NAYI GUDUN GARA CHAPTER 26
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 26
Da safe, a darare laila ta tsaya gefen ramadan tana zuba mai abinci, cikin sauri ta ke komai, saboda azalzalarta da ya shiga yi, saboda za su je wani meeting da shugabansu ya wakilta suje abuja, sabuwar lamba ke ta kiranshi amma bai da lokacin d’auka, dan ba kasafai ya ke d’aukar lambar da bai sani ba. K’arfe goma ya kammala yayi musu sallama ya tafi, sai alokacin laila tai hamdala sabida ganin yanda ya ke cikin yanayi na fada. Ga kuma mafarkin da tai daren jiya wanda ke damalmala zuciyarta. Dan tai mafarki wai ramadan ya saketa. Shi’isa tunda ta tashi ta keyin dari -d’ari. A sanyaye ta koma shashinta.
Shida abokin aikinsa suna tafiya suna hira. Inda suke ta kwararar gudu amota. Wayarsace ta shiga kuka, alamartana bukatar a kawo mata dauki.
lambar dake faman damunsa da kira ne ya gani, tsaki ramadan yayi ya yace “wallahi bana son damuwa,” sai ya d’aga kan yayi magana ta katse .Sai ga sakon text msg nan ya shiga wayarsa da sauri ya duba aka ce; “ka kunna data na turo wani sako ta whatsapp.”
Mamaki ne ya cika ramadan, sai ya samu kansa da kunna datar, sabuwar lambar dake kiransa ce ya gani, ya shiga hotuna ne guda biyar duk ya bude, biyu hoton murabus ne da laila suka dauka a adaidaita sahunsa, wanda alokacin da kyar laila ta bari suka yi shi, dayan ma su biyu ne, sai ukun suka zama screenshots na chating nasu shida lailar, ga lambarta nan baro-baro, dakejikinsa ya fara tsumuwa,yana jin wani daci na kishi da bakin ciki na mamaye dukkanin ilahirinjikinsa. Haka ya shiga karantawa wanda murabus alokacin daya dameta akan in ba suyi chat ba,sai ya takurawa rayuwarta, duk da ba wata magana bace, amma ramadan yaji haushi kamar ya kamo murabus ya makure, duk abinda yake bai bari abokinsa ya fahimta ba, sai dai duk ya rage walwala, lambarya kira ya ji akashe. Tunani ya shiga kan lokutan da yake ganin laila na waya, inta ganshi sai ta yi
sauri ta boye, in yayi magana tai karya tace mai adashi ce ko kawarta. Wani irin hucin zafi yaji kirjinsa nayi, tabbas ya gasgata laila na soyayya da saurayin, kuma
ya tabbatar shine na wajen dinner.
Ba su suka dawo kano ba, sai wajen shida na yamma, agajiye ramadan ya koma gida.
Bayan an kiran sallah ya je masallaci ya dawo ya zauna, don abin nan na damunsa. Duk
yanda laila ke masa rawar k’afa, amma fuskarsa atamke. Duk wani hidimarsa sai dai ya bukata wajen ladifa. Hakan ya sanya laila ta shiga k’unci.
Laila na daki misalin karfe tara na dare. Sai juyi take tana tunanin mijinta. Yananyin yanda duk ya sauya mata tun jiya, al’amarin da ya dugunzuma ruhinta kenan, a yanda take gano
fushi malale asaman fuskarsa, ta tabbatar abu kadan za tai ya saukar da fushinsa a kanta.
Mik’ewa tai cikin ruwan hodar sleeping dress tayi dakinsa. Ba bacci ya keba, amma
idonsa a rufe. A hankali ta taka har inda ya ke ta zauna agefensa. “Habeeby.”
Bai amsa mata ba, har saida ta kara maimaitawa.
“Yes! ina jinki.”
“Ban gane ba kwana biyu duk ka wani canja, haba Ramadan gaskiya ba ai min adalci wallahi, a girkina amma sai basar dani kake kana kula waccen matar taka.”
“ldan korafi kika zo kawo min akan abinda kike ganin an miki rashin adalci, to ki tashi ki fice min daga daki. ldan har ke bakya ganin lefin da kikai, to zaki iya cewa komai.”
Yana gama fadar hakan yajuya mata baya yayi kwanciyarsa gefe daya, alamar bacci zai. Wanda ba bacci yake ba, kawai tunanin kalar hukuncin da zaiwa murabus yake, ga kishi na cinsa.Wani irin haushin lailarya keji sosai.
A hankali ta mike taje bayansa ta kwanta ta shige jikinsa ta sakalo hannunta ajikinsa. Yana jinta amma bai kojuya ba.
“Yanzu habeeby dan kawai munje dinner nai rawa, nayi ciko, sannan wannan mutumin yazo ya nuna ya sanni shine za ka canja mini?.”
Afusace ya tashi yace “get out laila, tunda ke baki san abinda ya kamata ba, dan rashin ganewa ma yanzu duk wannan lefukan da kika lissafo shine ba laifi ba? ldan har to kina ganin su kadaine lefinki, to ki gane basu kad’ai bane, dan iskan saurayin da kika bawa dama kuna soyayya yake damuna da kira har dasu turo hotunanku, ko shima zaki ce ba laifi ba ne?.” Faduwar gaba ce ta bugi kirjinta. Lailai murabus na son janyo mata jangwaml. Rungumeshi ta kumai ta ce “sorry habeeby, wallahi banda laifi aciki, ni fa duk bansan me yake faruwa ba.”
Tsawa ya daka mata yace ta fitar mai daga daki, ganin yanda fuskarsa ta canja ya sanya ta mike ta fice. Tana zuwa shashinta sai ta fasa kuka, tunani ta fara yi kawai wulakantata
ramadan ke shirinyi. Aranar kowa da jin haushin dan uwansa ya kwana. Washegari da misalin karfe sha-biyu da rabi na rana.
Waya ramadan ke yi yana masifa yayi order kaya amma an samu matsala, ga haushin dake damunsa na al’amarin laila, duk suntaru sun dagula mai lissafi tsaki kawai yake
sakarwa akai-akai. ‘
Yana karasowa kasan, kamshin girki ya doki hancinsa. Ya tabbatar daga kitchen d’in ladifa ne, sai ya tunkari madafar, tana tsaye tana girki. Karasawa ciki yayi yace “mai ciki.”Da sauri ta juya ta ga shine sai tai dariya ta ce “harka ban dan tsoro.”
“Sarkin tsoro.” Ya fada tare da bude Hannunsa yace “zona gaisa da babyna tun jiya
rabona da shi.”
Matsowa tai tace “oh ni wannan babyn kardai ya fito ya kwacen ‘yar fadar dana fara samunta.”
Hancinta yaja yace Wane shi.”
“Hmm! tace gaskiya ne fa.”
Kansa ya dora akan kafadunta, hannunwansa dukka biyun na kan cikinta yana zazzagayawa. “Masha Allah. Ya ambata. “Saura ‘yan watanni ya fito duniya ko?.”
Dam! Gabanta ya fad’i, ta ce “hakane, ni wallahi har na farajin tsoro, ance haihuwa da
wahala.” “Insha Allahu lafiya lau za ki haihu. Karki sanya komai aranki, kin dai ji abinda likita yace.” “Hakane” Ta fadajikinta a sanyaye. “Me kike dafa mana ne?.” “Soyayyan kuskus ne me kayan lambu sai sai miya..”
Murmushi yayi yace “ai bakin naki ne kuskus.” Sai ta sanya dariya. Tare da d’aukan Wuka ta shiga yankan albasa tana yi suna hira. Yanayin kalamanta cikin lafazai masu dadi da russunawa, sautin muryarta, duk suka shafe bacin ran daya ke ciki, kashi 20 cikin d’ari, duk babi. Sai kallonta yake, azuciyarta yana yaba yanda take hidima da shi kalakala, duk da cikinjikinta, duk wani abu da zai ganta tana yi to hidimarsa ce. Sab’anin laila da wataran zai sanya ta abu, tai mai ba cikin dad’in rai ba. Tabbas! A yanzu ya dad’a gani sirrikan yarinyar wanda da ya gaza ganewa.lalle! Ya dad’a yarda mata suna suka tara, kowacce da halinta. Wani irin sonta ne ya kejin yana shigarshi . Yana jin idan babu ita rayuwarsa ba lalle ta ci gaba da wanzuwa adaidai ba.
Yar karamar kara ta sanya, ta saki wuk’ar da sauri ta rike hannun tana matsewa, da sauri ya matsa yace “meye ne ?.”
Nuna mai ta yi ta yankejini na d’an tsatstsafowa, duk da cewa ba da yawa ta yanken ba, hannun da ta yanke ya sanya abakinsa ya shiga tsotse matajinin dan raguwar zafin.
Jingina yayi dajikin wani tebur na yankeyanke ya tallafota ta shigajikinsa, still hannun na bakinsa idonsa na kan kyakkyawar fuskarta. Ita ko sai lumshe ido take , a hankali ta ce “dearna ya dan rage fa.”
Fuskarta ya shafa ya ce “maman twins, dole ne ki zamto abar kulawa a gareni, saboda yabon gwani ya zama dole.”
Wani kallo tai mai tanajin kamartai kuka, abinda tafiso kenan soyayya, tana son soyayya
da kulawa. Babu abin godiya face sarki Allah da ya karbi adduarta. Da ya fara cika mata burinta. Wataran idan ta zauna tana tunanin halin d’a namiji, sai taji ta sare, dan tana jin tsoron karya sabar mata yazo ya daina. Shi’isa akullu take dad’a kai kukanta gurin Allah ya dada basu zaman lafiya da fahimtarjuna. Dan duk sai da su komai ke tafiya daidai.
A nan ramadan ya shashance suka d’an fad’a gajeriyar soyayya, wadda adaidai lokacin laila ta fito za ta shiga kitchen d’in lad’ifa, dan ta samo citta.
Ganin ramadan aciki da salon yanda suke, ya sanya har da zata shiga sai ta koma da baya ta zauna a kujerar dake daidai saitinsu, kamar wacce akaiwa dole, idonta akafe ganin yanda ramadan ke wani nan nan da ladifa ita kuma tana wani narkewa cike da shagwab’a. Wani tsaki ta sanya tace “aikin banza wai mace da ciki ma amma sai an wani naniketa.” Ganin in taci gaba da zama, za ta iya fasa kuka ya sanya ta mike bagazan bagazan tai shashinta tana cewa “jarababbu kawai.”
A kitchen din kuwa sam basu ankare da laila ba, ladifa ganin lokaci naja, inta biyewa ramadan ba zatai aikin komai ba, sai ta zame jikinta ta matsa taci gaba da aikinta, wani sanyin dadi na kwaranyowa a kirjinta, wai yau itace ramadan ke wa soyayya wacce bata
taba zata ba,yana cikin kitchen din har ta karasa ta bude kofar baya ta dau wani
karamin bowl za ta fita. Yace “me zakiyi ne abayan gida baby.” Kallonsa tai ta ce “kasan na shuka zogale, tsinkowa zan ina son na dafa ne nasha ruwan.”
Murmushi yai, yace .”Na kula ad’an kwanakin nan akwai ki da shan abubuwa kala kala, har
wani zobo mara sugar kike sha.Meye amfanin shan su ne?.”
Duk magani ne fa, ta fad’a tana murmushi.” Ganin ta fita sai ya bita dan yaga inda tai
shukar
Lokacin laila ta kuma fitowa daga d’akinta, a zatonta har lokacin ramadan yana kitchen d’in, dan ta shirya ko ba ranar girkinta bane sai ta shiga ta zazzaga rashin mutunci, direct kitchen d’in ta shiga, ganin ba sa nan ta tsaya tana dubedube, glass jug din dake cike da lemon kankanar da lad’ifa ta gama had’awa ta gani agefen fridge, sai ta d’auka ta bud’e ta matsa inda sink ya ke ta tsiyaye shi tas!, ta dangwarar da jug d’in cikin sink d’in tana huci, kishin da takeji azuciyarta ya kai makura, dan ji take kamar ta farfashe komai na kitchen din
ga bakin -cikin halin da take ciki wanda murabus ya janyo mata ramadan ya fita
harkarta. Jin alamar maganar su sai ta fita daga kitchen d’in da sauri.
Ladifa na shigowa ta ga jug empty acikin sink duk alamar lemon a zube, kallon ramadan tai tace “zauji kallli lemon da na hada babu shi, nayi mamaki, zuciyarta ce ta hasko
mata laila, sai ta basar dan zato zunubi.
Shima bai kawo komai ba ya ce”watakil baki ajje shi daidai bane” Ya fita waje dan alken maigadi.
Bayan shudewar awanni.Wanda ya yi daidai da lokacin karfe tara; na dare.
Dukkansu suna falo. Ladifa na kwance a kaikaice, kanta na kan kujera, ta dora Kafafuwanta akan cinyar oga sai mammatsa mata yake, sakamakon jin kafar tata tai mata nauyi, ga kuma tsikon da taji tanai mata, hakan yasa ta langwabe sai matsa mata yake, hannunta rike da biscuit pure bliss tanaci, laila ma na gefe daga dayan bangaren tana kallon wani film, wanda rabin duk wani tunaninta na ga yanda ramadan kema lad’ifa,
duk da cewa tasan ba danjin dadi yake mata ba, sai dan ba tajin dadin jikinta ne.
A daidai lokacin wayar lailartai kara, ba ta duba sunan mai kira ba, kawai sai ta daga,jin muryar murabus sanya ta kalli ramadan da sauri. Sai ta kashe ta shiga tunanin ina ya samu sabuwar lambarta, Kuma bugowa yayi, sai ta tashi ta bar wajen jikinta na bari..
Kallonta ramadan yayi yana aiyyana abubuwa da dama aransa, maida dubansa ga lad’ifa yayi, yace mata yana zuwa, ta daga mai kai, sai ya mike yabi laila.
ltako tana tsaye dafe da gefen kanta. Waya akunnenta tana magana. “Yanzu murabus! yaya kake so nai ne? na kula baka da cikakken ilmi, ya ina matar aure za ka nemi doran masifa kasan masifar da kajawo min a yanzu ma kuwa?.”
Daga can ya fasa dariya “kamaryanda kikai mamakin yanda akai na samo sabuwar lambarki, dan haka karkiyi mamaki na, kawai kibi abinda na ce gobe kizo misalin k’arfe goma sha-biyu na rana,in ba haka ba, wallahi tallahi sai nai abinda na zartar.”
Jikinta ne ya hau bari. Ta runtse ido “zanzo ta fada ba tare da tunanin komai ba.
Sai ya tuntsire da dariya. Cikin fusata dajin dacin kalar haukarda yake mata. Za tai magana ta ji ya kashe. Sai ta bi wayar da kallo,juyowarda za tai idonta ya hadu dana ramadan tsaye ya harde hannuwansa, idonsa kirr! akanta, matsawa tai baya da sauri, sai ya taka ya isa gabanta ya mika hannunsa “ban wayarki.”
Kin bashi tai, har saida ya daka mata tsawa, wacce ta sanya cikinta kadawa, sai ta mik’a mai da sauri, bai magana ba ya fice yana jin ba zai taba kyale murabus ba har ita lailar.
A ranar duk acikin zullumi laila ta kwana, haka kawai takejin babu dad’i sai tsinewa murabus azuciya take, ayau ta yi dana-sanin yaudararsa, ta yi dana saninsa ma.Kai tayi dana-sanin tara samari ma. Da kyar ta samu bacci ya kwasheta. ‘
Washegarin Ranar asabar
Misalin K’arfe sha-biyun rana murabus na zaune a dakinsa yana dariya. “Wallahi nuhu ko yanzu kasuwa ta tashi d’an koli yaci riba, zuciyata ta fara sanyi, dan nasan na kafa matsala agidan laila.”
Dariya kawai nuhu yayi ya yace “ka dai kiyaye a toh!” ya tashi ya bar dakin.
Ramadan na zaune yana aiki a systerm wayar laila da ya kwace ta shiga ruri, ganin lambar murabus sai ya danna ya d’auka ya sanya a handsfree, murabus yace “laila ina jiranki misalin shabiyun fa. Saura 10mints tayi.” Bai jira mai za a ce ba ya kashe.
Wani irin zufa ce ta wanke ramadan ji yake da a kusa da shi murabus yake da ya kusa maida shi gari.
Mik’ewa yayi da wayoyin a hannunsa yayi shashin laila.
Tana tsaye afalo tana kaikawo sanye da dogon hijab, idonta na kan agogo,haka kawai ta ke jin gwanda tabi maganar murabus,dan tun jiya taji gwanda taje, ayi ta ta k’are, tai mai kalar rashin mutunci da bai taba zata ba, dan bata so aurenta ya mutu. Sam! alokacin laila bata tunanin mai zaije ya dawo. Da sauri ta dau purse nata da mukulli tai hanyar fita. Sai sukai karo da ramadan, ya kalleta sama da kasa ya mika mata waya.Tabbas! Wajen saurayinta zata ya ayyana aransa.
Wayarsa ce tai kara alokacin, ya dauka murabus ne akan layi “yace yallabai ina son ka sanda cewa matarka za tazo wajena yau, idan kuma ba ka yarda ba, to za ka iya zuwa inda zamu had’u.” Da magana mai karaji ramadan yace “karka bari mu had’u da kai stupid kawai.” Ya kashe wayartare da kallon laila yace “ke shige muje na kaiki wurin saurayin naki, ba unguwa za ki ba?.”
Sai ta diririce ta hau in..ina. Ganin taki motsawa ya ce ta shige suje cikin kakkausar murya. Fita tai ta tsaya a falo, tana jin gabanta na fad’uwa, shi kuma sama ya hau dan d’auko key, dan shi kam ya gaji da matsalolin laila, zama yayi a gefen gado, zuciyarsa ce ta shiga waswasi domin shi ji yayi kawai gwanda ya saketa ma ya huta, sai kuma ya tuno hajiyarsa kan kashedin saki. Runtse ido yayi ya tashi ya sauka kasan, ya shige gaba ta bishi a baya, suka shiga mota suka barwajen,babu wanda ya ce uffan a tsakaninsu, bai zame da ita ko ina ba sai gidan iyayenta, yana fakawa ya kalleta “fice min daga mota.”
A tsorace ta kalleshi murya na rawa tace “me hakan ke nufi.”
“Abinda nake nufi shine, ki zauna agidanku laila, har sai na waiwayeki nasan lokacin kinyi hankali, kin koyi fad’in gaskiya, kin koyi ladabi da biyayya da jin maganar miji.Sannan kin
dada tantance cewa aure fa ba wasa bane, ki kara sanin cewa aure ya katange ki ga
kowanne da namiji.”
Wani irin sanyi jikinta yayi ta kalleshi tana san magana ya daka mata tsawa sai ta fice jikinta na rawa, tsayawa tai harya bace mata da gani.
Juyawa tai ta shige gidansu hawaye na zuba,sai da tsaya a soro ta darji kuka, dan tsoronta Allah tsoronta haduwa da babanta, bata san wanne hukunci zai mata ba. Shiga tai ta shige falon gidansu ta zauna, mamanta na b’are danyar Gyad’a ta kalleta da mamaki.
Zama tai a gefen ummanta ta kalleta “ahh laila yau ziyara aka zo.” Kuka ta sanya. Gaban ummanta ne ya fad’i. “Subhanallah! me ya sanya ki kuka ne laila, ko wani abinne ya samu mijin naki?!‘ Kuka da k’arfi ta sanya ta ce “umma ramadan ne ya kawoni yace na zauna sai ya nemeni.” Wani faduwar gaba ne ya kuma ziyartar umman tace sai ya neme ki, me ya hadaku?,”
Sai tai shiru ta kasa magana. Sai da uwar ta kuma magana sannan cikin rawar murya ta ce “ni ma bansani ba, kawai ya ce dai na tawo ne. Ta fad’a cikin shashshek’ar kuka.
Tsaki umma tai ta ce “ban aminta ba laila, na san halinki, Allah yasa ba wani abun kikai ba, wanda har kika k’ure shi, na san halinki, hmm! ai sai ki zauna idan mahaifinki yazo ya tambayeki kya gaya mai dalilai, tunda ni kinki sanarmin, dan Wallahi na san kece baki da gaskiya.”
Da sauri lailan ta mike tai cikin dakin umma ta kwanta tana rusa kuka.
Shi kuwa yana barin kofar gidan bai zame ko’ina ba, sai police station, duk ya sanar musu abinda ke tafe da shi. Wato akan matsalarsa da murabus na yadda yake shiga huruminsa. Lambarsa kawai ya mika musu wadda ya ke kiransa.Su kuma suka ce za su kamo shi duk inda yake.
Gida ya zarce yana jin babu dadi, in banda zugi babu abunda kirjinsa ke yi, don arayuwarsa ya tsani ya ga ana farautar abinda ya zamo mallakinsa, ko da budurwa ce, kuma koda ba ya sonta kuwa, ballantana matar aurensa. Ya zame dole ya nuna ma murabus kurensa. ‘
Tuno da laila sai ya yi tsaki, ba don kar ya yiwa hajiyarsa laifl ba, da wallahi sai ya yanke igiya biyun da tai saura a tsakaninsa da ita.
Adaidai lokacin laila na kife tana shan kuka, sai ta tashi zumbur ta lalubo lambarsa ta kira ta hau ring.
Yana kallon kiran ya ki dauka, karshe ma ganin yanda ta dameshi da kira sai ya kashe dib!.
Kara kira tai ta ji akashe, Sai taci gaba da kukanta. Ta dafe kanta ta sunkwi da kai.
Ummanta na tsaye tana kallonta. Tabbas! ‘Yar tata ta bata tausayi. Koda kuwa ita ce da laifi, amma hakan ba zai sanya ta take gaskiya ba.
“Ku yaran yanzu sam! Ba a gaya muku abinda ya dace ku dauka, ahh sai dai kuyi ta tafka shirme aganinki wayewa ce ko kuma yanci, sai abu ya tunfke muku kuma ku zo kuna kuka.
Kullum cikin nasiha na ke miki laila akan rayuwa ba kya gani. Yau wa gari ya waya?.” Da sauri lailan ta kalleta ta ce “umma ki yarda dani.”
“Ba zan yarda da ke ba laila, har sai naji gaskiyar komai musamman ganin yanda kike
kuka. Saiki tanadi abin sanarwa da mahaifinki.” Ta fada tare da fita daga dakin. Sautin kukan ta kuma ya karu.