NAYI GUDUN GARA CHAPTER 23

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 23
Abubuwa goma da ashirin ne suka taru suka cakudewa laila, ta damu iya damuwa. Ba irin hanyar da ba tabi ba wajen ta shawo kan ramadan amma kamar dad’a ingiza shi take.Ga damuwar da ta sanya aranta dan ramadan yace zai kara aure. Misalin karfe sha-biyu na rana, tana kwance ad’akinta idonta biyu, amma ba bacci ta ke ba, wayarta ta dauka ta kalla wacce ta sanyawa password saboda tsaro, sai ta ajje ta gefe ta runtse ido. Ta d’au karamar wayarta wacce ta maida layinta cikinta ta bugawa ramadan, lokacin yana tsaka da aiki,Yana d’auka sai ta sanya mishi kuka .Cike da mamaki cikin dakakkiyar murya ya ce “ke meye ne?.” “Haba ramadan,yanzu dan nai maka lefi kalilan kake hukuntani, karka manta fa, murmushinka yakan sanya zuciyata tai sanyi, amma kayi dif da shi ko alamarsa na daina gani a fuskarka dan Allah kai hakuri.” 
“Kinga laila, idan ke awajenki abinda kikai karami ne to ni awajena babban lefi ne.” Ya 
fada tare da kashe wayar. 
Bin wayar tai da kallo. Sai ta bi gadon ta kwanta tana kuka, wanda har saida taji kanta na ciwo saboda abubuwan da ta sanya aranta ga fargabar murabus. Ga kishi. Ga fushin da ramadan ke da ita. So kawai take su shirya ko yace mata ya fasa auren.Ciwon kai ne me tsanani ya rufeta. 
Murmushi yake zuciyarsa fes! dan yasan duk inda hankalin laila yake ya tashi  adan kutsun nan, ya san dole ta tsorata da shi. Wayarsa ya dauka ya latso kiran lailar, yaji wayar a kashe sai ya saki tsaki. Yana zaune yana ta gwada kiranta. Nuhu yazo ya tsaya kusa da shi. Yace “ahh murabus ya dai? yau baka fita bane?.” ‘ Wallahi gani nan dai.” Zama nuhu yayi yace “wai ina ka kwana ne da maganar laila. ” Tsaki yayi yace “yanzu ma ita nake kira wayar a kashe.” D’an mintuna nuhu yaja kam ya fara magana yace “murabus da ace zaka hakura wallahi da yafi, ni wallahi ba na hango maka wata hanya mai bullewa, saijefa kai a matsala, sannan ko ta fannin addini ma ba kyau gaskiya sabida tayi aure fa.Wallahi ina jiye maka 
tsoro ace mijinta ya samu labari, wallahi kashinka ya bushe, baka san wanne iri ba ne.” “Ka gama, to indai wannan shawarar zaka bani ka rike abarka, kai ka manta abinda tayi min ne?.” 
“Ban manta ba, amma fa kaima da laifinka, saboda babu irin nusar da kai da ban ba,dan ka gane yanayinta duk na yaudara ne, amma idonka ya rufe sabida kaga big girl ka rikice .” D’aga kafad’a yayi yace “ban dauki maganarka ba,” “To Allah ya kyauta, ni tashi ka kaini kasuwa,” ya fada yana mai mikewa. 
K’arfe wajejan biyar na yamma. Ladifa ta sauko daga samanta da kasko a hannu za ta sanya 
turaren wuta ad’akinta, dan kwana biyu ta rabu da yinsa da ciki ya sanya mata. 
Kitchen ta shiga ta ajje, sai ta fito gidan tsit! sai tai tunani fa tabbas! yau ba taga gibtawar laila ba. “Ko lafiya? ta ambata afili. “Bari dai naje na gani,” ta fada tana mai taka kafafuwanta, harta k’arasa part din lailar, ta shiga falon. Sallama tai shiru, sai da ta kuma yi amma ba taji an amsa ba. 
Kuma ta san tabbas! laila na ciki, sai ta karasa dakin ta shiga, laila na kwance dukunkune tana rawar sanyi, da sauri lad’ifa ta cire takalmanta, ta shiga ta ce “laila laila baki da lafiya ne?.” Ba tai magana ba illa dafe kanta da tai ladifa tace “kiyi magana please.“ Sai alokacin laila ta d’an tashi ladifar ta karasa gefenta ta kalleta “sannu dama baki da 
lafiya ne.” ldon lailar da yayi luhu luhu saboda kuka, ta bud’e su dakyar tace wallahi zazzabi da ciwon kai ke damuna..” Cikin tausayawa ladifa tace “bari na d’auko miki magani,” nan ta fara tafiya irin na masu cikin da ya fara tasawa. Magani da ruwa ta dauko mata ta shiga ta mika mata, da kamar lailar ba zata karb’a ba sai ta amsa ta sha. Ladifa tace “kinci abinci ne? ta amsa mata da aa, sai ta fita ta hado mata ragowar faten doyar da tai da rana, ta kawo mata, sannan tace mata “Allah ya kara lafiya. Ta fita. 
Laila ko dakyar taci abincin nan, wanda alokacin ciwon kan har ya fara dan sauka, ta kwanta tana maida numfashi, wani yafitaccen bacci ne ya kwasheta na rabin awa,jin gumi na damunta ya sanya ta tashi,jikinta yayi la’asar ga zazaabin ya sauka sai ta mik’e ta shiga band’aki zuciyarta a cunkushe tayi wanka, ta fito ta shirya, ta fito falonta, ta kwanta akan doguwar kujera da tarin damuwa aranta. So biyu ladifa na lekawa ta nai mata sannu duk da cewa aciki ciki lailar ke amsawa. ‘ 
Karfe shida daidai ramadan ya dawo, lokacin ladifa na samanta tana bade shi da turaren wuta.Tana saukowa yana shigowa, sai tai murmushi ta k’arasa tai mai sannu da zuwa, tare da tayashi rik’e kayan da ya shigo da su, shi sama ya hau, ya yo wanka ya sauko k’asa. 
Kitchen d’in ladifar ya leka ya bud’e fridge ya dauko ruwa dan ya sha. Kanta naga aikinta ta ce “zauci laila fa bata da lafiya.” 
“Meke damunta?.” “Ciwonkai da zazzab’
Okey yace mata, sai ya Fita ya yi shashen lailar, ya shiga tana kwance lamo akan kujera tana ganinsa gabanta ya buga, sai ta runtse ido, zama yayi ta gefen kujerar yace “meke damunki laila?.” Zaune ta tashi tana kallonsa tare da ayyanawa aranta wannan ce damarta ta k’arshe na samun shiryawarsu, matsawa ta yi kusa dashi tace “kaina ne sai zazzabi.” 
Hannunsa ya d’ora agoshinta, yaji da d’an zafi, ganin hakan ya bata damar dora hannunta saman na shi, ajikinsa yaji tafin hannunta shima da dan ZafI.Fuskar tausayi tayi mai ta jingina da jikinshi, ta shiga matsa hannunsa. Kallonta yayi yace “ta shi muje asibiti.” 
“Habiby ciwon kan ya sauka, shima haka zazzab’in, sai dan ragowar kadalar jiki, sai ta dan bashi tausayi ya ayyana aransa cewar damuwar data sanya aranta ne. 
Kan kujerarya zauna sosai! hakan yasanya ta kwantar da kanta kan cinyarsa, tana tunanin 
ya zama dole tayi abinda zasu shirya, ita kadai tasan azabtuwar da take, musamman da abubuwa suka shakud’e mata, tana son ta gabatar mai da abubuwa, wanda ta kula babu dama in har basu shirya ba. Wani irin nanukarsa ta ke, tana dada shigar da jikinta da nashi, hakan yasanya dumin jikinsu ya had’u, sosai dumi jikinta ya yi saboda na dan zazzabin da take, yake 
shigarsa Duk da tasan cewa ba girkinta bane, amma wannan shine damarta. Kallonta ya yi yace “ke wai baki san ba girkinki bane, meye hakane wai.” 
Kobi ta kan maagnarsa ba tai ba ta shiga aiwatar da abinda ranta ya sanar mata. Miji da mata aka ce sai Allah,nan da nan ya biye mata, domin ko ba komai tanan bangaren yakan sara mata, sabida yanda take nuna nadamarta ta wannan hanyar cikin salon da dole ya biye mata. 
Wanda ita ta kula sauda dama ta nan take iya hakurar da zuciyarsa akanta. Wanda da 
zarar sunyi yake saukowa daga fushin.
Jin shirun Ramadan ya yi yawa, ya sanya ladifa ta doshi hanyar falon laila dan ta duba ko jikin lailar ne yayi tsanani, rage tafiyarta tai tun adan dokin kofa sakamakon jin kamar maganar lailar na cewa i miss you habeey. Da kuma nishinsu da taji. Sai ta runtse ido, dan tasan kwanan zancen. Da sauri ta koma da baya, ko kitchen ba ta koma ba, wanda ta manta ta dora girki. 
Wani irin mahaukacin kishi taji ya turniketa, musamman jin cewar aranar girkinta ne ma, 
wanda ita bata taba rab’ar ranar girkin lailar ba, amma ita koyaushe takan yi wani abun a 
nata girkin, sai ta runtse ido sai ga hawaye, gajin haushin aranar girkinta ga kuma na kishi soyewar data ji anai. Wayyo Allahna, ta fada ahankali tare da kifa kanta ajikin kujera, kuka sosai ta sha. Karshe ta fara da jan hasbunallahu wani’emal wakeel dan jin wani irin abu da ya tokare mata awuya, karfin hali tai ta koma kasan ta kashe girkin, da yake fararshinkafa ce ta kwashe a fulas, jikinta nayin bari ga wani gumi sai zubo mata yake. 
Wani kuka taji yazo mata, sai ta sunkuya ta shiga zubo da hawayen cikin raunin murya mai abar tausayi. 
Komai da komai na girkin su miya ta hadasu a dining ta haye sama, wanda ko kallon k’ofar laila bata sake ba, wani wawan haushinsu su duka ne ya tokere mata wuya. Afalonta ta zauna ta shiga raira kuka. Cikin magana tace saboda Allah dan an rainani a ranar girkina ace yaje wajen kishiyarta. Su kuwa mutanen basu suka dawo hayyacinsu ba, sai da kowanne yaji ya samu nutsuwa ainun! Adaidai kuma lokacin akai kiran sallah, alokacin ramadan ya tuna abinda yayi. Kai ya daga don tunowar cewa fa aranar girkin ladifar ne, tuno da cewar ba tasan mai ya faru ba, sai ya basar Laila dake wani irin murmushin jin samun nasara tace “habibyna ka fasa auren amma ko?.”. Dariya yayi yana mamakin furucinta. “Ke meye na damuwa da zancen ne.?.” Fari tai tace to ai”ogana dole na damu. ” “Yakamata dai ki sakawa kanki salama idan Allah ya kaddaro zan kara babu makawa atoh.” Hade rai ta yi. Tana adduar Allah ya sanya Allah bai kaddaro mai ba. Kallonta ya yi yana mamakin kishinta, yace “amma kinsan dai ba ranar girkinki bane ko.” 
D’an tabe baki tai tace “ai kaine, ka rikita tunani na da yawa, saboda kaki yafemin, dole na farmaka alokacin da ba nawa ba.” Ta fada ta bar wajen tana murmushi dan tayi wanka. Murmushi yayi kawai ya mik’e ya bita yayi samansa shima dan ya yi nasa wankan.Ya tafi masallaci. 
Lad’ifa kuwa, sosai ta dirji kukanta ta d’auro alwala ta hau gabatar da sallah, bayan ta idar ta ci gaba da jan carbinta, Tana nan a zaune ramadan ya shiga falon ya kunna fitila, haske ya gauraye, dan ankawo musu wuta. Ko d’aga kanta ba tai ba, ballan tana ta kalleshi. “Babya muje ki had’amin abinci.” Ko amsa mai ba tai ba ballantana ta kalleshi, sai ta tashi ta nade sallaya tayi cikin daki. Yana nan azaune ta fito yace “baby ba magana nake miki ba?.” 
Sai ta tsaya “ban jika bane gani.” Ta fada tana kauda kai. Murmuahi yayi ya mike “me gimbiyar keji dashi ne yau take min fushi.””Abinda duk kukeji da shi kaida matarka, sai muryarta ta fara rawa ta shiga kuka ta zauna agefe.Tambayarta ya shiga yi taki amsa mai sai ta kauda kai, tace “dan girman Allah ka kyaleni ramadan bana jin dad’i.Ka daina tambayata akan wani abu. Muje kaci din kawai.Saita mik’e tai gaba ya bita abaya, kasan su ka sauka tai seving nasa, ta koma gefe ta zauna, kafeta yayi da kallo yana karantar yanayinta, tabbas! akwai abinda ke damunta, kodai ta fahimci abinda ya faru ne? sai yayi sauri ya kauda tunanin aransa. 
Alokacin laila ta fito tana tafiya tana barin jiki. A kujerar dake gefe ta zauna tana kallo. Ta juya ta kalli ladifa sai tace “maman baby sannu da jiki.” Dan murmushin yake ladifa tai tace “yawwa laila nagode. 
Cikin dan nunawa ladifa cewa yes! itama mijinta naji da ita tace “habiby ina son sabon layi.” Bai kalleta ba ya ci gaba da cin abincinsa sai can yace “me zaki da layi?bayan kina da wanda kike amfani?.” 
Da fargaba tai magana ta ce “wallahi ina yawan ganin sababbin lambobi na kirana ne 
shi,isa, kuma ni hakan na bata raina..” Kallonta yayi yana tunani na d’an lokaci ya jinjina kai ya ce “okey” 
“Airtel nake so ta fad’a tana wani fari. 
ladifa ta kalleta ta d’an kauda kai ta saki tsaki a cikinta, da mugun haushin abinda sukai mata takeji wanda tana ganin dole ta tauna tsakuwa. 
Wata dabara ce ta fad’o mata sai ta fuskanci inda saitin ramadan ya ke wanda dama idanuwansa bini ~bini na karantar yanayinta, ganin yanda duk ta canja. Wayarta ta dauka ta shiga Whatsap tana dan dudduba sako, ta dad’e sai can ta sanya dariya ta ce “kai amma akwai drama.” 
Da sauri ramadan ya kalleta ya ce “yadai?” 
Sai ta dan motsa baki tace “hmmmm a wani group naga anturo wai IN kECE YAYA ZA KIYI? Wai wani mutum ne keda mata biyu..” Sai ta kalleshi “ina jinki?.” 
Sai taci gaba, A ranar girkin amaryarsa, sai mijin yaje wa uwargidan har abu ya shiga tsakaninsu. Kuma ita uwargidan tasan cewa ba ranar girkinta bane. Wanda ita Amaryar ta ga alamun haka, shine ake tambaya idan kece yaya za ki yi? wani irin hukunci ya kamata ta d’auka?.” 
Kallonsa tai sai taga kansa asunkuye murmushi tai tace “zauji idan da ace kai macece kuma kaine Amaryar akai maka hakan yaya za kai?!‘ 
Sai tajuya gefen laila tace “laila nasan kinji idan kece mai za ki? Tuni laila ta d‘an daburce dan gani take kamar ladifar ta gano su sunyi sha’ani a ranar girkinta ne. 
“Hmm innice kuwa sai nai hak’uri, meye aciki? ba mijinta bane?.” “Hmm kawai ladifa tace. Sai ta kalli ramadan tace “zaujifa in kaine yaya?.” Kasa daga ido yayi ya kalleta sai ya dan shiga danna waya yace “Hakuri zan yi kawai.”
Murmushi ladifarta yi tace “ni kuwa in nice zan gaya musu cewar abinda sukai bai dace ba, saboda kamar cin amana ne, wanda aganina ka ga ita d’ayar, idan ita akaiwa hakan, itama ba za taji dadi ba. Kuma ni namafi ganin lefln mijin, in dai yana san zaman laflya 
agidansa, bai kamata ya yi hakan ba, sam! Abinda wasu matan keyi ba ya dadi, domin abinda kasan ba zaka so ai maka ba, to karka fara, amma wasu san zuciya yayi musu 
yawa.” Ramadan sai ya mike yace “kinyi gaskiya baby.” “laila a yatsine tace “aiko.” “To ni sai da safenku.” Tai hanyar sama. 
Bin ta da kallo ramadan yayi domin yana tunani cewar lallai ta fahimta. 
Koda lokacin bacci ya yi, ramadan yaje d’aki, ya ga ladifa tajuya baya, bai san me ya sanya ba, a yanzu baya son fushin ladifar, yana damuwa da yawa. Sosai! Yafl damuwa da fushinta akan na laila. Kodan ita bata da yawan nunawa ne.Kwanciya yayi ta bayanta ya Juyo da ita, sai yaga idonta a rufe. “Na san ba bacci kike ba,oya gaya mini abinda ya sa kike ta hade min gira.” Sai ta bude ido idonsu ya sarkafe dana juna, a hankali ta dauke idon daga kallonsa don yana 
sanyawa taji fushinta na kasa. 
“Kai mijina ne, dole nai kishinka zauji,dan anga ina shiru ba wai bani da shi bane, banji dadi ba a yayinda ka jewa kishiyata a yayin girkina, dole naji ba dadi, nasan ba haramun kai ba saboda halaliyarka ce, amma ai duba da idon basira kamar d’aukan alhaki ne. Wanda kana ganin ko hannunka ban isa na rik’e a ranar girkinta ba.Ba zan maka rashin kunya akan haka ba, amma dan Allah ina rok’onka ka daina kai mata kwana na, saboda zuciyata za taci gaba da azabtuwa.” 
Yasan bai da gaskiya, sai ya shafa sumarsa yace. “Sorry maman baby ke yanzu ai hukuma ce sai da lallashi ko, dan saboda bake kadai bace yanzu.” 
Jan kumatunta yayi “kinsan al’amarinne a dazun nan….” 
Sai ta runtse ido “ni dai kace ba zaka kuma yin makamancin irin haka ba wanda koda akai 
nane.” 
 Ba case maman baby, amma a daina wannan damuwar, saboda kinsan bake kadai bace. Ba tace komai ba. Ta juya.  Washegari Har alokacin ladifa bata saki fuska ba, komai yinsa take ba tare da ta daga ido ta kalli ramadan ba. Sai shan kamshi take, Duk sai Ramadan ya kejin sam bai mata daidai ba. Yana fita laila ta fito suna waya da asiya. 
Alokacin ita kuma lad’ifa na yin breakfast. Suka gaisa sama sama kowacce ta dauke kai. 
Shi kuwa ramadan ko a office yini yayi yana tunanin ladifa, da yanda yaga tana kuka. Murmushi kawai yayi a aransa yace ba lalle ne kowanne namiji ya iya tsallake tarkon da lailan ta dana mishi ajiyan ba, indai lafiyayye ne. Koda kuwa ace abin baya ransa. 
Haka da dare ma abinda ya wakana kenan, domin ladifa ta yi fuska in banda shan kamshi babu abinda take. Ko ido tak’i bari su had’a da shi, komai in za tai mai kanta asunkuye, wanda kuma duk abinda take bata fasa ba, saima abinda ya karu. Wani birgeshi take 
ayanda take shan kamshi, musamman in tana tafiya yanda take yinta ahankali ta masu 
ciki, ga yanda tai da fuskarta, duk sai yaji tana burgeshi. 
Laila kuwa ko ajikinta. Don tasan ba yanda za ai da ita dan ta saci kwana. 
Ladifa ce ta dawo dauke da abarba da kankana yankakku tana sha, ta zauna itama tana kallo fuskar nan a tamke, shi dariya ma take bashi. Sai ya mike ya zauna gefenta, ya matsar da kwanon gefe ya ce “mum baby ya dai? kin hanani tab’a babyna ko?.” Ganin yanda laila ke satar kallonsu saita dan saki murmushi. “Da kai da kaya ai duk mallakar wuya ne zaujina.” “Allah k0 maman baby.” Ya fad’a yana shiga shafar cikin yana cewa gaskiyane.Allah ya saukarmin dake laflya.” 
Cikin lumshe ido ta kalle shi tace amin.” 
Wani tsaki laila ta buga ta mike ta barwajen, don ji tai kamar ta shako ladifa. Tana shiga falonta tace ” ya Allah ka bani ciki nima.” Haka tai ta ambata cikin zuciyarta da Murmushi ladifa ai ganin abinda ya faru, ko ba komai ta rama taji itama, duk da tasan cewa wannan ba wani abin damuwa ne bane, akan ita abinda ita lailar tai mata. Sai ta dan mike cikin kumbura fuska, ba tare sa ta sake kalllonsa ba, ta dau kwanonta tai saman bene. 
Binta da kallo yayi ya ce “well,” tare da d’aga kafada sama. Adaidai loakacin wayarsa tai kara sai ya daga. 
“Chairman, chairman, ramadan ya shiga fadawa wanda ya bugo. Daga can abokin nasa da aka kira chairman, yace baka da kirki Allah ramadan, yanzu ko dan harka na bikina ka ki kazo ka sanya hannu, ka tare agun matanka ko.” 
Shafa suma yayi yace “wane ni? kai d’in ne ai d’an kutsa can da nanne, ko yaushe k’afarka na can gari tana wannan gari.” 
“Kai awayama zan turo maka “”””””, dan kai ba saina kawo maka ba, dan haushinka 
nakeji.” “Wallahi sai naki halarta.” dakuwa ka yi kaffara. “Zan zo dinner amma ban da matana.” “akan me? wallahi sai kazo dasu dinner, dan kawai ta couples ce da kawayen amarya, haka zaku zo.” Yasan nacin chairman , ya sanya ya ce “okey ba damuwa zamu zo dan k’wal uba..” Dariya chairman ya fasa sukai sallama.Ya tashi ya haye saman. Bayan kwana biyu a tsakani. Ad’an kwana biyun nan laila ta samu sa’ida da jarrabar murabus, sakamakon canja layin da tai.Sai dai kullum adduar ta Allah ya sanya karya samu ramadan, yayi masa wata tsiyar dan tasan murabus ciki da bai. 
Da yake aranar girkinta ne. Lokacin ta fito d’auke da kofin da ta d’aukowa ramadan, ta ganshi sunkuyo a kusa da cikin ladifa, yana tambayarta meke damunta, yaya takeji? ita kuma tana murmushi tare da cewa ba komai. Kan dining taje ta ajje tanajira taga gudun ruwansu. 
Mikewa ladifa zatai sai ta kasa tashi duk da cikin nata ba wani girma yayi wanda zai sa ta kasa tashin ba, amma ganin laila ya sanya ta narke cikin cool voice tace “zaujina dan mikar dani na kasa tashi, sai ya mike ya ruko hannuwanta, ya mikar da ita, wanda har saida ya hada fuskarsa da tata suna murmushi. sai yayi kissing kumatunta. 
“To nagode,” ta fad’a zata wuce, da sauri laila ta ce “ke ladifa baki da da kunya k0? a 
ranar girkina ki na nanikar mijina,to wallahi zan mauje ki wannan ai daukan hakki ne?.” 
Wani kallon raini ladifa tai mata cike da takaici, mijinki mijina ki daina cewa mijinki ke d‘aya, ashe! dama gwano ba ya jin warin jikinsa! Ashe! son zuciya har yayi yawan da ganin gaskiya sai tayi wuya. Laila kin manta sanda kika saci kwana na, ko kin manta? to na tuna miki, wanda ba ki tab’aji na numa miki ba, saboda nasan akwai ranar kin dillanci to kuwa ga ta. Ko Ba kya aiki da hadisin da shugabanmu annabi muhammadu S.A.W ya fada ne? Yana Cewa imanin d’ayanku ba zai tab’a cika ba, har sai ya sowa d’an uwansa abinda yake sowa kansa. Idan kin manta na tunatar miki.” 
Harara ta buga mata “dallah yi min shiru, wallahi idan kika kuma sai kin gane ba ki da wayo.Kuma tun kafIn kisan hadisn nan na sanshi.” 
Murmushi ladifa tai tace “Ai ba ke zaki min kashedi ba, nice zan miki, last warning zam miki karki kara farautar min kwana, saboda ba nai miki haka, idan har bakya son abinda ya faru yanzu, to ke ma ki daina, kinga munyi one one kenan, wanda ni abinda nai ko rabin rabin naki banba.” 
Tana gama fada ta bar wajen, ko yanzu ta danji wasaai aranta, dan ta fitar da abinda wajen kwana uku ke cinta ba. 
Shi kuwa ramadan yana jinsu, breakfast nasa kawai yake yi yana smilling.Ga yanda ya kejin kansa na fasuwa ganin duk akansa suke fad’a. 
Kallonsa tai tace “yanzu habiby ba za kai magana akan abinda tai min ba ko?.” Hularsa ya dan karo gaba yace “me kike so nace miki laila, yarinyar nan kece kika kaita bango, ke kika shiga huruminta.Duk cikinku kowa nasan halinsa, kawai ya kamata ku 
kiyaye duk abinda ya kamata, wanda za a zauna lafiya don bana son tashin hankali.” 
“Ai haka za kace, abinda ya farun ai duk kaine sila. Don haka kaiwa matarka magana dan zan iya targadata”. Hade fuska yayi yace ” ki kula dai, duk abinda ya samu matata kece, saboda kinsan yanzu 
ba ita kadai bace ki kula saboda tsautsayi.” Yana gama fada ya dau mukullin mota ya tafi. Ta dade a tsaye cikin huci da jin haushin ganin kamar yabi bayan ladifa,ne sai ta koma daki.” 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE