dahu suna kitchen d’in tana tabara. 
“Muje falo naga wasu littattafan turanci, tunda maganin ya dahu kafin ya huce na karanta maka kaji.” 
Hannunsa ta farajah yayi saurin rikota tare da girgiza mata kai ta hade rai. Maganin ya dauka ya kai bathroom ya juye cikin bahon wankan Ayman sannan ya mayar da tukunyar kitchen ya kalleta ta zauna kan kujera sai cuno baki take yi ya zauna kusa da ita yana riko hannunta murya a sark’e yana narke mata idanuwa yace. 
“Cutie rigima, zo muje ai naki ne shiga ciki zaki yi.“ 
lNdo ta zaro idanuwa fuskana a d’aure tana mai wani irin bahagwan kallo, ganin yadda take kallansa a hagunce yasa shi shafar fuskarta yace. “Whats wrong?” 
“Shin bakajin nutsuwa dani ne k0 kuwa dai wani abun kakeji a tattare dani? K0 kuma me kake nufi malam Sadeeq da zaka kawon abu wai in shiga ciki…?!” 
Hannu yasa ya rike kansa tare da rintsa ido jin yadda ta mayar mai da abunsa. ‘Dagowa yayi idanunsa jawur sabida yadda ransa ya sosu dajin abinda tace ba tare da yayi magana ba ya d’auki phone ya kira Fateema bayan ya hadiye bacin ransa. 
“Hello baby na ya aiki? Yasu my sweet Ayman?!” “Lafoya lau baby ya skull kin dawo k0?” 
INdo ta mike zata bar gurin yayi saurin rikota ta fara kokarin kwatar kanta dan wani haushinsa takeji. Ji tayi ya cigaba da yin wayarsa hankali kwance kafin taji yace. 
“Ammm baby ko kina son na taho miki da wannan ganyen maganin naga wannan zuwan ma na kawo shi kina so?!” 
“Woww babyna ina so mana dan Allah kaje ka siyo karya kare please my awesome husband.” 
“Okey tom zan kawo miki insha Allahu bye zan kiraki anjima.” “Thank you baby a gaida min da Ayman my son.” “Insha Allahu.” 
Kashewa yayi yana kallon INdo wadda still fuskarta a had’e take. Janyo ta yayi ta fad’o jikinsa tana turesa ya matseta tare da zura kansa saitin wuyanta yace. 
“Banyi tunanin cewar akwai abinda zan saki kiyi amma ki tsaya tuhumata ba, Aisha ko wuta na rura nace kishiga hakan ya nuna min bazaki shiga ba sabida bakya sona da kina sona duk abinda zan ce kiyi bazaki tsaya wani tunani ko gaddama ba sai gashi kinyi na gani shi kenan na gode Allah yaso ina da wadda ta yadda dani
lNdo najin haka ta saka kuka shi kuma ya tureta ya juya kan kujeraryayi kwanciyar sa duk da yanajin kukan har cikin kahon zuciyarsa. Tashi tayi a hankali tana kukan ta shiga bathroom, shiga tayi cikin ruwan tana ciki tanajan majina yayi murmushi ya kuma ki bin bayanta, bata fito ba har sai dashi kansa yaga dacewar lokacin tafito yayi amma taki fitowa. Zaune ya ganta a cikk ta sa fusarta cikin cinyoyinta sai gunjin kika takeyi, karasawa yayi ya tsugunna a gabanta tare da saka hannu ya fara kokarin d’ago fuskar ta amma tak’i ta kafe. Taurin kai na lNdo sai addu’a ya mik’e tare ya d’agota cikin nuna karfl sannan ya fito da ita suka shiga bedroom yana rungume da ita suka zauna a bakin gado. 
A gabanta ya zauna tare da rik’o hannunta kanta a k’asa idanuwanta a rufe sai faman sauke 
ajiyar zuciya takeyi. Kallon fuskarta yakeyi cikin tsananin sonta da kaunarta yace. 
“Cutie nine fah ya kamata nayi kuka sabida kin kasa yadda dani, cutie i love you..ban san yadda zanyi na misalta miki ba duk abinda kikaga nayi dan ina sonki ne. Cutie koda kikaga na dage sai kin biyoni nan karkiyi tunanin cewar ko bana son kiyi karatune a’a ina son zuwa dake ne sabida ko bayan rai na kiyi alfaharin kema naje dake inda nake zuwa shi yasa kika ga na dage sai kin bini amma duk abinda nayi miki na rashin dadi cikin sani k0 rashinsa kiyi hakuri ki yafemin.” 
Hawaye suka kuma zubo mata ya tashi ya zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinsa yana buga bayanta cikin muryar kuka take magana. 
“Ni ka dena bani hakuri bayan baka min komai ba, nice zan baka hakuri sabida nice nake bata maka rai amma dan Allah abu Ayman kayi hakuri ka dinga yafemin koda a cikin zuciyar kane nasan ina bata maka rai dan All…” 
A hankali yasa hannunsa ya toshe mata baki yana kada mata kai alamar tayi shiru, da sauri ta rungumesa suka kankame junansu cikin shauki. Basu flto ba sai da kowa yasan ya farantawa dan uwansa sannan suka yi wanka suka ci gaba da soyayyarsu yana kuma koya mata karatunta cike da kwarewa yadda kuma zata gane ta fahimta duk da cewar tana dan dadewa kafin ya zauna a kwakwalwarta danma understanding takeyi ba wai hadda ba. 
Bayan sati uku 
Lokacin sun cika wata daya da zuwa cikin ikon Allah kuma ya samu INdo ta fara sakarwa su blessing fuska sai dai yawanci suna yin wasa da Ayman kasan cewar turancin INdo ba nisa yayi ba kamar su da yazama shine yarensu na biyu da sukeji bayan inyamuranci. ltama takan d’an leka gidan su amma ba sosai ba dan su kan yi yarensu wanda yafi bawa INdo haushi sabida ko “zo” bata iya ba su kuma sunfi yinsa. 
Sosai suka sake kulla babin soyayya dan zaman su anan su biyu ya kuma kulla sabuwar alak’a dan har basa son wani yayi nisa don ba sukanii har zazzabi amma da an hadu sai a warke 
zucnyar su ta ruga ta zama d’aya, duk abinda daya yakejl wala na dadi ko rashinsa sai duk sunji yanayin a jikinsu, ciwon kai idan d’aya yayi sai d’ayan ma yayi koda kuwa faduwar gaba ce wannan yanayin yana basu mamaki da al’ajabi, sun kuma sake tabbatar da cewa sunyi ‘MUSAYAR ZUCIYA’ ya karbi tata itama ta k’arbi tashi suna kula da junansu sannan ta rage yi masa taurin kai musamman da yake karanto mata tarihin annabawa dukdare idan 
sunje bacci. 
Ayman yana ta wayo suna kula dashi sosai sannan koda second d’aya Sadeeq be taba manta Fateema ba yakan buga mata waya a rana kusan sau biyar yayi missing dinta sosai domin ko wacce mace tana da nata matsayin a zuciyar miji musamman daya kasan ce ita ya fara furtawa kalmar So ya kuma fara auranta ya fara saninta a matsayin matarsa. Yana jin dadin zama da matansa su duka musamman yanzu da soyayyarsa ta kuma zama a cikin zuciyar INdo, yafi ta sonta amma yakan daure domin karya d’ora mata girman kai karta dinga d’aukar kanta a wani abun tunda yanzu ne yake dorata akan sabuwar rayuwa dan yanzu ne take kuma sanin komai na rayuwa duk abinda ya dorata akai zai ga shi takeyi bata taba ketare duk wani abu da ya karanto mata ya fassara mata ba. 
Watansu biyu suka shirya komawa lokacin INdo ta kuma wayewa tayi kyau tayi kiba ta zama tamkar wata karamar hajiya tayi dam kwanciyar hankali ya fito a jikinta da yanayinta dama yadda take gudanar da abubuwanta dan takanji zata iya gogawa da ko wacce irin mace a fadin duniyar nan duk da cewar iliminta bema kai na Fateema ba amma yadda zata gudanar da wani abun sai mutum ya rantse ko tana kanyin master’s ne. 
.. 
Kwance take a jikinsa tana kuka domin ba karamin rashinsa tayi ba wata biyu ba wasa bane a gurin miji da mata musamman idan basu tare. Gashinta yake shafawa yana kuma rike da hannunta yana matsawa Sadeeq yace. 
“Baby dan Allah kiyi shiru kinga dai ba zuwa nake garin can ina yawo in dawo ba, kinsan abinda nakeyi kinfi kowa sani tun kafin kowa ya sani hatta Abba kin fishi sanin me nake zuwa inyi dan haka bana son kukan nan please yana sani cikin shakku da kokwanto.” 
“Toh baby amma dai ka dena dad’ewa dan Allah. Ko kuma ka tattaro ka dawo nan kano shikenan kana tare damu koda yaushe.” 
“No… Fateema bana son zaman garin nan ga sa’ido sai dai ke idan kin yadda ki ajiye aikin ki idan zan tafl sai na tafi dake na ajiyeki a can kinga na huta kina can bani da fargaba ita kuma Aisha tana nan kun hutar dani .” 
“Nayi shiru baby nigara ku dinga tafiya da ita can babu kowa dan uwa dangi duk babu sai sababin da zaka yi na hakura zan dinga jiranka har lokacin da zaka dawo.” 
“Ummm kaji me wayo, wato ke kinki bina sabida alkln kl. Amma kina  son na dawo nan da zama shi kenan kullum a ce mijinku yana guri daya baya zuwa konan da can toh na gano ki kuma naki wayon.” 
Ya fad’a yana mata cakulkuli a cikinta suna ta dariya dan baya son yaji ta sako mai zancen rashin haihuwarta sabida shi be tabajin haushin hakan ba ko yaji sonta ya ragu a’a kullum yana jin sonta musamman da take mai biyayya da nuna soyayya. 
Haka Sadeeq ya cigaba da rayuwa da matansa cikin kwanciyar hankali duk da wani sa’in yakan fuskanci matsala ta kowane Bangare amma yakan warware ta cikin hikima ta yadda ya san halin kowacce a cikin su. ‘Daukar su yayi su duka sukaje aka yi musu hoto ya buda su ko wane gida yasa daya guda d’aya babu kuma wadda ta nuna mai bata so
“Hello, Rasheedat. Okey ai zan shigo nan da 11:00 tuna sai 11:30 ko.? Okay sai na shigo.” Kwance yake akan kujera INdo na kok’arin zuba masa fruits salad duk tana jin abinda yake fad’a ranta yayi mugun baci zuciyar ta na zafi kishi ya turniketa sai faman hade gira takeyi. Tashi tayi jikinta har rawa yake yi taje takai mai fruit salad d’in ya dago ya kalleta ganin 
yanayinta yasa shi riko hannunta ta fige ya kuma rikowa ta kuma kokarin fizgewa ya janyo ta kusa dashi ta zauna kirjinta sai dokawa yake yi Sadeeq yace. 
“Toh yau kuma me Sadeeq sarkin ‘yan masu laifi yayiwa cutien sa cikin ‘yan sakanni.?!” “Ba komai kyale ni zan shiga daki.” 
“Toh ki fara bani na gama sha sai kije kiyi aikin ki.” 
INdo ta kuma yin kicin-kicin a kufule tace. 
“Ka kira Rasheedat ta baka mana amma bani ba.” 
“Rasheedat kuma cutie? Kin santa ne ko kuma dan kinji muna waya ne zuciyar ki ta fara halin nata.” 
Turo baki tayi tana harare-hararen gefe ta kasa cewa komai, Sadeeq ya janyo ta jikinsa yasa hannu a tsakiyar k’irjinta yaji yadda yake bugawa cikin tashin hankali ya mike zauna dan da a kwance yake yana rike da ita. 
“Subahanallahi cutie kishi ne haka? Rasheedat ba budurwata bace dalibata ce yau zanyi 
musu lecture shine take tambaya na shin zanje nace eh su shirya shikenan fa.” 
Sadeeq yana jin sanda ta sauke wata muguwar ajiyarzuciya sannan ta kallesa ya sakar mata murmushi tace. 
“Toh banda basu da kunya meye na bugo maka waya, su ba students bane baxasu jira har kaje ba zasu wani bugo maka waya. Ina monitor da bazai bugo ba sai ita tana mace banza kawai.” 
“Tab cutie har ina cewa zan k’ara aure sai kema na barki anan ki cigaba da karatunki Fateema tayi aikinta ita kuma amaryar na barta acan kwara gidana na Ilorin kunga an huta 
da zirga-zirgar fitar ku ko.” 
Share sa tayi ta dibi fruit din a cokali ta sanya mai a baki, yana dariya ya karba har ta gama bashi sannan ya janyo ta kirjinsa yace. 
“Cutie I love you zan iya mutuwa a duk sanda kika juya min baya, ki kula damu dani da yaro na dama wad’anda zaki haifamin nan gaba please cutie.” 
Sumbatarsa tayi a goshi sannan ta kwantar da kanta a saman kirjinsa tana shafar kansa tace. 
“Nima ina sonka my super glue, your my Biggest compott..my breath… My heartbeat” Kai my everything but ka dena min zancen zaka kara aure, a cikin shekara d’aya kayi mata biyu sannan kace kana shekara ta biyu zaka yi ta uku ai sai ka jamana surutu. Dan Allah ka 
barmu mu biyu ka dena tunanin wata idan ba haka ba zanyi kuka.” “Yi muga irin kukan da zaki yi idan zan kara au…” 
Tayi saurin toshe mai baki da nata kafin ta cire ta kalli cikin idanunsa daya bude su a hankali duk sun zama na rigima tace. 
“Haka zanyi uhm..uhm..uhm..ahhh..wayyoooo
Suka kyalkyale da dariya Sadeeq ya rungumeta akan kujerar yanajin kaunarta har cikin ransa. Sun dade suna faranta ran juna duk sun manta da rigimar su ta baya Sadeeq ya kawar da rayuwarta ta baya a cikin ransa yana ganin tamkar dama a hakanta ya santa. Watan Ayman takwas kenan har gidan Fateema ake kaisa ya dan jima kafin a dawo dashi 
tana son yaron har cikin ranta domin tana masifar son mahaifinsa. 
Karfe takwas ya shiga gida, zaune ya ganta tana gyarawa Ayman kwanciya a falo, dariya yayi haryana rike ciki ganin yau kuma da salon da za‘a siyeshi can ta tsuke cikin riga da 
wando nan kuma tayi mai shigarta daya santa a real lNdon ta zamanin tana kauyan sani. “Kai malam Sadeeq he wani kallona kakeyi he kace baka sanni ba.” 
Wayyo dariya Sadeeq ya tsugunna agurin ya dinga yi dan gani yake tazo mai da wani sabon salon soyayya. Ta dashare mai baki tare da karasawa wajan sa tasa hannu ta rikosa da nufin ya tashi aikuwa ya janyo ta itama ta fada kansa suka dinga dariya cikin shauki. 
“Cutiel love you so much.” “I love you too Abu Ayman.” 
“Allah yajikan M tiwwine yasa rahama ta baibayesa yasa yana cikin farin ciki kamar yadda 
muke a yanzu.” “Amin ya Allah.” 
Ta fada tana wasa da mabullayen rigarsa nan suka dinga hirar baya suna dariya. Shirye shiryen bikin Haleematu suka farayi Sadeeq yayi k’ok’ari sosai dan dasu biyu suke had’uwa suyi komai shi yayi kayan dakin hawwa Abubakar kuma yayi na falo amma yanzu baya nan daga shi sai Abba suka dinga yin komai. Duk matan sa kuma sun zage anyi komai dasu cikin farin ciki dajin dadi, suna nan kuma har yanzu a tare mijin su yana sansu iya 
gwargwado yana bawa kowacce hakkinta. 

ALHAMDULILLAH. 

Allah na gode maka daka nuna min farkon labarin nan da kuma karshensa, Allah kaine abin godiya kuma abin alfahari alhamdulillah. Allah kajikan marigayi kasa aljanna ce makomarsa da aiyukan alkairinsa. Da Duk wadanda suka rigamu gidan gaskiya a cikin musulmai Allah ka yafe musu mu kuma kasa mu cika da kyakkyawan aiki Ameen. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE