NAYI GUDUN GARA CHAPTER 21

NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 21
Tsaki yaita saki akai -akai tare da tsuke bakinsa, ya ce “zan zame miki kamar cewgum. ” Sai ya mike yayi mika ya kuma kafa ido akan wayar, ya duba whatsap dinsa ya duba,yaga tabbas tana whatsap da lambar sai ya tura mata sako ya fice. 
Dak’yar ta gama shafa man nata, ta zira doguwar riga, ko kwalliya ba tai ba, ta koma gefen gado ta zauna ta dafe kunci, tabbas! tasan ta yi kuskure da bata sanar da shi aurenta ba, ta san daba lalle ya nemeta ba, sai dai su gama fadansu a waje, amma yanzu da matsala, sai taja numfasa ta mike ta fita falo.Ta duba agogo lokacin karfe goma shabiyu da rabi ta d’ora girki, yayinda fargaba ta cika zuciyarta,sai kallon wayarta take tana son kunnawa, amma kuma tana tsoron karta kunna ya bugo.wa.
Tana d’aki a kwance, dan tun safe ta kejin ba dad’i, wanda sai bayan fitar Ramadan abin ya ta’azzara,ko tashi ta kasa yi, dan data tashi jiri ke d’ibanta,da kyar tai wanka tanajin bakinta harwani dacidaci yake yi,gashi yau ramadan ya sanar mata a gida zai yi lunch,yau ya zatai ta ambata a zuciyarta. Sai wajen daya saura ta samu ta sauka kasan, fuskarta tayi fayau! ta dad’a dashewa, direct kitchen ta zarce ta zaro nama a fridge ta zuba ruwa, dan kankarar jikinsa ta salance kamshin jikinta ne ke shiga hancinta sosai takejin zuciyarta na tashi, wani iri takeji komai ba dadi sai ta zame ta zauna agefen kitchen din ta sunkwi da kai, ta dade azaune, har sai 
da taji jirin ya sauka,daga bisani ta mike ta bude fridge dan dauko citta, sai k’amshin danyen kifl ya bugeta, wani irin yunkurin amai taji ,da gudu ya taho mata, kafin ta kai ga fita daga kitchen din har ya zubo, sai ta sunkuya awajen tai ta yinsa kamar ta amaryar da abinda ya ke cikinsa. Tana gamawa ta zube agefe tana maida numfashi, ga kanta sai ciwo yake me tsanani, hawaye ne na ido daya ke ta zubo mata. Adaidai lokacin sallamar ramadan ta karade falon. Ganin kitchine a bude sai yayi wajen direct ya shiga, a yashe ya ga ladifa tana lumshe ido, da sauri yayi kanta yana “babyna meya faru? Cikin kidima ya dago kanta. “me ke miki ciwo?.” ta nuna kanta da cikinta. 
Kinkimarta ya yi kamar ‘yar baby ya fita kwantar da ita akan kujera. Sai ya diririce ya rasa mai zai mata, kiran laila ya fara k’walawa, tana d‘aki a zaune hankalinta atashe, dan bayan kunna wayarta taci karo da sakon na murabus, na cewa kota ringa daukan wayarsa, ko kuma yayi silar rushewar aurenta, ya hada mata tuggun da ba zata iya fita ba, dan komai game da ita ya sani, har gidan nata da mijinta. 
Abinda ya sanya ta kasa ko cin abincin data dafa kenan, wani irin kadawa cikinta yake sabida tsoron kar Murabus ya kawo mata nakasu a aurenta,dan tana son aurenta sosai! Jin karfin kiran ramadan ya sanya ta fice da dan sauri,turus! ta tsaya ganin yanda ya rike hannun ladifa yana matsa mata tare da shafa fuskarta. Kishine taji ya tokare mata kirji, sai ta karasa tace “gani habiby.” “Yawwa gyara wajen da baby tai amai bata da laflya ne fa.” 
Sai alokacin ta kula da yanda ladifa ba ta cikin hayyacinta, Sai fuskar lailarta canja, harga Allah kallon da taima ladifar sai taji ta bata tausayi sosai! dan laila tana da tausayin mara lafiya ta nan bangaren (mutum dama tare yake) 
Ganin yanda yake ta nanukar lad’ifa ya sanya taji kishi na dada damunta, yana kokarin kore tausayin da taji, sai da ya kuma kallonta. 
Tace “habiby jeka saman zan yi komai.” Dan daya zauna tana ganin abin haushi, gwanda tai aikin. Mikewa yayi ya hau saman yana tsallake step da sauri. 
Gyarama lad’ifar kwanciya tai sai ta shiga kitchen din, ta shiga gyara wajen bayan ta gama, ta fito dauke da cup da tea spoon tayi dining ta bude fulas na shayi, ta zuba ruwan tea yana turiri da suga da madara, ta koma kusa da ladifa tanai mata sannu, ta dan tashi zaune ta jingina da kujera ta kuma cewa “sannu ga shayi ki sha, ko kyaji kwarinjiki”, daga mata kai tayi ta karba, ita kuma ta zauna gefe tana kallonta, duk da tarin haushin ladifar da takeji amma ta bata tausayi, ganin yanda tashi d’aya ta dada figewa tai zururu-zururu. Alokacin ramadan ya sauko daga shi sai gajeran wando da vest, ya zauna ta daga gefen da lad’ifa take yace “baby ya jikin?.” 
Sai ta daga mai kai, kanta na wani irin bugawa, yace “daure ki sha, a ganin yanda take dan layi sai ya matsa ya shigar da itajikinsa ya shiga bata abaki. 
Dum! laila taji, sai ta diririce musamman ganin yanda lad’ifar hannunwanta ya sauka kan jinyarsa wanda ita bata san ma ta yiba, sai ta kumajin kishi na sasukarta har wani jan ajiyar zuciya take akai kai. 
Cikin karfinn hali tace “habiby kawo na bata, wani abun ai sai mata.” “Bar shi kinji laila.” Sai ta koma tana harararsa ta gefe kirjinta na bugawa saboda kishi, arayuwarta babu abinda ta tsana irin ta ga mace ajikin ramadan, ji take kamar ta mutu saboda kishi, sai ta tashi tace “Allah ya sawwake,” tai gaba k0 gabanta bata gani sosai saboda tsananin kishi. 
Wani aman ladifa ta kuma kwararowa ajikinsa, sai kawai ramadan ya tsaya ya kura mata ido, tunani kawai yayi suje asibiti, sai ya kinkimeta yayi sama da ita, bai zarce ko’ina ba sai bandaki, yayi mata wanka suka fito ta shirya, yana yi yana riketa saboda jirin dake dibarta ga kafafuwanta dake gaza daukanta 
Hijab ta sanya suka fito, tana taka matattakala ahankali saboda rashin kwarin jiki, tai luuuu! za ta fadi ramadan ya rungumeta ajikinsa gam! Wanda a idon laila, Nan ya kuma 
sunkutarta suka sauka kasa, sakin baki laila ta yi, “habiby ya haka da daukanta?” ko 
kallonta baiba yace “ki kula da gida kawai, banasan kishin nan mara dalili, kin san ai 
dalilin ba tajin dad’i ne ko?.” 
Sai ta tabe baki ta juya tana jin kamar ta nadawa ladifa duka, wanda duk tausayin ladifar da taji ya gushe saboda kishi ya danne tausayin. 
Yana ajjeta amotar, yaja suka tafi asibiti. Kafin suje ta danji dan damadama, koda suka je ma da kafafuwanta, suka shiga asibitin, inda likita ya duba ta ya tabbatar cewar tana da shigar ciki na sati shida, saboda tsabar murna ramadan sai yayi ta sakin murmushi. 
Likita yayi gyaran murya ya ce “saboda mshin kwarin jikinta, yanzu zan tura za ai mata karin ruwa leda uku, da allurai aciki, insha Allah kan dare za taji saukin jikinta. Bayan anjona mata karin ruwan, ramadan ya zauna gefenta idonta alumshe ta kalleshi “zaujina kaci abinci kuwa?.” 
Sai daya shafl gefen kyakkywar fuskarta yace “banci ba kyakkyawata amma yanzu idan na koma laila zata ban naci, sai ta kuma lumshe ido tace “zaujina kadaure kaci ka ji.” 
Murmushi yayi ya shiga shafa lebenta da yatsun hannunsa d’aya, duk da tana cikin rashin Iafia tana jin dad’in hakan, murmushi yayi ya mike yace i love you babyna.” 
tace “me too.” Har yama sai ya dawo “babyna me zan tawo miki da shi? Sai ta kalleshi “dearna hadin salad nake so kawai, mai tumatur da leman tsami, sai mai da magi.“ 
Hannunsa ya zura a aljihunsa ya ce “an gama ran gimbiyata ya dade maman unborn, bari zanwa nurse magana su kula da ke kan na dawo.” 
“Yawwa ka gayawa hajiyata da yaya karima banda lafiya, sosai ina son ganin hajiyata.” “Ba sai an gaya musu ba, anjima zamu tafl ai ruwan na karewa.” Sai tace to.” 
A hanya ya tsaya ya sai salad da tumatur da leman tsami ya tafi? gida, sai da yama koma gidanne ne ya tuna fa ya baro aiki a office, sai ya bugawa shugabansu kan matarsa ba lafiya ai mai uzuri. 
Direct shashin laila ya shiga, tana zaune tana kallo a wayarta. Ya tsaya ya ce laila, ta dago tace “yana ganka kai kadai ina ladifar?!‘ 
“Karin ruwa ake mata, sai anjima za a sallameta,please yankamin wannan ki hada ladifa ke sanci.” 
Yatsine fuska tai, “akanme zan zauna ina aikin kishiya. D’azu ma da nai mata ganin dama ne, kaine da hakki da ita sai ka gyara mata.” 
Za ki karba ki gyara ko saina mangareki. Ya yau ina yabanki sallah za ki kasa alwala, ganin d’azu abinda kikai, baki san yanda naji dadi ba, amma shine dan abin da kikai ba dan Allah kikai d’azun ba, shine yanzu kika fara d’agan murya.Wallahi idan ba ki d’auka ba sai na nuna miki ba ki da wayo.” 
Ganin yanda ya harzuk’o sai ta karba fuskar nan a had’e.” “Duk ka wani rikice dan mata ba lafiya.Kamar wata ‘yar gwal” Saboda takaicin maganar tata bai tanka ba ya fice, sai tai tsaki da kamar ba zatai ba, sai daga baya ta mik’e “Kinci darajar baki da lafiyaa ne wallahi, amma ba dan haka ba, babu abinda zai sanya na bata lokacina a aikin kishiya,tana yankawa tana zaginta azuci. 
Bayan yaci abinci, lokacin laila ta gama had’a salad din ta saka a karamin kwando ta kai 
mai, ya kalleta “ki taso man, ki duba ta ko zuwa anjima ne saboda zan dan fita ne inna kai 
mata. Tsaki tai, sai kuma tai saurin kallonsa taga ko yaji tsakin, dan tana tsoron cin zalinsa. Ganin yana danna waya baiji ba, sai tayi daki da sauri,ta dauko mayafl sai da ta tsaya ta 
getta fuskarta, ta goga hoda ta dan mutsstuka jambaki, ta bulbula turare 
lad’ifa Tana bacci suka je, lokacin har d’aya ya kare an kuma sanya mata wani, sunkuyawa yayi 
daidai fuskarta yayi kissing kumatunta, ya dago ya zauna gefenta, laila kamarta sanya 
kuka, tace “wai ni habiby mai yasa ba ka boye feelings naka akan yarinyar nan agabana ne?.” “Matarki k0 tawa, bana son sanya ido , ke in ke naiwa wani zai ce dan me?.” “Agaskiya bana so atoh,” ta fad’a tana huci. “Kar Allah ya sanya kiji din.” Sai ta tabe baki tajuya. Adaidai lokacin ladifa ta tashi tace “zaujina ka dawo?.” “Sannu da kokari laila na gode.” Hararta tai ta ce “ba danke nai ba.” 
Sai bata ce ma lailar komai ba, ta shiga kokarin tashi, sai ya dagota ta zauna ya gyara mata robar ruwan. Jikinta na rawa ta kalleshi “ina salak din,” yanayin yanda tai, sai ta bashi matuk’ar tausayi, ita kanta lailan ladifar ta bata tausayi. “Sunkwi da kai ta yi, ta kifa kanta jikin filo, dan kamshin turaren laila na sanyata zuciyana na tashi. A hankali ta fara yunkurin amai amma babu abinda ya tawo saboda babu abinci a cikin nata.” 
Rik’eta ramadan yayi yana shafa bayanta. Murmushi laila tai ta mik’e tace “zan d’an fita na duba wata. M.” To yace mata, ta fita tana murmushi dan ko ba komai ladifar taji ba dadi. 
Ruwa ya d’auko ya bata ta dan sha ta jingina, sai ya zauna gefenta yanajin kamar ya maida yarinyar cikinsa, dan yana jin ta zama jini da tsokarsa, ga farincikin gudan jininsa a jikinta, 
salak din ya dauka yajuya mata,ya shiga bata a baki yanayi yana shafar cikinta ahankali, 
yanajin wani irin dadi,ji yake babu wanda yakaishi farinciki a yau ace ga shi an haifa mai yaro ko yarinya. Haka yayi ta bata yanayi idonsa nakan lips nata, da maikon salad din ya dan shashshafi samansa, baisan sanda ya sunkuya ya shiga tsotsar lips d’in nata ba, ita kuma ta shiga lumshe ido, saboda abin yayi mata sai taji rashin lafiyar ma duk ta fara guduwa. Tanajin bata taba samun kulawa awajensa ba irinta yau. Alokacin laila ta shigo ta tarad da abinda yake ma ladifa. Wani irin buga kofa tai da k’arfl ta Fita, Hakan ce ta sanya ya dago da kansa ya kalli kofar, itama haka. 
“Wannan buga kofar tabbas! Laila ce sai yaja tsaki da haushin abinda lailar ke yi na rashin nutsuwa.” Ita kuma lad’ifa sai taji ba dadi tace “zauji ka bita gaskiya ba ka kyauta ba.” “Zaki fara k0? Me akai mata.” “Ni dai Allah banji dadi ba. ” “To ai kece d’in, ba ki ganin yanda kike dad’a kyau ne wai.” “Ni ce me?.” Ta fada kicin sanyin murya da shagwaba, ka bita please.” Sai ya ajje salak d’in ya fita. 
Tana can daga gefen wata mota daga can gefe, inda ba mutane a wajen, sai sharar hawaye take, ta juya baya, ya tsaya ya kalleta “laila me ya faru ne kika fita kika banko k’ofa?.” 
“Ban sani ba ramadan, kuma wallahi ba zan taba yafe amanta da ake ci ba. “Kinga laila, yarinyar nan ba laflya gareta ba, meye ne dan na kula da ita?.” “E! na san ba tada laflya , amma me ya sanya tunda ka zauna gefenta,baka da aiki sai tsotse-tsotse agabana? ko ni ba rai gareni ba. In bandajaraba ma mace ba lafiya amma ka kasa maida maitarka. 
“Gum! Ta ji ya bige mata baki.” Sai ta sanya hannu ta rufe bakin tana kuka a hankali. “Wallahi tallahi zan iya illata yarinyar nan a kanka, dan na kula kafi sonta.” “Bisimillah karki fasa, ke meye ba nai miki ne ko kin manta, matata cefa, halalina, kuma ranar girkintane, dan Allah ki saurara mini laila.” 
Karar wayarta ce ta karade gun, sai ta duba taga lambar murabus! duk sai ta diririce ta kasa dauka, ganin hakan ya kura mata ido, da sauri ta kashe wayar. Girgiza kai kawai yayi ya bar wajen. 
Yana barin wajen ya kuma bugowa, Sai ta samu damar daga wayar ta ce “murbus are you mad! Kasan cewa ina da aure,amma baka shayin bugomin waya, to karka kara.” 
Daga can murabus yace “Ba na san wani dogon turanci, kawai ki kaso auren nan, nazo na aureki, dan wallahi har yanzu kece araina .” 
Tsaki tai ta kashe wayar tana jin ya zama dole ta canja lamba saboda murabus ya fara damunta, danjiya har tsakar dare ya kirata. Allah yaso ramadan ba a dakinta yake ba, kashe ma wayar tai dukka ta wullajaka ta koma asibitin. ’ 
Sai dare suka koma gida lokacin ladifa ta warware, sai rashin karfinjikin, a hanya yatsaya yayi musu take away suka karasa gida. 
Bayan kwana biyu 
Tana tsaye gaban mudubi tana taje kanta, cikin riga doguwa daga sama ta dan kama, ta bude daga kasa. 
Adaidai lokacin Ramadan ya fito daga toilet ya tsaya yana kallonta, kirjinta yakewa duba, bai taba duban dan cikar daya kara ba sai yau, sai ya kalleta sama da kasa yana girgiza kai, ta baya ya rike kugunta yace yaya dai maman baby, naga nan da nan sun dan fara cika ne.“ Kunyama taji ya bata, “nikam bansan dalili ba.” 
Sai yayi murmushi tabbas yasan ana cewa dama ciki na karawa wasu matan cika, sassan jikinsu ya kan kara girma. 
Musamman da yake rigar Ladifar yadinta me rawa ne, hakan yasanya komai ya dada fitowa, data motsa sai komai nata su motsa. 
Nan fa oga Ramadan ya shashance duk inda tai idonsa na kai. Ita kanta al’amuran ramadan na bata mamaki, tunda ta samu cikin nan ya dada makalkale mata, ta rasa dalili, wanda shi a wajensa dadinsa kawai yake kwasa, musamman ganin abubuwan da yake wa kwadayi a kai sun dada girma,ga shi sosai cikin ya dada kara mata yawan ni’ima. Izuwa yanzu laila tasan da shigar cikin ladifa, duk ta damu kanta kishi karara take nunawa akan cikin, ko kuwa agaban ramadan dinne, musaman ganin yanda ramadan ke bawa 
ladifar kulawa, intai magana yace laulayi take saboda duk safe sai ladifar tayi amai haka duk dare, kamar ka’ida abin ya zame mata, ga shi ba kowanne abinci ta keci ba,dan in ta ci shinkafa da rana to da daddare ta ci ta haka za ta kwan tana zubar da komai da taci, ga shi cikin da tsirfa, ladifar tace dole sai tuwon hajiyarta za taci, duk dare ramadan bayan ya dawo daga aiki sai ya biya ya amso mata tuwon hajiyarta. Laila na shiga damuwa, hakan ya dad’a harzukata kullum cikin fad’a suke da ramadan, da k’arfin hali ta hana zaman ladifa a felon kasa, saboda sanin bata son turare, sai ta bulbulo shi, ta fito falon ta zauna tana tauna cewgum, ita ko da ta shaka za ta fara kwarara amai kamarza ta shide, ganin dalilin hakan ya sanya kwanta -kwata ladifa ta daina sakkowa kasan, saboda ta kula laila da biyu take sanya turaren duk dan ladifar ta jigata. 
K’arfe taran dare suna zaune ita da Ramadana a falonta, da yake girkinta ne wayarta ta hau kara kuma tana kusa da ramadan, sai ring take ramadan ya dauka, kan ya danna ta fito daga kitchen aguje ta wafce wayar, gabanta na faduwa, sai tai sauri ta kashe wayar ta soke a gefen zaninta, kallonta yayi cikin mamaki yace “ke me ye na kin d’auka, sai ta fara inda inda “dama…daman me adashi ce kuma ni ban san me zance mata ba.” 
Kallon yanda duk ta diririce yayi sai ya kauda kai yana ayyana abubuwa da yawa aransa. “Ban wayarta ki.? 
Sai tace “akan me?.” “Ki ban nace.” Jikinta ya hau rawa ban’ tace na zuwa,” ta shige kitchen da sauri.” Kwafa ya yi dan ya kula da yawan wayar da ake bugo mata. 
Ranar sabar laila ta samu ramadan a daki, yana tsaye yana gyara hularsa ya dan sunkuya yana duba mudubi, ta tsaya agabansa ta saki murmushi, aduk sanda ramadan yayi kwalliya, sai taji kishi ya turnuketa, sabida tasan dole wasu ‘yan matan su yaba, wani numfashi taja ta ce “habiby ina son zuwa gidan suna anjima, kaga na wancen satin banje ba, kuma wallahi naso zuwa.” Ba na son yawan fice -fice laila, ki buga waya ki mata barka mana.” Gaskiya ramadan ka barni naje, kaga sai ka dawo ka mik’a ni a motarka.” Ban baki iziniba, abar fitar nan daga baya kyaje barka.” Sai ta d aga murya. “Yanzu ya dace ace ba zanjje ba, wallahi nikam gaskiya sai naje.” “Amma ba da izinina ba na gaya miki.” Ya zari mukulli ya fita, sai ta buga cinya “wallahi sai naje, haka kawai kana san maida ni matar kulle,” da sauri ta bishi a baya.”Yakamata ka barni naje kaji, ta bishi tana mai magiya har waje. “Har abada ke ba a gaya miki magana alokaci daya kiji, sai kin kawo complain, wai ba kya duba lad’ifa ne ko tana son abu nace aa wallahi ta barshi kenan, amma ke sam.’ Ba kya duba irin haka.” “Lad’ifa da ban,ni da ban, dama ai ita lusara ce,ni ko ba zan lamunta ba ehe.” 
“Ai sai kiyi yanda kike so, ya shiga yayi riverse ya fice daga gidan.” “Atoh da yafi maka, Dan ka naiwa waccan, to ni ba ita bace.” Da sauri ta shige shashinta ta fad’a wanka, ta fito ta shiga fente fuska da kwalliya tayi shiga ta kece raini ta tafi tana mai jin haushin ramadan sam! Shi baya kulawa dakai matansa 
unguwa amotarsa, inba asibiti za a ba, ko gidan abokansa, sai dai subi titi, wallahi ba zata sabuba, kamar ita ace tana hawa motar haya, ta fada tare da tura get ta fice. 

Hmm

domin karanta wasu

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE