NAYI GUDUN GARA CHAPTER 19NA

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 19
Bayan gama gage man leban, sai ta daga kai ahankali ta kalli mudubin, tai ido hud’u da shi sai yayi murmushi, yajijina kai alamar yayi. Sai ta jingina da bayan kujerar, tana masa wani irin kallo da manyan idonta. Wanda ya kejin wani irin feelings nata na tashi a hankali. Adaidai lokacin laila ta waigo za tai mai magana, tai arba da yanda idonsa ke kallon titi yana kuma kallon mudubi, yana sakin murmushi. Juyawa bayan tai taga ladifa kanta jingine da kujerar tana dan wasa da mayafinta abaki, tana lullumshe mai ido. Anan ta fahimci komai. Cikin fushi ta waigo, karar awarwaronta ya sanya ramadan ya kalleta. Sai ta yasine fuska. “Yanzu abinda kai ya dace kenan ramadan?, dan wulakanci ina gaban mota kai idonka na kan wancen yarinyar, nina zama dodo-rudo kenan ko?.” 
Afuskance ya kalleta fuska atamke, sai ta danyi tsaki kasa-kasa tace “wallahi ba zan yarda da wannan cin amanar ba, a gaba na! Wallahi dole ta fito daga bayan motar nan, dan bazan Iamunta ba.” 
Ta fada tare dajan numfashi ta kuma Juyawa bayan ta kalleta “ke kuma makira, wallahi sai na nuna miki baki iya bariki ba.Karamar mara kunya.” 
Wani irin burki Ramadan yaja da karfl agefen titin, wanda sai da motar ta bada kara kuuuu! Ya kalli laila yace “get out laila, tun kafin na buge bakinki.” Ya fada cikin tsawa wanda Allah yaso glass din motar a rufe suke azuge saboda Ac dake aiki. 
Runtse ido ladifa tai jin kanta nasarawa ,dan tsawar da yayi ta shigeta, sai ta bude idonta fes! akan ramadan tace “zauji kayi hakuri please, ke kuma laila, karki kara gigin cemin yarinya. Dan ni ba yarinyarki bace.” Dallah! Yimin shiru munafuka algunguma. An gaya miki ni sa’arki ce? Dan kinga aure ya hadamu, na tabbata wallahi a kalla na baki shekaru 3 amma kina min kallon raini toki shiga taitayinki.” 
Wani murmushin takaici ladifa tai cikin sanyin muryarta tace “can ta matse miki laila, dama ai ko makaho ya shafa yasan na fiki yarinta, sannan ki sani a zaman aure nice gaba dake, dan ni kika zo kika samu. Atoh! dole ace da mijin iya baba.” Ta fada zuciyarta na kuna, dan laila ta matukar fara kaita bango. 
“Shut up ladifa, karna kara jin bakinki inna isa dake. Wai so kuke ku sanya ni hatsari ne akan wannan haukan naku,to ku shiga hankalinku.” Shiru ladifa tai tana jin kanta na neman ciwo.Dan ta tsani hayaniya komai kankantarta. Tsaki laila ta sanya ta buga harara tajuya tace “wallahi ba zan lamuci irin haka ba.” Tsawa ya daka mata yace “get out laila.” Sai ta tsaya da bala’in tana huci, yace “ki fita nace.” Kin fita tai, sai kawai ya bude motar ya fita ya zagaya bangarenta ya bude yace fita. Cike da mamaki ta kalleshi don bata dauka da gaske ya keba. Idonsa ya kada yayi ja! Sai ta futa tana kunkuni. Yayi wa ladifa alamarta fito. Saita fito cikin sanyinjiki ta shiga gaban. Jagwab! Laila ta zauna abayan ta sunkwi da kai, idonta na fidda hawaye. Ita kau ladifa sam! ba taso hakan ya faru ba, Sai daya kalle su sannan yace “daga yau duk wacce ke da girki, ita ce da alhakin shiga gaban mota, tunda kun mai dashi wani abun azo a gani.” Yana gamai musu kashe din, ya figi motarda wani irin gudu, zuciyarsa na tafasa, ganin hakan yasa ladifa ta shiga adduar Allah ya kaisu lafiya ganin irin gudun da yake kwasa, dadin dad’awa babu yawan motoci a hanyar. 
Kama hannusa dake gefe tayi, wanda ba dashi yake controlling sitiyari ba, nan ta dora hannunta saman hannunsa, ta shiga matsa mai, taushin hannunta da danshin hannun nata ya ratsa shi, Tace “ayi hakuri mijina. Allah ya taushi zuciyarka.” Cikin wani irin yanayi ya kalleta ya dan rage tamke fuskarsa. A hankali ya fara jin nutsuwa na dan shigarsa. Har suka karasa Gidan barkar. 
Suna tsayawa. Laila da kanta ke sunkuye ta daga kai suka hada ido dashi ta mirrow, ya kauda kai. 
Nan ya bude suka fita ya kuma bude boot, ya dauko kayan barka, har lokacin laila bata ga damar fitowa ba, sai da ya kumai mata magana azafafe sannan ta fito ta tsaya tana huci, har sunyi gaba ya tsaida ita yace “ina son ki saki fuskarki, karki soma nuna wani abu tsakaninki da ladifa, na dai gaya miki.” Harararsa tai ta ce cikin tamke fuska “inna kufa.” Shafa gemunsa yayi ya tabe bakin “zan maganinki ne laila.” Sai tayi gaba tana jin wani irin tsanar ladifa aranta. A ganinta itace sila. 
Sun shiga cikin gidan, wata mata dattijuwa ta tare su, tai musu maraba, su ka shiga falon gidan sai kamshin turaren wuta yake, kowacce ta zauna akan kujera, laila sai bugawa ladifa harara take, wanda ita kanta na sunkuye. Maijegon ceta fito cikin fara’a tace “Ah! ladida da amarya ne! sannunku da zuwa.” Sai ladifa ta dan sanya dariya. “Kai amma naji dadi, damanjiya muktar ke cewa, za kuzo.“ 
Ladifa tace “wallahi kuwa, an samu kai lafiya?.” 
Shukrab tace “wallahi alhamdlh.” Ta kalli laila dake danna waya tace “amarya kinyi shiru, koda yake amarya bata fiya magana ba dama.” Ta fada da dan fara’a. 
Sai alokacin ta dago tace “sannu maijego ya baby?!‘ ta amsa lafiya. Shukra ta kwalla wa wata kira, sai ga dattijuwar nan ta fito da baby a hannu,ta mikawa laila babyn tace “kai masha Allah yarinya mekyau. Allah ya rayata.” Shukra ta amsa da ameen. 
Ganin lailar ba ta da niyyar mikawa lad’ifa, sai ladifar ta tashi dan karbar jaririyar, ta sanya hannu ta karbi yarinyar, saboda tsabar masifar laila saura kadan ta sakar mata jarariyar tun kafin lad’ifar ta rike. Shukra na ganin hakan,gabanta ya fadi kar ‘yar tai kasa, dan ta kula a dan yanayi ta gane lailar basa jituwa da lad’ifa. Zama tai ta kalli yarinyar “kai shukra wannan baby haka! Tubarkallah, gaskiya kin iya haihuwa, kinwa muktar wayo Dariya tai tace “kar dai ya jiki, dan har musu muke, wai shi ta biyo.” Sai tai dan dariya. “Ramadan ma zai ganta yana waje.” Rike baki shukra tai, “kuma sai kuka barshi? haba dai, bari ace ya shigo.” 
Sai laila ta mike. “bari na sanar mai,” ta fita. Tana fita, shukra tace “ni wannan kishiyartaki Iadifa sai naga kamar za tai zafin kai.“ “Hmm! kawai lad’ifa tai, ta ce “Allah ya kyauta dai.” Ta fada tare da kawar da maganar. Laila ko na zuwa ta tsaya gefen motar sa, ta bude gaban motar ta zauna ta kalleshi. Da muryar sassauci ta ce “habeby ka shiga kaga baby.” Ko kallonta bai ba, sai data kuma magana yace “naji.” Sai ta dan saki murmushi, ta kalleshi tayi fari da idanuwanta da suka sanya idon kara kyau da gashin idon data sanya. “Am sorry habeby akan dazu, wallahi kishinka ne ke damuna forgive me please.” 
“Naji, ya kamata kina ganewa fa, komai a rayuwa yana da iyaka, tunda kika aureni ki ka san ina da mata, bai kamata kina tsuro da wasu halaye ba, ko gaba ina so ki gane bana son hanyaniya, bana son muryarki tana daga tawa kin gane.”Yana fada ya bud’e motar ya fita, lokacin wayarsa tai kara ya daga, yace “ai gamu mun zo gidan naka.” 
Muktar yace mai gashi nan ya kusa karasowa.” Jerawa sukai da lailar, suna shiga falon ta dinga dan sakin murmushi tana tafiya tana yauki.”. 
Kallo daya ladifa tai musu ta kauda kai. Shukra ta gyara hijabinta , cikin fara’a tace “ah baban baby na biyu, sai kuma kaki shigowa, kaga baby.” 
Dariya ya sanya “yanzu dai na shigo , wai mutumin yanzu yake ce min ya fita.” Bai dade ba ma wallahi, yanzu za ka ganshi ya dawo.” Ta fada tace musu tana zuwa.” 
Mikewa ladifa tai da babyn tana kallonta cikin sha,awa ta karasa gabansa ta mika ta mai, yace “nifa ban iya rike baby ba, dole saikin tsaya.” 
Nan ta zauna gefensa, ta dan saka hannuwanta ta rike babyn, shima ya rike. Yace “masha Allah! Allah ya raya tace “amin,” sai yayi murmushi . “Saura ke da laila ku haifamin nima,” ya kalli laila dake wani cika tana batsewa, dan kasa sarrafa zuciyarta take, har idan taga ladifa kusa da Ramadan, dole ko yaya sai taji matukar kishi, koda kuwan itama akusa da shi take. 
Sai tai yaken murmushi tace “ka samu kuwa habibyna.” Sai ya juya ga ladifa ya dan kashe mata ido yace “say something baby .” Murmushi tai tace “Allah ya kawo masu albarka.” Yace “amin” Adaidai lokacin shukra ta shigo da abubuwan sanyaya makoshi, tana ajjewa mukatar na shigowa. Cikin murmushi yace “angon mata biyu kana sha’aninka.” Dariya yayi sai suka tafa suna dariya Ramadan yace “yasan ranka? Kaima ya kamata ka dauko wata.” 
Shukra ta kallesu tace “wannan shawarar bata shiga ba, kar dai a zuga min miji.” Laila ta sanya dariya. Muktar yace jiya ma “ai Abdallah ya kawo matarsa salma..” Haka dai suka zauna sunsha hira, sunyi wajen awa daya, sannan sukai shirin tafiya, suka ajje kayan barka suka tafi 
Sun dan yi nisa, laila daga bayan motar tace “habiby karka manta dama nace zan dan shiga kanti, mu tsaya a Arewa store zan sai foundation, tawa ta gida ba tai min kyau wallahi.” Head ya daga mata, ba tare da yayi magana ba har suka karasa. Ya tsaya adaidai kofar kantin. ya juya ya kalleta yace “jeki fito.” 
Nan ta fita, har tayi gaba yace ta tsaya .Ya juya ya kalli gefensa yace “babyna fito muje k0 zaki sai wani abun.,” sai ta dan girgiza kai tace “kuje,banda abin siya.” Sai ya rufawa lailar baya har suka shiga ciki. Basu dade ba ta gama siyayyar bayan Ramadan ya biya kudin, har zasu fita sai yajuya dan ya sayowa Ladifa ko turare ne itama, dan ya san shine best gift da zaka bata ka burgeta,saboda ma’abociyar son turaren ce. 
Danjuyawa tai tana wani nuna alamar bata gane ba,“nafa gama siyayyar.” Sai ya kalleta yace “baki ganin kin sayi abubuwa da yawa kuma na biya. So itama lad’ifa zan dan sai mata.” Binsa tai abaya ganin ya doshi wajen perfumes, yana cikin dubawa yaga wanda tafi sanyawa, sai ya saka hannu zai dauka, alokacin wata budurwa tazo wucewa tana danna waya. Shi kuma lokacin yadan daga hannunsa sai hannun ya bigi wayarta, ta fadi kasa tass! 
Da sauri ya juya yaga abinda ya faru,sai ya sunkuya ya dauko wayar ya mikawa budurwar dake dan yamutsa fuskarta yace “sorry,” sai ta karba. Wanda adaidai lokacin  idon laila ya sauka a kan
Yarinyar da sai duba wayar take dan har ta dan tsage, sai tai dan tsaki ya juyo ya ce “ta fashe ko?.” “Eh wallahi.” Wani kishine ya turnuke laila ta tawo afusace, tana zuwa ta dauke yarinyar da mari. Ta kuma nunata da hannu “irinku ne matan dake bin mazan mutane k0? meye tsakaninki da mijina? har wayarki tazo hannunsa.” Cikin takaici yarinyarta ce “me nai miki za ki mareni?”Na mareki din.” 
Kam ta sauke maganar budurwar itama ta rama marinta tace “inke ba kya duba abinda ya dace tosai ki tambayi mijin naki, abinda ya sanya wayata taje hannunsa rubbish kawai.” 
“Nice ma rubbish.” “Yes “kece saboda na kula kina da karancin tunani.” “Wai laila mai yasa ba kya abu da tunani ne meye haka? zoki wuce mu tafi.” Bata saurare shi ba, ta kuma tsinke yarinyar da mari.” Cikin hawaye yrinyar ta kalleta ta daga kai ni kika kuma mara?.” “An mareki wannan ya zama izina ga ‘yan mata irinku, wallahi mijina yafi karfin irinku”. Tsawa ramadan ya daka mata yace “wai  aljanu gareku ne? baki da hanakali ne,ya kalli yarinyar yace please “kiyi hakuri, wannan ba cikakken kai gareta ba, wani abun bata sanin tana yi.” Kuka yarinyar keyi a hankali saboda marikan sun shige ta, sai cewa take ba zata yarda ba,lokacin har wasu mata manya dake gefe suna siyayya sun tsaya suna kallo, sai da suka sanya baki sannan yarinyar ta hakura. 
Cikin fushi Ramadan ya barwajen saboda kunya da yaji ta kama shi. Kallon laila budurwar tai tace “wallahi ba dan mijinki yaban hakuri ba,wallahi da sai kin gane baki da wayo, kuma in sha Allahu sai mijinki ya kara aurejaka kawai. Afusace ta matsa zata kuma bata mari matan nan suka ce “ke dan Allah ki nutsu man, kishi ai ba hauka bane.” 
Tsaki tai ta kallesu tai waje afusace. Wani irin takaici ke damun ramadan,ga kunya da yaji akan abinda lailarta yi, sai ya tuno ladifa lokacin data gansu shi da lailar a store, tabbas! Yaga tashin hankali a idonta, amma ko magana batai ba ta fice. Wanda ita dahir ma ta gani ta shanye. Amma ita dan bata da hankali ta tsinka shi gaban jama’a. 
Gaban motar ya shige, ya rike kansa, ladifa ta kalleshi sosai! sai ta dan juyar da kai. Tsaki ya sanya, tare da jan motar ya figeta a guje da yake ba motoci da yawa a hanyar. 
Kallonsa ladifar tai tace “ya haka zauji laila bata shigo ba fa?.” ’ “lad’ifa bana son ki kara cewa uffan.” Sai Tai shiru bata sake cewa komai ba, amma tasan tabbas ba lafiya. 
ltako laila tana fitowa taga babu alamar motar Ramadan sai ta kuma kuluwa .”lallema ga mari ga tsinka jaka,” ta fada tare da kokarin tsayar da dan adaidaita. 
Karfe 12 ya faka motar, ya bude ya fita, ladifa ma ta fito, suka shiga gidan.Suna shiga ita tai sama, shi kuma ya zauna afalo ya daga kai sama. Yana kaurara masifar laila. Don sam! bai ji dadin fitar ba. Sai wajen 12:30 ta shigo gidan a fusace
Tana shiga ta ganshi kwance kan doguwar kujera. Cikin fushi tace yanzu ramadan ni za ka wulakanta dan na nuna kishina akanka, wanda hakan ne ya dace. Shine har da karin tozarci kayi tafiyarka ko?.” Dago kansa yayi ya kalleta ya ce Pleasa ki bar nan wajen bana son ganinki Iaila.” 
Sai ta sanya kuka “wallahi sai ka gaya min wacece wannan, ita wacece ?meye tsakaninka da ita?!‘ “Idan ke kika haifeni sai ki sanya na gaya miki.” “Wallahi ba zan yarba ba, ai wannan cin amana ne?.“ Ladifa dake tsaye tun lokacin shigowarta ta dogare da karfen bene ta runtse ido, domin jitai gabanta ya fadi, jin da laila tana tambayar meye tsakaninsa da wata. Zama tai tana adduar Allah yasanya ba hakan bane.” Wallahi sai ka gaya min Ramadan. Mikewa yayi ya kalleta, “idan har baki da hankali, to ki cigaba ba.” “Ni ba shashashar mace bace da zan zauna na ganka da wata na kyaleka, wallahi sai ka gayamin.” Kafarsa ya taka yana kokarin hawa sama, ta tsaida shi tare da shan gabansa. Cikin kuka tace “wallahi ramadan baka isa ka ci amanata ba.” 
Wani zazzafan mari ya bata, ya nuna ta da hannu “laila zan aikata miki abinda baki zato ba, in har baki rabu dani ba. Ta yaya dan baki da hankali, daga ganin yarinya na bige wayarta ta fadi kasa har ta fashe, na dauko na bata hakuri shine zaki canja akalar maganar. Ki hau dukan ‘yar mutane. To dan Allah duk abinda zaki kiyi, idan ma zaki ce budurwa ta ce ki fad’a is your time.” Ya fad’a cike da fushi ya haye saman. 
Tana dafe da kuncinta tana kuka, sai ta bar wajen aguje tai shashinta ta banko kofa. 
Saman ya hau ya shige dakinsa ya cire rigarjikinsa, ya mike kansa har wani sarawa yake, sai sakin tsaki yake sai ya tuno ladifa da irin hakan ta faru yanayin data yi babu hayaniya. Wani irin sonta ne yaji ya dada mamaye zuciyarsa, girmanta yake gani aransa, kimarta na dada shigarsa, yanajinjina hakurinta. Shi kam har ya fara dana-sanin auren Iaila. 
Cikin sanyin jiki ladifa ta mike, dan ita kanta adagule ta ke donta,ta kasa ma gane ainihin abinda suke fada ma akai, sai ta watsar, saboda ba ruwanta aciki k0 menene ma sunfl kusa. 
Saman ta koma dan ta watsa ruwa, an dan fara zafu ita kuma mai yawan gumi ce. Nan ta watsa ruwan ta sanya yaloluwar doguwar riga ta mutstsuka humra dinta mai kamshi ajikinta, ta fesa turaren kaya ta sauka kasa dan dora girki, saboda itace da girki, yau weekend dole kuma tasan zai ci abinci agida. 
Tunda ta shiga bangarenta ta ke risgar kuka, saboda tsabar bakin kishi, da takaicin abinda ramadan yayi mata, ‘dama haka yake?’ Ta ayyana aranta, ba taji zafin marin da yayi mata ba, akan ganinsa da budurwa da tai, ta dade tana kuka a zaune dirshan. 
Tana cikin kuka wayarta tai kara,da kamar ba zata d’auka ba,sai taga mamanta ce me kira, sai ta dauka suka gaisa, maman taji alamar kamar kuka take, tace “laila me ya sami muryarki kamar mai kuka?.” 
Sai ta sanya kuka. “Mama dama haka aure yake? ni wallahi na gaji.” Murmushin manya maman tayi tace “Laila kenan, kin dauka auren wasa ne? kin dauka gidan morewa jin dadi ne har illa ma shaa, dole sai Allah yajarrabeka ko ta yaya agidan aure, to dukyanda kikai tunanin aure ya wuce nan, amma in dai kika dau komai na aurenki a ibada to zaki zauna lafia, kai komai ma na duniyar nan banda zafafa shi, ni dai fatana ki rike aurenki, kiyi biyayya.” 
Kuka kawai take,dan ita aganinta ba zasu gane abinda takeji ba. “Yanzu mama ya dace Ramadan.” 
Dagakatar da ita tai “ki zama mai boye sirrin gidanki, domin wataran inkin gaya mana zamu ji haushin mijinki, kuma ke kije ki shirya da mijinki, mu ki barmu munajin ba dadi. Komai ma ya faru, to ki sanya hakuri da salama, na sanki sarai laila baki da hakuri, hak’uri kuwa a zaman aure babban jigo ne dake rike aure, ki dinga kai zuciya nesa, ban da furta magana duk wacce ta zo bakinki, ki dinga taunata kam ki furzar, dan maza basa son mace mai kaifin harshe, 
Sannan Kibi mijinki laila, ni dai abinda zan gaya miki kenan, domin Allah ne ya sanya suka zama shugabanni a garemu. Kuma yace mu bisu. Kina da ilmin addini daidai gwargwado, to ina so kiyi amfani da shi a gidan aurenkinan wani abun bacin yayi miki kike san nuna mai bacin ranki, to bi dashi cikin salon zamantakewa mai inganci, idan kuma har ba zaki iya ba, to barwa Allah ai akwai ranar sakamako. “ 
Dama gaya miki zan, Fatiman baba atine ta haihu, ranarjuma’a suna, dan Allah ki daure kije, saboda matar akwai zumunci. Nan tace za taje sukai sallama. 
Nan tai shiru tana tunanin maganganun mahaifiyar tata, tabbas! tasan cewa gaskiya ta fada, amma ita bata jin zata dau nonsense din da namiji ba, dan harga Allah ita ba zata dauka ba, ita ‘yar baro-baro ce, “wallahi ramadan sai na rama wulakancin da kayi min.” 
Lokacin sallahr azahar ne yayi sau Ramadan ya tafi Masallaci. ltako ladita tana dakinta, bacci ne ya kwasheta. Wajen rabin awa ta wuce tana shakar baccin, har Ramadan ya dawo daga masallaci, cikin barcinta taji ana tashinta, dan indai ramadan na shashinta, bata samun ishasshen bacci da 
daddare, dan baya daga mata kafa, shi,isa da rana sai tai ta bingirewa time to time, sai ta 
bude ido ta ganshi tsaye a gefenta. Yace “kina ta bacci gashi can sai dana kashe girkinki ya kusa konewa.” 
Da dan sauri ta mike wallahi na sha’afa, bansan sanda bacci ya sace ni ba, sai ta fita da 
dan sauri, ya bita da kallo yana murmushi. 
Ksan ta sauka ta kwashe shinkafar a warmer, ta zauna ta yijajjagen kayan miya, ta yanka albasa da yawa tai miyarta kadan mai hade da kifi. 
Ta kuma yanka cabeji da salak da tumatur, karas, cucumber ta gama ta zuba sauran kayan hadin coslow, ta had’a. ’ 
Harhada komai tai da kayan dandano na miyar, ta rageta ta fita,sai tai wajen laila ta dan bubbuga kofarta sai taji shiru, dan shurun nata yayi yawa, saboda ko yaya kake zaune da mutum kaji shurinsa yayi yawa, to kadan neme shi, koda ba zaka samu tarbar arziki ba, kadai sauke hakkin makotaka, balle kuma yanda ta ga shigar lailar ciki. 
Ta dade tana bugawa amma shiru, laila na can na bacci mai daci daya kwasheta, wanda ya sanya ba taji bugun ba. Sai ta koma falo ta zauna tana jiran miyar ta karasa. 
Tayi wajen rabin awa tana falon, dam ma wayar dake hannunta ta dauke mata hankali, tana karanta wani labari, sai ta tashi ta shiga kitchi ta kwashe miyar ta zuba a mazubi, ta saka nasu a kwando, ta dauka tai sama bayan ta ajjewa maigadi nasa. 
Dakinsa ta shiga, ta zauna gefensa ta kalleshi, idonsa na kan laptop amma Kallo daya tai mai ta san har yanzu damuwar da laila ta sanyashi na nan daram! aransa. Sai ta dan matsa ta rungume gefensa ta baya, tace “zaujina komai yayi zafi maganinsa Allah. Dama haka zamantakewa take, duk da bansan me ya faru ba, amma dan Allah kai hakuri.“ 
Dagowa yayi ya kalleta “babyna lamarin laila ya fara isata, sai ya saki tsaki sam! Bata da hankali na rasa…” bai karasa abinda zaice ba sai tajuyo da fuskarsa suka fuskanci juna tana goga hancinsu waje daya tace “ka maida komai ba komai ba, ka ji nurul kalbina, nasan ranka ya baci,ta fada tare da lumshe mai ido,jinjina kai kawai yayi yana tuno irin tabarar da lailar tayi yau. “Baby wallahi.” Sai tai sauri a hankali ta hade bakinsu cikin nutsuwa ta shiga nuna kulawarta gareshi, bai wanija aji ba, ya biye mata, duk da bacin ran da yake ciki, yaji sassauci, saida ta sanya shi nutsuwa duk da tana period sannan suka numfasa. 
Sai yaji duk rabin bacin ran nasa ya ragu, suka fito falo suka ciyar dajunansu abinci.Wani alfahri yake yanaji da ladifartasa,har in ya kalleta. Bayan sun gama ci. Ta kalleshi tace “ni fa naji amaryarka shiru har yanzu bata fito ba.” “Bana son kina sanya kanki cikin abinda babu ruwanki ladifa,” ya fada fuskarsa ta dan sauya, dan sai ya nuna ma laila cewar yes shine mijinta. Bakinta taja tai shiru, saboda kar ogan nata ya birkice, fushin ya shafeta. 
Hmmm
Nan ake yinta

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE