NAILAH CHAPTER 2 BYAyshat Ɗansabo lemu

Koda Anwar ya isa gidan Hajiya Dadah samunta yayi tayi baƙi,suna zaune a barandar dake ƙofar shiga falonta nanne wajen da tafi son zama koda yaushe nan xaka ganta zaune bisa qawataccen carfet me laushi da ake shinfiɗa mata,xaka sameta ta kunna radio tana saurara, gaida baƙin nata yayi yai shigewansa falonta,memakon ya zauna kawai saiya samu kansa da kwanciya bisa doguwar kujeran 3 seater cikin kujerun dake xagaye da qawataccen falon nata tamkar bana tsohuwa ba, yana me lumshe idanunsa maganganun momy kawai kedawo masa,ahaka Hajiya Dadah ta shigo ta sameshi,fuskanta cikeda da damuwa don tun shigowansa ta karanto shalelen nata na cikin damuwa,hakan yasa tayi gaggawan sallaman baƙin nata ta biyoshi,jin shigowanta tana faɗin.”Likita bokan turai waye ya taɓo min jikallena ne ?”

Anwar ya tashi zauna yana sake kwaɓe fuska tamkar me shirin fashewa da kuka,cikin muryansa me sanyi da daɗi yake faɗin. “Dadah nida momy mana wallahi so take kaina ya buga……”

A hankali ya zayyanewa Dadah yadda suke ciki da momy,ya ƙare maganan yana faɗin. “Please Dadah ki taimakeni ki lallashi momy tabarni da Hudah ta janye maganan yarinyar da bamusan cikakken asalinta ba,kuma ni Dadah ban taɓa jin cewa zan iya riƙe mata biyu ba,Hudan ma dayaya tasameni bare ace za’a haɗamin da yariyan daban taɓa jin zan iya sonta ba bare in haɗa jini da ita,meyasa momy ta dage lallai saini idan son haɗa jini da ita take baga Hussain da Usman ba don Allah Dadah kisa baki nasan zata iyajin magananki ta janye xancen tun maganan baije kunnin yarinyan ba please…”

Yadda Dadah ke kallonsa baki sakene ya sashi yanke magiyansa,yana me sakkowa ya durkusa a gabanta yana riƙo hannunta,fuskan nan yayi jazir kiris yake jira ya fashe da kuka.Dadah ta janye hannunta daya kama tana faɗin.

“Anwar zauna muyi magana sosai.”

Tunda AA yaji Dadah ta kirayi sunansa sak yasan tana buƙatan hankalinsa sosai,hakan yasashi zama sosai yana jiran jin ta bakinta kafin tasoma da faɗin.

“Allah dai yaiwa Fateema albarka duniya da lahira,haƙiƙa wannan magana ya farantamin fiye da xatonka Anwar,na daɗe ina maka sha’awan wannan yarinya me sunan gayu (haka take cewa Nailah sabida sunan na mata wahalan faɗe ina ruwan Dadan mu ta mutunci lol)sabida yarinyar nada hankali da nutsuwa gata kyakykyawa son kowa ƙin wanda ya rasa Anwaru,dame wannan yarinyar me kama da siffan beraye ta fita? To wannan karon ni Dadah ina me baka shawara ka amshi xaɓin iyayenka da hannu bibbiyu,kada rashin sanin cikakken asalinta yasaka bijirewa mahaifiyanka,domin ta fika sanin hakan kuma duk yadda kake tunanin zaka so kanka wallahi Fateema ta fika son kanka domin itace tayi naƙudanka har kazo duniya,yo inbanda xamani har ace ɗa yakawo ƙaran uwarsa don ta nuna buƙatan haɗa alkhairy akanka,Anwar ni kaina yarinyar nan Hudah bata kwantamin araiba,da xakaji tawa da sai ince kabarta gaba ɗaya ka amshi wannan yarinya me sunan ƴan gayu domin ita ɗin tarbiyan iyayenka ne rainon Fateema ce data tarbiyantar dasu kaman yadda ta baku nagartaccen tarbiya.”

Dadah taƙare maganan tana duban fuskan Anwar,wanda tunda ta fara magana zufa ke jiƙa jikinsa saboda tsaban shiga shock,don bai taɓa tunanin Dadah zata juyawa masa bayaba,sai gashi itama tana cikin jerin masoya wannan yarinya anya ko Nailah ba mayya bace data lashe kurwan ahalinsa kowa ke sonta? abinda ya ayyana kenan aransa yana haɗiye wani miyau me ɗaci,Dadah ta ɗauke kai tana sakin murmushi,kafin ta tsinkayi muryan Anwar yana faɗin.

“Dadah yanzu kema abinda xakice kenan,kin gwammace ahaɗa ahalinki da mara asal…….”

“Ya isa haka Anwaru basai kakai ƙarshe ba,wannan yarinya koma miye asalinta kasani cewa batada laifi tunda haka ta tashi ta tsinci kanta,kuma babu inda addini ya haramta auren ire irensu,mussmman ita data samu tarbiya me kyau,ina me baka shawara daka bi umurnin Fateema domin ta fini sonka bazata taɓa zaɓa maka abinda xai cutar dakai ba,indai don wannan busasshiyar yarinyar Hudah kakeyi saika haɗasu duk biyun kaman yadda Fateema ta baka zaɓi tun farko,tashi maza ka ficemin daga gida domin ni bazan taɓa goya maka baya ka bijerawa nagartacciyan uwa irin Fateema ba.”

Cewan Dadah data katse Anwar cikeda jin zafinsa,domin ba taga abin tada hankali akan wannan abin alkhairin da Fateema ke ƙoƙarin ƙullawa ba,don tana masifan tausayin yaran da jinsu aranta tamkar jininta,ta yaba nutsuwansu musamman Nailah dake jinta shiru batada damuwa sam,Anwar zai sake magana tayi saurin nuna masa ƙofan fita baiyi musuba ya miƙe ya fice,Dadah ta rakashi da harara tana mitan yaran xamani sam basuda kunya.Hajiya Dadah kenan tsohuwa me shekaru 82 aduniya,itace mahaifiyan Alhaji Ahmed Mainasara duk cikin jikokinta babu wanda takeso irin Anwar,sai dai duk yadda take jinsa aranta bata taɓa yadda ta goya masa abaya akan abinda yake ba dai-dai ba sam.

Anwar a zuciye yaja mota yabar haraban gidan Dadah tamkar xai tashi sama batareda yasan inda zai nufa,yana jin wayansa na faman neman agaji amma baiyi ko gezauba,driving kawai yake zuciyansa babu daɗi,duk wani hope ɗinsa ya ƙare domin dama Dadah ce kawai yasan xata iya lallaɓa momy sai gashi itama tana goyan bayanta,Dady ko wannan bama xai sashi a lissafiba don yasan bakinsu ɗaya da momy ,haka yaita gararanba agari harya yanke shawaran zuwa cikin congo wajen wani friend ɗinsa likitane shima kamansa Doctor Khaleel,wataƙil zai bashi shawaran da zai zame masa mafita,yana son Hudah ba kuma zai iya rabuwa da ita ya zaɓi yarinyar da batada cikakken asali ba,sanin tsananin kishin Hudah da yadda xata amshi zancen idan ya amsa cewa zai haɗasu itada Nailah ya aura,ke sake jefashi cikin tashin hankali don yasan baƙaramin drama zasuyi ba kafin tagane cewa ba laifinsa bane.harya isa cikin congo yana saƙawa da kwancewane ya rasa mafita.


Tun daga nesa nake jiyo shashsheƙan kukanta,harna samu nasaran sanya kaina cikin haɗaɗɗan bedroom ɗin daya gaji da haɗuwa,komi na cikinsa cream colour ne hatta da cotten’s ɗin dake jikin window’s ɗin ɗakin,sosai bedroom ɗin ya birgeni saboda kallo ɗaya zakai masa kasan interio’s ne da suka san aikinsu suka tsara ɗakin,babban macece da xatai shekaru 42 ke kwance tana kuka me sauti harda shashsheƙa,wanda azahiri batasan sautin kukan nata ya fito fili ba,buɗe ƙofan akayi wani kyakykyawan magidanci ya sanyo kansa ciki ,direct kan gadon ya nufa yana janyota jikinsa bayan ya xare ƙaramin hoton kati dake riƙe a hannunta,ya kife hoton yana faɗin.

“It’s ok dear don Allah ki rifamin asiri ki daina wannan kukan,da idan kin farashi baki jin bari kinga su Nawwara sun kusa shigowa banso kullum suna ritsaki kina wannan kukan suyita tambayan dalilin kukan,ki fawwala Allah komi sai kiga komi yazo ƙarshe ,inaji ajikina tana kyakykyawan hannu insha Allah,please Razanah ki tsaida wannan kukan kodan darajan yaranmu da suke damuwa duk sanda suka ganki cikin irin wannan stuition ɗin.”

Yaƙare maganan yana wifing tear’s ɗinta tareda sake sanyata cikin jikinsa yana rarrashi,har saida yaji tana sauke tagyayen ajiyan zuciya tareda sake lafewa akirjinsa,ahankali yake shafa bayanta cikin ƙanƙanin lokaci yaji saukan numfashinta alamun bacci ya saceta,hakan yasashi shinfiɗeta yana gyara mata kwanciya bayan yakai baki ya sumbaci face ɗinta ma’abocin kyawu da cikar haiba,yana tsananin ƙaunar Raxanah sosai sabida yadda tazame masa mace tagari,hotan daya aje ya ɗauka yana me tsurawa ƴar ƙaraman kyakykyawan yarinyan dake jiki ido,duka bazata wuce watanni biyuba lokacin da aka ɗauki pic ɗin,bakinsa yakai ya sumbaci hoton yana jin wasu hawaye na zubo masa,yana tsananin ƙaunar ɗiyansa wacce itace Allah ya fara bashi kyautanta,yana ɓoye damuwansane saboda Razanah,amma bawai don shima bayajin irin abinda takeji bane akan ɓatan gudan jinin nasu,wanda har yau suke fatan Allah ya bayyana musu inda take idan har tana raye bata salwanta ba,shekaru ashirin da uku kenan suna nema da addu’a amma har yau Allah bai bayyana musu inda take ba,sunyi yawon gidan marayu a jihohi da dama amma babu labari,aje hoton yayi cikin side drawer yana ficewa daga ɗakin Razanah ya nufi nasa,wanke face ɗinsa yayi ya fito zuwa falo yana me xama cikin kujera,ko minti sha biyar bai yiba ya jiyo shigowan mota cikin gidan hakan ya tabbatar masa cewa yaran ne suka dawo daga hadda,ya kalli agogo ƙarfe 4 dot dama idan sun fita tun 7:30am bazasu shigo gidaba sai 4pm,babban cikinsu ce ta fara shigowa tana sanye cikin hijab har ƙasa,yayinda qanninta biyu ke biye da ita abaya kowanne riƙeda jakansa ahannu,direct wajensa suka nufo yana faɗin.

“Oyoyo yaran Abbah sun dawo.”

Nawwara budurwa me shekaru sha shida itace ta saki smile tana faɗin. “Abbah kai kaɗaine ina ummah?”

Kafin Abbah ya bata amsa Shaheed ya furta.” Abbah yau ya sheikh ya zane Aliyu saboda bai bada hadda da kyau ba.”

Nawwara ce ta zabga masa harara tana faɗin.”To faɗi ba’a tambayekaba daga shigowa har zaka faraba.”

Abban nasu ya saki dariya cikeda ƙaunar yaran nasa yake faɗin.” Nawwara rabu dasu kinji maxa kuje ku cire uniform ɗin azo aci abinci nima fita zanyi indawo,momy ta kwanta idan kinga 5 tayi bata tashiba kije kitada ita kinji ko.”

Nawwara ta amsashi ya sumbaci su shaheed yana ɗaukan car key ɗinsa ya fice abinsa.Su kuma kowa ya nufi ɗakinsa don cire kaya Nawwara saida ta fara leƙa ɗakin umman tasu taga bacci take sosai kafin ta nufi room ɗinta don cire kayan makarantan ta maida na gida,yinwa takeji sosai hakan yasata fitowa ta nufi dining don cika tunbinta,farace tas me sisirin jiki sam batada ƙiba sai dai fatanta amurje yake sosai,kyakykyawace da babu inda tabar kamanin Abbanta saɓanin yayansu da takejin labarinta ummah nacewa da ita take kama itama kuma taga hakan idan ta dubi hoton yayan nasu da take baby lokacin,kanta babu ɗankwali hakan ya bani dama ganin dogon gashinta dake reto abayanta,nace Allah ya bata suma sai dai ba baƙi sosai bane ataƙaice dai Nawwara kyakykyawace sosai,ta fara cin abincin bada jimawa ba su Aliyu suka iso dining ɗin suma,kowa ya zuba abinda zaici suka natsu suna cin abincin babu me magana acikinsu,Nawwara itace ta fara tashi ta koma can cikin falo ta zauna tana me canza channel ɗin TV daga mbc2 zuwa Bollywood ,ƙarfe biyar nayi ta miƙe don zuwa taso ummah kaman yadda Abbansu yace,tura ƙofanta yayi dai-dai da fitowan umman tasu daga toilet alamun tuni ta tashi don kantama,murmushi Nawwara ta saki tana zama bakin bed take faɗin.

“Ashema kin tashi kefa na shigo tashi Abbah yace idan naga 5 tayi nazo na tasheki .”

Murmushi umman tasu tayi har kumatunta na loɓawa,niko binta da kallo kawai nake kyakyakyawa da ita duk da cewa ita ba fara bace chaculate colour ce sai dai yanayin hutu da jin daɗi ya sake goge fatar yai haske,tana da diri irin na cikakkun mata masu baiwan ƙira,sosai nima naga kamansu da wannan babyn dake jikin pic ɗin da matan ke riƙeda shi ɗazu tana kuka,takowa tayi zuwa cikin ɗakin tana nufan closet ɗinta ta zaro hijab take faɗin.” Aina tashi Nawwara hala fita yayi bayan kun shigo ko?”

Nawwara ta gyaɗa kai tana faɗin ” Eh ummah yace zaije ya dawo.”

“Ok yayi jeki kiceda Rahane ta ɗaura doyan da za’aiwa Abbah sakwara,saiki fara ɗaura naman miya awuta kafin infito .”

Nawwara ta amsa tana ficewa don cika umurnin momy,tana matuƙar murna momy tace su shiga kitchen yiwa Abbah girki,tun tashinta tasan Abban nasu baya cin girkin su Rahane sai dai suyi na gida ita kuma momy tayi nasa.


Ƙarfe biyar da kusan rabi su Nailah suka shigo zaria,sun tadda Amal ta dawo daga katsina hakan yasa suna shiga suka ganta zaune afalo suka ruga da gudu suka rungumeta suna faɗin.”Oyoyo ya Amal.”

Itama rungumesu tayi cikeda kewansu datai tana faɗin.”Welcome ƴan biyun momy haka take tsokanan su Nailah sometimes.”

Dariya suka saki suna faɗin.”Munyi missing ɗinki ya Amal hope dai anzo mana da tsaraban Kt.”

“To sarakan kwaɗayi babu abinda tazo dashi.”

Suka jiyo muryan ya Hussain na faɗi sam basu kula dashi acikin falon ba,momy ta saki dariya ganin yadda Nailah ta zare manyan idanunta tana dubansa kafin ta furta.

“Laaah! ya Hussain ashe kana falon sam hankalinmu yayi kan ya Amal ina yini.”

Idanunsa akanta ya amsa da.”Lafiya lau Nailah ya hanya yau kuma Kd momy ta jaku kenan.”

Suka saka dariya baki ɗaya Nafeesa itama ta gaidashi kafin su nufi room ɗinsu don aje mayafi su sauya kaya,xuwa marasa nauyi don ita Nailah dama bata faye son lace ba gashi skat ɗin duk ya takurata,hakan yasa duk ta ƙosa ta cireshi ta huta,wani bubu na material red ta sanya yabi jikinta ko ya lafe,har zata fita babu hula akanta ta tuna boss ɗin gidan fa nagari,kuma ya daɗe da hanasu yawo kansu abuɗe especially ita daba gwanan son rufe kaiba haka take tun farkonta batason xama kanta arufe,dariya Nafeesa tayi tana duban Nailah dake shirin ficewa take faɗin.” Aina ɗauka haka xaki fita kan abuɗe ya Anwar ya ranƙwashi bati idan ya ritsaki ahaka.”

Nailah ta zabga mata harara cikeda tunxure baki take faɗin.”Muguwa to aidai natuna dama aini yafi tsana shiyasa yafimin mugunta duk a cikin gidannan,tuni na daɗe da gane shi kaɗaine bayi ƙaunarmu kamanma ƙyamanmu yake.”

Taƙare maganan tana ficewa batareda tabari Nafeesa tace komiba,bayan Nailah Nafeesa tabi da kallo tana juya maganganun Nailah,tabbas itama ta jima da gane ya Anwar bayi ƙaunar xamansu agidan,sam baya taɓa sake musu face kaman yadda yake jan qanwarsa Amal ajaki,tun abun baya damunsu har hakan ya fara taɓa xuciyansu,suna ɗaukan hakan da yakeyi amatsayin ƙyamansu yake don suɗin bakowa bane face marasa galihu da aka ɗakko su daga gidan marayu aka kawosu muhallin da sukansu basu taɓa xaton zasu rayu acikin irinsa harsu samu ƴancin kansu da cikan burinsu nayin karatu ba,ta sauke ajiyan azuciya tana kawar da tunanin azuciyanta,ta sauya kayan jikinta tana ficewa itama zuwa falo inda Amal da Nailah da ya Hussain ke xaune,don momy ɗakinta ta shige basu jin kuma xata kuma fitowa sai zuwa dare idan xa’a haɗu ai dinner kaman yadda aka saba…✍🏻

Ga page 2 nan na NAILAH ina fata kun fara enjoying buk ɗin lol,karku manta NAILAH is for sale with just 300 naira,dazaran kun gama karanta free pages zaku biya 300 don samun cikakken labarin.

Aysha Ɗansabo ✍🏻

DOMIN KARANTA CI GABA DANNA👇

https://arewabooks.com/book?id=62a4973c772e179ad6e577b4

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE