MUSAYAR ZUCIYA CHAPTER 5

MUSAYAR ZUCIYA
CHAPTER 5
Tafiya take tana dirzar hak’oran ta da k’asan hijjab ko zata samu suyi fari itama, ai kuwa da ta gogo zata duba jikin hijjabin taga gurin yayi yellow ta girgiza kai tare da cewa. “Kai…! Kuma fa da gaskiyar sa wallahi, dan gahi ina kankarowa yalo na fitowa, amma shi hak’oran sa har wuta-wuta suke yi sabida kyau.” Wani shago ta tsaya a nan kusa da gidan su Sahura ta kalli me shagon tace. “ldirisu kana siyar da burushi da abin matsawa…?!” Yace “A’a bana siyo shi lNdo sabida ba’a siyan shi, sai dai kije kasuwa ranar laraba ki siyo.” Tsaki tayi tare da fad’awa gidan su Sahura, ita dai sam ba ta son zaman gidan su domin bata taba yin cikakkiyar awa d’aya sai ta fIta, bata taya Inna da aikin komai sai dai da taji yinwa taje taci idan ba’a gama ba ta hau sababi. Sai kusan magariba sannan ta koma gida shima dan tana son tambayar baban su kud‘i zata je mahad’a wato inda ‘yan mata da samari ke had’uwa suyi hira ne. Tace”Baba sannu da gida.” Yanajin haka ya san akwai abinda zata tambaye sa dan haka yayi mata banza, ta kuma fad’a sai ya d’aga mata kai kurum ta ciza yatsan ta cikin ranta tace, “Wallahi sai ka bani abinda nake so, kaji shi daga gani na baba yayi wani shiru.” Kusa dashi ta k’arasa ta zauna shi kuma da yake a kishin gid’e yayi saurin danne aljihun sa me kud’in a ciki dan ya san tun da ta fara wannan shisshige mai d’in toh rok’on sa zata yi shi kuma naira d’ari da sittin ne garesa kuma goma ba zai bata ba dan yau da kyar ya samu a gurin sana’ar sa. INdo ta cire hijjab d’in jikinta sannan ta kalli mahaifin nasu duk da ya had’e rai hakan besa taji zata fasa tambayar Sa ba, cikin rashin ladabin magana ta kallesa tace. Baba nera (naira) hamsin zaka bani anjima zanje mahad’a, daga can idan naje kaga zan siyo burushi harda abin matsawa sai kuma ka bani nera ashirin wadda zan siya abubuwa naci..” “Bani da kud’i uwata yanzu, amma ki bari gobe idan na samu zan baki.” Kallonsa tayi da alama bata yadda da abinda yace ba, ganin tana kallan sa yasa shi kuma kishin gid’a kan aljihun kud’in yana k‘ara volume d’in rediyon sa duk kuwa da yanajin ana k‘iran sallar magriba amma ba shi da alamar ta shi yayi alwala. “..’Yar nan zo kije kiyi alwala bana jin yauma k0 sallar asubahi kinyi bare kiyi sauran.” Inna ta fad’a tana kashe wutar kararen da ta gama tuwo. INdo naji ta turo baki sam bata kaunar taji ance tayi wani abun a harkar rayuwar ta abu in dai ba wasa bane k0 kuma naci toh sam bata kaunarsa bare tayi. Bacci ma ban da barawo ne da baza ta dinga yi ba, ta mik’e tsaye 
ta shiga d’aki ganin baban nasu bashi da niyar bata ko sisi. Garam-garam inna tajiyo ta tana tattaba mata kwanukan jeranta na d’aki, saurin bin bayan ta tayi nan taga sai faman bud’e-bud’e take yi mata cikin fad’a inna ke magana tana kallon INdon tace. 
“Me kike nema anan? Ko kinyi ajiya a gurin ne zaki d’auka..?!” 
INdo ta ajiye kwanon hannunta kana ta kalli lnnarta tace, “Inna fisabilillahi baba ba zai bani kud’i naje mahad’a ba, salan naje naga su maryam su sahura Da sauran k’awaye na suna siyan abubuwa su yi min gori…?” “Toh banda abinki baya ce miki babu ba idan ya samu zai baki, toh kiyi hak’uri mana nima kuma basu gare ni ba bare na baki.” 
K’ad..! INdo tayi da harshe alamarjin haushi sannan tayi waje fuuuuu babu wanda ya kula ta shima baban nasu yana ji ana k’iran sallah amma ba shi da niyartashi yayi yana kishingid’e abin sa. Tana fita ta shiga gidan Rukayya wadda amarya ce aka kawo ta unguwar take yin kayan siyarwa su alawar madara, gullisuwa, b’alli-k’a-k’au, yajin masau da dai sauran kayan siyarwa na yara, shine INdo take zuwa ta karba tana siyar mata sai ita 
kuma ta ringa bata ladan nera talatin ko asshirin da biyar. “Uhm su INdo sai yanzu aka ga damar zuwa ko..?!” Rukayya ta fad’a tana kallan ta, zama tayi a kan tabarma tana dariya Rukayya ta idar da alwala tazo ta zauna kusa da INdon tana kallonta tace “Toh me ya hanaki zuwa yau da wuri gashi ma har an siyar sabida yau na samu ‘yan sari duk sun siye sauran albishir kawai na naira tamanin..” 
lNdo ta zaro idanuwa tare da dafe k’irjinta yau kenan ba ta da kud’in siyan gyad’a, cikin karad’i tace, “kai Rukayya amma ko ki jira nazo ba komai tun da abin ‘yar haka ce..!” Rukayya tace “A’a lNdo ina zan tajiranki bayan har gidan Ku na tura kizo aka ce min bakya nan, sai kawai na zauna jiranki bayan ga kustoma sun zo..” “Ai shikenan yanzu ki bani albishir d’in na tafi dahi..” Shiga cikin d’aki Rukayya tayi ta fito hannunta rik’e da leda ta mik’a mata. Amsa INdo tayi ta lek’a cikin ledar sannan tayi dariya cikin ranta tana addu’arAllah yasa yau ta had’u da Shu’aibu saurayin ta ya ce ta shanye ya biya kud’in. Mik’ewa tayi tasa takalma tana cewa Rukayya. “Toh na tafi sai na dawo Rukayya kiyi mana adda’a (addu’ah)..” Tayi dariya tana gyara hijabi tace, “Toh lNdo Allah ya bada sa’a a siyar baki d’aya.” Tana fita ta d’auki guda d’aya tare da jefawa cikin bakin ta, zak’in ya gauraye mata bak’i ta lumshe ido tare da sosa cikin kunnanta. K’ofar wani shago taga malam Sadeeq hakan yasa ta k’arasa tamkar bata ganshi ba ta kalli me shagon tace. “Wale kana sai da burushi da abin matsawa..?!” Wale me shago yana k’ok’arin bawa malam Sadeeq klin da sabulon da ya siya yace. “Eh guda nawa za’a baki..?” INdo ta kuma kallon malam Sadeeq sai taga ko kallon tama baya yi sai kud’i da ya zaro yana k‘irgawa zai bawa me shagwon ta tabe baki. Yana sane ya zamar 
da naira d’ari k’asa as in be sani d’in nan ba sannan ya mik’awa wale kud’in sa ya mai da sauran aljihu. INdo na ganin kud’in tayi kamar zata d’auki dutse kawai ta d’auke d’arin ta matse sai mazurai take yi taji ko wani zai ce ya ga sanda ta d’auka, da taga babu wanda yace komai sai ta mik’awa wale kud’in tana cewa. “Toh bani guda d’aya-d’aya ka bani canji na.” Sadeeq na gani ya wuce yana mamakin ta ashe har sace-sace da d’auke-d’auke take yi, lallai yarinyar bata da tarbiya sam sai dai be san dalilin da yasa yak’i yi mata magana ba bayan ya san hakan da tayi ba dai-dai bane ba a cikin addini dama rayuwar ta gaba d’aya. D’akko mata yayi sannan ya bata canjin naira talatin ta k‘ar6a tayi gaba abinta. Cikin mararta ta tura brush da makilin d’in sannan tayi gaba tana d’aukar albishir tana sanyawa a cikin bakinta sai farin ciki take yi yau ta fito da sa’a zata yi brush ta basu mamaki gobe. Tana zuwa zata sha kwana taji ance mata “ke zo nan.” Ta juya tana kallansa ganin malam Sadeeq yasanya ta rik’e kugunta tana girgiza jijinta tana harararsa “yes..” Ganin yadda take mai ne yasa shi kuma d’aure fuska yace mata “fito min da naira d’ari ta da kika d’auke ko kin d’auka ban ganki bane
INdo najin haka ta gyara tsayuwar ta tare da sake danna brush d’in dan karya gani, cikin wayan basarwa tace “kai malam Sadeeq kud’in ka? yaushe na d’auka zaka ce in baka…?” Matsawa yayi kusa da ita tayi saurin yin baya ya mik’a mata dogon hannunsa tare da bud’e mata tattausan tafukan hannun da nufin ta sako mai kud’in sa ta kallesa tana muzurai tare da tsuke baki cikin yake tace. “Ni ban d’auki kud’in kaba, a inama muka had‘u bare na gani na d’auka.“ Ya kuma had’e rai sai taga yayi mata kwarjini k’irjin ta ya hau harbawa ta fara jin tsoron Kodai ya ganta, toh me zai mata k0 ba malam Sadeeq bane d‘ayan ne masifaffan. Ganin yak’i d’auke hannunsa yasa ta tabbatar da cewar lallai ya ga sanda ta sace amma ya aka yi be nuna ya ganta ba a gurin? Cikin borin kunya tace. 
“Toh na d’auka abakacin kalamin sharrin maita da kayi,min ai dama nace ban yafe ba toh yanzu ka biya ni hike nan.” “Ki mik’o min kud’ina nace bana son maganar banza kina jina…” Jin yana masifa yasa ta cewa “Toh na siyo burushi dasu ba kune kuka min wulak’anci ba, shi yasa nasiya nima na dinga yi wallahi a gobe zaku ga bakina sai yafi naku fari.” Tana kaiwa nan tayi gaba haushi da takaici suka cika Sadeeq yama rasa gane meye matsalar yarinyar sai dai yafi dan gana hakan da cewar k’ila tana da aljanu. Gida ya wuce domin so yake daya gama had’a result ya tafl gida tunda anyi hutu sai kuma an dawo wanda yake son kafin sannan ya samu canjin gurin aiki. 
Cikin kwanaki uku ya kammala komai yabar garin sai farin ciki yake yi dan ba k’aramin takura yake yi ba da k’auyan. 
Fatan alkairi ga masu bibiyar wannan labarin, ina ganin sakwannin ku Allah ya bar kauna‘ 
Muje ga CHAPTER d’in gaba wanda daga shi ne zaku fara gano sirrin cikin labarin._

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE