NAYI GUDUN GARA CHAPTER 28
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 28
Hannuwanta ta sanya ta dafe gefen cikinta da taji ya kame, sai ta runtse ido tana salati, ta dade a yanayin, sannan ya lafa, sai ta tashi. Alokacin ramadan ya shigo gida Idonsa ya sauka a kanta. Da kewa tai tayi mai sannu da zuwa,shi kuma ya zauna a gefenta yace “na ganki ba daidai ba baby ya dai ko haihuwar ce?.”
Murmushi tai tace “ba najin fa komai, kawai dai dan ciwo marata keyi.“
Da kinji dai babu dadi ki sanar min baby, dan kinga likita yace da kin fara nakuda akaiki asibiti, saboda ba a son zama agida idan ka fara jin hakan, kinji me yace dai. ”
To tace mai to tana runtse ido tashi yayi ya haye sama.
Ita kuma taci gaba da runtse ido, a hankali ta mike dan ta hau saman, sai taji mararta ta wani amsa cikin ya wani irin juyawa, sai ta danyi kara ta dafa kujera, gadan-gadan ta fara jin ciwo.Wanda a daidai lokacin ramadan kuma saukowa, ganin halin da ta ke ciki, ya ta karaso aguje, yace “kawai muje asibiti.”
Bata musa ba, ya dauko mata hijab suka tafi.
Koda suka je aka tabbatar cewa haihuwa, ce amma da sauran lokaci k0 zuwa anjima. Nan aka sanya ladifa ta ringa kaikawo tana zuwa ta dawowa.
Ganin hakan yasa ramadan komawa gida, bayan nurse tace ya dauko duk wani kayan baby da ta gaya mai, dama can sun had’a komai shi da ita. Bai zarce ko’ina ba, sai gidansu, ya sanarda hajiyarsa. Sannan ya sanar da hassan yayan ladifa kan ya fadawa hajiyar ladifa.
Kan uku duk sun hallara a asibiti, hajiyar ramadan da kareema wacce hajiya tace taje asibitin, har lokacin ladifa babu labari.
Tana labour room tana cin kwakwa da nakudar ta lafa sai ta tashi. Ramadan duk ya damu sai kaikawo yake,ji yake kamar ya maido da ciwon da ladifar keyi a jikinsa, musamman jin yanda take salati.
Hajiyar ladifa na gida, bini -bini ta bugo waya tace “ta sauka,” kareema tace har yanzu dai, nan hajiya ta shiga addua tana cewa “Allah ga baiwarka ladifa na kan gwiwa. Allah ka sauketa lafiya, ya Allah ka bata juriya. Haka tai ta addu’a tana tuno ‘yar tata.
Sai wajen shida na yamma ladifa ta sauka ta samu baby boy. Hamdala akai ta saki, bayan da nurse ta sanar dasu ta sauka, kan bakwai na dare an gyarata ita da baby an shirya su, da yake lafiyarta lau bayan hutun data samu na awa biyu aka dada duddubata, zuwa tara aka sallamesu.
Ramadan kuwa sai rawar kai yake, bayan hajiyarsa taga jariri ramadan ya maida ta gida, ya dawo ya dau karema da ladifa ya tafi kaisu gidansu ladifar dan acan gidan iyayenta zatai wanka.
Ladifa kuwa duk sai murmushi take dan ba bakin magana, sai kallon babyn take. Tana dadajinjina hukuncin Allah wai ita ce yau ta haihu ta zama uwa. Sai girman hajiyarta ya dada darsuwa aranta.Musamman tuno irin gurmurzun da tasha.
Dada kallon babyn tai daya kwaso kyau, hancinsa irin na ladifar, amma inka dauke hancin da ya dauko na ladifar duk ramadan ya dauko komai. Hakan sai ya dada sanya yaron yayi kyau sosai.
Suna zuwa gida, kareema ta dau jariri suka shige, ramadan ya dawo saitin ladifa yace “thankyou baby Allah yayi miki albarka.”
Daga mai kai kawai tai tana murmushi tare da cewa amin.
Laila Tana shiga gidan ta shiga falo sai ta zauna ta shiga tunanin yaya zatai ne? umma ta fito daga kitchen tace “har kin dawo laila?.”
Ta kalleta tace “eh umma. Amma yaki amincewa, dan Allah ki bawa baba hakuri ya bashi.
“Hmm! laila kenan, ai babanki ya ce bashi da hannu akan wannan matsalar sanda mijinki yazo ya dauke ki to. Ya kamata ki dage da addua ki maida lamuranki ga Allah. Duk abinda Allah ya kaddarawa bawa shi nashi karba ne hannu biyu. Ya kuma jure da sannu Allah zai saukaka mai
Hawayen fuskarta ta share ba tace komai ba, sai tarin tunanin data shiga yi, sai ta tashi ta shige daki. Umma ta kalleta ki ciro kayanki kizo ki shiga kitchen.”
“Yaraf! ta zauna agefen gadonta, al,amarin ya fara kaita bango, tsoro kawai take kar aurenta daga haka ya guntule, Lumshe ido tai tana ayyanawa aranta dole ta dage da addua.
Ganin zaman ba zai fishsheta ba, ta canja kaya ta daura zani ta shiga kitchen.
Yau kwana biyar da haihuwar ladifa. Hidima sosai ramadan ke yi, kullum yana hanyar zuwa ganin baby da babarsa, kuma koyaushe da abinda zai shiga da shi, yauma wajen karfe hudu ya tafi gidan ya shiga sitting room dake kofar gida, dakin nata k’amshin turaren wuta, aka mika mai jararin dake ta kwasar bacci cikin blue din kayan jarirai masu kyau,sai kamshi turarenjarirai yake, yana zaune ya kurawa babyn ido, lokacin ladifa na wanka,
tana fitowa hajiya tace mata ta mijinta na dakin kusa da waje, sai data shafa mai dasu
turarenta, ta mulka powder da kwalli ta tafi wurinsa, yana zaune ya kasa ajje babyn ganin yana neman tashi.
Zama tai tace “zaujina,” ya kalleta yace “babyna, koda yake yanzu fa kin tashi daga baby…. Sai dai maman baby.”
Sai ta danyi dariya cikin magana mai shagwaba-shagwaba tace “Allah ni ina nan a babynka.”
Sai ya matso daidai inda takejikinsu na gogarjuna. “Yace “kinfa dan kiba wallahi.”Murmushi tai tace “abinda kake so kenan, to kibar ciki ne murna sai ta koma ciki.”
Dariya ya sanya tare da zame hijabin da kejikinta.Yana cewa “ba kyajin ana zafi ne kika
wani maka hijab.”
Tace “Bar mini abina, dan tunda nazo kullum cikin rufe jiki nake, kasan ba a son mejego
tana barin jikinta na kwasar iska. Idan na tafi kya maida.” Ya fada tare da kokarin zare hijab d’in.
Sai tai murmushi kawai, gashinta dake tsefe a kwance luf yana kamshin man gashi, ya shiga shafawa cikin magana mai dan rada-rada yace “Ba zaki gane ba ladifata.” Hmm! Kawai tace, wanda adaidai lokacin baby ya fara kuka ladifa ta daukeshi, ramadan yace “ki bashi abincinsa mana, sai ta juyar da kai yace “kunya?.”
Sai ta sunkwi da kai, dan ko agida kunyarsu hajiya take dan sai ta shiga daki take bashi.
“Ni wacce kunyana za kiji, oya in baki iyawa bari kiga. Sai ya cire hannusa tsam Daga gashinta. “Me za kai zauji? bai magana ba. Ya gyara mata babyn kan cinyarta, ya daga rigarta ya shiga kiciniyar sanyawa baby,bra ya rike babyn a hannunsa, dayan hannun kuma ya shiga kokarin sai ta mishi, sai ta juyar da kai dan wani irin kunya takeji, jin yanda baby ya cafka da karfi ya fara sha sai ta runtse ido tace “ash!” Tare da rike babyn da sauri.
Ramadan yace “sorry tawan zafl ko?.”
D’aga mai kai tai kamar za tai kuka. yace mata “sannu” Matsawa gefenta yayi sosai ya
sakala hannunsa ya riko kugunta ta gefe ya kura musu ido, sai kallon yanda babyn ke tsotsa yake, hakan ya sanya yake dan murmushi, daga kai yayi ya kalleta dan wani irin burgeshi sukai babyn da ladifar. “Yanzu fa shi kenan baby ya kwacen fagena ko ladifata.”
Sai ta sunkuyar da kai cikin jin kunyar maganarsa, dan ta gane abinda yake nufl, ta rasa mai yasa yau takejin kunyarsa sosai, dago fuskarta yayi suka kalli juna “ko ba haka bane?.” Sai ta juyar da kai tana murmushi tace “hmm kaida babyn ai duk naku ne karka damu….”
Wani irin murmushi yayi ya shiga wasa da k’afar babyn yace “nasan ladifata dabance.” Tare
da jan dogon hancinta a hankali. Kokarin cire babyn ta shiga yi,yace “ehem! abar mini little ya koshi.” Cikin muryar shagwab’a tace “zafi fa zauji.” Sai ya kwaikwayi muryana. yace “oya acanja masa wani.”
Nan ma ganin taki maida shi daya bangaren, ya sanya hannu ya maida shi, yaron yaci gaba da aikinsa, ganin yanda ta dan turo baki tana yin alamar cije leb’e saboda zafin yanda
yaron kesha,ji take kamar ta saki kara sabida zafi. Ramadan ya shiga mata dariya tace “zan rama ne.” Yace “da wa zaki rama ne kyakkyawata? ai sai dai ki rame.” “Hmm haka kace ko?.”
Sai tai murmushi kawai. Nan dai sukai ta hira har aka yi kiran magrib ya tafi, ita kuma ladifa ta tashi ta shiga gida da babyn a hannunta, ya kareema dake cikin dakin tana waya kan
driver yazo ya tafi da ita, ta karbi babyn bayan ta kashe wayar tace “Oh! ni Mijin nan naki fa da alama ba zai daga miki kafa har 40 ba.” Ladifa tace ” kai yaya?.”
“Ai gaskiyane musamman ganin yanda kike kyalin jegon nan zai iya ribatarki. Ai irinta wata
kawata data kuma samun ciki watan yaron biyu.”
Gaban ladifa ne yace dam! yaya shima ai yasan ban warke bafa.” Kareema tace “hmm ladifa kenan.” Sai ta sunkwi dakai.Tana tunanin yanda zata dan dingaja baya in yazo, dan ita kanta ta kula da yanayinsa yanda yake mata wasu abubuwan Dan kam bata manta gumurzun haihuwa ba.
Haka kwanaki suka tafi har akazo ranar suna, sosai sunan ya kayatu aka dauko DJ mata na
ta warkajami, ga abunci a wadace kala-kala,
maijego tayi kyau itada babyn kamar ba ita ta
halhu ba, tasha gyara tayi kyau sosai, Yaro yaci sunan baban Ramadan sai aka sanya za a
na kiransa FUAD.Haka aka ci suna aka kare kowa ya kama gabansa.
Nan ladifa taci gaba sa wankan jego, agefe hajiya na gyaranta irin na manya. Sosai hajiya ke gasa ‘yartata, da bata abinci wanda zai dumama mata jikinta, dan acewarta wannan shine gatan da zatai mata. Jikinta ya yi kyau sosai. Ta dayan bangaren kareema ita ma tana nata gyaran, ladifa na samun gata da gyaran jiki da waje. Hakan ya sanya ita da babyn ke dada samun nutsuwa da sukuni sosai suka dada murjewa, sukai kyau. Kai ba kace ta haihu ba. Ga babyn tubarkalla laflyayye ga hakuri.
Ramadan ne zaune gefen hajiya yana sauraronta tace “akwai maganar da nake san tambayarka, wai ina matarka ne laila?. Tun da akai sunan matarka ‘yan uwanka da sukaje
naji suna maganar cewa Basu ga laila ba. Mai ya faru ne?
Sai ya sunkwi dakai yace “ai hajiya yau kusan wata biyu da kwana Goma sha-d’aya tana
gidansu. “Subhanallah mai ya faru ne dan nan har da saki.” “Ban saketa ba hajiya. Kawai na maidata gidansu ne ta koyi hankali.”
Hmm! Kawai hajiya tace irin na manya “yanzu ban cancanci ka sanar min da matsalarka ba ramadan ko? Meye hakan ke nufl? To yakamata ka maida matarka.
Runtse ido yayi yace “hajiya wallahi yarinyar ce ba taji, nafi so sai tayi hankali sannan na komar da ita. ”
Shiru hajiyar tayi ganin ya kafe dan ba zata tilasta mai ba, tace to Allah ya kyauta, amma
kar abin yayi muni” Nan ya tashi ya tafi.
Laila taji labarin ladifa ta haihu.Suna zaune suna hira da umma tace “umma kishiyata ta haihu.”
Hajiyar tace “kai masha Allah. Kinsan gidansu ne?.”
Tace “eh!
“To yakamata kije ki mata barka, duk wannan ma wani dada samun salama ne, hakan tabbas! Zai dada sanyaya zuciyar megidanki. Ban so ki sanya azuciyarki cewa ai kishiyata ce, ba zani ba sabida kina kishi, ah ah kije kodan zaman taren da kukai.”
“To ta cewa hajiyar.
Haka washgari ta bugawa Ramadan waya wanda da kyarya dauka ta tambayeshi kan tana son zuwa unguwa. Da kamar yace mata Aa sai kuma yace taje. Haka ta shirya ta tafi.
Lokacin da taje karfe goma sha-biyun rana. Ta shiga.Cikin mutunci aka karbeta saboda hajiyar ta ganeta, sosai ta samu karbuwa hajiyar ta kaita d’akin da ladifar ke zaune. Tana zaune tana gyarawa babyn hular kansa taci kwalliya sai kamshi take. Laila na kallonta taji wani
kishin ganin yanda ladifar ke wani daukan ido, Sai ta basar ta yi murmushi tace “mai jego.”
Cikin murmushi ladifa tace “kai kai! Ashe! Second mother din fu’ad ce munyi murna.”
Sai laila tai yaken murmushi tace “wallahi kuwa ni ce.” Ta zauna tana dan kallon dakin tana dan jujjuya ido, ladifa ta kawo mata jaririn ta karbe shi ta kura mai ido, sai taji dama ita ce ta haifeshi dan yayi mata kyau sosai Sun dade suna hira ta tashi ta tafi, bayan ta ajje kayan barka atampha guda biyu da kayan baby set biyar. Ladifar tai mata godiya cikin kissa lailar tace “haba za ki ban kunya mana lad’ifa, ni da dana har sai anyi godiya ai yiwa kaine.” ‘
Ladifar taji dadin ganin abinda lailar tayi. Tace “to an gode.”
Ba ta dade da tafiya ba ladifar taiwa ramadan waya. Tana sanar mai zuwan laila barka, tare da gaya mai irin abin arzikin da ta kawo. shi kanshi zuwan nata ya dan burgeshi sai yace “mungode mata.” Ladifar na son sanyo mai maganar komowar lailar sai yayi sauri ya katse, dan ya fahimci abinda za tace…. Haka dai satuttuka sukai ta wucewa, har aka haura wata daya, wanda alokacin saura
kwana goma ladifa suyi arb’ain.
Ranar Larabar misalin karfe hudun yamma.
Yayar laila ce da tazo suna zaune suna hira a falo, ta kalli laila dake kwance kamar mara lafiya tace “agaskiya ni dai umma yakamata a san fa me ake ciki, wannan mijin lailar fa wallahi duk kwana-kwana yake, idan ya san ba yayi kawai ya saketa, amma saboda Allah yazo ya jibge mana kanwa, bata san a wanne matsayi take ba. Yanzu fa sauran dan kwanaki tai wata hudu a gida fa.”
“Umma tace to yaya kike so nayi? kullum sai na yiwa mahaifinku magana, amma sai yace ko menene ma ita ta jawa kanta. Ni kaina yanzu ganin yanda duk ta sanya damuwa arai tausayi take bani.”
Suna cikin hirar laila ta mik’e da sauri tai tsakar gida, ta shiga kwarara amai. Sai duk suka bita da kallo.Kowanne da tunanin abinda ke ransa.
Dawowa tai ta zauna ta kwantar da kanta kan cinyar umma. Mahaifiyar ta kalleta tace
“laila.” Tace “na’am” sai ta duba tafin hannunta da kwarin idonta. Tace “yaushe rabonki da al‘ada
laila?.” Shiru tai ta lumshe ido tana jin ba dadi. Yaya zulai tace “ki magana mana laila.” Sai tace “tunda nazo gidan nan banyi ba.”
“Ikon Allah ke kuma naki cikin ta haka yazo. Wallahi naso fahimtar yarinyar nan nada ciki, amma sai tunani na ya kau.”
Yaya zulai tace “ni tun wani zuwa da nai ganin yanda ta dashe na fara tunanin da ciki, kawai shiru nai ina tunanin ko duk abinda ta sanya aranta ne. Kinga ikon Allah ko laulayi batai ba.”
Umma tace “Ai akan samu mata su yi irin hakan. Ina ga wannan dalilin ne ma ya sanya bamu gano ba.Allah yasa cikin ya zamo maslaha na komawa gidanta.
Zulai tace. Ameen
Laila kuwa wani irin dadi ne ta ji ya kwaranyo mata.
Umma tace “idan babanku ya dawo sai a sanar mai ajje asibiti, kinga ayanzu ai ya nemi mijin nata.” Haka dai sukai ta hira akan mas’alar
Karfe biyar na yammar ranar.
Ramadan na tsaye afarfajiyar falon kasa yana waya, hannunsa rike da cup yana shan black
tea. Yace “maman fu’ad yakamata fa kidawo.”
Tana zaune agefan gado tana feeding din fu’ad, sai taja dariya tace “haba zaujina saura fa kwana goma mu dawo, zumudin me kake ne? kai da keda laila.”
Sumarsa ya shafa “ba zaki gane bane ladifata, a kullum nazo na ganki dakyar nake iya controllig din kaina, hakurina yakai makura fa, bani da maraba da gwauro. Baki san yanda nake kewarki ba ne,ina missing din komai naki mum fu’ad”
Murmushi tai najin dadin maganar tana yi tana shafa sunar fu‘ad tace “Allah ko mijina, nima d’in ai kewarka ta dameni, saboda kaine farin-cikin ruhina. Sosai tunaninka ke rage min dadin bacci na”
Kurbar tea din yayi cikin jin dad’in kalamanta ya kuma shafar sumarsa, yace “ko nazo yau
mu fita ne?.” “Ina zamu ne dearna.” “Hmm! Muje ki rage min zafi mana ladifa.”
Sai ta dan zaro ido na mamaki kamar yana gabanta tace “haba dai zauji, yakamata ka
karasa ladanka dearnaaa.” “Ba zaki yarda ba kenan. Toni da gaske nake.” “Zauji.” Dakatarda ita yayi kan ta furta abinda ke zuciyarta, “baza dai ki yarda ba ko?.”
Ganin yanda yake neman birkice mata ce ” ta canja maganar, a gaskiya yakamata ka
dawo da laila gaskiya.” “Da sauri yace “zanfa zo mu fita anjima.” Sai tai shiru. Yace “ki shirya.“ Za tai magana taji kit ya kashe.”
Sai ta kurawa wayar ido jikinta yayi sanyi. Tsoro kawai takeji kar yazo dan ita kam bata san yaya za tai da ramadan ba. Dan tun wani zuwa da yayi yaji ance tana sallah ya taga ya fara ra ra gefe. Sai taja numfashi ta gyarawa fu’ad kwanciya, ganin ya koma bacci.
Hmmm