NAYI GUDUN GARA CHAPTER 22

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER22
Hankalinta kwance tai ficewarta, sam! ba ta gano cewar gatse ramadan yayi mata ba. Musamman da taje ta hadu da ‘yan uwa da abokan arzik’i. Wata mata mai saida k’ananan kayan mata kala -kala, ta bajewa laila tana ta siya, hakan ma ya dada sata shan takewa. Ta yiwa matar nan ciniki sosai, ba ita ta tashi komawa gida ba sai wajen shida. Faka motarsa yayi ya shiga gidan, shiru falon babu kowa.Direct saman ya yi dan bai tunanin cewa laila ta fita ba, saboda shi ya san gatse ya yi mata. Dakinsa ya shige, wanka yayo saboda zafin da yakeji. Sannan ya fito ya shiga wajen ladifa baby. Tana zaune da kofi a hannunta tana shan kwalaba da nono, sanye take da riga da siket mai siririn hannu. Mikewa tai tace “sannu da zuwa zauji na, ban san ka shigo ba.“ 
Hadata yayi da jikinsa ya ce “ke da ba lafiya ba maman baby, acici kullum bakinki na motsi.” Dariya ta sanya “wallahi nima bansan mai ya sa nake yawan ci ba, tunda 
babynka ya fara girma, nama d’anji dama-dama fa.” 
Cikin jin dad’in maganarta ya shafi cikin nata da ya dan fara turowa. “Haka nake so bari naje na kunna inji. Ki gyaran daki, ba na son ana barmin shi da datti.” Tana tsaye ya juyo “ko baki ji bane.” “Naji, kawai dai na san girkin laila ne kar na shiga ina sherewa ta zo abu kuma ya zama na magana.saboda ni duk ranar girki na ina gyarawa.”
“Za kije ki gyara ko sai raina ya baci. Dan ita ba ta gyara ba,ke kuma sai kiki?.” 
Ganin yanda ya kafeta da ido fuska atamke tace “Allah ya baka hakuri bari naje nai.” 
Fita yayi ya kunno inji, yana kunnawa direct wajen laila ya yi, yaji kofar a rufe. Sai ya tsaya turus! Yajuyo da mamaki a ransa. Alokacin ladifa ta fito daga kitchen d’auke da mopper a hannu, zata hau saman. 
Ganin fuskarsa a had’e ya sanya gabanta yadan fadi sai ta kalleshi tace “zauji ya dai?.” Dan tsaki yayi, yace “baby fita laila tai ne?.” “E! mana, ai na dauka ka sani, baka dade da Fita ba, itama ta fita suna.” 
Kwafa yayi “laila, laila ba ta ji yanzu saida ta man.” 
Shiru ladifar tai bata sake magana ba, alokacin aka kira sallah.Ya tafi masallaci ita kuma tai sama dan ta karasa gyaran dakin. Tayi kuma sallah. 
Laila kuwa na fitowa daga gidan sunan. Duk tunaninta yayi gida kar ramadan ya dawo ya tarar ba ta nan. Tafiya take dan ta karasa titi, adaidaita ya zo wucewa tai sauri ta tsaida shi, ya faka ta gaya mai inda zai kaita. Ba musu ya dauketa suka fara tafiya. Sai da suka hau titi Dodar, sannan ya ce “hajiya zan dan biya ta can na zuba mai, taso ta gane muryar, amma hankalinta sam! bai 
kawo ba, tace “ba matsala dan Allah kai sauri.” 
Bai magana ba, ya tatari adaidaita sahun.Bayan ya sha man, titin daya kamata ya mike ba nan yayi ba. Lokacin kanta na kan waya tana duba sak’on da aka turo mata. Dagowarta ya sanya ta fahimta. Kai malam meye na biyo damu ta nan.” ’ 
“An biyo da ke din,” ya fada tare da waigowa. 
Da sauri ta dafe kirji, “murbusl na shiga uku.” 
Sai ya fasa dariya “kina mamaki k0? please ka sauke ni, dafa da yanzu ba 
daya ba, kiran ma da kake min ya isa.” 
Bai magana ba, ya kara gudu kamarta kurma ihu . Kallon tiiti tayi babu damar ta dira saboda suna tsakiya hakan zai iya sanya inta dira wata motar tabi ta kanta.Sai ta fasa taci gaba dayi mai magiya. 
Sunyi tafiya mai nisa, tana ta addu’ar Allah ya sanya su samu goslow ko danja,in suka tsaya ta dira.Wani karamin titi sukai da ba mutane, kuma babu motocin da suke wucewa, titin ko fitilar gefen titi babu, nan yaja ya tsaya, da 
sauri ya fito ya tsaya ta gefe d’aya yace “laila mushan badda musulmi, wato 
kina ganin ruwa tasha kin yaudaren ko?.” 
Wani banzan kallon tai mai “kai asuwa? dallah malam ka sarara min ta yaya 
ma kasan cewa ina wajen suna?.” 
“Ki bini a sannu, dan wallahi zan iya keta miki mutunci, kalli gabas da arewa 
kinga alamar mutum ne?.” 
Gabanta ne ya fadi ta ce. 
“Dan girman Allah ka kyaleni, kai bakasan darajar aure bane wai?. 
“Na fiki sani ma, farko kin blocking dina a whatsapp, kina kashe min waya, in da nasan yau za ki fita, kin manta ina cikin followers naki a IG ko, to anan naga hirar ku da sister naki, na zaki suna, take tambayarki karfe nawa za ki, ki ka gaya mata, wannan dalilin ya sanya nazo gidanki na lafe, lokacin da kika fIto dan tafiya na bi bayanki har kika hau adaidaita na biku a baya. Na ga inda kika shiga, haka nai ta bulayi,har lokacin da kika fito, to ki sani mai son abinka ya fika dabara.” 
Wani tsoron da bata san tana da shi ba, ta ji ya bijiro mata, babu abinda take tunowa sai tijarar ramadan.Please murabus indai kana ganin naci kudinka ne, dan Allah ka gayan na baka kudinka da naci, ina son aurena karka kashe min. Kusa da ita ya zauna sai ya kyalkyale da dariya. Yau da ace ni dan iska ne wallahi da saina kwashi rabona ajikinki. Amma ki sani ina da ilmi ba zan shiga gonar wani ba, shawara nake baki, da ki kaso aurenki kizo muyi, duk da ma yanzu na ganki kin dawo kamar ba laila mai jikin dake daukan hankali ba, amma ko a hakan kika fito zan maleji, inba haka ba wallahi saina kunsa miki salalan tSIya.“ 
Yana magana ta sanya kafarta ta dayan bangaren da sauri ,ta sunkuci jaka, kobi ta kan takalminta ba tai ba, ta barshi a cikin adaidaitan, ta fara gudu shima da gudu ya fito ya rufa mata baya ya sha gabanta, sai ta tsugunna ta 
saki kuka “dan Allah murabus ka rabu da ni, wallahi zan biyaka kudinka” 
Wallahi bana son kudin ke nake so.” Ya fad’a yana mata wani irin duba. 
Sakala jakarta tai a wuya, dan bata son ta fad’i, saboda da muhimman abubuwa aciki,ganin tana kokarin gudu, ya kuma shan gabanta, yace “oya muje ki shiga, wallahi in ba haka ba zan mauje ki,” 
Kuka take na fitar rai, yau tayi dana sani fitowa unguwa da tai, tiryan -tiryan ya tasa ta agaba ta shiga adaidaitan. Ga wayarta na ring ajaka amma tsoro ya hana ta d’auka. 
“Wallahi, wallahi idan banji gamsasshen zance ba, ba zaki bar nan ba. Kuma duk gudun da za ki saina tarad da ke, kina dai ganin yanda titin yake, ina jinki.” 
Dabara ce ta fado mata tace “naji zan kaso, kuma zan cigaba da charting da 
kai.” “Kinyi promise ko?.” 
Ta gyad’a kai.Nan ya tashi babur d’in ya bar wajen, sai da suka fita can babban titi, sannan ya ajjeta ya fafara yabar wajen. 
Da sauri ta kuma tsaida da d’an sahu, ta gaya mai inda zai kaita, tana shiga ta zaro wayar, miss call din ramadan ne rututtu, gabanta ya fad’i “Na shiga uku,” 
ta fada tana duba agogo tara saura. 
Yana tsaye a falon yana kaikawo saboda tsabar bakin ciki. Ladifa kuwa na samanta dan bacci takeji sai shi kad’ai. Sai kawai ya kashe TV da wutar falon.Ya haye saman. 
Basu, suka zoba sai wajen tara da rabi, laila ta sauka ta tura get takalmi a hannu, dan ta san ramadan ya dade da dawowa. Sadaf sad’af! har ta bude falon ta shiga, ganin wutar falon akashe ya sanya tai hamdala ta doshi hanyar d’akinta. 
“Daga ina kike?.” taji ya ambata tare da kunna fitila. 
Cikin karkarwa ta fara in’ina ta kasa magana, sai ya matso daf da ita, yace “ki 
gayamin daga ina kike? ya fad’a da tsawa. 
Dabara ta kwace mata, dan gani kawai take ramadan ya dawo mata tamkar zaki, kuma magana yayi tare da jijigata wanda ya sanya saida ta saki ‘yar 
kara saboda da karfi yayi mata. 
“”Yan daba ne sukai fad’a akan hanyarmu shine ‘yan sanda suka rufe hanyar, tun shida na fito, saboda goslow ne ya hadu wajen, daga baya ne mukayi yanke, to adalilin hakan ma mai babur din yayi yanke da mu, muka dad’a 
b’ata lokaci.” 
Kura mata idon yayi zuciyarsa na san karya tata, marairaicewa tayi sam! Bai 
aminta da abinda ta fada ba. Yace “ki koma inda kika fito.” Ya juya zai barwajen. 
Da sauri ta rungume shi ta fasa kuka “ka yafemin mijina, wallahi gaskiya na 
fad’a maka, karka hukuntani akan abinda ban ba.” 
“Makaryaciya kawai, Laila wallahi kina cin darajar mahafinki me mutumci ne, amma wallahi da tuni na rabu dake saboda bakya biyayyar aure, bakya darajani, bakya bin maganata, amma kici gaba, kuma da sannu zan gano duk abinda kike ciki, wallahi idan na kara ganin kafarki awaje sai na babballaki ke ko koyi da abokiyar zamanki ba kyai.” Yana gama fada yayi wajensan rufo gidan. 
Duk da ta ji haushin yabon lad’ifa da yayi agabanta.Amma sai data saki hamdala tai nata wajen da sauri. 
Karfe goman safe laila na kunna wayarta taci karo da msg nata shigowa ta whatsap.
Shiga tai sai ta gansu birjik akan lambar murabus,dan ta cire shi a blocking, tana bud’ewa ta ga hotuna na matan banza kala kala. Dafe kirji tai a k’alla zasu kai kala ashirin, duk babu kyan gani, duk kuma bakake ne, sannan ya rubuto mata cewar: “idan har kin duba wannan pictures kala -kala, to wallahi kinji na rantse kamar yanda matan nan ke a hakan, haka zan yi kulumboto, na san yanda za ai fuskarki ta koma kan jikin matan nan, na kuma aikawa mijinki, dan ina da hotunanki, kuma na sanar da mijinki komai, kinga kamar tonuwar asirininki ne, da rugujewar aurenki, dan nasan me zan ce mai, sai ya turo mata da lambar ramadan, yace ki duba nasan kin hardace lambobinsa, to nayi hakan ne dan ki tabbatar da nasan mijinki, ina so tun kafin mukai ga 
hakan nan to ki samawa kanki lafiya. 
K’ir! wayar tai kara, ta ganshi akan layi da sauri ta dauka ta k’unduma mai ashar! tace idan bai rabu da ita ba wallahi hukuma ce za ta rabasu. 
Dariya ya kyallkyale da ita “ki na wasa da ni, babu ‘yar iskar yarinyar data isa ta yaudareni na kyaleta, kiyi tunani ki kashe aurenki. 
Kashe wayar murabus ya yi, sai ta zube awajen ta dafe kunci, ta rasa madafa ko dai ta gayawa ramadan ne? Nan tai tunanin kiran sara, tana dauka laila tace. “Aminiya sai yau na fahimci maganar da kikai ta gayan kan murabus, gashi yanzu yana son kasheni da jinin jikina.” 
“Me ya faru ne? ta fada cikin mamaki. 
Nan ta kwashe komai ta gaya mata Sara tace “cabdi, amma murbus baiji dadin halinsa ba, koda laifinki ai shima da nashi, shawara ki canja lamba, na san dole mijinki zai tambayeki dalili, sai ki cemai damunki ake da kira da 
wasu gariban lambobi ne, shi ke nan sai hankalinki ya kwanta.Kuma karki goge komai na whatsap da murabus ya turo miki, kinga koda kin canja lamba bai kyaleki ba, to muddin ya aiwatar da abinda ya fada d’in, to kinga already muna da evidences da zamu gabatar. Shi murabus ma bai dabara ba anan ma ya kama kansa.” Wani sanyi laila ta ji tace. “Yauwwa sara, na gode wallahi, duk da hankalina ya tashi. 
Fushi gadan-gadan ramadan ya tsiri yi da laila. Duk ta bi ta damu saboda tsoro da ya cikata, gani take idan har murabus ya tunkareshi kamaryanda ya fadar, tasan za ta fuskanci wulak’anci dan ya kware. ‘ Laila na son tambayarsa tana son canja layi, amma ba fuska, d’an yar sa’insar da suke ma, baya ba ta fuskar suyi, ya d’auke mata wuta dif! Ta rasa yaya za tai, yau ta dada dana-sanin fitar da tayi a jiya, da ace ta bi maganarsa da tasan kashi daya cikin d’ari na matsalarta bai faru ba. Karfe taran safe da yake weekend ne ba aiki. Yau da safe kuma ladifa ta karbi girki, Sai ta haye saman tana son sanar da shi canja layi, falon lad’ifar ta shiga wanda sai tace tun zuwanta gidan wannan shine karo na uku da ta shiga, lad’ifa najikinsa suna soyewa sai zuba shagwab‘a take. Rinewa idon laila yayi da ruwan kishi ya feso a ciki, take cikin fushi ta daki 
gefen wani teburjug na glass ya fado ya tarwatse. 
A razane lad’ifa ta juyo tace “innalillahi wa’inna ilaihi raji’un! dan ta tsorata ainunl Ganin laila ce sai tayi d’an yake, tace “ashe! Kece laila, ban ji sallamarki ba,” ta fad’a tana gyara hannun rigarta da ya zame. Ramadan ya dago ido suka had’u dana laila ya daka mata tsawa “get out laila, nan ma kinzo ki batan raine? Tunda har ban isa da keba, to ki sarara mini. Kinzo kawai kin mata barna” Sai ta fita cikin fushi ta koma shahinta ta shiga kai kawo, ita kanta tasan takai 
Ramadan bango. Shiri kawai take so suyi, saboda tasan in suka shirya matsalolinta zasu ragu. Bayan kwana biyu 
Karfe shida na yamma laila ta kimtsa komai na shashinta yana ta kamshi, taci kananan kayan da ta siyo, an ci uwar kwalliya afuska kamarza a biki, sai faman tauna cewgum take. Dan ta sha alwashin sai sun shirya yau ita da oga Ramadan. 
Koda ramadan ya dawo laila ta tareshi, bai wani saki fuska ba, dan haryau yanajin haushin lailar. Murmushi tai bayan ganin ya gama cinye abincin, sai kwarkwasa take, cikin 
fari ta kalleshi “habiby baka ga kwalliyar da nai ba ne?.” 
Hade rai yayi yajuya yana latsa wayarsa. Numfashi taja dan ramadan din duk ya wani birkice mata ya dawo wani kalar rashin mutunci. “Ni na rasa me yasa innai kwalliya baka yabawa, alhalin kan muyi aure ko yaushe cikin yabani 
kake.” “Ba sai na wani yabe ki ba yanzu, saboda ganin yanzu na mallakeki, da din ma dan ban same ki bane kin gane. Sannan ina umartarki da ki cire wadannan kayan dan wallahi ba suyi miki kyau ba, baki duba kanki a mudubi ba ne? bai fiya yiwa iriki kyau ba.” Wani irin bakin-ciki ne ya tokare mata wuya, sai ta tashi cikin fad’a.Wulak’ancinka ya isheni ramadan ya isheni, kushenin da kake, ai haka ka ganni ka auro.” Murmushi kawai yayi na takaici. “Ni ba a haka na ganki na auro ba, kin manta yaudarar da kikai min da ciko? Wallahi da a hakan nan kike sungul amama ko kallo ba ki isheni ba.” Wani irin takaici taji ta kallashi tana jin kamarta rufe shi da duka, sai ta zube  awajen tace “wallahi ramadan ka cucueni, ai sai kaje ka auri super mama karewarta” 
“Kamar kuwa kin sani laila, dan wallahi muddin naga mace mai irin tsarin da nake so sai na auro ta.” Cak! Ta tsaya da maganar. “Au! da gaske kake? wallahi karya kake ramadan 
baka Isa kan auretaba, mu biyun nan zaka zauna damu.” 
Ta shi yayi yace “idan nace zan yi sai ki hana. Ke babu aure aka auroki?.” Ya sanya tsaki ya fita ya bar mata falon, danji yayi kansa na bugawa. Da gudu ta bishi ta sha gabansa. “Wallahi baka isaba, ni laila nafi karfin kishiya wallahi sunana kenan, inko ka ce zakai min sai na tayarda hankalin duk kan kowa a gidan nan.” 
Matsar da ita ya yi daga gabansa ya bar wajen. Yana jin laila ta ko’ina ta fice mai daga rai, shi sai yace tunda ya aureta yake fuskantar matsaloli, ya rasa wacce irin macece, lalle Lad’ifa ‘yar aljanna ce. Ya fad’a aransa. 
Huci ta tsaya tana yi duk sai taji firgicin da murabus ya sanya ta aciki. Ya bace jin magaanr kishiya ya dad’a dugunzuma ta “Wallahi ba ka isaba, kayi kadan, ni laila na nafi karfin kai min kishiya,” ta fada da amsa amon murya. 
Ladifa na zaune tana cin kwadon zogale, ta tashi don sakkowa kasa,dan jin hayaniyar ramadan da laila, kicibus sukai da shi ya wuce bai ko kalleta ba, sai tasha jininjikinta. Azuciyarta tace ‘kai Allah ka kara mana zaman lafiya.’ Ta koma falonta. Dan tasan in ta bishi ciki zai iya yi mata itama fadan. Sai ta barshi sai anjima ta shiga, ta san kan lokacin ya dada hucewa. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE