NAYI GUDUN GARA CHAPTER 2

NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 2
Da safe suk’uk’u ta tashi da wuri, da ya ke zaije office, shiyasa ta tashi da wuri saboda ta san halinsa, k’arfe bakwai ta kammala, ta jera a dining sannan ta koma daki ta kwanta, don jin baccin idonta da ke neman damunta, dan jiya bata samu ta yi shi sosaiba, lumshe ido tayi tare dajan bargo bacci ya fizgeta da k’arfl. Sama -sama takejin amon muryarsa na tashi, da sauri ta bude idonta,ta ji sautin muryarsa na kiran sunanta da hanzari ta mik’e ta fita tana layi, hada step ta dingayi harta k’arasa, ta baya ta rungumeshi tana shak’ar k‘amshinsa, wani irin kewarsa ke shigarta, fincikota yayi ta yi taga-taga za ta fadi, cike da tsoro ta kalleshi, idanuwansa dake d’auke da tarin masifa take kallo cikin dad’a tamke fuska ya kalleta yace
“Yanzu wannan abincin shine breakfast? an gaya miki ni ma’abocin cin k’osai da kunu ne?” Wani irin mamaki ne ya kamata,cikin rawar baki ta ce “haba zauji, abin fa marmari nai maka, sanin cewa za kai farin-ciki da shi, tun da ba kullum ake yiba…” Katseta ya yi da sauri, “ban san zancen banza aida, kin tambayeni kafin ki yi? to bana ci, dauke shiriritarki.” Runtse ido tayi, tare da tuno tun sanda take k‘ok’arin had’a k’osai da kunu din  amma ga abinda ya saka mata dashi. Numfashi taja, “amma dai bai kamata kai min haka ba, ka san lokutan dana dauka ina hada maka? haba zauji, ka dinga rangwanta mini mana,wai ko dai wani laifin na yi maka ne? Idan na yi maka ina rok’onka da Allah ka gaya mini Dan na nemi gafararka.” Ko uffan bai ce mata ba, saima had’a bak’in shayi da yayi ya hau kurba, sai da ya sha rabinsa, sannan ya kalleta, “ki dauke ki cinye, dama na san kinyi ne dan ki cinye duka, kinga kya ma k’ara kumari ko’ina ya cika.” Idan akwai abinda ta tsana bai wuce gorin da yakeyi mata kullu yaumun ba, cikin fushi ta ce: “Koma dai menene na flta hak’k’inka, ,nina rasa wanne irin hali gareka  komai nayi ban birgeka, tun daga kanjikina, kai komai nawa ba ya birgeka, haka girki ,innai sai kace bai yi ba, kuma idan na tambayeka wanne irin girki ka ke so nayi maka, sai kace na yi kowanne, idan kuma na yi, saika zo kace nayi bai maka ba, haba yaya kake so nayi da rayuwata ne? nima fa mutum ce kamar kai.” “Kinsan me nake so dake, so nake ki zama mace ko ta’ina,dan ke kam kota’ina zero CE.” Yana fada ya mik’e. Da sauri ta sha gabansa, “ya kamata ace kasan cewa ni matarka ce, me ya sa babu wacce wulak’antantarka ke samun matsugunni agunsa sai ni?! ina soyayyarmu? ina sonka gareni, ina riritanin da kai alk’awari, ko dama duk dad’in baki ne? yanzu saika ce mini duk babu a wannan lokacin,yanzu ya kamata na zamo abar tattali a wajenka, amma yanzu ne na zamo shara a wajenka, nima fa macece.” Ta fad’a cike da rawar murya hawaye na zaryar zuba akan kuncinta. fincikota yayi ya matse ta ajikinsa, sai da ta saki ‘yar k’ara, “da wannan jikin zaki zama macen gaban goshi a wajena, ko ina qashi.” 
Nan ya shiga matsata yana cewa “jibi fa babu Inda zaka tab’a kaji laushi ko nan da zai kasance me girma da laushi shima babu,bayan ni ma’abocin San mace mai cika ne,,” da k’arfi ya matsa k’irjin, nan ta saki k’ara, ya turata gefe ta buge hannunta gum! ta saki kuka. Cikin kukan tace “duk wannan ba shine mafita ba, mafitar shine tun da ka raina tsayuwar wata sai ka hau ka gyara,sannan mai yasa kana ganin mata masu cikar ka nace mini sai da ka aure ni..?” Bai bata amsa ba sai ma sakin tsaki da ya yiya fice. itako ganin hakan ya Sanya ta zame ta zauna dab’as akan tiles da ta shiga raira kukan data saba, ga shi duk sanyin da ake bugawa amma bata damu ba, hakan take dad’aa malalewa tana risgar kuka da sanyin safiyar nan
Taunar cewgum take b’as-b’as, tana k’ok’arin sanya siket, da k’yarya shigeta, haka rigar ma da k’yarta shiga, nan ta fente fuskarta ta yi das da ita, ta coka d’aurinta ta bulbula turare, daga k’arshe ta d’au yalolon mayafi ta sak’ala a kafad’a, sannan ta manna glass kalar brown cike,da takun k’asaita ta dau madaidaiciyar Jakarta ta flce, wani irinjuyi take da k’ugu tamkar tarwad’a, sanin cewa hajiyarta za ta ganta a haka kuma bata son fad’a ya sanya ta warware mayafln, girmansa ya bayyana ta yafa shi, tana fita ta tararda hajiyarta zaune kan sallaya, da alama ta dad’e da idar da sallar la’asar. “Hajiya zan tafi bikin Asma’un,” ta fad’a tare da juya bayanta dan kar hajiya taga d’amewar dajikinta yayi, nan hajiyar ta d’aga ta kalleta, ganin ko‘ina jikinta a rufe, ya Sanya ta ce “to ki dawo da wuri Laila kan babanku ya dawo” “To hajiya.” Ta Sanya kai ta fice. Cikin taku d’ai-d’ai ta doshi titi tana juya jiki, duk Inda ta wuce sai ido, ba ta dad’e ba ta samu adaidaita sahu, direct jifatu store ya kaita, ta sauka ta shige ciki, bangaren kayan kitchen ta nufa sai dubawa take tana k’arawa, k’arshe ta d’auko wani dinner set, ya zam shine za ta bawa amarya gudun mawa. Juyowar da zatai ta bangaji mutum. Da sauri Ramadan ya maida idansa kanta,tabbas itace wadda ya ke fatan k’ara had’uwa da ita, ganin bai magana ba, ya Sanya ta juya tana mutstsuka baya, Binta da kallo ya tsaya yi,shi bai tafl ba, haka bai motsa ba, da gangan take duk wani sarrafa takunta, domin ta San yana kallonta. Da Sauri ya bita, idansa na kan k’irjinta ,ganin hakan ya sa tai d’an murmushi ta kauda kai. ‘Yammata idan ba za ki damu ba. Dan Allah ki bani lambarki.” Yatsina fuska tai irin Jan ajinnan. “Sorry fa,” ta fad’a cike da kashe murya. “Please, bai kamata ki kasance d’aya daga cikin masu hofantar da Wanda ya damu da su ba, Sam! Ba kiyi kala da irinsu ba,” ya fada tare da kuma kasheta da kalkonsa. 
“Okey ba matsala.” Nan ta karanto mai, tajuya tana cigaba da kafa gwabnatinta da fatan Allah ya sa adace a zuciyarta. Wajen counting taje, kamar hadin baki, sai ga shi nan ya mik’a ATM card nashi, dan a zari kudin kayan da ya d‘auka da nata. Kamar bata san ya mik’a ba, ta mik’a kudinta. 
“Meye amfanina beauty. Ki barshi na biya.” 
Bayan gama biyan suka fita, idansa na kan manyan kirjinta kamar su Faso Riga, sai faman hadiyar yawu yake. ‘Yau da shi dan bariki ne da babu abinda zai saka ya bar yarinyar nan batare da ya kashe k’ishinsa akanta ba, sai de ba shi da wannna halayyar saboda ya San ba dabia mai kyau bace, tabbas! wannan itace matar aure ya ayyana a ransa.‘ Kallonta ya yi cike da so, ya ce “ya kamata gimbiya ta Shiga mota ta in kaita lnda zata.” Cire glass dinta tai ta watsa mai kallon da saida yaji kamar ya sume awajen , “no problem,” ta fada da salon magana. Gaban motar ya bude mata ta zauna, idanuwansa kafe akan faffadan kugunta, yana maijin kamar yaja ta jikinsa. 
Rufe mortar yayi ya zaga ya shiga ya tada motar ya fafareta. “Ina muka dosa ne gimbiya.?” “Court road.” Ta bashi amsa.” “Okey,” nan ya ba da wuta suka mik’a, har gidan bikin ya kaita ya ajje suka rabu. Daga nan bai zame ko’ina ba sai gidansa. Lokacin k’arfe shida na yamma. Zaune ta ke akan kushin tana shan kankana, idonta kafe akan TVtana kallon shirin gari ya waye a tashar arewa24. Amsa sallamar ta yi ciki-ciki, da kamar ba za ta tashi ba, sai kuma wata zuciyar ta kwabeta, kan ta ci gaba da mai abinda ta saba, tinda gashi har girki ta yi mai wanda akan wulak’ancin da ya yi mata da safe, da ta d’au alwashin ba zata yi ba, sai zuciyar salama ta tausheta. Musamman ta data tuno cewar ibada take. Cike da sanyin jiki ta mik’e ta isa gare shi ta karbi jakar hannununsa, sannu da zuwa”, ta fada tana mai sakin murmushin da ta san yana so. Murmushi yayi, “sannu dai ladifa ya gidan?.” Ta amsa lfy”kalau”. Tare da ayyanawa aranta,yau ‘yan kirkin na kan zaujin nata. Nan ta dan juya dan kai mai jakardaki, ya bita da kallo. ‘Ga kyau har kyau a fuska ,amma jiki ba labari,‘ jan tsaki ya yi “dole ya san abinyi.” 
Saida ya je ya yi wanka ya dawo ya ce ,a yanko mai lemo da kankana ya sha. Hakan ta tashi jiki na rawa, dan wani dadi takeji yau bai mata wulak’anci ba. Ba ta dade ba ta dawo ta ajje mai, “ga shi zaunjina,” ta fada murya asanyaye. Kamota ya yi ta shige jikinsa, “ya dai baby? sorry fa, dazu da safe raina ne a bace.” Murmushi tai “babu komai zaujina,” ta fada tana san cigaba da maganar, sai kuma ta sunkwi da kai. ‘ “Fadi mana babyna
“Wai me ya sa kake mini abubuwanda ban jin dadi ne? ga shi kaita kushe ni ,wataran idan nai girki sai kaitA gwasalewa.” 
Murmushi ya yi “karki damu baby ya ci ace kin gane ni, ba wai ina miki hakan dan bana sonki bane, ko dan wani abu ba a’a, wasu lokuta ne nakanji raina na baci shiyasa‘ “Dan ALLAH ka dainaa, wallahi ina shiga wani hali sosai.” “To babu komai.” Wata leda ya zaro ,”karbi wannan maganin sa ka kiba ne , naje gurin doctor dazu na amso miki.” Mamaki ne ya kamata, “wai sha ka fashe kake so na sha? Nidai gaskiya bazan sha ba. Ance fa lalata jiki yake ni kam gaskiya A’a
“Ba shi bane, ba irinsa bane, kawai zai sa ki marmaro ne.” Kicinkicin ta yi da fuska, nan ya rik’ota ya shiga lallashi, k‘arshe tace za ta sha. “Yawwa kuma ambani shawarar kina shan maltina da madara, ki hada insha ALLAHu zaki ciko.” 
Ahaka suka shashance a ranar, sai da ya mantarda ladifa duk bacin ran da ya k’unsa mata a kwanakin baya. Karfe goma sha-biyun dare, Ramadan da Lad’ifa na kwance sai shafa sumarta ya ke, inda ya lula tunani babu k’arya yana samun gamsuwa awajenta, numfashi yaja yana tuno surar laila, sosai ya ke san mata masu cika ta ko‘ina, take ya furzarda wani numfashi, wani sonjin muryarta ne ya shige shi. Ganin lad’ifa ta yi bacci, ya sashi zare jikinsa ya fada toilet yayo wanka ya fito ya fita can falo, lambar laila ya danna yaji busy, wani masifaffen kishi ne ya darsu aransa, sai ya kuma samun kansa da kara kira sai Ya ji ta shiga cikin shauk‘i ya ce “laiiiilahhl,” ya fada tare da jan sunan, cikin wani murya daga can tace mishi “ya dai?.” “Ba kiyi bacci ba?.” Ta ce, “ya kuwa zanyi? bayan ka rik’eni kan cewa karnai bacci zamuyi waya.” “Hmm ai kina raina lailata, duk kin rudani da yawa yau, tinda na hadu da ke nake cikin farin-ciki, wallahi 
i love you.” Ta sabajin kalmar nan a bakin samari, Amma yau daya kalmarta shigeta abakin Ramadan, tabbas shine mijin da ya dace da ita, wanda ke iya taba zuciyarta da kalmominsa. Haka sukaita hira,wanda shi ya manta yana da mata, ita kuma laila ba tai tunanin hakan shiga hak’k’i bane, duk da ba ta san cewar yana da matar ba, sai wajen k’arfe biyu da rabi suka rabu. 
Tafawa sukai da k’awarta saratu, “amma wallahi laila kina sharafinki.” ‘ “To ya san ranki, dole fa saida hakan, kinga gidanmu ba wani k’arfi garemu ba, dole sai ina 
waufta a wajen samari dan na inganta dakina da bikina.” Saratu tace “ni fa abinda ban gane ba lailal, wai ni kuwa sammarin nan ba sa tattabeki kuwa? saboda na san babu wanda zai baki ba tare da yana samu shima ba, dan fa ban gishiri in baki manda wasu samarin yanzu ke yi, wallahi duk sun baci.” Dariya Laila ta fasa, “ke a ta yaya zan bari a lalubeni cab! so kike a maida hannun agogo baya,jini nan, nafa san me nake, hmmm! ke dai barni yanda kika ganni, dan ni ban yarda da wani jin dumi na samari ba, duk da cewa samarin dai-daine wanda za su tunkaro ki ba tare da sunso taba ki ba, sai na hadu da ‘yan naci ne muke shan lolipop.” Dariya sara ta saka, atoh an dai taba din, kenan ko hakan ma ba kyau, shi’isa kullum mu ke addu’ar miji na gari.” “Daga nan dai ba k’ari, wallahi idan na ga gaye ya na cewa zai je gaba, sai na kora shi.” “Shegiya Laila, adai juri zuwa rafi.Kina matsejiki ba dole samari irinsu su na binki ba, waike farin-jini.” “Ke k’yaleni’ lokacina ne, nafa san me nake.” ‘ 
Hmm Yanzu wasan zai fara. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE