NAYI GUDUN GARA CHAPTER 17
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 17
Zama tai ta bude flaks din, tiririn kazar ya daki hancinta, kallo d’aya tai ma kazarta san ba zata iya cinyewa ba. Tsam! ta mike ta kuma sauka kasan, dan dauko flate da serving spoon. Tana kitchen din ta ji dariyar laila sun fito falon. Flate din da cokalin ta dauko, da kunun aya a wani karamin jug, nan ta fito ta ajje kayan a kasa, ta jawo kitchen din, dan indai tana sama to kitchen din na rufe,kai tsaye ta wuce, sai kuma ta tsaya, saboda tunowar cewa sallama na daga cikin cikon addini. Sai alokacin tajuya idonta ya sauka akansu, sam basu lura da ita ba saida tayi gyara murya, ramadan ya waiwayo da sauri, sai ta yi dan yake tace “sannunku Amarya ya bakunta? Barka da rana my oga.” “Barka dai baby?.” Kallon da take mai, duk sai yaji kunya ta kama shi.Dan ya san kallon tuhuma ne, ganin ya
shareta kwana biyu. A hankali ya mike laila dake gefensa ta hade rai tamau Kamar an aiko mata da sakon mutuwa. “Ya kadaici lad’ifa?.” Laila ta fada tana dan murmushin gulma. Sai ladifar ta kalleta itama cikin dan murmushi ta ce “kadaici Alhamdililah saboda yana wuyan kowa.” Nanta juya zata wuce. Ramadan ya riko hannunta, sai ta tsaya ta kafeshi da manyan magananta, yiri-yirin kitson da maman Raudat tai mata ya kafe da ido yana yabawa a zuciyarsa. A fili kuma yace “me zakici ne? na ganki da flate da cokali?.” “Abinci zanci?‘ ta bashi amsa atakaice. Jug din hannunta ya karba ya bude murfin ya yasha.
“Kunun aya ne , shine baki tuna dani ba.”
“Mutum da gidansa inya umarta ai zai samu.” Ta fada tana dan murmushi, tai gaba, ya bita da kallo sai ya shiga taka kafafuwansa zaibi ta saboda ya kwadaitu da lemon kuma yana bukatar kari.
Sai yaji laila ajikinsa, “habeeby zo kagani.” Ya kalleta “me zan gani?.”
“Kai dai zo kaga, sakon da zaka kai gidan kawata na manta ban baka ba, kuma yayi nisa, tsawona ya kasa kaiwa, zoka daukon dan Allah. “Haba dan Allah mana wai laila. Ki bari na hau ta wajen baby na sauko mana, ban san
yawan damuwa fa.” Wani irin kishi takeji inya ambaci baby tsaki ta sanya aciki-ciki, dan tayi alkawarin, ba wajenta da zai je anar girkinta. Ganin yana yana shirin hawa da sauri ta daura bakinta saman nashi suka bar duniyar da suke suka koma tasu ta ma,aurata. A hakan taja shi falonta, nan suka bar duniyar mutane suka koma ta su. Daga nan ya shashance da san zuwa shashan uwargidansa.
Duk taga lokacin da Ramadan ke san binta laila ta hana. Bata sanya haka aranta ba, sabida ta fahimci manufar, domin tun ajiya ta gano laila bata son Ramadan ya ma leka wajenta, ita abin na bata mamaki ta yaya mutum da mijinsa a hana shi ganinsa. Wannan ai ba adalci bane, son zuciya ne kawai, wannan ai handama ne da babbakere, dan dai ana takamar
cewar amarya bata laifi. Runtse ido tai tana adduar Allah ya daidaita zamansu, dan ita tana jin ba zata iya wannan abunba, akan kishi ta hana mijinta zuwa inda abokiyar zamanta take, tana ganin kamar zalunci ne baza ta iya ba.
Zuba naman tai a flate ta zauna taci sosai ta Shanye kunun ayar da yasha madara da kayan kamshi, ta ajje ragowar naman a na’urar sanyi, daga bisani ta zauna taci gaba da karanta novel dinta, saboda lokacin ba wuta balle tai kallo. Babu dadewa akai kiran sallahr la’asar, ta mike tai alwala tai sallah tai adduointa ta shafa. Da hijabin da tai sallahr ta sauka kasa tai kitchen, ta duba inda take ajjiye kwai, dan hura
dan garwaashi, sai taga babu.
Tsayawa tai tana tunanin inda za ta samu, maigadi ke sayo mata, kuma yau tana da bukatarsa. Sai tayi tunanin zuwa gidan maman rauda ta amso. Shashin laila tayi tana tunanin Ramadan na ciki. Jin shiru ya sanya ta koma, tana jin kamar da alamun mutane aciki.
Sai ta zauna akan kujera, bata dade ba, sai ga ramadan nan ya fito, ya sanja shiga, sanye da jallabiya ruwan kasa da hula, hade da darduma zai je masallaci, laila na biye da shi ita ma ta canja shiga, ba wanda ta ganta dazu dasu ba. ldonsa ne ya sauka akanta. Sai yayi murmushi ya ce ” Ki min drink din dazu please.” “Tom kawai tace mai. ” Harya yi gaba sai tace “zauji ina da magana.” Sai tai dan gaba, ganin yanda laila tayi babakere a wajen. Shima sai ya bita suka fita can
wajen. Tace “Daman gidan maman rauda nake san shiga zan amso kwai.” ldonsa kafe kan bakinta, yanda take motsa sai hakan ya burgeshi. Laila na gefe a bakin kofa tana kallonsu Jerawa sukayi yana ta borin kunya “wai bata saukowa, duk ta mai da kanta gefe. Kallonsa tai tace “amma dai amatsayin maigida shugaba shine ke da alhakin duba matansa ko da, baya dakin wancen kuwa.”
Cikin fada ya shiga cewar ba wani nan ita ke san tsiro da wani abun. Sai kawai tai shiru. Dan ta san zai iya shuka mata tsiya inta tsawwala. Wani zai dauka kalaman kauna yake gaya mata nan kuwa fada yake.Nan ta kalleshi tana ayyana son zuciyarsa, ita ba tace ya manta da ita ba, sai shi zai s
hau fadar magana, haushi ya sa tai gaba tai hanyar gidan maman rauda, Suna Fita Haushi ya turnike laila. Haushi kamar ya kasheta. Domin ganin da tai musu a tsaye duk ta dauka wasu kalaman yake gaya ws ladifar. Lumshe ido tai tana jin wani irin tsanar zamanta da kishiya, a tsarin rayuwarta ba tada burin ace ta zauna ita da kishiya, tafi so ta zauna ita da mijinta ita kadai ba wata, ko farko ramadan ba ta san yana da aure ba, har sai da sonsa yayi mata kamun da ba zata iya rabuwa da shi ba, sai daga baya ya sanar mata. Wani irin kishin Ramadan take ji na shigarta, sosai ta tsani ta bude ido taga ladifa na ko kula shi. Tsaki tai ta juya domin bata da mafita, dole ta hakura saboda ita tazo ta tarar.
Da sallama ladifa ta shiga gidan maman rauda, tana tsakar gidan tana gyara salak, tace “uwargida ran gida in baki gida ya zama kango.” Dariya ladifa ta sanya ta ce “ita kuma amarya bata laifi kota kashe dan masu gida.” “Au! Haka zakice.”
Murmushi tai domin ta yi hakan ne dan bata so a sako mata zancen amarya, har a shiga wani babun kuma. Nan dai suka gaisa tace “ya hakuri kuma.”
“Hakuri akan me?.”
“Au baki san me nake nufi ba?ai yanzu dole sai hakurinki ya rubanyya, saboda za ki ga
abubuwan da zaki iyajin zuciyarki ma na tafasa.” Ladifa tace “gaskiya ki ka fada, dama kwai zaki bani.” “Ai ko kinci sa’a akwai.” Nan ta tashi ta zubo mata a leda, tana cewa sai na shigo ladifarta fita tana cewa “Allah yasa.” Laila na zaune a falon ladifa ta shiga, tace “laila ashe! kina zaune.” “Gani nan kam azaune kamar duniya.” Murmushi tai tace “nina hau sama, zan dan yi aiki.” “To,” tace tare da binta da harara. Tana hawa saman ta shiga aikace aikacenta, dan gobe ramadan ke hannunta, dole ta gyara, duk da cewa ma ba wani kura shashin nata yayi ba, saboda kullum tana gyara abinta, ita ba wani mararinsa take bama, sabida bata ranta da yayi, to amma ba zata tsaya tai sake ba, tana ganin dan zaki ya girmemataba Ta dade tana goge -goge wanda har shashin ramadan ta gyara fess dan bata san gobe komai ya kacame mata, shi,isa ta fara ragewa. Alokacin taji dawowar ramadan daga
masallacin. Kuma saukowa tai dan ta hura garwashi, adaidai lokacin ramadan ya fito cikin shirin fita da alama sauri ma yake, da wata takarda a hannu yana cewa “please ki dan saurara laila ba dadewa zan ba.” Haba Habeeby ta fada cikin wata iriyar murya. “Bafa zan tare a gunki ba, ke ko …..
Sai tai dan sauri ta rufe mai baki tare da kashe mai ido daya karka karasa, kaima kasan cewar baka gundurata, kasan karshen zancen, yaune fa end a garemu, dole na fara kewarka, ta fada tana mai dada kashe mai ido. Ladifa kuwa na kitchen tana kokari hura wuta, duk tanajinsu, sai ta dan tabe baki kawai. Tuno cewar ba ta da kankana da take san amfani da ita. Sai ta fita falon ta zauna gefen kujera. Tace “zaujina.” Sai ya maida kallonsa kanta yana gyara hularsa. “Ya dai babyna?.” “Yawwa dama kankana nake san ka tawo min da ita dan Allah.”
Wani lumshashshen kallo ya ke sakar mata, bai sani ba ko kewarta ke sanyawa indai ya ganta yakejin jikinsa a mace.
Ganin hakan yasa laila ta juyo da shi facing nata, tace “kawo na gyara maka hular .” Sunkuyar da kai ladifa tai tana wasa da bakin hijabinta. “Kin yi shiru baby, babba ko karama kike s0?.” Murmushi tai ta daga ido suka hadu da nasa, sai ta lumshe su tace “babba na keso, karfa
kamanta mijina.” Ta fada tare da mikewa. Tabe baki laila tai ta ce iyayi kawai a zuciyarta ta bishi a baya tana kwarkwasa. Ladifa ta bita da kallo tana dariya kasa-kasa‘ Ita a yanda ramadan ke wani kusheta bata da gaba da baya. Ta dauka zai Auro cikakkiyar mace full option kamar salma matar abdallah, wacce gaba da baya komai tubarkallah kamar ita ta dasawa kanta. Sai kuma ta ga sabanin hakan wacce tana ganin ko ita da bata da kiba jikinta yafi na lailar kyau. Ikon Allah tafada tajuya. Gama hura wutar, ya sanya ta haye sama ta dan saka turare, falon ya budade ta zauna tana hada hadin dilkarta. Bayan dawowarsa da dare ya kai mata kankanar har sama,ji yayi kamar karya fito, saboda missing din kamshin dakin ladifa da ya dade bai shaka ba. Allah ,Allah ya ke gobe tayi dan ladifa ta karbi girki.
Ganin ya nace a dakin ya sanya tace ya koma gurin amaryasa saboda tsaro.
Karfe goma na dare ta shafejikinta da hadin kurkum, lalle, kwai, hade da gishiri ta kwanta.
A bangare laila kuwa, ta hana Ramadan sakat adaren nan, saboda wai za tai missing nasa, kuma tasan inya koma dakin lad’ifa, ba zai kuma irin dadewar nan ba, sai dai kwana 2 kwana 2 In kun tuna, na gaya muku ramadan na da rauni sosai! Wajen ta shin sallahr asuba) To tunda laila ta tare ya rage zuwa masallaci da asuba,wanda dama ladifa ke dagewa yana zuwa, to da yake mutane kala-kalane ya sanya, ita gogar ba tashinsa take ba, sai gari ya dan fara fisha! suke tashi, a hakan sai ya tashi yake tashinta.
Tunanin da ladifa ke yi kenan, da asuba bayan ta tashi sallah ta murjejikinta da dilka
sosai! Tai wanka tai sallah, tun tana wankan take sanji ko zai fita taji tsit saboda bata jin
karar bude get yanzun, tun bayan zuwan laila gidan, dole ta san yanda za tai. Karfe takwas daidai ta tashi daga barcin data koma, da dan sauri tana ta’ajjibi, saboda
tasan yau zai koma aiki, kuma dole yaci breakfast kafin ya tafi
Da sauri ta yi kasa yana zaune kan kujera, gefe ga laila na hawaye zaune ajikinsa tana
cewa “hubbeey zanyi kewarka.” shi kuma yana lallashinta kan cewa ai yana nan,jibi zai dawo shashinta. Ganin saukowar ladifa ya sanya laila ta dan saki yaken murmushi, “mun tashi lafiya?.”
Lad’ifar ta amsa mata cikin sakin fuska. Ganin hakan ya sanya lailar tashi ta shiga shashenta.
Mikewa yayi dan haramar tafiya, “yace uwar bacci sai yanzu ko? gashi harna shirya baki koyi min break fast ba.” Dan jin ta bakinsa tace “Aina dauka amarya tai maka.” Duk da tasan cewa lailar ba tai girkin ba, amma dan jin me zai ce ya sanya ta fadi hakan. Murmushi ta danyi tare da shafar fuskarta da tafukan hannunta tace ” Ya dai zaujina me kake so nace da kai yanzu?.”
Numfashi ya sanya yana jin wani irin abu na yawo a sassan jikinsa. Abinda ta dalilinta kadai ya kejin abun. Kuma bai gane bs, har sai da yayi wannan aure.
“Yanzun nai maka mai sauki-sauki?.” “Ke rabani da sanyinki, har abada ke ai ba kya komai da hanzari, komai sai nayi dai magana ko.” Ya fada tare da kafeta da idanuwansa. Hmm kawai tace “Allah ya baka hakuri.” “Okey nina tafi tai mai rakiya ta dawo.
Falon ta dawo tana jin wani iri aranta. ‘Lalle ta yarda kishiya, dole mata suji tsoronta in dai masu karancin hakurine.” Ga shidai yanzu Ramadan dai kiri~kiri ya wani hau ta da fada. amma ita laila dan tana amarya ko shayi bata taba dafawa ba, kuma bai magana ba sai ita. “Allah ya kara mana hakuri,” ta fada.
Ragowar kazarta ta dumama ta cinyeta tas! Tare da shan zumarta.
Itako Iaila tana falonta tanajin duk duniyar tai mata zafi, dan wani irin damuwa take ciki, komawar Ramadan wajen ladifa, dan yau ji take kamar taje ta makure ladifar. Sai kawai ta koma daki, ta tsiri bacci, dan jiya batai sosai ba. Karfe biyar na yamma, ladifa ta cire kunshin da tai ja akafa da hannu, dan ta iya zana shi ya yi kyau sosai! yayi ja, da alama kan gobe yayi brown, abinka da kunshi akan farar kafa da hannu nan da nan ta haska. Tana gamawa ta shiga kichen ta dora tuwon shinkafa miyar agushi da zogale da naman rago. Wajen shida da rabi ta gama, sai tashin kamshi girkin yake, sannan tayi kunun aya me dadin sha da, sai ta hada da yin zobo, saboda duk ramadan ma abocin shansu ne. Tana gamawa ta zuba awarmer ta ajje a kitchen ta rufosh tai sama.
Ta gama wanka, wanda ta hada ruwan wankan da turare, ita kanta tasan cewa jikinta yayi silbi sosai! sabod ta dade tana gyara, ga kamshi ya zauna daram ajikinta. Tana cikin wankan taji dawowar Ramadan. Shi kuwa yana dawowa sama yayi ya shiga dakinsa dan yin wanka. Tana fitowa da yake, ta hada dan gamashinta a kaskon wuta ta zuba turarenta ta rufa, yana ta shiga fatarjikinta, ta dade sannan ta maida kaskon falo, kamshin turaren duk ya budade falon har dakin, nan ta zauna tai shafe shafe shafenta, ta mulka turarukanta masu matukar kamshi, ta hade cikin riga da siket na wani red din yadi irin mai kama jikinnan ya lafe a fatar mutum, duk ainihin surarjikinta tabayyana duk rashin kibarta amma sai da surarta suka bayyana,musamman kirjinta daya dan dada tasowa, ita kanta taji ta burge kanta, ta shafajan jambaki a bakinta, wanda tasan bakinta yana daya daga cikin abinda ke susuta ramadan, girarta mai cika ta taje sannan ta sanya kwallli yafito radau! ta shafa
powder ta yafa farin mayafl me santsi, da ratsin ja a gefe-gefensa.
A karshe ta farfesa turaren kaya. Ta sanya flat shoe fari, ita kanta tasan tayi kyau, ta burge sai dai mai hassada zai kasa yabata.
Kasan take kokarin saukowa dan taje ga maigidan nata. Zuciyarta ba jin dadi take ba, saboda irin abinda yayi mata,
Sanin cewa yanzu fa bada bane ya sanya ta saki ranta, sannu a hankali ta ratsa falonta ta
sauko kasan. Kan Iaila ta gani ta tsakanin kujeru tana jiran ya shigo dan ya fita masallaci,
sai daya tsaya ya kunna inji sabida dauke witar da akai, sannan ya karaso da darduma a
hannu. Da gudu Iaila ta tare shi. “Ashe har ka dawo habeeby ka fita masallaci ban sani ba.” “Saurarar dayarku zan yi ne?.”
A hankali take saukowa,nan fa ramadan ya kame yana dubanta tun daga sama, wani irin
canjawa yaga tayi mai, karasa saukowa tai tana tafiya cikin salon tata tafiyar.Harta karasa.
Laila ta kalleta sama da kasa ta tabe baki, domin wani tarin hassadane ya shige ta ganin tayi kyau sosai! k0 ita ta yaba, to ballantana kuma oga kwata-kwata, hannunta ta sanya ta
karbi dardumar. Sai yayi caraf! ya rike tafin hannunta, wani dumi yahi,ga taushi, ga kamshin da
ke shiga hancinsa.” Wani irin tsaki laila ta sanya. Domin ita a ganinta wulakanci ne ma ya sanya tai hakan. Rike ladifar yayi suka zauna akan kushin, cikin taushin murya tana “zaujina sannu da
hanya, dazu bansan ka dawo ba ina wanka.” Kamar wani faster ya dawo yana ta lumshe ido sai faman shafar sajen dake kawata mai
fuska yake. Bakinta yake taiwa duba, gashi duk ta shigejikinsa, domin dama yasan ita san jiki gareta. “Abinci ko wanka? Ta fada cikin wata iriyar murya. Jan dogon hancinta yayi. A hankali ya ce “kina can kina min kwalliya nai wankana.” Murmuahi tai Ta mike har mayafinta na dan sauka ta kafadarta, gashinta da yaji mitsi
mitsin kitso irin na ‘yan maiduguri ya bayyana. Laila ta kafa mata ido sanda ta mike “cabdi! sai fa na dage, ta fada a zuciyarta.
Ladifa ta dade da barin wajen, amma bai dawo daidai ba, laita ko taci ka tai fam! Saura kiris ta fashe. Bangarenta ya juya ya kalleta “Amaryata ya gidan?.” “Lafiya, ai naga duk ka wani sususu ce ganin yarinyar can.” “To laifl ne? ni da matata, ke kin manta ne?.” Sai tayi murmushi, hmm habebey kenan! yau zan kwanan gauranci.” dariya kawai yayi. Adaidai lokacin ta dawo da kwanukan ta ajiye, nan ta zuba mai tace “laila kizo muci mu biyu ko.” Wani banzan kallo tai mata ta kasa tana danna waya a zuciyarta tace “ni ban san kinibibi’ a fili tace “no barshi na gode.”
“Haba dai har dake na hada ai an zama daya.”
Tana magana idon ramadan na kanta, hannunsa daya na gefen jikinta yana faman shafa,ji yake zuciyarsa sai harbawa take, shi’isa har ya kasa tankawa a maganar tasu yace lailar ta sauko su ci, amma hakan ya gagara,ya kai makura, abinda ya keji ko laila da take amarya baya jin hakan, bai sani ba ko dan kewarta tayi mai yawa ne, zumudi kawai ya ke kawai ya ganshi daga shi sai ita, sai yake ga kamar ma ita ce amaryar, musamman ganin yanda take wani daukan ido, fatarta kallo daya yayi mata yasan ta sake taushi, gashi tunda ta zauna kamshinta ya cika wajen. Ji yayi ma abincin dukya fice mai a rai, sai ladifarsa yake wa marari, ga shi sai dada shigewa jikinsa take tana dada bashi assignment.
Gyara zamanta tai ta dan matsa daga jikin nasa, saboda su samu suci, dan ta kula fatsar da tajefe ta kamo kifi da yawa, nan ta shiga bashi abaki, itama tana ci suna hira, kadan kadan. “Oya amaryata zo muci mana, meye na komawa gefe?!‘
Wani irin gumi ne laila taji tana hadawa duk da cewa akwai fanka da ac a falon. Wani irin abu takeji ya tokare wuyanta. Nan ta saki tsaki ta tashi ta shige shashinta ta bango kofa. Sam! Ramadan baiji dadin abinda tai ba, sai yayi kwafa. Sai da suka koshi sannan ta debe kwanunkan, tai kitchen, ta zuba wani abincin a wani mazubin, ta yi shashin laila, Ramadan ya bita da ido, dukjikinsa a mace ko motsai ya kasa yi. Da sallama ta shiga wajen laila, tana kwanace kam kujera three seater tana kallon wani film the habit tace “laila ga abincin nan na ga kinki ci tare damu.”
Dan tabe baki tai tace “Thanks.”
Falon ta koma tace “ni zauji nayi sama zanyi sallah.”
Mikewa yayi yabi ta abaya, ita ko tana sane tai nata falon ta rufe kofar. Murmushi yayi ya shiga nasa dakin dan ganin lad’ifar da yayi, ya sanya dole saiya sake wanka kafin yayi sallahr isha’i, Oh! My god! Ya fada tare da shiga toilet d’in. Haka yayi ya saka jallabiya ya fice dan yo sallahr isha’i. Zamanta tai a falonta tana murmushi, sai kuma ta mike ta shiga daki dan yin tata sallar.
Sai wajen tara ya dawo, lokacin gidan yayi tsit! falon yayi din dim, kowacce na shashinta, direct saman ya hau. Tana kwance tana kallon arewaz4 ya sameta, zama yayi kusa da ita, sai ta dan juya, ya kalleta tare da janyota nasajikin, sai ta dan kwace ahankali yace “ya haka?.” Cikin rawar murya tace “Yanzu wannan tsarin daka gabatar sai naga bai kyau ba, tun da ka tare da amarya ba kazo shashina ba, koyaushe sai text msg, wallahi banji dadi ba, sai naga kamar ba kama damu dani ba, kaifa zaka zama shugaba, bai kamata afara da haka ba.” “Wait! Ladifa. Lokacinta ne fa! ba nasan fa kishi, ke da kikai naki lokacin waya takura miki.” “Au! Takura muku nai ma, bayan kai ka shareni, Sai ta sanya kuka sosai ta tashi tai daki, runtse ido yayi yace “rigima.” Sai ya mike ya bita dakin, zama yayi a gefen gadon ya dago da ita yace. “look at me ladifa, bana san yawan korafi, bana son ki shigo da wani abin na daban fa.. ” Kallonsa tai ta kwace jikinta tajuyar da kai ta ci gaba da hawaye. “ls okay zan gyara amma kibi abinda nace.”
“Ni baka gane abinda ma nake nufl bane, ba korafi bane, kawai nace bai kamata bane, yanzu kaga yau ne ka dawo sashina, sai kaje ku yi sallama da amarya, duk wacce ba a wajenta kake ba, to za kaje wajenta safe da dare ka duba ta, saboda zaman laflya.”
Tana magana idonsa na kan bakinta dake matukar burgeshi. A hankali ya juyo da ita ya tallabo fuskarta ya hade bakinsu waje daya, ji yayi kamar ana saukarwa jikinsa da ni’irma, nanfa ya rikice mata,jikinsa har wani rawa yake. Lulawa duniyar masoya sukai. Sosai suke nuna kewar junansu a aikace.
Da kyar ya kyaleta. Ya kalleta da limsassun idonsa da suka kankance saboda halin da yake ciki,yace i miss you so much lad’ifa.” Ya fada yana mai san shashantar da maganarta. “Numfashi taja cike da shauki tace “Me to zaujina,” dan Allah kaje kai mata sallama,”ta kafa mai ido, numfashi ya furzar tare da murmushi ya fita yana jinsa daban, tabbas dadin da yakeji in yana kissing din ladifa baya musaltuwa.
Musamman da yayi kewarta din nan. Ita kuwa tayi hakan ne saboda duk abinda ya faru itama tana ciki, domin idan tai hakan kamar yiwa kaine, dan ba zata so ace yana shashin wata ba, ya shareta, dan bata ji dadin yanda sukai mata ba, Nan ta garkame falonta tai wucewarta daki ta canja kaya ta sanya sleeping dress me kyau ta kuma getta kanta sosai! tayi kwanciyarta tayi addua ta shafa . Shi kuwa da yaje bangaren laila ma korafi ta shiga yi mai, kan yau rana daya ya fara
mantawa da ita. Hade fuska yayi. “Mai ya sanya dazu kika tashi kika banko kofa? kan kawai ance kici abinci.” “Banga dama bane.” “To daga yau bana son wannan halayyar.” “Sai yanzu na gane bayan matarka ka kebi, dole fa ra’ayina zanbi.” “Ba zamu shirya dake ba kenan, in har kika ce za kina musu dani, kuma kina kin bin
abinda nace.” sannan ta dan tsorata dashi , kan cewa za tayi abinda yake so din.
Barin shashin yayi yana mamakin halayyar mata ‘oh dama haka mata fiya da daya suke (yanzu ma aka soma Ramadan)
Har ya karasa kofar dakin ladifar, Turus! ya tsaya yaji ta rufe kofar, ya dan buga yaji tsit! itako tanajinsa don ba zata bude ba sai taja zarenta. Tsaki ya yi ya bar wajen, ya koma nasa dakinsa ya sake wanka yayi su brush ya dawo ya shafa mansa da turaren maza, ya yi shirin kwanciya, Sai ya kasa bacci, ya san tayi hakan ne dan kar ya koma. Tashi yayi ya zauna, Yanajin ba zai iya bacci ba ba tare da yajita a tare da shi ba, sai ya buga wayarta, tana ring tana ji taki dauka, sau wajen uku sai ya tura mata massage, tanaji ta share. Dan wani irin haushi ta keji, sai ma yanzu ya san da zamanta. Wajen awa daya ta kumajin dirar msg saita dan tashi zaune. Ta duba wayar taga yace
“ladifa kinsan cewa yau wajen wata daya kenan bamu hadu ba ko, kizo na baki umarni a matsayina na mijinki.”
Ajje wayartai. Sai kuma ya bata tausayi itama din kawai karfin hali take, dan tunda taci hade haden ya karima takejin ba daidai ba.
Runtse ido tai tuno nasihar yaya karima tace. “Auta karki bari kishi da shaidan su janye zuciyarki, har in mijinki ya dawo karki hanashi kanki., Domin wasu matan da yawa hakan na faruwa, sai kaga an bige da sa’insa saboda ta ki bashi had’in kai saboda kishin yayi amarya. To anan idan kikai sake har ya koma koma gun amarya, kin kade, dan ya samu mafaka kenan, itama inta gane za ta raina ki, kuma da sannu zata mamaye komai, ke kina gefe
kishi ya gama turnukeki. Sai kiji mace na fadin ai miji ya juya mata baya. Saboda ya yi Amarya.
ldan yazo ki amshi abinki, nuna mai kinyi kewarsa, bashi salonki, anan zaki karawa kanki wata martabar.
Gama tunanin yasa ta tashi ta yo wanka da brush ta fito ta dad’ma mulke jikinta da turaren da karima ta bata, ta kuma gyarawa ta saka tom-tom abaki ta fita, a hankali take takawa,
kofar tasa a bude, ta shiga yana kwance hannunsa da waya yana latsawa. Ya daga kai suka had’a ido ta kauda kai, tsam! ya mike ya fuskance ta yace “ni kike guda ko baby.”?.” “Meye lefina ne? ai ka sani, ta fad’a idonta na son kawo ruwa. Kyakkyawar fuskarta ya shafa “na amshi lefina zan gyara na kwatanta adalci.” Cikin sanyinta ta matsa gefen gadon ya bita da ido, komai ahankali take yinsa cikin salon dake burgeshi. Wani murmushi kawai yayi ya shafi keyarsa. ya kashe kwan fitilar ya barta bed side, ya haye gadon.
Ganin yanda take wani dan babbasarwa hakan yasa ya shiga lallasshi “wallahi i need you
ladifata, please ki ce wani abun”, ya fada yana mai shinshina wuyanta. ltako mamaki take domin kalmoninsa, kamar bashi ne mai amarya ba, tayi mamakin wannan zumudin da yake akanta, kalmomin da yake gaya mata yau ta dade da daina jinsu, ‘tun tana amarya. Sai idonta ya tara ruwa domin tasan cewa tabbas adduarta ba zata fadi k’asa banza ba. Kuma ta san cewa ba komai ke dawwama ba dama, yau fari gobe baki. Lumshe ido tai ta kalleshi tace “nima ina kaunarka zaunjina, inajinka har raina. Nima ina muradinka adaidai wannan lokacin.”
Mood din yayi masa dadi fa, nan fa ya kuma hade bakinsu ya shiga aika mata da sako kala kala, wanda ya sanya suka fara fita hayyacinsu, da yake itama cikin kewartasa take, ta bada hadin kai suka shiga faranta ran juna, tare da lulawa cikin duniyar da ramadan yaji kamar bai taba zuwa ba, haka …..
Hmm masoya