NAYI GUDIN GARA CHAPTER 11
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 11
Bayan kwana 2
Misalin k’arfe bakwai na safe. Laila na zaune gefen abbanta yana mata magana cin fad’afad’a. “To kingani ko? Yau wajen sati biyu da maganar yaro zai aiko,amma shiru da alama dama ba aurenki zai ba.” “Baba wallahi cewa ya yi nai hak’uri suna nan zuwa.” “Ban yarda ba, saboda na gaji da yawan k’orafin da ‘yan uwana ke min akanki, kan na kyaleki kina yawo, kullum k‘afarki awaje, ke ba aure ba, ba aiki ba, tunda kin k’are karatu.Duk da cewa mutane ba a iya masu, amma gaskiya suka fad’a, to na magantu, yau ak’allah shekararki 24, dan haka idan kina son kanki da arziki ki tashi ki bugawa yaronnan waya yanzu -yanzu, dan nasan duk inda ya ke ya fita aiki yanzu, ki ce yazo yau in har da gaske ya ke. Ko kuma ki bani muyi magana da shi, idan banji tsayayyiyar magana ba, to wallahi anjima sai an tsaida maganarki da d’an lami na gaji. Ta shi kije ki mai waya ina jiranki.” jiki asanyaye ta mik’e, ta koma d’akinta, ta d’auki wayarta ta take kwasar caji. Cirewa tai ta zauna agefen gado ta latso lambarsa tana kirasa. Wanda adaidai lokacin ko tashi ba suyi ba, yana mak’ale da matarsa, bayan gwagwarmayar daya sha, dak’yar da sud’in goshi ya shawo kanta, suka shirya. Da yake ya yi kewarta,ya sanya suka sha soyewarsu. Inda bayan sallar asuba ma, suka sha kamar wanda sukai shekara ba sa tare.Wanda ya kai Ramadan ga makara.
Cikin kunnenta takejin ringing d’in waya hakan ya sanya ta bud’e ido a alumshe da alamar bacci,ta kalli Ramadan dake bacci, wanda fuskarsa ke fidda annuri, kana gani kasan yanajin dad’insa, murmushi ta yi tuno darensu, ta kuma lumshe idonta, tana kumajin mijin nata aranta. Wanda duk lefin da ya yi mata duk ta ji zuciyarta ta yi sanyi a kansa.Saboda ganin yanda duk ya damu da sab’anin nasu. ‘ Wayar ta d’auka tana son tashinsa, sai kuma ta ga rashin dacewar hakan, ta kalli kan screen d‘in wayar ta ga an sanya Habibty, da sauri ta runtse ido, kishi ya rufeta ‘lalle ma wannan, bata da hankali da sanyin safiya ta hau bugo waya.‘ D’aukan kiran tai, cikin taushin murya ta ce “wacece ne?” Dum! gaban laila ya fad’i, sai ta dake ta saki murmushi. “Ba ki ga sunan da ke kan screen din wayar bane. Dan haka ba dake zan magana ba ki bawa me wayar.” Cikin muryarta me taushi tace na gani shi’isa abin ya bani mamaki, kamar dai mace bai dace ace ta kira namiji yanzuba da keda iyali. Indai ba wai mahaifiyarsa ko ‘yan uwansa bane.” Ki bawa me wayar bana son dogon magana.Don yanda kikejin kanki cewar matarsa ce, to nima nan da d’an wani lokaci zan shigo.” “Yana bacci, ki bari sai sanda kika zamo mallakin nasa, sai ki yi duk gadarar da za kiyi, amma yanzu ni ce mamallakiyarsa.” Kit ta kashe wayar.
Tsaki laila tayi, ta k’urawa wayar Ido, “lalle ma wannan matar,bakisan baki Isheni ko kallo ba, zan maganinki ne da zarar na shigo gidan.” Sanin cewa abban najiranta ya sanya ta mik’e ta gaya mai wayar Ramadan akashe, anjima za ta k’ara bugawa. Yace yana jira ya fita. Tsaki ladifa ta sanya ta ajje wayar. Dawa kike wayane? Kike tsaki.” Batai magana ba, ballantana ma ta kalleshi, sai ma tashi da tai tana k’ok’arin fita, da sauri ya mik’e yace “Lad’ifa baby wait,” yana duba wayarsa. Ya ga wanda ya kira, sai ya ga Laila. Bai kokarin kirantaba, sai ya fita ya yi d’akin ladifa. A fusace.
Kaya take k’ok‘arin cirewa zatai wanka, fuskarnan a had’e ya shiga, rik’eta ya yi ta k’wace hannu. Ba ta kalleshi ba, sai shigewa da tai jikinsa, ta ce “ina kwana zaujina, hope ka tashi lafiya?!’ Ya amsa yana mai karantartar Zamewa ta yi za ta shiga toilet yace “amma kinsan na haneki da d’agan waya ko?.” Kollonsa tai tare da d’an harararsa, ta shige toilet d’in. Fincikota yayi kafin ta k’arasa, ya ce “da ke nake, ki tsaya ki saurareni k0 ba magana nake miki ba?.”Ya fad’a fuskarsa na k’ok’arin canja yanayinta zuwa na fushi.
Na ji ai abinda kace.Kawai banda amsar baka ne.” “Umarni nake baki amatsayina na mijinki, ki gaya min me ya sanya kika d‘auka.” Ba zan iya yi maka musu ba, saboda kaine shugaba na, ta kalleshi cike da kissa, ta ci gaba da magana. Banga wani abu ba, dan na tab’a wayar mijina, domin da kai da kaya duk mallakar wuya ne.ldan akace emergency call ne sai na kasa d’auka? Hmm nice ma zan magantu, akan kowacce macece dake k’ok’arin bugo maka waya acikin lokutan da kake a hannuna. Dan haka a gayama kowacce mace, karta k’ara gargarin kiramun wayar miji da sanyin safiya, saboda ban sallami mijina ba. ldan na sallameshi ya fita can waje, komai ya wakana. Ta fad’a tare da shigewa ciki. Tana maijin haushin yanda ya ke fad’a dan an d’au kiran budurwa.
Sakatoto yayi yana kallonta har ta shige. Cikin murya me k’arfi yace “ke uwata ce kenan, shi,isa kike bani umarni na yi abinda kike so ko?.” Shiru ta yi ba ta tanka ba. Lek‘awa ya yi band’akin ya kalleta, tana k’ok’arin sirka ruwa. “ina miki magana kina min shiru ko lad’ifa? dan kinga ina lallab’aki ko? Yayi miki kyau, kuma ki fito kije ki min breakfast dan sauri nake.” Cak! ta tsaya, a ciki-ciki ta amsa da to, nan ta fito ta wuce shi ya bita abaya,har suka k’arasa kitchen yana binta abaya. Lad’ifa me yasa kike k‘ok’arin canjawa ne,Ehe?.” “Idan kid’a ya canza dole rawa ta canja.Wallahi ba zan lamunci d’aukar raini daga kowacce mace ba, har idan kai ka yi mini na shanye, na san kai mijina ne.Amma wallahi ba zan bari wata mace tana neman kawon nak’asu ba, ina da hak‘uri amma bana d’aukan raini ga wani indai ba wanda suke iko dani ba.” “Na dai gaya miki karki k‘ara d’aukan wayata in dai kika ga ta bugo, warning d’in k’arshe da zan miki kenan.”
Kallonsa ta yi idonta na neman kawo ruwa, ka yi hak’uri zan bi abinda ka ce, amma dan Allah nima ka gaya mata karta k’ara bugo maka waya kana tare dani, walau da daddare ko da sanyin safiya, if not, wallahi zan baka mamaki.” ‘ “Na ji,” ya fad’a yana mai komawa falo. Turo baki tai tana magana ciki-ciki. Me kike cewa ne? Ya fad’a yana kusantowa kitchen d’in . “Ni bance komai ba fa.” Ta fad’a cikin shagwab’a. Murmushin gefen baki ya sanya. “Lad’ifa rigima, kefa yanzu hukuma ce sai da lallashi. Da murmushi mai had’e da ‘yar harara ta ce “ai kaine.” Dariya ya yi ya k’arasa bayanta ya sak’ala hannuwansa kungunta yace “ni me?.” “Ka fa zame min jela yanzu.” In dai akanki ne nafima jela.”
Yak’e tayi najin dad‘in ganin ya d’an damu da ita ad’an tsukun nan. Amma dai tasan duk na d’an lokacine dan ta san kayanta ciki da bai. “Ka barni nai maka da sauri kalli agogofa.”
“To madam.”D’ora ruwan shayi tai mai d’auke da citta da kanunfari. Bayan ta d’ora , ta d’auko k’wai hud’u ta fasa, ta yanka albasa da attaruhu k’anana,da d’an kori kad’an da magii ta kad’a ta soya. Sannan ta d’auko bread me yanka -yanka ta d’auki kowacce waina ta sanya a tsakiyar bread d’aya ta rufe da d’aya , tai guda uku, daga k’arshe ta d’auko toasterd’inta da ke ajje ta goge ta da tissue na kitchen, ta d’auki bread d’in nan ta d’od’d’ora ta gasa ta ajje su a flate ta rufe ruf! ta d’auka duk ta kai dining, yana zaune a falo, murmushi ya ke kawai yana binta da kallo, kallonsa tai “ya dai?.” “Hmm na ga saurinki fa.” “Ai nasan kana sauri ne shi’isa nai maka simple, bari na had’a maka ruwan wanka, kai wanka.” “kefa za ki min.” Dariya tai mai cike dajin dad , ai ba wani abu bane, muje ta kalli agogo “ka ga takwas saura.” Nan suka haura saman, ta had’a musu ruwan wanka suka dirjijunansu cikin nishad’i dajin dad’i.Wanda Lad’ifa ji take dama su d’ore a haka. Da suka fito idanuwasa na kanta yana murmushi,kashe mai ido d’aya tai, ya zauna bayan ya goge jiki,ta fara mulke shi da mai. Bayan ta gama ta fita zuwa nata d’akin dan ta shirya, shi kuma ya sauka k’asa ya zauna yana k’ok’arin had‘a tea yasha, agogon rolex da ke d’aure a tsintsiyar hannunsa ya kallah ga takwas da minti 25 har tama yi, nan yad’an saki tsaki, ya makara sosai. Sakkowa tai sanye da doguwar riga bak’a, turare kawai ta sanya ta sakko dan karya tafI, fuskarta d’auke da murmushi ta k’arasa, idonsa na kanta yana shan ruwan tea yana mai tuno daransa da ita na jiya, sosai yarinyar ke ba shi kulawa takowanne b’angare, wani nishad’i ya keji na shigarsa, ‘yakamata ace kaima kana kwatanta nuna taka gudunmawar agareta’ ya Ayyana aransa. Sai da taje kusa da shi sannan ya ankara. “Kin d‘aukemin hankali ne baby,” ya kalleta yana mai murmusawa. “Hmm!” kawai tace domin tana mai godewa Allah a zuciyarta, lalle addua bata fad’uwa k’asa banza, Allah ya sa ba duk na toshiyar baki bane, saboda auren da zai,hmm tace Allah ya sanya ya d’ore a haka. “Tunanin me kike ne?.” Murmushi ta yi “ba komai”, nan ta zauna suna hira jefi -jef| har ya k’are breakfast d‘in ya tashi. “Oh kinga baby na mata wayata d’auko min.” “To”, tace tare da mik’ewa,da sauri ta shiga d’akin ta d’auko wayar ta ga alamar haske akan screen d’in, sunan habibtyta dad’a gani, sai ta cunno baki dan ta tsani sunan, da sauri ta shiga editing ta canja sunan ta sanya dumb’aru, dariya tai ta kai mai wayar, yace “to na tafi.”
Nan ta zauna tana k’ok’arin k’arashe sauran kayan karin da ya bari, nan ta tuno nasihar yayarta, a yayinta tai mata waya tana gaya mata cewar Ramadan zai mata kishiya, inda karimar ke nusar da ita tana cewa: “Tabbas! ki riga ki sanyawa kanki cewar cewar mijinki mijinkine,kuma Allah ne ya halatta mai k’ara aure. koda zai auren, to karki wofantarda abinki, ki dad’a jansajikinki koda kuwa ace yana basarwa ne,wani namijin da zararzai k’ara aure zai fara wulakanta ta gida, amma mafi akasarin maza , aduk sa’ilin da za su k’ara aure; to fa k’ok’ari suke su taushi uwargida, ya dinga yawan lallashi.Wani kuma ba zai ma lallashin ba harkokinsa gabansa zaina yi kawai. To idan kika kula mijinki na tausarki na ban hak’uri, to kija abinki, to ta nan mace ke dad’a samarwa kanta k’ima a idonsa, koda ankawo amaryar sai dai ta bi tsarinki, idanko mace ta tayarwa da kanta hankali tana zuba uban kishi kamarwacce hauka ya kama, ta ki nitsuwa, sai hargowa da fada’a, to wallahi sunanta sorry, wasu matan ma k’azanta su ke maidawa komai nasu, wata ta daina girki, wata ta daina kwana da miji, wata kuma ta hanashi sakewa.Kuma duk tsiyarta sai yayi. To mai gari ya waya. ldan har kika yarda Allah ne mai hukunta komai sai ki zauna lafiya duniya da lahira. Domin Aure Allah ke k’ulla shi. ldan a k’addarar bawa ya halatto mai auren mata 4 to fa sai yayi duk tsiyarki. Wata ma garin hauka taje ya saketa ta yi biyu babu kenan. To wannan abin da tai shi zai dad’a rage mata k’ima a idon mijin, sai ki ga in anyi auren amarya ta rainata, ta zo ta ganta barhaza da ita, to anan amaryar idan me wayo ce take kanainaye mijin, ki ga ana cewa ai yayi amarya yana wulak’anta uwargida, itace duk ta yada damarta. Jajirce da rok’on Allah ya sanya miki dangana ki shanye duk abunda za ki gani, saboda amarya kota buzuzu ce sai an d’okinta, dole mace ta ji kishi, idan kika rufe idonki kika k’iji kika k’i gani sai ki zauna lafiya.” ’
Numfashi taja tana dad’a godewa ya karima da wannan karantarwar da tai mata, “dole zan d’ad’a aiki da karatunki yayata,” ta fad’a kamar ya karimar na wajen. Shi kuma yana fita ya tsaya, ya tsiri kiran laila, don hankalinsa dukya koma wajenta ,tunda ya fito ya keso ya kirata, sai ya nemi sunan nata ya rasa, ya dad’e yana dubawa, sai k’arshe ya sanya lambartata sai yaga ta kawo mai suna dumb‘aru, dariya ya sanya ya san aikin lad‘ifa ne. oh rigima.” Nan ya kirata sau wajen 3 bata d’auka ba, sai ana hud’u ta d’auka ciki ~ciki ta amsa. “Am so sorry laila.” “karka cemin komai, bayan ka gama bawa matarka dama ta gayan maganganu san ranta.” ‘Oh! My god, mata,mata problem ne.‘ “Ban sani ba, me tace ne?.” “Hmm! wai har ni zata sanyawa doka karna k‘ara bugo maka waya, to kai mata kashedi.“ “sorry gimbiya laila.” “Ba wannan ba, abba yana son ganinka.” “To ya amsa, kina son wani abu ne?.” Babu ta fad’a tana mai jin haushi ta kashe.wayar 6:pm Direct gidan k’anwar mamansa ya zarce, ya shiga gidan, tana zaune kan kujera ‘yar tsugunne, ya yi sallama. “D’an albarka, ka dawo? ai nasan hankalinka na nan.” “Dolene ai mama amina,” ya gaidata yace ya “kukai da hajiya?.” “Kasan dai hajiya da kafiya, wallahi da k’yar ta yarda.” Hamdala yayi azucyarsa. “Ai gwanda kai auren, yo wannan k’armasheshshiyar matar taka, na kula ba ta da niyyar haihuwa,shekara d’aya da aure ba amo ba labari..” Bai magana ba. Hakan ya sanya ta ci gaba, “ta amince, amma da sharud’d’a sai kaje kaji.” godiya ya yi wa mama amina, ya ajje mata kud’i ya tafi. Daga nan gurin hajiyarsa ya yi. Nan ta ke dad’a jadda masa cewar bata san ya wulakanta uwargidansa dan yayi amarya, sannnan ya kwatanta adalci dan ko yaya ta ji wani b’atanci ransa sai ya b’aci.” Nan ya ce mata ya amince ,ya tashi ya fita, direct b’agaren k‘anin babansa ya je, sukai magana kan gobe za aje mai neman aure da sanya rana. Yana flta, gidansu laila ya tasamma, kafin ya k’arasa, ya tsaya yayi sallah a masallacin hanya, sannan ya k’arasa gidan, yana zuwa ya kirata awaya ta fito, sai tashin k’amshi take, saboda tasan dama da zuwansa, sun dad’e suna hira, nan yake tambayarta abban sai take
cewa yana masallaci sai anyi ishai zai dawo. Suna cikin hirar aka kuma kira sallahr isha’i, ya tashi ya nufi masallaci dan yayi. Komawa tai gida zuciyarta fess! ta dad’a talle fuskar nan, ta fito das! da ita ta, zauna tana jiran ya dawo. Ramadan kuwa,tare suka dawo da abban laila, saboda ya gansa a masallacin nan ya ke ke shaida mai in sha Allah gobe za suzo tambaya da sanya rana ahad’e. Abban cikin farin-ciki, yake ce mai Allah ya kawo su, sukai sallama ya shiga gidan, ya ce da laila ta je su yi sallama. Sai da ta bari ya shige d’aki, dan inya shiga ba ya k’ara fitowa, sai kuma safiya, ta fice. Dan
yau sai ta k’untatawa Lad’ifa, sabida abinda taimata, ba zata bar mijin nata ya koma gida da wuri ba, tunda ta san tabbas 6 yake komawa Murmushi ta yi “bakisan wacece lailaba..” Gaban motar ta shiga, yace “komai dai ya kusa zama, end. dan da wuri za a sanya rana fa agoben nan, idan su ka zo.” ‘Naisa ta matso kusa, daman itama amatse take da auren ta fad’a aranta.’ Tana sane ta bar mayafinta yayi k’asa, manyan k’irjinta da suka fito ta saman riga suka dad’a bayyana. Kallonsa tai cikin kashe shi da kallonta, tace “ba yanzu zaka tafi ba, naga har tara ta yi.”
“Kinsan idan ina gabanki bana tuna komai lailata.” Dariya ta sanya, na ga alama.” ldanuwansa k’em! akanta, sai had’iyar yawu yake, dan shi abinda ke dad’a fusgarsa da laila kenan, tana da duk wani Quality da yake san mace ta kasance da shi.ln dai na surar jiki ne. Hannunsa ya sanya ya shafo saman k’irjinta, abinda bai tab’a yi ba sai yau. Daaar sauri yayi ya janye hannun tare da yin istigfari. Kallonsa tai irin da mamaki. “Gyara mayafinki.” Domin ya san cewa tabbas akwai shed’an a tsakaninsu, muddin taci gaba da sakin mayafin ,dole saida taka tsan-tsan.
Ta yi hakan ne dama duk dan ta dad’a shagalar da shi,dan karya tafi da wuri.
Sun dad’e suna hira, har zuwa goma, anan yace zai tafi, da gangan ta cire awarwaronta ta jefa a daidai inda k’afarsa ta ke. “Ohsh! Ka ga awarwarona ya fad’o nan bansan ya fita ba.” Sai ya sunkuya dan d’aukowa, tana ganin hakan da sauri ta sanya baki tai kissing d’in rigarsa, shatin jambakinta ya mai rad’au! Ya fito, da ya ke farin kaya ne ajikinsa. Tai baya da sauri ganin zai dago. Hakan hannunsa ya kuma gogar bakinta jan bakin ya kuma goga. Sai ta sanya murmushi. Ya mik’a mata ta karb’a. Zan shiga gida naga goma na dare ta yi.” Nan sukai sallama ta fita tana murmushi, dan ta san dole ta had’a bomb. “Dole ne na b’ata ranki Lad’ifa a daren nan,” ta fad’a tare da shigewa gida sad’af~sad’af. Shi kuma ya ja. Mota yayi gida
Shin me zai faru muje dai zuwa