NAYI GUDUN GARA CHAPTER 10

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 10
Tun da ta shiga d’an adaidaitan take sharar hawaye, da ta share wani ke sakkowa, tun d’an adaidaitan bai ankara da ita ba, har ya ankare. Hajiya ki yi hakuri komai yayi zafi maganinsa Allah. Babu wani dawwamammen abu dake dorewa,duk abinda ya sameki, ki fawwalawa Allah, ki dogara da shi, domin Allah yana fad’a a cikin littafinsa mai tsarki; “Waman yatawakkaltu alal lahi Ia huwa hasbuhu, innal lahu balugu amra. Dan haka kiyi hak’uri duk da bansan me ya sanya ki kuka ba. Sannan ki yi hak’uri idan nai miki katsaladan. dan na kula kamar kina buk’atar tallafawa ne shi isa, amma na yi dan Allah ne. Sannan kuma Almuslimu akul muslimu.” Nagode. Allah ya saka da alheri da wannan tunatarwa.” Ta fad’a muryarta na rawa. “Babu damuwa ya fad’a.” Har suka k’arasa ya ajjeta ta bashi kud’i ta shige gida,koda ta shigan ba ta zame ko’ina ba, sai sama, nan ta watsar da ledar aka’asa, ta fad’a kan gadonta ta ci gaba da kuka. ‘Ni ramadan zai na cuta, ni zai dunga cin amana. Tabbas! Ya kaini mak’ura da wanda zan dad’e ban waiwayenshi ba,sau da dama maza su kaga mace na yin hak’uri sunfi wajigata. Ba zata fasa mai biyayya ba,amma dole ta canja salonta.’ Haka ta zauna tana ta tunani, tare da magana da zuciyarta. Shi kuwa gogan naka,tunda ya koma store d’in, ya kasa samun nutsuwa, duk sai walwalarsa ta d’auke, yaƙ’e kawai yake wa Laila. har suka gama ya maida ta gida. 
Lokacin shida saura ya karasa gidan, a hankali yake taka k’afafuwansa, har ya k’arasa saman dakinta, ya murd’a zai shiga yaji gam~ gam a rufe, nan ya shiga d’ayan d’akin bai ganta ba. Ko ina saida ya duba bai ga alamarta ba. ya kuma dawowa d’akin yana bugawa. “Lad’ifa bud’e please.” 
Ganin lokaci naja, ya sanya ya d’auko spire key ya bud’e d’akin, ya shiga yaga ga ledar da tai shopping nan, amma ba ta ciki. Nan fa hankalinsa ya yi matuk’ar ta shi. Yana tambayar kansa ina ta shiga ne?. Bai tsaya ba. Ya fita wajen maigadi ya tambayeshi ko ta Lad’ifa ta dawo? “Na ga dawowarta, amma gaskiya banga fitarta ba.” Dafe goshi ya yi ya koma gidan. ltako tana bayan gidan,wurin da shuke-shuke suke tana ta kukanta. Da yake akwai k’ofar zuwa bayan ta kitchen, ya sanya ta bi ta nan ba tare da maigadi ya ganta ba. 
Tana zaune kan tabarma ta kalli sama tana ta tunanin rayuwarta, mafarin fara had’uwarta da shi. .
Ya ce agun Alhaji muktar da sadiya, itace auta kaf! gidansu, fulani ne gaba da baya, wato b’angaren uban da uwar, gidane gidan tarbiya da kamewa. Suna da rufin asiri, wanda ba za a kira su masu kud’i ba, kuma ba za a kirasu talakawa ba. Atsaka -tsaki suke. Lad’ifa tana da yayye mata biyu. Wato hadiza itace babba da ke aure a kaduna, sai Karima mai binta Da ke 
nan kanon. Sannan maza biyu hassan da hussain da ke bin karimar. Sai Abdul mai binsu. Sai Auta Lad’ifa. 
Mahaiflyarta tsayayyiyace, mace mai sanin ya yakamata, shi’isa suka tashi cikin halin dattako, wanda duk wani tarbiya da Lad’ifa ke gwadawa agidanta, ya samo asali ne daga kiwon mahaiflyarta. Wanda tun tana k’arama ta ginu akan haka. Tafe take cikin tafiyarta mai nutsuwa, sanye da hijabi mai hannu,jin dad’i kawai take, wai yau har tai wata uku da yin candy. Babu abinda take da sha’awa irin ta ganta a university ko college, tana buk’atar k’arin karatu. Amma sai dai ta san al’adar gidansu, yarinya ba ta ci gaba da karatu, sai dai ko ad‘akinta idan mijinta ya barta.Hakan ya sa duk burinta ya yi k’asa. Ta shiga Kwanar layinsu taji anai mata horn, bata juyoba, sai kawai tai gefe kanta ak’asa. Motar ba ta fasa binta ba. Har saida wata mota ta zo wucewa daf da ita, hakan ya bata damar tsayawa, inda Saurayin da ke binta amota ya futo, ita kuma adaidai lokacin ta ci gaba da tatiyarta. “Yan mata.” Ya fad’a yana binta abaya. Ba ta juya ba, saida ya sha gabanta. Ta tsaya ta ce “malam laflya?.” Nan ya yi murmushi. “lambarki na ke so.” “I’m am so sorry, bana ba da lamba akan hanya.” “Please ki taimaka, wallahi bana son ki kufcemin.” “Koma menene za ka iya zuwa k’ofar gidanmu, ka nemi izinin mahaifana, idan ma lambarce sai na baka,” ta fad’a tana mai ci gaba da tafiya.Murmushi ya yi ya koma motarsa yaja, yana mai jin wani irin k’aunarta aransa. Bin ta a baya ya yi, har yaga gidansu. Ramadan kenan, d’a ne ga marigayi alhaji sa‘id. Mahaifinsa tsohon mai kud’i ne,ya dad’e da rasuwa, ramadan shi ne d’a na biyu a gidansu, su biyarne maza uku mata biyu. Ya mutu ne tun kafln Ramadan ya kammala Uni d’insa. Bayan gamawarsa aka raba musu gado. Wanda tangamemen gidan da suke ciki ma da Lad’ifa, yana daga cikin gadonsa. Bai b’ata lokaci ba kuwa, har saida ya samu keb‘ewa da Lad’ifa, bayan neman izini gurin babanta. Cikin d’an lokaci kad’an ya kafa gwabnatinsa, ya tsaya da kafarsa ya kori kowa, sai shi kad’ai, saboda shi ladifa ke so, soyayya suke mai ratsa zukata. 
Arana sai ya bugo mata waya yakai sau goma, kuma su dad’e suna waya, domin itama Lad’ifar abin ya zame matajiki, ga shi kashe mata kud’i ya ke kamar hauka, har saida mahiflnta ya hana, amma ya k’i, duk cewar ko’ita ba ta san yawan kashe matan da yake. Da zarar tai magana zai ce shi Aa ihsanin So ne. Wani irin wutar sonta ke rura jikinsa, hakan ya sanya ya ce da zafi-zafi ya ke san ai aurensu. Don ko fad‘a sukai da Lad’ifa duk sai ya damu, har hawaye ya ke zubarwa duk dan ta yi fushi. Ada akwai k’anin babanta da ya ce d’ansa za ta aura, Saboda shima ya nace yana sonta, hakan fa ya dagulasu, domin shima baban nata sai ya bi ra‘ayin k’aninsa. Shi da ita duk suka tashi hankulansu, musamman shi, dan zuwa ya ke gidan k’anin baban Lad’ifar yana kuka, duk ya hana su sakat! da jeka ka dawo, ganin irin yanda ya ke nuna zafin sonta. Ya sanya aka hak’ura zata aure shi. Ramadan duk da cewa ya fl san duma -duman mata, dan akasari duk ‘yan matansa masu jiki ne, shi baya ma budurwa ramammiya, duk wacce za ka ganshi da ita alokacin da yake Uni, to za ka ganta acike taf! Dan shi bai d’au siririyar mace a mace ba, wannan ra‘ayinsane tun bai kai haka ba ya ke sha’awar mace mai cika. Duk da cewar ‘yan matansa irin zab’insa ne, amma bai tab’ajin koda kwatankwacin irin son da ya ke wa Lad’ifa ba da su, abin na ba shi mamaki, danko budurwar da aka kusa sanya ranarsu da ita duma duma ce. Wacce k’addara ta sanya aka fasa ba shi ita, saboda dalilansu na san had‘a ta aure da d’an uwanta. To ko’ita baiji sonta kamar na Lad’ifa ba Yanayin zafln sonta da ya keji, shi ya sanya ya kore duk wani yanayin jikinta a zuciyarta, sai ya kejin ko ahakan zai iya aurenta.Dan in bai aureta ba yana jin ba zai iya nutsuwa ba. Lad’ifa tana da matuk’ar kyau afuskarta sosai, ga yalwar gashin kai. Da gashin gira mai yawa. Doguwa ce be can ba, za a iya sanyata a midium size,yanayinta komai cikin sanyi, in tana tafiya kamar wacce ba ta san taka k’asa, fara ce , ga fatarta a murje, kuma sirantakarta bai fito sosai ba, saboda a murje take, ga kalar sauk’in kai da hak’uri kwance a kyakykyawar fuskarta. Yanayin kyawun fuskarta sosai ke fuzgarsa. A haka dai akai aurensu, inda alokacin ta ke da shekara 18 a yayinda yanzu kuma ta shiga 19, dirzar soyayya su ka yi san ransu, ko tari Lad’ifa tai sai ya tanka, watan su biyu da aure yad’an fara canja hali, irinsu zafin rai, da yawan fad’a ga k’orafl, a hankali sai ya tsiri cewa dama ace ita lukuta ce, da sai ta fi kyau, kai yakamata ki yi k’iba Lad’ifa, zan samo miki maganin k’ari, abubuwa dai kala -kala. Cikin lokaci k’ank’ani munanan halayensa wanda ba ta sanshi da su ba, sukai ta fitowa a hankali, har suka wanzar da canjuwar akalar zamantakewar na su. 
Da yake yayi mata alk’awarin za ta ci gaba da karatu da zarar sunyi aure. Hakan ya sanya tayi mai maganar. Bud’ar bakinsa ya ce “na fasa ki zauna k iyi bautar Aure.” Haka ta hak’ura, da yak’inin idan gaba Allah ya rubuta za ta yi to zatai. Numfashi ta ja tace: ” Namiji kenan
Bai tunanin ya duba bayan ba, dan ya san ba ma’abociyar zuwa can bace. Cikin tashin hankali ya shiga motar yaja ya fice afusace. Tana jin an kira sallah, ta taso ta koma cikin gidan, girki ta tsaya ta d’ora, da ya ke tana da soyayyar miyarta, sai ta d’ora farar shinkafa kawai. Ta d’auko miyarta d’umama , ta zuba a k’aramin flask. Ta koma d’aki kan shinkafar ta dahu. A saman tai sallahrta tai lazimi, sannan ta sauka k’asan, lokacin shinkafar saura kad’an ta dahu, ta zauna ta jira har ta k’arasa ta da’auko tajuye aflask, ta d’auka ta ajjesu a dining, ta d’au nata data zuba a flate ta haye samanta, ta kulle d’akin ta bar muk’ullin ajiki. Bai zame ko’ina ba sai gidan karima,bai nuna mata cewar neman Lad’ifa yaje ba,su ka gaisa, ya ce mata unguwar yazo, shi,isa ya shigo su gaisa, bai dad’e ba ma. Sai da ya tsaya yayi sallah a masallaci, sannan ya wuce gidansu Lad‘ifar nan ma bai ga alamarta ba, nan ya koma gidan cike da zulumi.Domin a yanda ya ga ta fice daga sahad da sauri ya san komai zai iya faruwa. Afalo ya zauna ya dafe kai, idonsa ya kai kan dining table, ya ga flask, da alama dai tana nan. Sai ya juyar da kansa, idonsa ya sauka akan hotonta, wanda ta d’auka lokacin da tai sauka, rike da zayyana.Yanda tai murmushi kamar ka saceta ka gudu,ji ya yi har ya fara kewarta. “To Ina ta tafi ne?.” Ya fad’a afili. Ji yayi wata irin yunwa na sasuk’arsa,nan ya tashi yaje ya zauna yana cin ci abincin,ji yayi sam baya ma wani jin dad’i. Domin ya saba da cin abinci tana gefensa, da ace tana nan da ita ce ma zata ba shi, k0 in ba ta bashin ba ma, to tana zaune kusa da shi tana zauji na kaza, zaujina ya dai sauransu.” Duk sai ya ji gidan ya yi mai fad’i. Itako tana d’aki, ta ci abinci ta zauna lamo tana tunani, tabbas! a wannan karan saita nunawa Ramadan itama macece, kuma mutum ce Da taga shirun yayi yawa, kuma ba ta san tunanin takaici, ya sanya ta d’auko Qur’aninta ta zauna tana bi, sannu a hankali take jin zuciyarta na washewa. Ta dad’e tana yi har wajen 9 sannn bacci mai nauyi ya d’auketa. Ramadan kuwa, bulayi yayi ta yi dan ya gano inda take, har ya gano tana cikin d‘akinta ta datse. Ya dad’e a falo, ganin ba ta sauko ba, sai shima ya wuce d’akinsa, ranan dai bai samu daddad’an bacci ba. Washegari kuwa, da yake duk a weekend ake, tasan tabbas sai  zai fito, sai ta tashi Karfe7 tai gyare gyarenta, ta yi musu breakfast, k‘arfe goma ta gama komai, sannan ta d’au nata 
Ta wucewarta d’aki ta sak’ala muk’ulli. Sai 11 ya mik’e ya fito ya ji falon na k’amshi, tabbas! ta fitoo ya fad’a aransa, direct dining yaje ya yi break ya koma saman ya shiga bugun k‘ofar. “Lad’ifar Bud’e muyi magana, tana jinshi ta share, d‘an ta riga ta yi zuciya. Ya dad’e yana bugu,sannan ya koma d‘akinsa, duk sai yaji gidan babu dadi,cike da kasala ya yi wanka ya bar gidan, sai da ta ji ya bar gidan, sannan ta sakko falon tai zamanta tana kallo,sam! sai ta ji duk wani k’uncin zuciya da take ciki ya yaye, saboda karanta Qur anin da take yi. Amma tababbas sai ta nunawa Ramadan itama tana da zuciya,tana hak’uri ne saboda darajar aure. 
Misalin takwas na dare, tana kitchen tana wanke wanke, ya rutsata aciki, ya tsaya abakin k’ofar yana kallonta, tasan ya shigo sai ta yi burus! da shi. “Lad’ifa,” ya fad’a yana mai matsowa, waigawa tai ta kalleshi, still dai da wannan kallon da tai mai a store shine yanzuma ta jefe shi da shi. Kauda kai ta yi ta sunkuya ta ce “barka da dare.” Ta fad’a ba tare da ta kuma kallonsa ba. Ya amsa a cikiciki. “kin gama gudun?wai meye hakane haka lad’ifa? tunjiya kin maida gida kamar mak’abarta haba, ki tsaya muyi magana mana.” Kallon ka raina min hankalin tai mai. Tare da tsame hannunta tsam! daga ruwan wanke
wanken. “ Murmushi mai k’awata kyakykyawar fuskarta ta yi , ta ce “me akai ne megida. Aini babu wani abu ta wajena, ai ina gidan, sab’ani dai inaga mukai ta samu, amma ban tsammanin baka damu ba ko Maigida?” ta fad’a tana mai yi mai kallon nan da ya kula ta fara shi tun jiya, dan shi kuwa ya kasa gane mai kallon ke nufi nan ta rab’a ta gefensa ta fice daga kitchen d’in, ta barshi tsaye k’ikam! Yana mamakinta, ‘anya kuwa lad’ifarsa ce da ya sani mai yawan rauni akansa.‘ Jinjina kai ya yi tare da sakin Tsaki ya fice ya zauna afalo yana kallo. Yana nan zaune ta dawo za ta shiga kitchen d’in, ya ce “Lad’ifa.” Ta tsaya cak! “Wani abu ne? ta fad’a tare da kafeshi da kallonda ke sanya ya kasa duk wani katab’us, wanda ya ke sawa yanajin kamar ba Lad’ifa ba ce.Kuma ya ji duk ya muzanta.”Ki zo muyi magana akan abinda ya faru jiya.” “Sorry oga maigida, ni ai ba kaimin komai ba,wannan ba wani abu bane,” ta fad’a ta bar wajen ta koma ta cigaba da aikinta, ta gama ta zo tai wucewarta.  
Yau wajen kwana hud’u kenan duk ladifa ta canjawa Ramadan, ba ta zama su yi hira, ‘yar tarairayarnan duk ta daina, babu murmushin da ya saba gani afuskarta, da shishigemai da take, wanda ke sashi girman kai. Sai dai ta fesa wanka ta bulbulo mayen turaren da yaya karima ta bata, wanda in dai ta sanya. dole sai yaji ajikinsa, sannan ta bazo gashinta baya da yake bata fiya san kitsoba. Tazo ta zauna. 
Ba abinda ke had’asu, sai gaisuwa sai girki da zatai mai, wanda duk bata fasa ba, haka za ta shiga d’akinsa ta gyaro duk bata fasa ba. Yauma ya kuma samunta kan ta tsaya ta fuskance shi, amma fafur tace ita ya k’yaleta, ta rigada ta shafe komai a zuciyarta, kawai ya je yaci gaba da harkokinsa da ‘yan matansa ya barta a haka.K’arshe da ya takura mata,kuka ta sanya sai ya k’yaleta. Haka zaman na su ya dawo, dan duk ta zuba shi a kwandon shara, ko kallonsa ba tai, kayan da ya ke cewa ba sai mata kyau, wato k’ananan kaya, su take sanyawa, ta bazo turaren da ke tsuma shi, ta zo ta zauna ta d’ora kafa d’aya kan d’aya, wataran tana taunar cewgum,wataran kuma ta kwanta ta hau karatun novel na yak’i, sosai ta kejin nishad’i in tana karantawa, har mantawa ma take yana wajen, ita kanta tana mamakin kanta, ada takan damu in suka samu sab’ani, amma a tun san da abin ya faru, ta ji komai ya daina damunta jin ya yi mata magana ta ce. idan ya san maganar can zai mata to ya rik’e abarsa. Ganin abun nata ba na k’are ba ne, sai shi ma ya yi fushi, ya d’auke mata wuta d’if! ya tsiri harkokinsa, ya daina shiga sabgarta shi wai yaga k0 za ta shiga hankalinta, ta dawo su koma kamar da, sai ya ga abun nata ma dad’a yawa yake kamar wani canjata ake, domin ko ajikinta da fushinsa,wanda idan da kwanakin baya ne tashin hankalinta za tai har sai ta ba shi hak’uri ya sakko, harkokinta ta ke san ranta. Har su wakoki take in yana wajen, kuma ba ta tab’a bari su hada ido, duk abin ya dameshi.d’an tarairayar da take mai, da shigewajikinsa da take, da nuna soyayyarta gareshi, duk yana missing d’insu. Sosai ya shiga wani yanayi 
Sunyi wajen sati d’aya a halin nan, amma ya ga abin na ta bana k’arewa ba ne, ya ce dole yau sai ta saurareshi. Tana d’akinta, tana k’ok’arin sanya riga, bayan ta gama goga kayan k’amshinta, taga shigowarsa ta mudubi, sai ta kauda kai. “Lad’ifa ki tsaya muyi magana.” “Dan Allah oga maigida ka k’yaleni, ni gaskiya bana son takura,” ta fad’a cikin salon shagwaba tare dajuya baya zata fice daga d’akin. Jitai ya rik’o hannunta Sai ta tsaya “dole yau ki tsaya muyi magana.” “Ni kuma nace bana son magana dan bansan wacce magana bace.” Sai ta kauda kai tana jin ranta na suya. Fuzge hannunta tai ta fice daga d’akin, ta yi kasa ta zauna tana girgiza k’afa. Afusace ya sauko k’asan. “Ke dan wulak’anci inai miki magana kika fito, danke baki da kunya ko?.” “Inda kunya take banje ba, dan haka ka yi hak‘uri.” “Fincikota yayi ta yi taga-taga zata fad’i. “Dole ki zauna muyi magana, na gaji da wannan canjin na ki, bana sonsa, gwanda ace mu zauna mu yi wacce wacce akan wannan sabon tsarin na ki, yana cuta ta da yawa, domin bansan me kike shiryawa ba, na sanki farin sani Lad’ifa tunda na ga bakiyi magana ba. Ki gayamin, sannan kuma ki zo ayi ta tak’are.” “Ni fa babu wata magana da za muyi” ta fad’a muryarta na rawa. “Dolenki muyi magana.” “Kallonsa tai da manyan idonta, ta k’ura mai ido, ‘yauzu da ace ita mara kunya ce, da ta sakar mai zafafan maganar da zai kasa motsawa,amma tarbiyarta ba haka take ba, ba a koyar da ita fasalinba, ko ita ba a san ranta ta canja ba, dan tafi san rayuwarsu ta baya duk da bajin dad’in zaman take da shi ba, amma ta kula dole sai ta tauna tsakuwa dan aya taji tsoro. 
Sai ta yi murmushin da ya fi kuka daci kin saka abu arai salon, ciwo ya sameki ki sanya ni a uku, to wallahi yau dole ayita rta k’are, domin ni na gaji da walagigi, kin sabar mini da duk wata tarairaiya amma yanzu kin dena ya kike son na yi ne?.” Kallonsa ta kumai tana girmama san kansa irin nasa. Sam! Kansa ya sani. Ada da take mai, bai tab’a tunanin itama tana san kulawarba, shi dai ai mai kawai, cikin zafln da ta ji k’irjinta na yi ta ce “Ashe ma ina da amfani to malam ka saurara min..” Ta juya ta shige kitchen, afusace ya bita ya janyota ya matseta a jikin bango, “dole kice wani abu “Ba zan fad’a ba, na gaya maka, ta fad’a tare da sanya kuka, cikin muryarta da bata fitowa, wani irin kuka take mai kassara zuciyar mai sauraronta. 
Jikinsa ne yayi sanyi lak’was ganin yanda take kuka. Cike da Raunin murya ta ce. “Ramadan ka yi min illa, bansan cewa sanka zai zame min damuwa ba sai yanzu,anya kuwa Kana kaunata kuwa? Sai ta girgiza kai lalle na yarda sona kawai kake banda k’auna. baka san cewa shiru na yafi maka alkairi ba, muddin zan bud‘e 
muryata to dole na fad’i abinda zai sosa ranka, wanda bana fatan haka.Ba dan ibada nake ba, da sai na ce aurenka ya fice min arai. Kuma zancen wai na daina yi maka tarairaya. Duk ba ta taso ba, mutumin da ke neman aure ai ba zai damu ba sai ya zauna har amarya ta shigo.” 
Dafa bangon yayi yana son rarrashinta ammma girman kai ya hana shi Yana cike da mamakinta, yanda ta ke cemai Ramada gatsal! babu ko d’an sirkawa da Zaujin. Sai ta mik’e a kasalance tai sama, ya bita abaya, kan ta rufe ya danna kai. Yarfa hannu tai irin alamar gajiyawa, danji take kanta na sarawa so take kawai ya k‘yaleta. “Kin ganni rannan da budurwa a store, shine abinda nake so mu tattauna.“ Bakin gado ta zauna tana lumshe ido na gajiya da dukwani abu da ya danganci Ramadan. 
cike da dasasshiyar muryar da ta sha kuka ta ce: “Au! dama akansa kake wannan?.” Sai ta sanya dariya, ai band’au wannan wani abu ba, tunda har ganinku ya canja ni, ya sanya na fahimci wata rayuwa aiko na gode maka.” “Ah baki damun bane za ki na guduna?duk kin canja wallahi, kamar ba Lad’ifar da na sani ba, ina sauk’in kanki ya ke? k0 hak’k’ina ba bakya bani yanzu.”Murmushi ta yi ta ce : “Muddin kazo kace in baka, to zan baka, naka ne fa, mallakinka ne, idan ban baka ba me zan da shi, wannan ba halin lad‘ifa ba ne..” Cikin sanyin jiki da tarin sha’awarta ya matso ya rik’e hannunta ya shiga murzawa idansa na lumshewa. “I‘m so sorry Lad’ifa, na san na yi kuskure amma ki yi hak’uri. Kauda kai ta yi, tare da Fincike hannunta, hawaye na zuba cikin tarin takaicin da ke cinta kwana da kwana ki ta ce “yanzu ace har budurwa tafl matarka ta sunna, ba zaka tab’a iya mik’ani ko’ina amotarka ba, ni bankai matsayin da za aka sanya ni gaban motarka ba, anya akwai adalici a tafiyar nan kuwa? Na san na yi miki babban laifi, amma ki yi hak’uri kinji. “Wacece ita?.” “ltace wacce zan aura.” Tab’e baki tai “Allah ya baku zaman laflyaIa ta fad’a tare da kwantawa ta juya mai baya. Tab’a ta ya ke san yi, amma sai ya kejin shakkar hakan. Sai kawai ya yi shiru ya k’urawa bayanta ido. Ita kuwa Kishi ne ke nuk’uk’usarta, wani irin kishi takeji wanda tasan idan ta bud’e baki ta kuma yin magana, komai zai iya faruwa. Shirun shi ya fi alkairi a gareta. Tasan idan ta tayar da fitina ba zata canja zani ba, muddin namiji ya fada  zai aure, to fa dole fa sai ya yi, namji ba a iyar mai. Gwanda ta tsaya ta ga gudun ruwansa, kuma ta daina d’aukan raini. “Ba ki hak’ura ba kenan?.” Ya ji tsit! nan ya kalli fuskarta ya ga idonta arufe, sai ya yi zatan tai bacci, ya fice yana jin kamar ba shi da kowa.Yana fita ta sanya kuka mai cin rai, tabbas! tata k’addarar kenan, tasan idan ta ce za tai kokawa da k‘addara to za tai jayayya ne da hukuncin Allah, gwanda ta zuba eyes, Allah ba azzalumin bawansa ba ne, gwanda ma ya aurota za tajin kwanciyar hankali kan irin hakan. Shi dai baiga canji ba, amma ta hak’ura, komai ne dai bai dawo normal ba. Wani tunani ya yi,washegari kuwa sai gashi da sabuwar waya fill kirar samsung Galaxy note edge ya kawo mata. Ba tai wani murna da ita ba. Amma dai tace ta gode.shi ko ya yi hakanne duk dan ya toshi bakinta.Ya kuma wanke Iafinsa. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE