NAYI GUDUN GARA CHAPTER 24
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 24
Gun mahaifiyarta kawai take son zuwa don ta dade ba taje ba, dan sai tace tafi wata uku, ga al’amuran dake wakana sun cunkushe mata arai, har yanzu abinda ramadan yayi mata bai dusashe ba, don har yanzu taki sakar mai fuska duk raragefen da yake.
Karfe goman dare tayi dakinsa, dan ta tambayeshi zuwa gida gobe, ta shiga yana ganinta ya danyi murmushi dan aganinsa ko hakuri tazo ba shi.
Hijabinta ta cire ta kwanta agefensa, sai ta dan juyo da kanta tace “baban baby dama ina son gaya maka gobe ina son zuwa gidan mu.” “Me za kije kiyi?.” “Dan zanje gidanmu har sai an tambayeni abinda zanyi?.” “Ba zaki ba.” Wani irin tashi tai da sauri wanda har saida taji cikinta ya amsa tace “akanme ?.” “Ra’ayina ne ki bari next week kyaje?!‘
Tafarfasa taji zuciyarta nayi,dan haka kawai takejin haushinsa adan kwana biyun nan, tun abinda ya faru wanda sukai mata shi da laila. Haryau abinna damunta.. “Amma zauji….” Sai ya dago ya kalleta “ladifa ban sanki da musu ba.” Tsam! Ta tashi jikinta na rawa tace “ban taba zaton zakai min haka ba, yaci ace ka duba ka hanga, ina son ganin mahaifiyata, kasan ita ba ma’abociyar zuwa gidana bace, bai dace ka hanani ba, amma ai kai kullum kana ganin taka.” “Abinda za kice kenan ko?.” Ko kallonsa bata sake yi ba, ta sauka ta daura dan kwalinta ta fice daga dakin, sai ya tsaya shiri Yana binta da ido “me yarinyar nan ke nufi ne?.” Dakinta ta shige ta saka kuka ita auren ramadan ya isheta, a yanda take jin zuciyarta kamar ta fito saboda zafi, musamman tunda ta samu cikin nan takejin haushinsa sosai.
Tsam! ya tashi ya bi ta d’akin, amma a kulle. Magana ya farai “ladifa bude,”
tana jinsa tai mai banza, dan ko zai mutu ba zata bud’e ba.” Ya dade a tsaye ya koma dakinsa, duk ya damu musamman sanin cewar ita ba cikakkiyar laflya ba.
Cikin kunci ta kwana. Da safe ba ita ta bud’e d’akinta ba, sai wajen goma saboda weekend ce, fitowa yayi yana waya sai ya tsaya ya kalleta ta dauke kai, dan yau tana jin daidai take da kowa. Kasan ta sauka. Laila na zaune tana girgiza kafa, dan duk ranar girkin ladifa haka take duk safiya, zata zauna tana huci tana hararar ladifar dan kawai ta fito daga dakin miji.
Direct kitchen ta zarce ta shiga dama kunu, dan shi ta ke sha’awa, ta jima aciki ta fito da kofi a hannu. Ta zauna a gefe tana shan kunun da ta dama d’in dan yunwa take ji sosai. Alokacin ya sauko, idonsa akanta. Kallonsa tai ta d’auke kai, sai kawai ta mike dan had’o mai nasa kayan karin, domin tana kula da kallon da laila ke musu, ita kuma ba zata taba
bari laila ta fahimci fad’
a suke ba. kitchen din ta shiga ta dauko fulas din shayin da ta dafa mai kayan kamshi, ta ajje adining ta tsaya ta harhada mai komai na bukata ta koma ta zauna. Mikewa yayi ya fita dan aiken maigadi ya sayo bakin mai na inji. Tana zaunenta tana shan kununta hankalinta akwance, laila ta tashi, kamar da gayya tabi ta kan kafar ladifa da karfi. Yar kara ladifar ta sanya ta ajje kofin da sauri. Ta kalli Lailar tace “kina gani kuwa kin taka
nifa.” Cike da kallon rainin hankali tace “au ban zata ba, na dauka dutse na taka.”
Cikin fushi ta kalleta dama a cikin fushi take, kuma tana cike da ita na tun abinda sukai mata, ga bakin-cikin ramadan ya hanata zuwan gidansu, ga na lailar wanda tun a jiya take bangazarta. Da sauri ta tashi tajuyo da kafadar lailar tayi taga -taga za ta fadi tanajuyowa ta wanke ta da mari ,za tai magana ta kuma bata wani marin a daya kuncin. Sannan ta nuna ta da yatsa “ki shiga hankalinki, hakuri ba wai tsoro bane gudun magana ne, ya isheki na kula tun jiya kike takalata. Dan wulakanci kamar kin taka dutse?.” Wani tsalle laila ta buga “ni kika mara?.”
Kokarin rama marin za tai ladifar ta rike hannunta. Tare da rarumar remote ta kwada
ma lailar agoshi.
Lalla! La! Laila ta kuma fada tare da juyawa da sauri tayi shashenta ta dauko wata
siririyar muciya. Tana zuwa ta nuna ladifa da ita “wallahi sai jikinki ya gaya miki.” “Idan nijikina bai gayan ba wallahi ke naki ya gaya miki..” Tun adan farfajiya yakejiyo hayaniya sai ya kara sauri. daidai lokacin da ya shigo. Alokacin kuma laila ta daga muciyar’ nan zata makawa ladifa. Cikin sauri ladifar ta rike muciyar. Sai suka fara kiciniya kowacce na son kwata.tsawa daka musu wannan wanne irin rashin hankaline sai kace
kishiyoyin kauye kuna doke–doke? Wani kallo ladifa tai mai ta kauda kai. Ta rike muciyar gam Laila ta kasa kwata. Cikin fusata laila ta bawa ladifa mari. Tare da daga murya ta hau bala’in in ladifa bata saki ba sai ta raunatata. Amma ko gezau ladifa taki’ sakin Muciya.
Ramadan yace ” ladifa yanzu kina cikin wannan halin da juna biyu kike fada.” “Kome ma zan iya ba damuwata bane In har ban nuna ma matar cewa kowa fa dan yau ne ba
hakuri da kawaici, ya sanya ake barin wani abun,” “Ina Umar tarki daki saki muciyar nan.” Jin abinda yace sai ta saki muciyarta tsaya tana huci dankwalin kanta ya zame. Ya kalli laila yace “maida muciyar nan,” ko motsi ba taiba, sai faman girgizajiki da take.
Muryar lafifa na rawa tace “Zauji wallahi idan ba kaiwa matarka katanga dani ba zan nuna mata mai hakuri bai iya fusata ba.” “Ke kin isa har nawa kike ladifa, wallahi sai dai ni nai maganinki.” “Kallon lailar ya yi yace shut up mara hankali kawai.” Ladifa tace “idan ke baki mun ba ni zan miki.” “Wai ba magana nake muku ba ne?.“
Zuciyan lad’ifa kamar za ta faso ta kalleshi “bakin-cikin da kuke kunsa mun ya ishe ni,
wallahi wallahi sai na nunawa wanan matar sunana lad’ifa.”
Ko kallonsa laila ba tai ba ta wawuri muciyar nan tayi kan ladifa.Tazo zata makawa ladifa Ramadan ya kare dukan ya sauka akan hannunsa wanda sai da yace ash Sai kuma tai cak Ta kalle shi. Ta matsa kusa da ladifar tana huci . “Karamar mara kunya wallahi ba don ya kare kiba da sai kinji ijinki.”
Lad’ifa tace “idan baki zo kin dake ni da itaba, ai baki cika sunanki laila ba, wallahi da kinga yanda ake hauka ko da ciki.” Wani ashar laila ta lailayo ta bankawa ladifa tace “kece karamar mara kunya, dama ina Cuke dake.” Dariyar takaici lad’ifa tai tace “idan kin isa ai komai zaki iya.”
Cikin fushi ta kuma saitawa zata makawa ladifa, Ramada dake jinyar hannunsa ya kuma tarewa ta maka mai a gefen kafada, ash! Ya kuma cewa.
Sai ta saki muciyar da sauri ta ce “sorry habiby ba kai naso makawa ba.” Wanka mata mari yayi, wanda sai data ga wuta, “baki da hankali ne bakiga tana da ciki bane.”
Kuka ta sanya “Baka ganin irin abinda tai min ne? koni ba mutum bace.” Muciyar ya dauka ya ajje akan dining, ya shiga kitchen dan neman ruwan zafi ya gasa hannu.
Ganin haka ya sanya ta zagaya taja gashin ladifa, zafi ya sanya ladifar ta rike hannun lailar gam! sai kokawa Allah ya bawa ladifa dama ta tura ta gefe lailar ta bugu da gefen kujera, ta kasa tashi, cikin zafin nama tayi wajen dining da sauri ta dau muciyarta dawo ta makawa laila agefen kafa.
Laila ta tsanyara kara. Fitowa Ramadan yayi ya daka musu tsawa “wallahi zan sab’ar muku in har baku daina ba.” Kalllon ladifa yayi dake huci, yace “bani muciyar nan.” Ko kallonsa tai ba. Sai ya rike muciyar zai ‘kwace sai ta shiga fusge-fusge, sai kace mai aljanu, “ka sakarmin ta fada tare da kallonsa idonta yayi jajawur Wani irin fad’uwar gaba yaji dan ya kula bata cikin hayyacinta.
Da karfi tace “ka saki nace,” sai ta fara kuka duk ta fita hanyyacinta, sai gumi take tana kuka “wallahi tallahi idan baka saki ba, sai na baka mamaki.”Murde hannun yayi ya kwace, sai tayi kitchen da sauri ta rarumo tata muciyar ta yi kan laila dake matsar kafa tana zagin ladifar, tana cewar sai ta fitar da lad’ifar daga gidan.” “Muciyar ladifa ta saita laila zata maka mata, Ramadan yana kokarin rik’e muciyar ta sauka akan d’aya hannun sai ya saki muciyar da sauri ya dafe wajen.
Ko kallon aika aikar da tai mai ba tai ba, ta makawa laila a kugu. Tace “idan kin isa ki fitar dani.” Tashi lailar tai zata kuma cakumar lad’ifa.”
Ramadan yace muddin suka kuma wani fada to wallahi duk hukuncin daya yanke to su suka siya.”Kowacce ta bace mini da gani,” Ya fada da kakkausar murya. Wadda ta sanya suka dawo nutsuwarsu. Barin wajen laila tai cikin kuka,rike da gefen kugunta da ladifa ta makawa muciya.
Kallon ladifa yayi dake sharar hawaye yace “ke kuma muje sama.”Sai taki tafiya yazo ya rike hannunta ta fusge “karka kara tabani.” Jin yanda jikinta yayi ya sanya yace “kije nace.” Sai ta zube awajen tana kuka “wallahi ramadan ni ka maidani gidanmu zuciyata ciwo take.” Ta fada tana dafe kirjinta, sai yayi sauri ya riketa, yaraf! ta kwanta ajikinsa tana jin kirjinta na bugawa. Tsorone ya kama shi saboda ganin yanda duk ta fita hayyacinta. A hankali yaja ta sukai sama ta fusge hannun “Wallahi ni gida za ka kaini in ba haka ba, wallahi sai na tafi, ni ka barni,” ta fad’a tana kuka. Dakinta ta shige ta kwanta, sai yanzu take tunanin gangancin da tai na yin fad’a da ciki. Abinda ko agida ba zata ce gada wacce tai fad’a ba.Sai yanzu takejin ciwo a jikinta. Zama yayi a kujerar falon ya dafe kansa dake mai ciwo, duk sun daddoke shi. ‘Wai dama haka ladifa take in tai zuciya, duk sai yaji jikinsa na bari sabida tsoron kar wani abu ya samu ladifar, tashi yayi ya bita dakin tana kwance lamo, ya zauna gefenta tana kuka please “ladita kiyi hak’uri kinsan bake kadai bace, karki jejininki ya hau ba a son me ciki na sanya damuwa.” ‘ Ramadan “kasan ina da cikin kake sanya ni a matsala, yau wajen sati daya kenan, ku na sani bakin ciki tun lokacin da ka kaiwa laila yini na, to wallahi na gaji.” Sai ta tashi dakyar. Ya janyota ya rungume yana jin babu dad’i a zuciyarsa, shafa bayanta ya shiga yi yana bata hakuri.
Zare jikinta tai ta shiga toilet dan yin wanka, yana nan zaune ta fito ta shafa mai ta sanya wata doguwar rigar abaya, ta sanya turare ta daure tulun gashin kanta ta d’au mayafin abayar da purse ta fita. Da sauri ya mike “ina za kine wai ladifa?.” “Hajiyata nake san gani,” ta fada tana kuka. Dafe kansa yayi dake barazanar fasowa, “ladifa wai me ya sanyan abinda bakya yi yau zaki fara ?.” Sai ta yi gaba yace “okey bari nai wanka na kaiki ban aminta ki fita ba.” Zama tai tana ci gaba da kukan, karanto duk adduar da tazo bakinta ta shiga yi, ahankali ta ji zuciyarta na sanyi, tana nan zaune sai ga shi nan ya fito cikin shigar jins da tshirt. “Tashi muje,” tai gaba yabi ta abaya. A kofar falon laila ya tsaya ya shiga, ba ta falon tana kuryar d’aki, itama tai wanka ya shiga ya tsaya yace “abinda kikai kin kyauta laila.” Sai tajuyar dakai tana kara tamke fuska.
Yace “mun tafi asibiti da ladifa”, da sauri ta juyo kan tai magana ya fice.
Suka fita ta shiga gaban motar. Ya tuka su fuskarta atamke tana kallon gefe, asibiti suka fara zuwa aka duba ta normal, amma likita ya jaddada mata rage yawan damuwa, saboda
yanzu abu kadanne zai sanya jininta yayi sama.
Bayan sun baro asibitin direct gidansu ya sauketa akofar gidan,ta fice yace “yaushe zanzo na d’aukeki?.”
Bata juyo ba tace “sai karfe goman dare” Ta shige ciki, da kallo ya bita yana raya abubuwa da dama aransa, dafe kansa yayi yana
dama haka mata suke! in suna fada, shi ladifa taf bashi mamaki yanda lokaci daya ta
haukace musu, tabbas sai yanzu ya dada yarda mai hakuri bai iya fushi ba. Wajen abdallah abokinsa ya tafi direct. Koda yaje bai shiga ciki ba Abdallah ya fito suna hira, ya kalleshi “yana ganka haka a birkice?.”
“Wallahi yau na shiga komar mata.” Nan ya gaya mai Abdallah yayi ta kwasar dariya. “Maganinka ai ni nafi ganin lefinka idan baka tsaya tsayin daka agidanka ba,wallahi sai gidanka ya dawo karamar kasuwa. Nayi mamaki ma matarka mai hakuri, amma sai da fitinanniyar Amaryarka ta kaita bango wallahi, wallahi ina gaya maka ka lallaba ladifa wallahi irinta maza da yawa suke, zumudi kuka sanya hakurinta ya kare to wallahi sai kun raina kanku, dan mai hakuri bai iya fushi
ba. Wallahi duk randa ta kile sai ta amayar muku da duk hakurin da tayi dakai da matarka, ya kamata ka zama tsayayyen namiji agidanka, amaryarka zaka takawa burki tunda ita ce fitinanniya.”
Sumarsa yaja baya yace. “Maganarka na kan hanya.” Da dariya ya kalli abdallah yace “ko kaima za ka karo wata ne?.”
“Ah rabani ni mace d’aya ta ishe ni, banda ra‘ayin mata da yawa, indai ka ga na k’ara aure. To Allah ya kaddaro ne.” Haka sukai ta hira har suka rabu. Laila kuwa itama kanta mamakin lad’ifa ta ringa yi, lta a tunaninta ma lad’ifar ko aljanu ta tayar, musamman ganin yanda idonta yayija jawur! gashinta ya bazu, sai taji wani shakkarta na shigarta.
Tana shiga gida, taji sanyi aranta, sai ta shiga kwadawa hajiya kira, hajiyar na k’uryar daki, sai hassan dake cin abinci afalo, yace “oyoyo my beautiful gambo.” Murmushi tai tace “ni kaga yaya bana son sunan nan.” Zama tai gefe shi kuma yaci gaba da dariya “to ai gambonmu ceke, k0 kin manta?!’ “Na tuna, ta fada tace “ina hajiyata.” Alokacin hajiyar ta fito tace “wa nake ji kamar autata.” Da sauri ta mike ta rungume hajiyar sai hawaye. Cikin shagwaba “ni hajiya yanzu kin daina yi na, ko zuwa inda nake ba kya yi, Allah yau kwana zan anan, tunda bakya zuwa, sai dai nai ta missing dinki, kuma shi ba ya barin fita.” “To ke hakan bai fi miki ba? meye amfanin yawan fitar.” “To hajiya ki ringa zuwa mana.” “Inje in miki me? ba karima na zuwa ba, kuma ai muna waya.
Zama tai agefe tana sharar hawaye,ji take kamar ta sanar da hajiya abinda ke ranta, kallon hajiyar tai tace “zanci dan wake, ta fadaa tana hararar hassan dake mata dariya ganin tana kuka. Hajiyar tace “dole ne autata.”
Mikewa hajiyar ta yi ladifar ta bita suka shiga kitchen, tana hada abin danwaken, karshe ita ta karba tana yi, suna hira, kashi sabain na damuwarta taji yayi kasa. Suna nan zaune akitchen har hassan ya gama ya fita, alokacin ita kuma dan wake ya kammalu, tunda kad’an akai mata.
Falon suka koma ta zauna gefen hajiyar tana tambayar ta babansu, hajiyar ke sanar mata ya je bichi d’aurin aure. Shiru tai tana cin danwaken.
Hajiyar na karantar ‘yartata, bini -bini yanda take shiru tana dan tunani. K0 bata fad’a ba
tasaan akwai damuwa aranta, kuma ga yanayin ciki dole dama me ciki wasu yakan zo musu da zafin zuciya. Amma duk da hakan ta karanci yarinyar tata akawai abinda ke sasukarta, zurfin ciki ba zai barta ta fad’a ba.
“Ni kuwa ya zaman naku da abokiyar zamanki ne ladifa ?.” Kallon hajiyar tayi sai taji tana san sanar mata, amma ta kasa sai tace “Alhamdulillah.” “Lad’ifa akwai damuwa aranki gaya mini.”
“Hajiya wallahi ni lamarin fin karfl na yake, ina sarewa da wuri, kishiyata na yawan nuna zafin kishi a gareni. Kuma ba ta boyewa.” Murmushin manya tayi “yo ba sai ki tura mata aniyarta ba. Tunda kin gano ita me zafin kishi ce, to ke ringa yawaita boye naki, kodan samawa mijinku kwanciyar hankali da buduwar arzik’i, duk da nasan kina kwatantawa amma a kara. Kuma da kin fahimci akwai wani neman ta da zaune tsaye da take san kawo miki, yi sauri dinga nanata hasbunallahi wa niemal wakeel. Komai ya shige miki duhu kai kukan ki ga Allah mahaliccin mu. Shi kad’ai zai iya share miki hawaye. Mu duk ‘yan shawara ne.
Sannna abu na biyu da nake son gaya miki “kinga namiji, har idan ba a samun wacce ke nusarda shi a matansa ko yaya, to fa shi ba ruwanshi, wani namijin dukyanda mace ta bi dashi zai biyu, ke koda kuwa kwananki ne wani zai iya kai mata, muddin tasan hanyar hilatarsa.
Abinda ya kamata ace kinyi shine ki yawaita nusar da shi illar duk wani abu da kika ga yana neman kawo muku nak’asu, da yawaita nuna mai hanya mai kyau, amma ba wai cikin gadara ba, cikin salon k’irsa da lumana da kaskantar da kai. Saboda namiji ba ya son a matsayinsa na maigida kice wai zaki gaya mai daidai, wani gani zai kin raina shi ma, amma da kaskantar da kai, kice ni wane sai naga kaza yafi kamar kaza. Kuma kina yi kina kambama shi namji yana son a dinga kambama shi ana kuran ta shi, kamar adinga nuna mai shifa jarumi ne a wuri kaza, to zaki ga bai san ma sanda zai d’au shawararki ba. Ki na Jina?. Cikin ladabi take sauraron maganar mahaifiyartata.
“To indai kinsan hanyar kirsa, wallahi duk tanan zaki dinga dora shi hanyar da kike so? komai kuwa baudewarsa, don akwai baudaddun maza masu gaza fahimtar matayensu. Mace ta gari itace zata dinga saita mijinta. Tana dora shi kan turba mai kyau.
Wata kuwa macen, kanta kawai ta sani babu ruwanta, indai zata na samun abinda ranta keso awajensa. To fa babu ruwanta koda kuwa hakan yana zamantowa silar kuntatawa abokiyar zamanta, ita ya kyautata Mata.
Wanda bata san cutar kanta da kanta take ba. Amma kinga idan aka ce tana saita shi, to da sannu zai doru, kuma ya zauna akai har kiga silar hakan ya d’ayar matar.”
Wani sanyi ladifa taji ko ba komai ta samu wasu idears a wajen mahaifiyarta. Tabbas babba babbane sai ta kwanta gefen hajiyar tace “insha Allahu hajiyata zan kwantata.”
Kissoshin mataye na gari tai ta bata, tarihin matayen annabi muhd S.W.A taita ba ta, wanda ba wai
dan bata sansu bane ahh, tun tana karama mahaifiyar tata ta sabar mata dasu. (Shawara ga iyaye mata yakamata ace yaranki mata tun suna kanana kina yawaita basu kissoshin mataye na gari da irin fad’i tashin da suka sha. Hakan zai zama ya zauna a
kwakwalwarsu wanda zaki ga burinau kawai su kwatanta irin abin kwaran nasu.)
Tanaji tana yin murmushi dan taji dad’i, tana son kissoshi a rayuwarta. Wanda hakan ke dada sanyawa taji komai na duniyar ma ba komai ba ne. Wani bacci ne ya kwasheta wanda ba ta san ta yi ba. Murmushi hajiyar tayi ta kalli fuskar yartata sai ta bata tausayi dan tasan zama da kishiya sai hak’uri. Ganin yanda kanta yake ba kitso ya sanya tana baccin hajiyar tata tayi mata. Ba ita, ta tashi ba, sai wajen biyu da rabi, tana tashi ta ji kanta da kitso, tasan hajiyar ce tai mata, alwala taje tai yi tazo tai sallah. Tana idarwa hussain da hassan suka shigo, nan fa hira ta barke atsakaninsu, suna yi tana cin shinkafa da wake da salak hade da su tumatur cucumber da soyayyen kifl, wanda hajiyarta yi da kunun aya, saboda tasan favourite food din lad’ifar ne, sosai ta ji tama manta da wai wasu laila da ramadan,duk bacin ranta ya gushe, tana jin kamar ta dawwama a gidansu.
Sai misalin bakwai na dare mahaifinta ya dawo, shima suka gaisa yayi ta sanya mata albarka ya karai mata nasiha kan rayuwa da aurenta.
Wajen tara da rabi sai ga ramadan yazo sai ta sanyawa hajiya kuka tace ita kwana za tai, hajiya tace “yau naga shak’iyiya, kamar wata karamar yarinyar, ke tashi bi mijinki.”
“Hajiya dan Allah ki barni sai gobe.” Hade rai hajiyar tayi, ganin hakan saita mik’e.
Gwangwani babba hajiya ta dauko mata cike da zuma mai kyau tace ” kullum da safe ki sha kan kici komai auta. Nasan yasan cikinki watansa biyar ko, naso baki ma tun yana wata hudu, amma sai yanzu aka kawota mai kyau ce, Za ta kara miki lafiya da abinda ke cikinki. Sannan ki yawaita karatun alkur’ani koyaushe da addu’oi kinji, Ki gaida abokiyar zaman taki.”
Sannan ta mik’a mata bak’ar leda cike da kayan kwad’ayi, hassan su ka rakata tana sharar hawaye, gaban motar ta shiga ta zauna, idansa na kanta tsoron magana yake mata dan ya kula bata sauko ba.
“Babyna bari’ na gaida su baba,” saiya fita ya shiga gidan tare da su hassan suka gaggaisa, yana shigowa ya tarar da ita tana kuka, magana yayi mata ta murguda baki, sai ya saki dariya.
“Hukuma sai da lallashi, me kike so ne a siya a hanya nasan bakin baya rabo da kwadayi..” Wani kallo tai mai tajuya tana sharar hawaye. Dan har ga Allah bata son komawa gidan.
Sai kallonta yake ganin yanda take sharar hawaye. So yake kawai ta kalleshi amma taki, agefen mai tuku bar tsire ya tsaya “a saya ne?.”
Ba naci ta fada ba tare da ta kalleshi ba.” Adaidai layinsu ya tsaya ya kalleta “yace “wai kukan nan na meye ne?.”
“Ni ba zan iya ci gaba da zama agidanka ba, sai dai ka raba mana gida in dai kana son zaman lafiya.Danni ba zan iya da jarabar amaryarka ba.”
“Oh! My God baby me yasa za kice haka?.”
Kukan ta take sosai tace “Wallahi ni bazan ci gaba da zama tare da matarka ba, indai kana son zama dani sai dai ka raba mana gida.”
Ganin yanda take kuka sai ya matsa gefenta ya janyota jikinsa ya shiga shafa bayanta yace “Nayi laifi babyna, ki yafemin, bana son raba gidan nan, kinga ga inda kika fara zama ba zai kyautu a canja ba, tunda Allah ya wadata nan da girma sosai, am so sorry babyna.” ‘
Kukanta take yi kawai. Ganin hakan ya dada nutsuwa yana gaya mata kalamai masu dadi. “Ina son ganin giftawarki babyna a kullum! Kinga idan na raba gida saifa sanda nake wajenki zan ganki son raina, kece rayuwata babyna, please kiyi magana lad’ifa.” “Shi kenan, amma Allah indai makamancin wani abu ya dad’a faruwa Allah zaka neme ni ka rasa.” “Kitson kanta ya shiga bi layi layi yana shafawa biyu sosai yayi kyau sai kamshin man kitso yake. Cikin jin dad’i ta hakura, Cikin muryar da ya san ladifar naso ya shiga rad‘a mata kalamai masu sanyaya zuciya akunne.
Lumshe ido kawai take tana jin dadin moments d’in. Tsam! Ya rungumeta yana shafa gefen fuskarta. Tun tana hade rai har sai da tai murmushi. Wani lumshe ido yayi, ya bata peck a goshi yace “I love you.”
Wanda bata amsa ba sai ma wani bacci-bacci da taji ya fara daukanta, ga sanyin iskar wajen dake ratsowa tana shigowa ta glass, hakan ya sanya suka dada nutsuwa suna jin numfashin juna. Sun dad’e a hakan cikin motar sannan ya tada motar suka karasa gidan.
Suna karasawa gida ta fita ta shiga gidan tayi samanta. Laila na falo a zaune kamar ta fashe, babu wacce taiwa wata magana a tsakaninsu.
Yana shigowa laila ta tare shi. Zata farai mai korafl. Yace “yanzu abinda kai ya dace.”
Sai ya daga mata hannu. “Dan Allah laila ki rabu da irin wannan hali ba naso,kome ya faru ke da ita duk zamuyi magana gobe, kaina ke ciwo tun safe ban runtsa ba, haba koyaushe matsala matsala.”
Leda ya mika mata ta karba. “Kije ki kwanta gobe zamuyu magana.” To tace kawai sukai sallama tayi hanyar dakinta. Shi kuma yayi sama.
Akwai abubuwan da nake so ku fahimta game da labarin nan, kacokam! dinsa ya ta ‘allaka ne akan muhimmancin hakuri da zamantakewar aure da kishiya, a yanda rayuwar mu take tafiya a yanzu, kuma labarin nan kashi 90 cikin 100 true life story ne, 20 ne kawai wanda na kara, kunga kenan dole sai ana tankade da rairaya,kuma dole aringa ganin abubuwa kala kala. Bawai son zuciya k0 bin bayan amarya ko uwargida ba, ahhh komai yana tafiya ne bisa halayya.. Akwai maza bila adadin irin Ramadan. Haka akwai mata da yawa irin ladifa wanda ni nasan wadanda wallahi halin da suke ciki yafi na lad ifa kuma haka suke hakuri, wanda zance yafi na ladifarma. Idan Allah ya kaddarowa bawa abu babu yanda zaiyi dole sai dai yayi hakurin, in kuwa baiba sai dai yasha wahala kuwa. Wasu har su mutu cikin halin suke, babu yanda za suyi saboda kaddararsu ce, akwai kuma wanda gab: hakurin su ya kaisu inda ba suyi zato ba, indai kaga mutum baici riba arayuwa ba, to hakurin sa baiyi yawa bane. Akwai mata irin laila wasu ma sun wuce ta. Ni dai fatana kawai mutun ya dau abinda yasan zai karu da shi. Sannan ga tambaya ina so ku gaya min wacce riba Ladifa ta samu tun daga farkon zamantakewarta da ramadan har izuwa yanzu da suka zama su uku.???
Akwai nasarorin data fara taka wa ina son ku gaya min su watakil daya ne ko biyu a ciki