NAILAH CHAPTER 1 BY Ayshat Ɗansabo Lemu ✍🏻

 

Ƴan matane guda biyu keta shiri da alamu unguwa suke shirin fita,ɗaya baƙace amma baƙin me haske ne da ake kirada wankan tarwaɗa,ɗayan kuma kai tsaye xamu kirata fara,duk da dai farin bamai irin tau ɗinnan bane amma dai tanada haske sosai,dukkansu kaya iri ɗayane ajikinsu wani mint green laces me shegen kyau wanda keda touch ɗin red and silver,bambancin ɗinki ne kawai na baƙar half straight gown ne rigan me tsagu gefe da gefe sai straight skat,sosai ɗinkin yai fitting ɗinta domin Allah yayi baiwan halitta awajen,tanada sura irin na cikakkun ƴan mata akwai gaba da baya masha Allah,kyakykyawan fuskanta me ɗauke da dogon hanci zar da fararen manyan idanuwa masu sheƙi,wanda baƙin kwallin data saka ya sake fiddo kyawun idanun,tana da kwantaccen saje me santsi baƙi siɗik dake ƙarawa shafe ɗin face ɗinta kyau,dogon gashi gareta wanda tsayinsa ya zarce kafadaɗunta sosai, me asalin santsi da laushi irin na fulani ko buzaye ɗan ƙaramin bakinta yasha red ɗin lips stick,kallo ɗaya xakai mata ka ayyana cewa tana da jiɓi da jinsi ɗayan biyu kodai fulani ko kuma buzaye,faran kuma sanye cikin gown take daya amshi jikinta sosai domin itama akwai ƙira masha Allah,face ɗinta yafi na baƙar shan kwalliya sosai domin ita ma’abociya son fente fenten face ne bakamar baƙar bane wacce bata son yawan kwalliya sosai barta dai da simple make up ɗinta .

“Nailah don Allah bani wannan pink ɗin lips stick ɗin,kuma kiyi hanzari nasan yanxu momy zata fito bamu ida shiryawa ba.”

Cewan faran cikin kenan idanunta akan wacce takira da Nailah ,baki Nailah ta taɓe tana faɗin.”Nafeesa aini nagama shiryawa sai dai ke dakika tsaya wannan shegiyar kwalliyan me ɓata lokaci,ni mayafi kawai ya ragemin insaka saiko ɗan kunni.”

Taƙare maganan tana saka wani siririn ɗan kunnin me kyau a kunnuwanta,nan da nan tasake yin kyau abinka ga kyakykyawan mace ,Nafeesa ma cikin hanzari tagama shiryawa sun fito fes sai tashin qamshin mayatattun turarukansu ke tashi masu sanyi,muryan momy da suka jiyo tana ƙwalla musu kira yasasu fita kusan atare suna amsa kiran nata,tsakiyar falon suka ja tunga ganin dodon gidan tsaye kyam yana latsa waya,haɗaɗɗan saurayi me jida kyau da kuruciya,dogone me ƙiran ƙarfi irin cikakkun maza,bashida ƙiba sai dai murjewa farine sosai babu inda yabar Momy a kamanni,yana da dogon hanci daya qawata doguwar fuskansa,me ɗauke da zagayayyen saje baƙi siɗik dayai masifan qawata fuskansa,ƙaramin pink lips ɗinsa da dara daran idanunsa sunfi komi ɗaukan hankalin ƴan matan dake matowa akansa,gashin giransa baƙine kakkaura atakaice dai guy ya haɗu ƙarshe,dole idan kikai masa kallo ɗaya ki ƙara,daga zaune cikin seater kuma momy ce ke amsa waya hakan yasasu Nailah durƙusawa suna gaida Doctor AA Mainasara wanda ya amsa gaisuwan nasu batareda ya kalli koda inda sukeba,idanunsa nakan wayansa da yaketa faman latsawa,fuskannan ahaɗe tamkar bai taɓa dariya ba.

Momy ce tagama wayan idanunta akansu Nailah tana faɗin.”Yauwa ƴan matana kun gama shiryawan gaskiya kunsha kyau,yanzu maza ku fara fita kuceda Bilya ya fiddo mota ganinan fitowa idan na gama da yayanku.”

Nailah itace tafara amsawa tana miƙewa ta nufi ƙofar fita falon baki ɗaya,Nafeesa na take mata baya saida suka tabbatar sun gama ficewa daga haraban baki ɗaya kafin Nailah ta saki ƙaramin tsaki tana duban Nafeesa take faɗin.”Nafeesa yaushe kuma ya AA yadawo garin?shikenan mun bani dodon gidan ya dawo bakada sauran sakewa,kinga yadda yake wani cika da batsewa kuwa hmm! wannan bawa badai ilimin isa da miskilanci ba ke harda girman kaima duk ya haɗa,Allah ni sam haushinsa nakeji tamkar ba Momy ce takawo sa duniya ba nikam natsani mutum mare fara’a arayuwata.”

Dariya Nafeesa tasaki tana faɗin.”Uhum! kedai bari kawai Nailah aidai mun kusa hutawa tunda ya kusa aure matan dai xatasha iyayi da tsare gida.”

Nafeesa takai ƙarshen maganan suna kwashewa da dariya atare,kafin Nailah ta ɗaura da faɗin.”Ammafa yanada kirki akwai tausayi kuma kedai barshi da fitina da miskilancinsa,kodan yaga shiɗin ya gama haɗuwane ta kowani fanni oho….amma ina tausayawa koma wace zata aureshi gaskiya.”

Yadda Nailah takai ƙarshen maganan ne yasa Nafeesa sakin ƴaramin dariya suna ƙarisawa wajen Bilya don sanar dashi umurnin Momy ɗin.

Acikin gidan kuwa Doctor AA Mainasara ne zaune bisa kujeran dake kusada Momy,bayan ya kwashi gaisuwa dukkanin hankalinsa nakanta don saurarenta,idanunta akan babban ɗan nata namiji kuma mafi soyuwa axukatansu daga ita har Dady,kafin ta buɗe baki tana faɗin.
“Anwar kaman yadda mukai magana dakai sati biyu da suka wuce,ina sake jaddada maka inanan kan bakata bana son wannan auren naka da Hudah don sam tarbiyanta baimin ba,ina so kasa acikin zuciyanka Nailah itace zaɓina itace nakeda burin tazama mallakinka,kuma shima Dadyn naku yana goye da bayana domin yafi kowa sanin Nailah tarbiyanmuce,kaman yadda kaima kasan hakan kana kauda kaine sabida wani banzan ƙudirinka da baida tushe,don haka nabaka nan da safiyan gobe ka zaɓa kodai asaka bikinka da Nailah ature maganan Hudah ko kuma ka haɗasu duk su biyun ka aur…..”

Wani uban tarine daya sarƙe Anwar ɗin ya hana Momy ƙarisa magananta,ta tsuramai ido fuskanta na fitar da murmushi me sanyi,har tarin ya tsaya batace dashi komiba,shinema yayi saurin faɗin.” Momy kimin rai don girman Allah kiji tausayina nayi ƙarami dayin mata biy…..”

“Dakata Anwar na rigada na gama magana kuma wallahi kaji nayi rantsuwa dole kaxaɓa kodai aurensu su biyu ko kuma ka zaɓi zaɓina kabar naka,kana tsaidamu zamuyi rana,don har gidan marayu zamu biya donsu Nailah sunjima basuje ba saboda tunda suka fara bautan ƙasannan basuda time .”

Taƙare maganan tana miƙewa tsaye tareda gyara zaman hijab ɗin dake jikinta,wanda ya ɓoye adon doguwar rigan bubu na atamfar Holland dake jikinta,bata sake kallon Anwar dake dafe da kansa da duka hannuwansa biyuba tayi ficewanta ranta aɓace,domin bataji kome xai faru xata iya sauya ƙudirinta,ita kaɗai tasan yadda take jin son Nailah azuciyanta tun daga randa tafara sanyata a idanunta lokacin da ƙafafunta suka taka gidan marayun na Nasarawa Kaduna shekaru goma shabiyar da suka wuce har kawo yau,babu abinda ya canza na ƙaunar yaran da tausayinsu acikin zuciyanta,mussamman Nailah wacce itace tafi soyuwa aranta har takejin tamkar daga jikinta tafito,hakan yasa takeji babu wanda zata amincewa da auran Nailah face jininta da takeda iko dashi,jinin natama Anwar wanda takeda tabbacin bazai iya watsa ƙasa a idanunta ba,sai gashi makauniyan soyayyar da yakewa Hudah na neman sashi ya fifita zaɓinsa sama da nata zaɓin,wanda taci alwashin indai tana numfashi to tana addu’an Allah ya cika mata burinta na haɗa Nailah da Anwar aure koda duka su biyun basa son juna ta tabbatar nangaba zasu so junan nasu harma suyi alfahari da kasancewansu inuwa guda aƙarƙashin inuwan aure…..

Koda ta fice harsu Nailah sun shiga mota,Nailah ta zaɓi zaman front seat yayinda Nafeesa ke baya zasu zauna tareda Momy kenan,Bilya shiya buɗewa Momy ta shige ya maida murfin ya rufe tareda zagawa ya shiga mazaunin driver,suka fice daga ƙaton gidan na Alhaji Ahmed Mainasara,lokacin da agogon cikin motan ke nuna ƙarfe shaɗaya na safe,haka Momy take sam bata son tafiya da rana tsaka musamman idan barin gari xatayi,hanyan Kd suka ɗauka suna tafe suna hiransu cikeda nishaɗi ,itako Momy ita kaɗai tasan tunanin dake cin zuciyanta akan Nailah wacce sam batasan me ake ƙoƙarin ƙullawa akanta ba.

12pm dai-dai suka shiga Kd direct gidan Alhaji Matawalle suka fara isa,abokin Dady ne sosai Amaryansa ne Hajiya Sarah ta haihu shine Momy ta taso ƴan matan nata su rakota suna,daganan kuma su wuce don sada zumunta da gidan marayun dake Nasarawa,sun samu tarba daga uwargida Hajiya Suwaiba wacce itace suke aminta da Momy nan da nan aka cika gabansu Nailah da kayan ciye-ciye,bayan sunci sun shane a part ɗin Hajiya Suwaiba sunyi sallah suka nufi part ɗin me jegon nan ɗinma sun samu tarba da karramawa,ƙarfe biyu suka bar gidan sunan suka nufi Nasarawa.

Tunda suka dosa get ɗin shiga gidan marayun Face ɗin Nailah ke cikeda annuri da farin ciki,tayi missing gidan da take bugan ƙirji ta kirashi da tushensu domin anan ta buɗi ido ta ganta,anan ta tashi harta fara karatu a makarantan gwamnati ,kafin Allah ya jeho su Momy da Dady su ɗauke su daga gidan alokacin suna da shekaru takwas itada Nafees,tana alfahary da gidan marayu da irin rayuwan datai acikinsa kuma bataji kome xata xama aduniya zata iya juyawa gidan baya,barin numfashi daga gangar jikinta ƙaɗai takeji zai iya mantar da ita rayuwan datayi a gidan marayu da irin gudunmuwan da gidan ya samar arayuwanta,alokacin da uwa mahaifiya agareta ta zaɓi ajeta agidan tun tana tsumman goyo tazo tasauketa itada ƴar takaddan dake ɗauke da sunanta dana mahaifinta,tareda bayanin dake nuni dacewa ita ɗin ba ƴar xina bace da ubanta,sai dai bata bayyana dalilinta na zaɓa mata rayuwa a gidan marasa galihu ba,wanda ayanzu babu abinda Nailah keda buri irin ta sanya uwanta a idanunta kodan tarin tambayoyin da suka cinkushe kwanyanta takeda buƙatan samun amsoshinsu daga bakin mahaifiyanta,buɗe murfin motan da Nafeesa da Momy sukayine ya dawo da Nailah daga duniyan tunanin data lula cikin hanzari itama ta ɓalle murfin motan ta fice can ƙasan zuciyanta na mata wani suya da raɗaɗin rashin sanin cikakken itaɗin wacece?

Ahankali take takawa cikin takunta me cikeda tsantsan nutsuwa da Allah ya bata,harta jera dasu Momy duka fuskokinsu bayyane da fara’a,suna gaisawa da ma’aikatan gidan da sukai sabo dasu,har suka shige cikin ainahin gidan daga Nafeesa har Nailah Babah Hinde kawai idanunsu keson tozali da ita,dattijiyan data rainesu ta basu tarbiya me kyau,ko kaɗan bata barsu sunyi kukan rashin uwa ba,koda suka isa ɗakin dasu Babah Hinde ke zama aguje suka isa suka rungumeta,itama cikeda farin ciki ta rungumesu tana faɗin .
” Lale dasu Nailah ƴan Zaria su Nailan Babah angama zama cikakkun mata sai aure kenan boko yaƙare.”

Babah Hinde tayi maganan cikeda zolaya,hakan yasa su Nailah sakin dariya suna ba Momy waje ta zauna suka shiga gaisawa da Babah Hinde,wacce halayyan Momy ke birgeta na tausayi da sanin darajan talaka,sam bata cikin jerin matan masu kuɗinmu na yanzu dake ƙyamatan talaka,waɗanda suke ɗaukan talaka ba komibane face wanda zasu bautar don biyan buƙatan kansu,kullum tana ma wannan baiwa addu’an Allah ya raya mata iyali ya biyata dukkanin ƙoƙarinta da aljanna tareda biya mata buƙatunta na duniya da lahira,sunyi gaisuwa a mutunce kaman ko yaushe kafin Babah Hinde ta jagorancesu zaga gidan kaman koyaushe idan sunzo,su Nailah suka shiga neman su Hameeda dasu Naja wanda suka taso tare agidan aka shiga hira,su Hameeda kaman ko yaushe suna yaba yadda rayuwan su Nailah ya inganta fiye da tasu,tunda gashi har sun samu cikar burinsu na kammala deegree suna bautan ƙasa ayanzu saɓanin su da iya secondary suka gama sai makarantan koyan sana’a da suke zuwa yanzu suna koyan sana’an hannu,sun shafe fiyeda awa biyu a gidan marayun kafin suyi sallama dasu bayan ansauke uban kayan da Momy takawo cikeda boot,sai godia ake zabga mata haka suka bar gidan marayun kaman koyaushe Nailah da Nafeesa nata share hawaye,a duk lokacin da zasuzo gidan su fita sai sunji zuciyansu ta karye tareda tunasar dasu cewa suɗin sunada tarin ƙalubale agabansu na sanin cikakken asalinsu.

****************
AA Mainasara kuwa tunda Momy ta fice yakasa koda motsawa daga inda yake zaune,yana cikin ruɗu da tashin hankali ga matsanancin soyayyan Hudah dake sake mamaye zuciyansa,shi kansa yana mamakin yadda tai nasaran mamaye zuciyansa cikin ƙanƙanin lokaci,ya rasa meyasa Momy ke tsananin son yarinyar dako cikakken asalinta basu saniba,basu san ita ɗin ƴar halas bane dagaske kaman yadda uwarta ta rubuta ko kuma shaci faɗine kawai,ya lumshe idanu yana sauke zazzafan ajiyan zuciya lokaci guda yana sake jin tsanan yarinyar na ratsa zuciyansa,shi kansa yana mamakin yadda yake jin tsanan yarinyar aransa duk da cewa shi mutumne me tausayi amma akansu Nailah ya kasa jin hakan har gwamma Nafisa bazai iya cewa yana jin komi akanta ba,amma Nailah sam yarinyan batai masaba sai shegen kyau kaman aljana haka yake faɗi aduk sanda tai masa shirme,amma ya kula kaf ƴan gidan suna tsananin ƙaunarta,hatta da Hussain da baya shiga sabgan kowa yana son Nailah yana yabata akoda yaushe da cewa tafi Amal da Nafeesa nutsuwa da hankali ga brain na karatu gifted ce sosai,hakan yasata fito da first class, buɗe idanunsa yayi da suka sauya launi sukai jajir sabida shiga ruɗu,ya yinƙura ya miƙe yana rangaji ya fito ya nufi part ɗinsa dake can ƙarshen gidan,koda ya isa bisa kujera ya zube yana jin kansa na sake toshewa,baisan ta yadda xa’ai ya iya amsan mata biyu as his age ba,yana ganin yayi yarinta da mata biyu a shekarunsa na 35 aduniya dako auren fari baiyiba,bakuma zai iya rabuwa da Hudah ba kaman yadda ya kula hakan Momy tafiso,wani sashi na zuciyansa ke sanar dashi asheko ya xama dole ya amshesu su duka amatsayin abokan rayuwa tunda dai har Momy tayi rantsuwa to babu fashi dole ya xaɓi ɗayan biyu,Hajia Dada ce ta faɗo ransa yana ji ita kaɗaice xata iya share hawayensa taba Momy baki ta janye maganan haɗashi aure da yarinyan da basusan cikakken asalinta ba,hasalima shi babu abinda yake ji gameda ita sai tsantsan ƙiyayya da idan antsaresa shi kansa baisan miye dalilin da yasa yaje jin hakan akantaba.

Agaggauce ya miƙe ya zari mukullin motansa ya fice don zuwa gidan Dadah dake gaba dasu kaɗan koda ƙafafunsama zai iya takawa yaje……

*Ina godia ga Allah daya bani ikon fara wannan littafi me suna asama,Allah yasa ku anfana da saƙon dake ciki,kuskuren ciki kuma Allah ya yafe min,

Aysha Ɗansabo

 

 

DOMIN SAMUN CI GABA DANNA👇

https://arewabooks.com/book?id=62a4973c772e179ad6e577b4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE