NAYI GUDUN GARA CHAPTER 18

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 18
Laila har lokacin daya kama kusan ka’arfe 11 bata daura damarar bacci ba, kaikawo kawai take a tsakar falonta, tsabar kishin dake cinta arai, tsaki kawai take saki. Zama tai ta dafe kai domin tana bala’in kishin Ramadan, dan ayanda taga ya wani rikice akan ladifa, tasan dole ya manta da ita a wannan daren, runtse ido, tai sai ga hawaye. 
Shaaaa Shi kuwa oga ramadan, sumbatu yake ta kwasa, dukya birkice sai sakar mata zafafan kalamai yake masu nauyi, saboda yaji shi a duniyar da yaji ta canja mai, kuma yaji bayi ita. 
Bayan komai ya lafa. Yana gefenta sai kallonta yake, idonta a lumshe ko hannunta ba ta iya dagawa saboda tsabar gajiya. Rungumeta yayi tsam! Tsam! Ajikinsa, yana sakin ajiyar zuciya,sai shafa gashinta yake yana maijin wani irin nishadi. Tashi muyi wanka babyna,” ya fada mata adaidai kunnuwanta, tare da sakar mata kiss agefen kumatunta. 
A lumshe ta bude idanuwanta tai murmushi, ta sanya hannunta ta shafi sajensa. “bacci na keji zaujina, sai da asuba nayu” Ta fada cikin sanyin murya tare da rufe idon. Don sau tari suna gama gabatar da sunna take zuwa ta tsarkake jikinta. Amma yau dai gajiya ta saukar mata da yawa. 
Murmushi yayi ya mike ya shige toilet din yayi wanka ya fito, ya kwanta tare da shigar da ita jikinsa yana jin wani irin nishadi, danji yake kamar an kawar mai dala da gauron dutse akansa. Asuba Kiran sallahr asuba ne ya tasheta, sai taji saukin gajiyar, ta juya idonta ta kalli mijin nata, sai ta saki murmushi ta kuramai ido tana lumshe ido, tare da tuno karon battar da sukai jiya, sonsa ne taji ya kuma mamaye zuciyarta, sai ta kejin kamar ita kadai gareshi. Nan ta tashi tai wanka ta dauro alwala, sannan ta tashe shi dan yaje masallaci. Dan yatsine fuska yayi, yace “baby har asubar ta yine?.” Tace “eh man.” 
Da rangaji ya mike ya yi toilet din, yana jin ba zai fita ba anan zai sallahr sa, watsa ruwa yayi sannan yayi brush da alwala ya fito ya sanya jallabiya, ganin alamar anan zai, cikin taushin murya tace “zaujina masallaci.” ‘ 
“Baby sai naje kenan ko?.” Dariyar takaici tai tace “ai shi ne dacewa dai.” Nanta mikamai darduma,ya fita sai ta tada sallahr ta. 
Bayan ta idar. Ta zauna tanajan carbi , ta dade tana jan abinta. Tare da yin adduoin samun zama Iafiya da maigidanta da abokiyar zamanta. Tana niyyar tashi, sai gashi nan ya dawo. Ajje dardumar yai ya haye gadon. 
Ita kuma ta mike ta cire hijab, ta ninke zanin sallahrta, ta hau gadon tana dan hamma, idonsa akanta.Tai kwanciyarta, kamshin jikinta ya dan daki hancinsa, dan bayan fitowarta daga wankan sai data mutsikka turarenta, 
Gefen wuyanta ya shafa, wani irin numfashi yaja alokaci daya, yanajin son ya kuma komawa duniyarta,juyowa tai ta fuskance shi tare da lumshe mai idonta, tace “mai kake 
sone ruhina?.” 
Abinda ya keji yana yawo ajikinsa, yasa ya kasa amsa mata, sai da yajawota jikinsa ya shiga murzarta sannan yace “ke nake so babyna.” 
Cikin kwanciyar hankali suka kuma komawa ruwa, a wannan lokacin ma Ramadan sunbatun ya shiga yi, duk ladifa ta rikitashi. Sai kusan 7 suka dawo hayyacinsu. Babu batun komawa bacci, sai ma wanka da suka shiga su kayi.Suna fitowa ta taimaka mai da shafa mai, sannan ta fice zuwa nata dakin, ta zira doguwar riga kawai ta fesa turare. Ta fita da sauri dan yin abin karin safe. Bayan ya shiirya ya sauka kasan, wajen laila ya shiga, tana kwance tana shakar bacci ya dan bubbuga ta, ta bude ido jajawur! sai tajuyar da kai, yace “kinyi ko sallah?.” Tasan ba taiba, sabida rashin samun baccin da batai jiya da wuri ba na kishin data sanya a ranta, kawai sai tace mai tayi. Yace “yawwa kin kwana lafiya?” ta amsa tana jin wani irin kishi ganin yanda yake cikin annuri. “Office zan tafi yanzu.” 
To sai ka dawo,“ ta fada ta koma ta kwanta, yana fita ta mike da sauri ta shiga toilet ta yi alwala dan yin sallahr. 
Shayi mai kayan kamshi da na’a na’a ta dafa, ta soya mai kwai ta hada dasu bread duk takai kan dining, lokacin bakwai har da rabi. Karasowa yayi ya zauna, tace “fatan kayan breakfast din sunyi, kasan yau ban Fito da wuri ba.” Daga idonsa yayi ya kafa mata su, saita sunkwi da kai, dan kunyarsa taji tanaji, kanta asunkuye ta hada mai shayin ta kaimai gabansa, ta ajje sai ya rike hannunta yana matsawa, idonsa akanta, dan shi kam yana mamaki danjinta  yayi kamar wata sabuwa, shi kadai yasan dadin da ya kwasa agun ladifarsa, ga salonta ya matukar burgeshi. 
Itako sai dan sunkwi da kai take saboda kunyarsa, dan jiyan nan ita kanta tasan ta zuba rashin kunya, kan irin salo salon da tai ma zaujin nata. Haka kawai ta ji tanajin kunyarsa, “Kalli lokaci dearna, karka fa makara?.” Numfashi yaja, “ke din ce ai duk kinsa na shiga wani yanayi.” Murmushi ta sanya ta mike ta ce “bari na dan gyara kitchen, kaga sai kayi breakfast din a 
nutse.” Bai ce komai ba sai binta da kallo da yayi. Adaidai lokacin laila ta fito sanye da rigar bacci mai dan kauri iya kasan gwiwarta, da hula akanta, ta zauna ta kalleshi yana shan shayin ta ce “habeeby baka tafi ba ashe?.” 
Kallonta yayi yace “kinsan sai na karya nake tafiya.” Sai ta gyara zama suna dan hira. 
Lokacin ladifaa ta kuma fitowa, kamshin da ya zauna ajikinta ne ya sanya laila ta jiyo kamshin sai ta dan juya ta kalleta, ta hade rai tajuyar da kai. Ah! Laila sannu da fitowa, fatan kin tashi lfya.“ “Lafiya,” ta fada fuska atamke, dan wani mugun haushin ladifar takeji. 
Ramadan kuwa idonsa na kan ladifa, yana wani irin smiling din da sai ka kalleshi sosai! za kasan yanayi. Tun laila ba ta gane kalar kallon da yake wa lad’ifa ba, harta gano, ganin hakan ya sanya 
ta danyi tafi kamar na wasa, sai alokacin ya kula sai yaja numfashi yace “ni zan wuce.” Ladifa Tace “har ka koshi?.” Wani irin kallon yayi ya ce mata “na koshi ba kadan ba.” Murmushi tai dan ta fahimci maganarta sa tace “to muje nai rakiya.” Ya kalli laila yace “Amaryata sai na dawo.” 
Murgud’a baki tai tajuyar da kai gefe. Yake mai kama da dariya ya sanya. “Ya fita yana girmama rigimar lailarsa aransa. Dan duk ya fahimci kishin da take yi. Ladifa kuwa, bayan ta dawo daga rakiyar, sai ta koma samanta bayan ta karya. 
Sai wajen sha-biyu ta tashi daga baccin, shima ringing din wayarta ne ya tasheta. Sunan ramadan ta gani a saman screen, saita jinjina kai tana mamakin kiransa awannan 
lokacin,dan bai saba kiran nata ba. Cikin taushin murya tace “barka da rana zauji.” 
Yana kan kujera yayi baya da ita, ya lumshe ido muryarta tana ratsa shi, yace “babyna ya gidan?” Sai ta sanya murmushi tace “alhamdlh.” “Me kike yanzu?.””Ba komai bacci ma nake wayarka ta tashe ni, juya kujerar yayi yace “ko nazo mukarasa tare?.” Dariya ta sanya “kai dake aiki,hmm! kai zamanka.” 
“Ba abin mamaki bane ki ganni yanzu, dan kewarki ta dameni. sosai nake kuma son jin duminki.” Kasa magana tai saboda yanda takeji a zuciyarta da gangar jikinta, sai daya kuma magana tace “Duk yanda ka zartar, so ni taka ce zaujina, babu haufi acikin maganarka, dan fin hakan ma zaka samu.” Allah ko?.” “Tabbas! amma yafi ka karasa aikinka.” “Hmmm to sai na dawo, ki tana dar min sweat.” Tai murmushi sukai sallama. Ta rike wayartana murmushi, abinda take so kenan ga ramadan tun aurenta dashi, amma bata samu ba sai yanzu, Addu’a ta shiga yi kan Allah ya sanya yazarce a hakan, dan ita sai tace ta wannan bangare alheri ma aurensa da laila ya zame mata. 
Saukowa tai daga gadon, sai taji alamar dumi ajikinta, sai taji kamar ruwa yana bin gefen kafarta, ta duba sai ta sanya dariya har dasu tafa hannu “oh! Allah mai girma,” ashe! har ta shiga wannan yanayi daga waya. Saita kuma sakin murmushi, domin tasan gyaran da tasha ne, nan taji ta dada girmama ya karima a ranta. Da zumudi ta kirawota, karimar ta dauka tace “Autarmu.” 
Yayata ta kaina, ina wuni?.” suka gaisa tace “yaya nagode Allah ya saka da alheri ya biya miki bukatunki.” “Duk me ya canyo haka auta?.” 
Sai ta zauna gefen gadon tace “wallahi hidimar da kikai dani nakewa godiya, abubuwan ne da kika bani fa sosai naji dadinsu.” Dariya ya karima tai tace “lalle autarmu, au dama su kike magana, ai nasan da wuya kici kazar nan, da wannan zumar baki gode mun ba domin tana da kyau sosai, in dai hadin ya karbeki za kiji dadinsa sosai yake ciko da mace ya kara mata ni’ima.” 
“Kimin wata to yayata.” 
“Ahhh ita idan akai tana dadewa, ta kan kai wata uku k0 shida ajiki, ba tare da kinsha wani nau’in kayan kara niema ba, Ki daici gaba da shan kayan fruit sosai. 
Sannan ni abinda zan ta nusar dake, dan Allah karki bari zuciya ta sanya ki cuci kishiyarki, inason ki dauketa da zuciya daya kinji koda ita akwai wani abu a ranta to Allah ba zai bata tasiri ba. 
Kin dai ga yanda hajiya sukai zaman amana da mama uwa ko kafin ta rasu, kin san dai kamar ba kishiyoyi ba, to nasan kinsan duk kin san komai, to dole sai ana tunatar miki saboda kishi ba abinda ba ya sawa. Ko da kin kula ita kishiyartaki bata da kirki, ke dai karki mata rashin kirkin, kuma ki ta addu’a kinji. Da sannu wataran komai zai wuce.Dan za ki ga wasu kishiyoyin saboda tsabar kishi ba sa magana ajunansu, basu san cewa wannan duk ba dabia mai kyau bace, koda kishiyarki ba tai miki maganaba ke kiyi mata, domin kece da samun ladan sallama. Sannan Ki rik’e mijinki ki kyautata mai, kiyi mai ladabi da biyayya. Saboda Aljannarki na tafin kafarsa. Saboda wallahi duk matar da ba tabi mijinta ba. Allah sai ya kama ta. Ni kaina idan ina tunatar dake toji nake kamar kaina nake dad’a tunatarwa. Wannan shi ne soyayyata ta agareki a matsayina na yar uwarki.” Tsoron Allah ne ta dadaji ya shige ta, cikin sanyin murya tace “ya karima wallahi “U are the best sister in this world. Insha Allahu zan amfani da nasiharki, na gode.“ Nan sukai sallama, ta shiga bandaki dan gyarajikinta. 
Bayan fitowarta taji yunwa tana sasukarta. Sai ta sauka ta dora taliya, ta zauna a falon kasan kafin ta karasa. 
Laila ce ta fito cikin rigar baccinta ta tun ta safe, ta dora a saman rigar, hannunta rike da waya, tana ganin ladifa sai ta canja akalar maganar. “Ina gaya miki Asiya, wallahi idan kinga yanda nake shan riritawa wajen angona sai kin sha mamaki. Jiya k0 da zai bar shashina, muna zaune a daki duk fitowar maganarsa dayan biyu, sai ya ce “zanyi missing dinki laila, wallahi har tausayi yaban.” 
Sai ta dan sa ci kallon ladifa dake dan danna tata wayar. 
Ta juya tare da zama kan kushin din taci gaba “yo daman ai buyagi ne ai, ai idan ki kaga miji ya sake aure to, a binciki matar, sosai angona ke yabani yana cewa zuwana gidan nan yaji canji.” 
Daga can asiyar tai magana, sai lailar ta sanya Dariya ta ce “Allah ko to sai kinzo.” Ta kashe wayar zuciyarta wasai, koba komai ta aika sako. Ta kuma satar kallon ladifa taga yanda fuskarta za tai, sai taga bata wani canja ba. 
Duk da cewar ladifar taji mai tace sai ta kalleta tace “laila ya gajiya?.” “Gajiya sai ke ladifa.” Ta fad’a cikin muryar shakiyanci. 
Lad’ifar bata kuma cewa komai ba, ta mike tai kitchen, laila ta kalleta azuciyarta tace ‘yar iyayi nasan maganata ta shige ki.‘ Taliyar ta sauke ta tace ta,ta kuma daurayeta da ruwan zafl, ta barta ta tsane,sannan ta dauko kwanon maigadi ta zuba mai ta fito ta kai kofar falon gaba ta ajje tajuyo. 
Ta zubo musu ita da laila ta ajje tace “muci abinci laila.” Juyar da kai tayi tace akoshe nake.” “Ni kuma yayi min yawa, dan har dake na zubo, ina zuwa.” Sai ta mike ta rage wajen farar daba miya, ta zuba a wani mazubin ta kara wata taliyar, ta zuba miya ta sanya cokali ta kaiwa laila “to gashi dai naki.” Ta rufe kitchen din ta kalleta “ni nayi sama laila.” “To ta fada ciki-ciki, abincin ta kalla kamshin miyar ya dan dake ta, sai ta ji tana son cin abincin, dan ita babu abinda ta girka, saboda kiwuya dauka tai tayi nata shashin, ta zauna tana ci tana yatsina kamar ladifar ce a wajen. 
Yau ma tarba me kyau ramadan ya samu daga wajen ladifar, ya tawo da ledoji biyu a hannunsa. Laila bata fito ba alokacin, sai ladifa ke ta kaikawo wajen kula da maigidan, sai data tabbatar ya ci abincin sannan ta zauna ta shige jikin abinta suna kallo. 
Alokacin laila ta fito tayi wanka tana ta kamshinta itama, sai alokacin ya tuna da 
ledar da ya shigo dasu. 
“Babyna daukomin ledojin kan dining din can, na manta ma dasu, tashi tai ta dauko ta 
tsugunna ta ajje ta koma ta lafe ajikinsa. Saboda tsabar haushin data bawa laila ya sanya bata san sanda maganarta fito ba tace “waike ladifa mage ce ne? kullum bakya gajiya, bawan Allah na zaune kita nanukarsa. Ta fada da sakin tsaki. 
Duk sai suka kalleta, ladifa ta dan tashi dan ita har ga Allah mantawa take yi fa ashe basu kadai bane yanzu, domin ta riga ta saba tunkan zuwan lailan, sai tace “menene to ba mijina bane, ko haramun nayi? haka nan nake ba wai yau na sababa, dan tun kafin zuwanki.” “To ai yanzu sai ki bari, dan ba zan lamunta ba.Tunda yanzu bake kadai bace.” Rike baki ladifa tai da mamakin karfin halin lailar, ta ce “to sannu, tunda ke kika ajiye ni, naga ai ba ranar girkinki ba ne.” Tsaki lailar ta sanya tace “daga baya kenan.” Dariya ladifar tayi tace “Allah ya huci zuciyar hakima.” 
Ramadan dake sauraronsu, shi abin ma dariya ya bashi, sai ya dago ya kallesu yace “ba nason shirme fa, baruwan wani da abinda wani yayi, kowa yayi abinda yaga yafi mai a zauna lafiya atoh!.” Au hakama za kace ramadan, ai wannan salon wulakanci ne wallahi.” 
“Kinga laila, dan Allahi ki bar maganar nan, tunda ita tayi shin kema kiyi mana, nijawo min ledar.” Cikin hade rai taja mai gabansa. Ledoji biyu ne manya, ya kallesu yace kowacce ta dauka daya, sai kowacce ta dau na gabanta. ‘ 
Duk sai suka bude ledar, wani lace ne mai tsada da kyau hade fa sarka fashion, sai 
mayafinsa. Na ladifa yellow ne da digon blue ajiki, ita kuma na laila red ne mai adon baki. “Kai masha Allah, zauji munfa gode.” cewar ladifa nata murna,tana kuma cewa “amma fa ka iya zabe, kowanne bana yarwa”, ya kalleta “wallahi kawai abokina ne ya kai office, duk ya sanya muka siya ba niyyya.” Laila sai ta ajje nata tace “ni gaskiya na hannun ladifa nake so, dan kaga ita fara ce zai fi mata, wannan ni be mun ba.” 
Sai ya kalleta “ya haka wai laila? ba kowa dauka ya yi ba, kinga bana son tashin hankali.” “Habiby daman na gane da biyu kai hakan to ba naso.” Girgiza kai kawai ladifa tayi tace “karbi wannan din.” 
Sai ko ta saka hannu ta amshe. Ladifar kuma ta dau na laila tace “wallahi ni nafi ganin kyan wannan ma.” 
Tamau! ramadan ya hade fuska, dan baiji dad’in halin da lailan ta nuna ba, ko sake kallon shashinta bai ba, sai data dau kayan nata ta shige daki, ya bita da kalllo ya girgiza kai. Ganin yanda ransa ya baci, ya sanya ladifa ta maida hankalinta kansa ,suka haye saman, sam! Baiji dadin abinda lailarta yiba, sai sakin tsaki yake a hankali. Domin ba yanda za ai 
ya gayawa laila magana a karon farko tayi abinda ya ce, sai ta tanka. Har lokacin kwanciya yayi suka kwanta bai koma daidai ba. 
“Tofah ladifa tace saboda tasan ogan nata akwai rike abu, in bai mai ba ,dan lefin ma zai iya shafarta. Suna kwance a hankali ta matsa kusa dashi ta fara Kissing dinsa ta kota’ina, nan da nan ya maida hankalinsa,ta mantar da shi duk bacin ransa,sun sha love ma aranar, sosai! wanda ladifa ta kula ramadan yana enjoyed sosai! kamar jiyan ma, hakan yasha zuba mata sumbatu, har da su alkawarurruka.Yana cewa baby na baki kaina,baby zan sai miki gida,karki barni, wallahi i love you.😁😁  (Hhhhh su Ramadan kenan) Sai bakwai daidai ya fito, saboda ya kuma maimaita irintajiya. 
Laila na falo ta cika tai fam! Yana saukowa ta mike ta tare shi, tace “sai ma yanzu k0? Ga shi can na hada ma break.” Shi kuwa basar da ita ya shiga yi, dan har lokacin yana jin haushin abinda tai. Kuma magana ta yiya kalleta “look laila, ki rabu dani please sauri nake.” ’ Ya fita ko kallonta bai sake ba. 
Sai tabi shi da kallo baki sake. Kwafa tai tace “zaka dawo ne, tunda yau a wajena kake. Ai makirar can ta gama kulla maka ka dauke,” ta sanya tsaki ta koma. 
Haka rayuwarsu taci gaba da wakana, domin ramadan ya riga da ya gane da bambanci, dan yafi samun tarairaya da farin-ciki , annashuwa har idan yana wajen ladifa, saboda a wajenta yake sauke duk wani gammo daya dauko, duk da cewar itama lailar yana samun nutsuwa a wajenta, amma gamsuwa da nutsuwa hade da nishadi duk yafi samu wajen ladifa. 
Saturday 10:am Ladifa na tsaye gaban mota, dan zasu ne gidan abokin ramadan, matarsa ta haihu zasu barka. Sanye ta ke cikin shigar atampha mai ratsin yellow and red, ta yafa mayafi yellow, kafarta sanye da dogon takalmi mai tsini kalar red, sai red jaka, ta kafa d’aurin kai da ya k’awata fuskarta, fuskar nan ta sha powder da white lips sai kwalli data zirara a idonta ita kwalliyarta kenan simple, amma ta fidda wani sihirtaccen kyau, sai tashin kamshi take, wanda sai ka matsajikinta za kajishi. Adaidai lokacin laila ta fito itama cikin wani dark blue lece, ta dora farin mayafi da farin takalmi sai bluejaka mai ratsin fari, fuskar nan tasha fentin makeup sosai sai walwali take har dasu sanya gashin ido . Bakin nan yasha pink jambaki, ita ma tayi kyau sosai. Alokacin Ramadan ya fito yace su shiga su tafi, ladifa na shirin zama agaban motar, laila ta matsar da ita ta shige gaban tai fuska. Duk abinda suke idon ramadan na kai. Sai ya kauda kai yana dariya, ladifa tace “amma kinsan ranar girkin mutum shine da gaban mota k0.” “Bansan da wannan ba, dan haka keta jawa.” Ta fada tana wani daga ido sama. Kallonta Ramadan yai yace “kinyi adalci kenan?.” Saita juyar da kai. Juyawa yayi ya maida idonsa kan ladifa yace “baby shiga bayan kawai.” Tace mai to kawai, ta bud’e bayan ta shige. Tunani ta shiga, dan ta tuna ranar da zasu gidan hajiyarsa, lailar ke da girki dan har lad’ifar ta zauna agaba, saboda masifa saida ta sanya ta fito, tace ranar girkinta ne ita ya kamata ta zauna. 
Amma dan tsabar son rai tai wannan bakin halin. Sai tai d’an tsaki ta jingina da kujerar bayan, dan abin sai bai wani dameta ba, dan da ai ba hawa ma motar take ba, sai dai ta hau ta haya, yanzun ma tasan saboda bakin mutane ne ace mata biyu yana kyashin kaisu unguwa a motarsa. ‘ Sun fara tafiya sai hira suke shi da lailar sai zuba iyayi ake. 
Shi ko Ramadan ta mirrow na gaba ya hasko lad’ifa tana kallon titi, sai ta dan daga kai ta kalli gefenta sai ta sunkwi da kai, hannunsa ya sanya yana shafar hab’arsa, ya dan turo hularsa gaban goshi, sai kallonta yake yana murmushi domin man leb’an da ta sanya bakinta, in banda kyalli ba abinda yake,ji yake kamar yajishi a gefenta yana …… 
Magana laila tai mai sai yajuya ya kalleta, tace “please in mun dawo zan sai abu a kantin can,” yace “to zan tsaya Amaryata.” Wani dad’i ta keji, sbd da ita yake hira. Komar da idonsa yayi kan ladifar, yace “baby” 
Sai ta dago suka hada ido ta mudubi, “please baby a dan rage wannan man bakin, in so samu ne ma a gogeshi duka.” Ya fada yana mai dada kallonta danji yayi yana kishin wani ya kalleta. Da sauri laila ta juyo ta kalleta. Sai Ta juya tana dan dariya, dan bata gano cewar wai dan kyan da ya yiwa ramadan ne yasa yace hakan ba. Kuma kallon mudubin tayi suka had’a ido, sai ya dan mata alamar kiss da hannunsa irin na turawa, wanda alokacin laila tana kallon waje. Ladifarta gane abinda yake nufi, sai tai murmushi tare da sunkwi da kai ta rage man daidai 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE