NAYI GUDUN GARA CHAPTER 20

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 20
Yana zaune gefen adaidaita sahunsa, ya zuro kafafuwansa waje. Ta daya bangaren ga abokinsa kamilu suna hira. 
Kamllu ya kalleshi “Wai ni kuwa Murabus ina labarin laila kuwa?!‘ 
“Hmmm’ yace wallahi Ina nan ina kirga kwanakin aurenta, na shirya tsaf Wallahi idan ban kashe auren nan ba. to sai na dagula mata zaman auren nan, akanta sai da nai sati daya a bayan kanta, ai yarinyar nan ta yaudareni wallahi,yau da ina dayayan banki, babu abinda zai sanya na damu dan tayi aure ko taci kudina, amma kaga kullum hajiya zancenta kenan Allah ya kara da aka yaudarenka tace min tunda ban sharar masallaci ba, ai ga shi nayi ta kasuwa. 
Daniya kamilu ya iasa “ho ho ho, wallahi ina gaya maka kai hakuri, nuhu duk ya gayan komai, kawai Allah ne ya tsara hakan, ni dai shawarata kai hakuri, shi hakuri arayuwa yana da rana, ka barshi, baka san gaba wacce irin mata Allah zai baka ba. Inaji maka tsoron ka sanya kanka a matsala” “Kai billahil azim! sai na nuna mata cewar nima dan zamani ne.Ni zata yaudara, kai wallahi anjima zan sayo sabon layi, wallahi a yau zan fara aiki, murabus fa nake. wanda yayi tashen rashin kunya a da, kai ai ka sani bana barin ta kwana, yanzu ne shiriya ta zo, dan ta ganni talaka me tukin napep, shi,isa ta daukeni a matsayin me kaita unguwa.” Ya saki kwafa. Dariya kamilu ya kyalkyale da ita, “maji ma gani, wai an binne tsohuwa da rai.Me raban shan duka ba yajin kwabo sai yasha.” . 
“Duk naji me kace, kawai ku samin ido”, nan suka gama goge babur din yaja suka tafi Ba ita ta fito daga daki ba, sai wajen biyar, idonta ya yi luhu -luhu, indomie kawai ta dafa taci, tai wanka ta fito public falo. Gaban tv stand taje tana dube -dube, adaidai lokacin ramadan ya sauko cikin shirin fita,ta juya ta kalleshi tajuyar da kai, shi ko cikin takunsa, ya iso ya giftata ya fice ya bar mata kamshin turarensa, hakan ya kuma kular da ita. Haka al’amarin yaci gaba da gudana, dan sun dai nayiwa juna magana, baya cin abincinta. baya shiga dakinta, haka itama bata dafawa da shi. 
Ladifa na gefe ta zuba musu ido, dan tana kula da irin abinda suke, dan akalla yau kwana hudu kenan suna gaba da juna. Washe gari 
Leila na zaune a falonta, suna cin dan waken da tayi wa kawayenta Asiya da sara da suka kawo mata ziyara. 
Sai kyalkyala dariya suke Asiya tace “ina kishiyarki ne wai?.” Sara tace ‘yakamata ki kaimu mu gaisa, saboda ke da ita yanzu ai kun zama d’aya“ 
Tsaki tai’ laila tace “tana bangarenta ai bakin hali gareta, yaushe zaki ganta a kasa? ke kuwa sara dawa aka zama dayan? Allah ya sawwake kawance da gwauro.” Asiya tace ‘Lalle! wallahi laila saikin tashi tsaye,zama da kishiya ai wahala ne.” Sara tace “kinji ki ke asiya da wani zance, ai tasan yana da auren ta aureshi ko. Ni wallahi ina ganin sankai na wasu matan, wai mace ta shigo gida ta taradda mace, amma ta dinga nuna kishi. Ai wadda akaiwa kishiya inaga sai tafi jin kishi tunda ita akai yowa.” “Ba zaki gane ba aminiya, dan bakiyi auren bane kawai.” “Tabe baki sara tai tace “wallahi baku da wayo, aini wallahi ba zan irin wannan halayen da kuke yi ba.” 
Laila tace “kinji dashi dai sara.” Asiya tace “gaya mata dai. Bari ki gama, na tawo miki da guzurin’,” nan tajawo jakarta. Ta fito da maganin mata kala-kala tace “gasu nan wallahi, masu matukar kyau ne, ta rada mata magana akunne suka sake fashewa da dariya. ‘Amma fa naji dadi wallahi, dan ma bama magana da ogan, kin ga idan na sha ma abanza.” Gyara zama Sara tai ta turo dankwalinta gaba, tace “amma wallahi ban taba sanin laila wayonki na banza bace sai yau, ban taba sanin laila budewar idonki ba ko’ina taje ba. Yoko wadda ba taje school ba ai ba zatai haka ba. Waya gaya mlki mace mai kishiya na haka? Gaba ma ko da gama-ganin mutum kike yi ai ba dadin ji ballantana ma miji.” Sara kyaleni ni, nifa ba ‘yar dadi miji bace irinsu wa’e ta sama, dan haka in akai min kan kara, sai nayi na kwando.‘ ‘Hmm laila kenan, mace mai kishiya ai dole sai tana dan kawarda kai ga wani abun, indal tana san ta samu fada ga miji,in dai baso kike ki koma bora ba, mace mai kishiya a bangaren miji babu sanya. Koda za kiyajin aikin ai baifi kiyi na kwana biyu ba.Yakamata ki tsaya ki fahimci yanayin yanda mijinki yake. Sanin halin mutum sai kaci maganaim zama da shi. Ni dama banyi aure ba inajin ba zanyi wannan abun ba wallahi.” 
Asiya tace “kin ga sara. “Me daki ai shi yasan inda yake mai yoyo, wallahi ina bayanki laila, mazan zamanin nan sai ka zama kai tsaye ni tsaye ake zama IafIya.‘ “Wallahi fa Asiya, ko fa kallo ban isheshi ba, saboda ta sama na juyarda akalarsa. Kin sanni ban daukan raini, wallahi k0 wata za ai sai dai muyi ta tafiya a hakan.” “Hmmm ni dai ina gaya miki ki canja salo indai ta bangaren miji ne Allah indai kece da laifi ki bashi hakuri, in kuwa shine yayi miki laifin sai ki nuna fushinki ta dabaru.”Cewar Sara tana danna wayarta. Tabe baki Asiya tai tace “wallahi ni banga wani laifin laila ba, kin min daidai. Yau da ace kishiyarce ma tayi miki tsiya, dana baki salon cin kaniyarta kwando-kwando. Ta karashe da sanya dariya. 
“Baki da dama asiya. ‘ ‘Yo ai gaskiyane mu ‘yan tabbatar da samun ‘yanci ne a gidan aure,, bama daukan raini.‘ Cikin jin dadin maganar asiyar suka tafa cikin shewa. Sara kuwa kawai kallon laila ta ke, ta raina wayonta,saboda ita sam shawamarin asiya basu shige taba. Karfe hudu sukai shirin tafiya, Suna tsaye a public falo, Ramadan yayi sallama, Sara ta amsa sallamartare dayi mai sannu da zuwa. Laila ko ta sanya tsaki ta kauda kai. Asiyar ma ta gaida shi. Yana barin wajen Sara tace ‘wai keya haka? Miji ya dawo kin dauke kai waike fushi ko? Har da sakin tsaki. Wai ina iya kissarki da kwarkwasarki ne laila? Wannan ai babu ladabi a ciki. 
Haba! ldan ke wata ce da yana shigowa in yayi sallama koda bakwa magana amsa sallamar ki karbi kayan hannunsa. Kinga ko dan ganinmu ma ba zai ce zai gwasale ki ba, kinga ko daga nan kin fara samun damar da zaku shirya. Dan nasan Wallahi har zuciyarki kina son ku shirya din.” “Aminiya kenan, sai akace miki neman shirin nake? Ke dai kawal ai sha’ani, ki bar laila a yanda take, kema zakiyi auren nan gaba zaki gane.” Asiya tace “gaya mata dai.” Ai shi kenan “Allah ya shiryaki ki gane hanya.‘ Asiya kuma tace “aci gaba da gashi laila, aikinki na kyau, wallahi maza sai da haka, dan idan suka shuka maka wata tsiyar, sai ka kusa kaiwa barzahu, amma in ka tauna tsakuwa dan aya taji tsoro to zaku zauna lafiya.” Tafawa sukai tace “shine magana.” 
A bangaren ramadan tunda ya shiga daki ya shiga mamakin laila, wai kamar shi mijinta amma ya shigo sai kwayene za su amsa mai sallamarsa, bai samu komai ba daga wajentaba , sai tarbar tsaki daga gareta, lalle dole ya taka mata burki.” Jinjina kai yayi, ‘indai tanajira sai nazo neman shiri gunta, to sai dai ta dade. Ruwa yaje ya watsa. Ya saka kaya sarau sarau na maza ya sauka kasan. Direct shashin lailar ya shiga, tana tsaye a kitchen cana tauna cewgum kas-kas tana d’an raira waka, sai kokarin hada maganin mata take. 
Laila,” ya ambaci sunanta, sai ta juya ta kalleshi ta yatsine fuska. Azuciyarta tana ce wa ‘hmmm ai dole azo a sameni inda nake.’ A fili kuma ta ce “meye?.” Tsayuwarsa ya gyara yace “laila abinda nake so ki dada ganewa shine “nan gidana ne? To dole mace sai tabi abinda nake so, domin wallahi tallahi laila in har kika ce zaki ci gaba da yimin tsaki wallahi sai na fasa miki baki, nine nan na auroki ba keba, wai dan rashin tarbiya in dawo daga nema. amma baki da bakin amsa sallama ta sai kawayenki ko, dan ke baki da tarbiya ko?.” “Ka ga malam ka saurara mini fa! ban shiga harkar kaba, saboda Allah a dakeni a hana ni kuka, kai ka manta me kai min, kuma wallahi yanzu na soma. Ta kuma sakar mai tsakin. 
Bata karasa ba, ya finciko ta ya murde bakin wanda sai da ta sanya kara. 
Ko kannena ba sai min tsaki. ballantana ke da kike karkashina, wallahi kika karai mini tsaki saina tattaka ki anan, wadda ba tada hankali.” 
Kuka ta sanya tare da dora hannu aka “wallahi ramadan ka dauko ruwan dafa kanka, kuma Allah saiya saka mini. Ka dade ba kayi duka abinda kai niya ba. Ta kumajan tsaki da karfinta
Cikin fushi ya wanka mata fuska da mari ya matse bakin, wanda har saida da ya tara jini ya rike bakin tamau!. “Daga yau inhar ba zaki saita bakinki ba,wallahi ni ramadan banda mutunci ba zan dauki raini ga mace ba. Na kawo kici ki sha, nai miki suttura, na biya miki bukatunki, kuma kizo kina min rashin kunya impossible.” 
Cikin kuka tace “karka kara dukana danni ba jaka bace wallahi inka kara saina yi maka barna.” Tsayawa ya yi ya juyo sai ta koma bayan kujera tana kuka. “Laila idan kina so ki zauna lafiya dani, dole sai kinbi abinda nake gaya miki,bana son gaddama da rashin kunya. Amma na kula ke duk kin kware akansu. To ina jaddada miki ki nutsu. Ya yi kwafa ya fice. 
Ko kukan ma ta kasa, sai burgima take “wayyo na shiga uku, wallahi na san shiga tsakaninmu akai, kuma ban da tantama makirar yarinyar nan ceta sama.” Haka ta zauna taita kuka tana maganganu. Can waje ya fita ya zauna akan kujerar roba, ya daga kansa sama idonsa a runtse, ya rasa yanda zai da Iaila, yarinya kullum sabbin halayenta ne ke fitowa. Yana nan zaune yanajin iskarwaje na shigarshi. Ladifa dake sama tana kok’arin saukowa ta leka ta ganshi zaune a wajen, dan tasan bai fiya zama a wajen ba, yanayin yanda ta ganshi ta san ba daidai ba dan ta jiyo hayaniyarsu da Iaila a kasa 
Sai tajinjina kai ta shiga magana cikin zuciyarta, tabbas dama duk wanda yaja ruwa shi kan doka, yau da ace auren an dauko shi tun farko ta turba me kyau anyi shi dan Allah da annabinsa, da kome ma zai faruda sauki. Yau auren dama aka yi shi akan turbar gaskiya ana fuskantar matsala. to inaga wanda tun farkon ma ba a d’auko shi akan turba me kyau ba. Tabbas! ta tabbata auren Iaila da ramadan akwai dan abinda akayi shi, dan bata manta lokacin kafin auren, in suna waya tsakar dare wataran yakan fita ya koma falo dan kar taji, takan tashi tazo ta tsaya ta kofa tana jin me ya ke cewa, surar lailar na birgeshi, yana son ya jishi yana wadakarsa.Da kyakkyawar surarta. Dole inya aurota yasan ita ce mace…. Wasu kalmomin ma bata tajin za ta iya tunosuba saboda tsabarsun yi girma. Tun anan ta gano cewar dan surarta yake son aurota. Musamman dan ya ga ita lad’ifar ba tada abinda ya keso’ numfashi taja tace “Allah kenan, komai mutum ke shukawa yana kallo,” ta fada tana mai sauka kasa. 
Ta bayan kitchen ta fita, harta karasa zuwa gefensa da ruwa a hannunta, tana zuwa ta durkusa tace “zaujina sha ruwa,” kamar kuwa tasan yana da bukata ya karba ya shanye, 
ta kalli idonsa yayi ja, sabida tsabar takaici. Kallonta yayi, yace “zan samu abinci a wajenki? yau na shawo yunwa.” Dan shirutai na lokacin, tace “ai zauji yau ban yi Girki bane, hala ka manta a shashin laila kake?
Had’e rai yayi “yanzu dan ba na shashinki ba zance ki ban abinci ba, tun breakfast na safe ban kuma sanya komai a cikina ba, sabida ban saba da cin abincin waje ba.‘ “Ba haka bane, ban so na shiga cikin hakkinta ne.” ‘lna da iko da kowacce, koba ran girkin ta ba. umartarki nake kawai.‘ ‘To me zan girka maka.” ”Komai ma me sauki”. Sai ta mike tafi dan aiwatarwa. 
Shima mikewa yayi yabi bayanta, dan an kusa kiran sallah. Yana shiga falon sai ya tsaya a kitchen din yace “please baby kiyi sauri ki gama. Kafin na dawo daga masallaci kinji.” “To tace mai. Wanda a kunnnen laila ya fada dake bakin kofar shashinta,tanajan zuciya na kukan data gama. 
Tana ganin ya wuce saman, sai ta shiga kitchen din ta tsaya. ta juyo da kafadar ladifa da karfi tace wallahi “last warning da zan miki akan shige wa mijina ranar girkina, na kula ba ki da alkunya.
Ko kala ladifa batace ba, sai kokarin zuba macaroni da vegetables dan yin jallof da take. Kuma juyo da kafadarta tai da karfi,har sai da lad’ifar tace “wash tajuyata kalleta ” laila ki kula kar hannunki ya kara tabani, ban shiga shirginki ba, ke kuma kina shiga nawa?. Kije ki tambayi mijin naki mana, ldan ni najawo shi.Domin shi ya sanya na dafa maitunda ni ya isa dani“ 
“Kina nufin ni bai isa dani babe “Bance ba, amma Ina gaya miki ki rabu dani‘ 
‘Kome za kice ta bayan kunne na zai shige, ya fice ta gaba, kashedina kawai nake so ki rike.‘ Jinjina kai kawai ladifa tai tanajan hasbunallahu wani’emal wakeel, dan ko kadan bata san hayaniyar, dan rasa kalmomin da zata maidawa laila dinn take. 
Kiran sallahr da aka kirawo ne ya sanya lailar ta juya tanajin kamar ta shako ladifar. 
Ita kuwa, tana gama zuba macaroni da kayan hadi, ta rage wutan ta fice daga kitchen dinn tai sama. Bayan shude war min tinoni. 
Tana Idar da sallahrta sai tabi kan dardumar ta kwanta Dan kwana 2 din nan sam ba tajin dadin bakinta, ga kasala dake damunta, ta rasa meke damunta. Tuno girkin data dora shi ya sanya ta mike cikin kasalar ta sauka kasa,tai kitchen din ta kwashe jelof din a flask, ta kai dining ta aje da filet da cokali, ta koma ta dauko gorar ruwa me sanyi da cup, ta ajje ta zauna akan kujera. Ba dajimawa. Ramadan ya dawo, bai shigo ba sai da ya kunna inji dan ba wuta. 
Yana shiga ya nufi dining, ladifa ta mike dan zuba mai yace “Na hutashshe ki, ya zuba abincin a filet ya zauna yana dan ci. Tana zaune a gefenshi tana kallo suna dan hira samasama, dan dama ramadan ba ma’abocin yin hira bane. Can ya kalleta yace ta zo taci sai ta girgiza kai tace “wallahi bana sha’awarcin abinci yau, abin ruwa -ruwa nake so. ldan ma dole sai na ci to gasasshiyar hanta nake son ci.” Jinjina kai kawai yayi yana ci gaba daci danyanajin dadin abincin. Turus! ta tsaya tana huci, ladifa ce ta fara ganinta ta dan juyar da kai 
Sai ta karaso tsakiyar kujerun gaba kadan “Yanzu adalci ne anan? ranar girkina ka zauna ka nacin girkin wata, haba ramadan,” sai idonta yayi kwal-kwal alamar taruwar hawaye. Wallahi abinda ake min agidan nan yana yawa, ni ga shi can na dora girki, amma ka zauna kana cin na wannan, amma Allah yana gani.” Sai ta koma da baya ta shige dakinta. Ladifa ta kalleshi “kaga k0 zauji,sai da nace ni ba zan ba, amma kace dole.” Wani kallo ya yi mata, sai ta sukwi da kai yace “laifl ne dan nace ki min? alhali ita bata girka mini ba,yau wajen kwana biyar kenan. Ni bance tai min rashin adalci ba sai ita,wallahi halinku mata sai addu,a.”Karasa cin abincin yayi ya mike. Dan sunyi zasu hadu da abdallah abokinsa, sai ya dau key zai fita. Lad’ifa tace “zaujina karka manta min da gasasshiyar hantar da icecream.” Dawowa yayi yana murmushi, ya zauna gefenta ya ce “anya babyna ban yi ajiya ba kuwa? naga kwana biyu fa kwadayi kawai ki keji.” Ya fada yana mata wani irin kallon da ta kejin tsikarjikinta na tashi. 
Sai ta rufe ido dan kunya. “Ni dai babu wata ajiya, kawai dai ji nai ina sha’awar su.” 
Murmushi yayi. Ya sanya hannunsa ya shafo cikin nata ya dan matsa. yace “Allah yasa fatana ya zama gaskiya.” 
Sai kawai ta kifa kantajikin fillown kujerartana dariya.” Murmushi ya kumayi cike da shauki yace “zan tawo miki da su, na tafi .” 
Sai da ya fice ta dago tana murmushi itama tana fatan ace hakan, sai ta kuma sanya murmushi tana haskota da cikin Ramadan dinta, saita kuma sanya dariya, ta maida idonta tv tana fatan ace ya zama gaskiya. 
Ita k0 laila tunda ta shiga shashinta taci gaba da kuka, sai ta tashi ta duba girkin da ta dora, taga ko ya dahu, ta duba ta ga bai karasa ba, tana dawowa ta zauna ta kurawa tv ido ta dau flllowta sanya akan cinyarta, tunani kawai take yi ita kanta, ta san tana cutuwa yau kwana biyar kenan, dole tai kewar mijinta, nasihohin mahaifiyarta dana aminiyarta sara taita tinowa, tabbas gaskiya suka fada, sai ta tuno hudubar Asiya taji tafi aminta da natan, amma ba tajin zata kai kanta ta ba shi hakuri (girman kai rawanin tsiya) 
Haka tai ta saka da warwara, sabida rashin samun madafa, sai kawai ta mike tai kitchen ta kwashe abincin ta zubawa ramadan nasa a mazubin da take zuba mai, tana yi tanajin haushin ganin ladifa tayi mai girki a ranar girkinta, waya sani ma ko har kwananta yake kaiwa ladifarma ta ayyana a ranta,  hakan da tai a zuciyarta. ne ya dada harzukata, ta hada masa abincin ta dauka ta kai can falo ta ajje akan dining 
Ta komata zuba nata taci, bayan gama cin natan. ta dawo falon ta zauna itama tana kallo. Ladlfa ta kalleta tace “sannu da aiki laila.‘ 
Ta amsa a ciki-ciki. Haka suka zauna kamar kurame, kowa da abinda yake sakawa aransa. 
Wajen tara ramadan ya dawo ya bawa ladifa sakonta. da murna ta karba ta zaro ice cream jikinta har rawa yake ta fara sha tana lumshe ido. Ya ce .”uwar kwadayi.” ‘ 
ya kalli Iaila yace “ke ga naki.” Sai tabi ledar da harara. Cikin karfin halin ta tajanyo shi, dan tana son nunawa ladifa cewa ba wai abincin ne bata iya ba, har da zaice tai mai. “Ga abincinka nan a dining.” Daga mata kai kawai yayi yajuya. “Hamma ladifa ta fara yi, sai ta mik’e da robar icecream din,tai musu sallama, ta dau ledarta tai sama, dan bacci ta keji. 
Su kuwa suna zaune kamar kurame, sai kallon juna suke a fakaice. Musamman Iaila da duk ta farajin ta fara saukowa daga fushin. Musamman ganin Lad’ifa na son wadaka a ranar girkinta. Sai yanzu ta gano abinda sara ke nufi.Karshe itama tashi tai ta dau tata ledar tai nata waje. 
Shi kuwa sai goma ya bar wajen, bayan ya karkashe komai, wanda ko kallon abincin lailar bai ba. 
Adaidai lokacin Iaila ta dawo falon ta kunna fitila tai wajen dining, duk sai ta bubbude flasj, flask din, taga babu abinda ya taba. Ji tai kamar ta kurma ihu, tasha wahala wajen girkin, amma ko tabawa baiba, sai taji zuciyarta na wani irin suya.Sai kawai ta dauke ta ajje a ma’adane sanyi dan kar su lalace. Ta koma dakinta ta zauna ta tallabe kumatu, ta kwanta ta runtse ido,juyi kawai take cikin damuwa, ga maganin matan data d’irka sun fara aiki, saijuyi take, a nan amon muryar mahaifiyarta da na sara yayi ta zuwar mata kunnuwanta, kan shawarwari da suka bata, 
juyawa tai ta ga har sha-daya, saita saddakamanta tashi ta fesa wanka, ta mummulka humra kalakala, gyara can getta can, ta saka kayan bacci wadda dasu da babu duk daya ne, ta zumbula hijab ta futo ta rufe shashin nata tai sama. 
Ahankali take takawa harta kai karshen da zai sadaka da dakinsa,tana kokarin bugawa sai ta ga alamar kamar abude take, turawa tayi ta shiga, yana nan bai bacci ba. Hada ido sukai yana gaban laptop yana latsawa ga takardu birjik agefe. Dauke kai yayi yajuyar da kai. Karasowa tai tana son ta karfafawa kanta gwiwar aiwatar da neman sulhu, ba tare da ta bada kai ba. Cire hijabin tai ta matsa gefensa, ta shiga shigewa jikinsa tana mai magana. Cikin wani irin salo. K0 kallonta bai ba. Duk da kamshin humrorin da ta sanya na shigarshi matuka. Sai ta kalleshi ta runtse ido “habeeby magana na ke son muyi.” Sai da ya dade sannan yace “Ehem inajinki.” Sai ta gyara zama ta ce “kan duk abubuwan da suka faru ne. “Yanzu ya dace ace ka kula wata a super market harda karbar lamba, sannan ya dace ace kayi tafiyarka ka barni? sannan ya dace ka daina cin abinci na? har kana bawa wata damar maka girki a time dina?.” Sai tai shiru tanajiran taji me zan ce, can yace “lalla ba kida ganewa,tunda komai bakya yinsa cikin nutsuwa, ai sai ki tayi.” Cikin daga murya tace “amma ai kai kajanyo.‘ “kinga, kinga, ban janyoki ba, ki fita kawai in hauka zaki min.” Cikinjin haushin maganarsa tace “ba inda zani, sai ka gaya min dalilai.””Dalllai kike so ko? to nayo tahowa tane saboda na isa, baiwa budurwa Iamba kuma bai shafeki ba.” 
Nan da nan ta harzuka, sai garin ta nuna nadamar sai ta kuma burkicewa sai sakin maganganu,take nan suka dada harzuka su dukansu. 
Ladlfa na daki tai juyi, cikin barci taji kamar hayaniya, tashi tai, Sai tajiyo tashin muryoyinsu. Tsaki tai tajuya ta koma ta kwanta, tana kamo addu’a a bakinta. 
Har inji ya mutu wajen Daya  na dare suna fada, wanda alokacin amon muryoyinsu yafi tashi saboda dare. 
Sai wajen 2 suka lafa. Nan kuma Iaila ta shiga nuna nadamarta kan yayi hak’uri. Shi kuma alokacin ya dada harzuka yace ta tashi ta fice mai daga dakinsa baya bukatarta. Ganin ta ki tashi sai ya tashi shi ya fice ya bar mata dakin.Haka taci kuka ta gode Allah bacci ya kwasheta. 
Da safe karfe bakwai ramadan na toilet yana wanka, Iaila ta shiga dakin, bayan ta dawo daga shashinta, ta dada gyara kanta, babu wani shamaki ta bude bandakin tai shigewarta, tun shigarta ciki zance ya sha barnbam. wanda fitowarsu sai da suka raya sunna, tabbas kowanne yayi kewarjuna. Lalle babu abinda yafi zaman laflya dadi. Sai wajen karfe goma suka fito Iaila rike da hularsa tana dariya. Alokacin ladifa ta fito. Tana ganinsu tai murmushi tace “zaujina an tashi lafiya ya kafeta da ido “kalau sweat heart.” 
Murmuahi Iadifa tai jin sunan daya kirata wanda da take bidar ya gaya mata su, yau gashi a arha ya fad’a mata. 
Tana son taiwa Laila magana. Sai ta kula wani shan kamshi da take, ga wani yauki da take tana kwarkwasa, sai wani babbakewa take kamar basu nejiya suka narki fada ba. 
Sai itama ladifar ta d’auke kanta tai wucewarta abinta. 
Ayau laila Junta take kamar an dauke mata wani gungumen dutse daya tokare duniyarta.Fita yayi ita kuma ta koma d’aki. 
Tana shiga dakinta, ta zube akan gado,ta kalli silin dakin tace “dan dak’yau, lalle ta yarda ramadan ba kanwar lasa ba ne, dole ta canja takunta. 
Kwance yake a dakinsa, dake dauke da katifa sai sauran kayan tarkace na maza, hannunsa rike da waya. Nan ya Ialaubi lambar laila dake adane a ma’adanar lambobi, yana kokarin kiranta da adduar Allah ya sanya layin na aiki. 
ilai kuwa sai gashi ta shiga, nan ya gyara zama. Bayan an dauka yace “ranki ya dade, har yanzun kina maidugurinne? na matsu faki dawo irin yana yi kamar bai san tayi aure ba. 
Laila dake gaban mudubi lokacin ta fitone daga wanka tana shafa mai, sai taja da baya, dan tabbas muryar murabus ta keji. Sai ta samu gabanta da faduwa dam!dam!. 
Cikin in’ina tace “wane ne?” Cikin takaici yace “au bama ki gane ni bane? to murabus ne yaushe zaki dawone?.” Bata san sanda tace mai ba “kai nayi aure fa, dan Allah ka daina kirana.” “Ke dakata ko baki fada ba nasan kina da aure, dama so nake naji ta bakinki, lalle laila kefa ‘yar duniya ce, wato ni kika yaudara ko? to wallahi tallahi sai kin gane waye murabus.” 
Da sauri ta kashe wayar gabanta na tsananta faduwa cikin tsoro,babu wanda ya fado mata sai Ramadan “cabdi Ta ambata da karfi. 
Nan fa wayar ta shiga ruri’. data mutu saiya sake bugowa, da sauri ta dauka ta kasheta dukka 
To fa Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE