NAYI GUDUN GARA CHAPTER 3

NAYI GUDUN GARA 
CHAPTER 3
Takaici ne ya kuma cika ta, ganin yanda ake sallamewa a sallar asuba, amma zaujin nata koma juyi bai yi ba, tun farkon tashinta daga bacci kafin ma tai alwala, ta tsaya ta tashe shi, amma bai motsa ba, ita ta rasa wanne irin miji gareta! kullum sababbin halayensa ke fitowa
’Ashe! haka aure ya ke, tabbas! sai yanzu ta dad’a gasgata manya dake cewa ai ta hak’uri, wato irin matsalolin da ta ke fuskanta, in ba dan tana da hak’uri ba, ai ta san da tuni duniya ta sani.’ Ta fad’a aranta cike da k’unar rai, ‘ga shi, shi ya fita hankali da shekaru kuma dad’in dad’awa shine shugaba agareta, amma wai kuma komai sai ta d’ora shi a saiti wanda shine ya kamata ace yana mata hakan, wanda ta kula idan har tace za ta kauda ido ga lamuran mai gidan nata, to tabbas za a yi ‘ya kwance uwa kwance, numfashi ta ja tare da rok’an Allah ya k’ara musu fahimtar juna ita da shi.’ D’aga kanta ta yi ta kalleshi, wani irin takaici ne ya kuma buge ta,jin yanda ya ke kuma sakin munshari, gashi har an ma idar da sallahar. A fusace ta tashi taje taja bargon da ya Iullub’a, tana janyewa, yayi mik’a, sanyin Ac ya buge shi, nan ya bud’e ido ya tashi zaune yana mutsitstsika idon. “Ke meye haka? Wai meyasa ba ki da hankali ne?.” Wani irin kallo ta yi mai, tana dad’a kaurara rashin son afad’a mai abinda ya manta,shi Sam bai san gaskiya. Hmmm! kalli ka ga lokaci, an dad’e da idar da sallah, amma kana kwance kana sharar bacci, haba! Magidanci kamarka wanda ya ci a ce kai kama ta sheni ka wuce masallaci amma kaine da rauni, wai me yasa baka damu da shiga jam’i na sallahr asuba bane, haba! ka 
ko san falalar yin sallahr asuba alokacinta?.” Dakatar da ita yayi, “wato rashin kunyarki har ta kai intaha ko? har ta kaiga kina tsayamin aka kina san cewa ban san addini ba ko? to ki shiga hankalinki wallahi,bana son saka ido kabarinki ko nawa? ni ne dai nan shugaba agareki kuma sai kin bini za ki samu aljanna dan haka ki iya bakinki.” Runtse ido ta yi ta bud’e su tar! akan fuskarsa, zuciyarta na dad’a zaf‘l. “Allah ya ba ka hak’uri, wai dama gani nai lokaci zai k’ure, kuma tunatarwa tana da muhimmanci.” 
Tsaki ya yi ya tashi yana layi ya shige toilet, dam bacci ne aidonsa fal! saboda jiya bai samu ya yi da wuri ba, saboda wayar da yayi da Laila. 
Hijabinta ta d’auka ta fita daga side d’in nasa ta yi nata d’akin‘ Da yake Ranar weekend ne, yana gama sallar ya koma bacci, haka itama ta koma. 
Ba su suka tashi ba,sai goma da rabi,sai da ta yi wanka, sannan ta sauko k’asa ta shiga kitchen dora ruwan shayi, ta d’ora farfesun naman rago, sannan ta hau feraye dankali. Bayan ta gama ta soya dankalin tare da kwan ta ta kai duk kan dining, ta zauna ta had’awa kanta kayan karinta ta hauci. Takunsa ta ji wanda kamshinsa shi ya daketa, ba ta d’aga ta kalleshi ba, saima dad’a maida hankali da tayi wajen 
kwasar abincinta. Ke! ya fad’a fuska a had’e, d’agowa ta yi ta kalleshi tare da d’an sakin murmushi. “Barka da safiya zauji.” 
“Yawwa,” yace mata ya zauna agefe. 
Ta shi tai ta had’a masa, dankali da k’wan, sannan ta zuba mai farfesun a wani mazubin,ajje bread agefe, da kofln shayin da ta had’a tayi ta tura mai gaba. Tsaki ya saki. “Yanzu me ya kaiki sakamin madara da bombita a shayi? kin san cewa bana so ko?.” Kallonsa tai, gabanta ya fad‘i. ‘Safiyar fa tayi, yanzu zai ta k’orafe«k’orafe sai kace makaho.‘ Ta fad’a aranta.”Zauji ai na ga da madara da bombita ka ke had’awa, idan nai wannan had’in.” “Sai kuma akace miki yau ina da buk‘ata ko? Wai me ya sa ba kida kan gado ne?.” “Ka yi hak’uri, na yi kuskure, dan naga rannan dana tambayeka kace kana so ne shi’isa.” Nan ta mik’e ta d’au shayin, “bari na shanye wannan sai na had’a maka bak’in tea, tsaki ya yi ya k’ura mata ido kamar ya maketa ya keji. 
Nan ta had’a mai ta tura mai. “Allah ya huci zuciyar me gida.” Ko kallonta bai ba ya hau 
aikawa tunbinsa. Da yake sanin cewa ba zai fita yau ba, ya sanya ta zauna a falon kan doguwar kujera, tana kallon wani film. Bayan gamawarsa ya shige d’aki, bai dad’e ba ya fito da waya a hannunsa. Zama ya yi a d’aya daga kujerun yana danna wayartasa. Kallonsa ta yi ta gefe, tuno hud’ubar yayarta kan nesa da miji, ya sanya ta mik‘e ta isa kusa da shi ta zauna ta shige jikinsa, tana cigaba da kallonta, kallota yayi yadan matsa, nan ta kuma matsawa ta kuma matse shi, ya ce “wai ke ne ye haka ne?.” 
Tqce Meye danna rab‘i mijina, ta sakar mai manyan idanta, murmushi kawai yayi ya kauda kai, sun dad’e a haka. Barci ya kwasheta ajikinsa. K’ura mata ido yayi ya kafe fuskarta da ido, nan ya manna bakinsa kan nata ya tsotsa ya d’auke ya maida hankalinsa kan wayarsa Ta b’angaren whatsap, msg ne ya shigo ya duba lambar laila da ya yi seving, tana online ya duba dp nata, hotonta ne mai d’auke da wani wankakken hoto k’ura ma hoton ido yayi ya lumshe idon ya maida mata da amsa, nan suka fara hira, sai zuba kalamai suke, wani irin nishad’i yakeji a ransa, kowa na fadin abinda ke a aransa game da dan uwansa. Jin yanda ya ke kod’a surarta, kanta ya fasu, musamman yanda yake fad’a mata ta doke 
matarsa ta gida a komai, Take kanta ya kuma fasuwa. 
K’arshe ya buga mata waya yace zai je gidansu anjima, dan shida k’arfinsa ya ke santa, kuma aurenta zai yi. Su kai sallama suka rabu. 
K’arfe biyar na yamma ya yi shiri, sai tashin k’amshi ya ke, ladifa na tsaye tana d’an goge TV ta falo ya f’Ito, kallonsa ta yi taga yanda ya yi kyau, saida gabanta ya fadi. 
“Zauji ina zuwa haka?.” “lnda kika aikeni,” yasa kai ya fice. Haka kawai jikinta bai bata alheri ba sai kawai ta basar. Taci gaba da ayyukanta. Bai zame ko ina ba sai gidansu Laila .Tana gaban mudubi, gyara nan, saita can, getta nan, matse can, sai da taga ta flto das! da ita, ga turare kamar anyi b’arinsa ajikinta,jin k’arar waya ta d’auka cike da kashe murya. ‘ “Ka iso ne?.” Ya amsa yana waje. Nan ta flta. Hajiya na tsakar gida tana yanka alaiyahu, tace. ” Laila ina za ki haka?.” “Hajiya dama zan sanar miki ne yanzu bak’o na yi.” 
Murmushi uwar ta yi, domin so ta ke ace yau ga Laila ta fidda miji tai aure, don ta gaji da dan surutun da ake mata akan yar tata. Amma kin san dai ni ba na son kina sa ka turare da yawa in za ki hira ko? kin san cewa turare in ya yi yawa yana da matsala ko? musamman ke da waje za ki flta,adai dinga kula Laila, shi,isa Allah ma yayi hanin saka shi ga matan Aure in za su fita, ko budurwar ma bai dace ta bulbula turare ta flta ba, wanda hakan kejan hankulan maza, shaid’an kuma na gefe na ingizasu,haba jifa kota’ina k’amshi ko na waje zai iya jiyo.”
“Wallahi sai da na saka da yawa na tuna kin hana, amma ai afuwa hajiya.” “A dai kiyaye akula.” 
Ta fice cike da takun jan hankali take takawa harta karasa gaban motar, wani irin murmushi ya ke yi. Wani fari tayi da idon da ya sha gashin ido, hakan ya karawa idon kyan gani. ta shige gaban motan domin ba sabonta bane shiga gaban mota ,sama da k’asa ya ke 
kallonta, ya karkatar da kai yana cizon lebensa na gefe. Yace “Kina da kyau lailata.” Allah k0?” ta fad’a cike da yauk’i, wani iri yaji, ga wani yanayi na shigarsa, turarenta da bai tab’ajin irinsa ba, duk da cewar turaren da ya ke sawa masu tsada ne ainun! amma na jikin laila ya tafl da shi, tunda ya shak’i turaren ya kejin ba daidai ba, ga yanda komai na Laila ke d’imauta ruhinsa, kamar ya kamo laila ya rungume. 
Ya daure yace lailata, yaushe zan flto ne? “Wallahi na matsu na ganki a gidana, domin a yanda nakejinki araina,wallahi kamar na zauce,kina burgeni da gayunki, “yar gayu mai tarin k‘amshi komai na ki na dabanne baby..” Wani lumshe mai ido take tana bud’ewa irin na matan da suka rik’a akan rik’e saurayi. “K’amshi ba ki bani amsa ba, yaushe zan gabatar da kaina ga iyayenki.? “Murmushi ta yi ta fara tunani aranta, sam! ba ta san ta nuna shi a gida yanzu, domin ta kula da zafi zafi yake so,ita kuma ba hakan ta ke so ba, ta fiso su d’an jima, ta tatsi manyan kud’i a gare shi, sannan ta gabatar da shi. Wani juyi tai da ido da wani salon kallo ta ce “kar ka damu Ramadan, ai komai mai sauki ne, kai dai mai kake ci na baka na zuba ne, kawai mu bi komai a sannu, ai insha Allahu ni taka ce.” ” Allah ko? ya fada tare kuma kafeta da ido.” Eh mana. Saida taga shida ta gabato, sannan ta sallamesshi, saboda ta san lokacin babanta zai dawo, nan ya bata bugun abuja bandir d’aya,da farko ta yi fulako, amma da ya matsa sai ta karb’a ta flta tanajuya jiki. Nan ya bita da kallo ya saki ajiyar zuciya, ta dad’e da flta, amma duk ta barshi da k’amshinta cike da kasala ya tafl gida. Ita kuwa mutuniyar tana shiga gida ta shige d‘akinta ta fad’a gado, ita kanta tana san Ramadan so mai nutsuwa, kuma ta kula surarta na matuk’ar rud‘ashi, tsai ta yi na sakankuna, kamar mai tunani, sai kuma ta saki murmushi ta ajje kud’in, ta mike tsaye ta fada’ toilet dan d’auro alwalar magriba Tun da ya koma gida ladifa ta kasa gane kansa, sai wani abu ya ke mata a zafafe kuma tsawa-tsawa, duk laila ta gama rikitashi,ji yake in bai mallaketa ba,zai iya susucewa, ga 
wani irin feelings d’inta ke shigarsa kota’ina. Wanka yayo ya fito falo,in banda tunanin laila babu abinda ya ke, kallon shashin da lad’ifa ta ke ya yi,nan ya mik’e ya isa gareta,wani irin dakuma yakai mata, nan ya shiga yamutsata sai wani irin furzar da numfashi ya ke. Ita kanta ta yi mamakin meke damunsa ne? batun yau yake mata haka ba, yau kwana uku kenan ya nai mata hakan, ciccib’arta ya yi ya shige bedroom da ita , nan ya shiga sarrafata, 
wanda bashi ya k’yaleta ba, har sai da ya ji ya samu nutsuwa, sannan ya k’yaleta. lta ko sai gurza kuka take, wani irin nunfashi ya ke fltarwa ya kalleta. Meye kike mini kuka?.” Wani irin takaici ne ya dad’a, rufeta ‘au! ya manta kiran sunan wata da ya ringa yi kenan,’ Ta fad’i aranta. 
“Na tabbata ba sunana kake ta kiraba, meye ya kaika kiran sunan wata bayan kana tare dani?.” 
Shafa sumarsa ya yi, sai fa yanzu ya tuna abinda ya faru, domin a yayinda ya jishi aduniyar ma’aurata, sai ya ji tamkar da Laila ya ke tare, bai san cewa ya furta sunanta ba. Da sauri ya yi dabara,” haba lad’ifa, ko kin manta kece matata, mai zai saka na kirawo kuma wata, ke wanne suna kikaji na kirawo?!‘ Harararsa ta yi, wallahi naji suna, kuma ba sunana ba ne, farkon harafin sunan daga L ya fara.” 
Dariya ya saka, ko kin manta sunanki daga L ya fara, to cewa nake wayyo ladifa ta, lad’ifa ta, ai kin rikitani da yawa. Ke kawai kin daiji ba daidai ba ne.” Nan ya bagarar da ita, da ya san tabbas cewar sunan Laila ya kira, amma saboda duniyanci yasa ya wayince sai da yaga ta sakko , sannan ya shige toilet Tunda ta koma d’akinta, saita kasa nutsuwa, saboda zuciyarta da ke dad’a gasgata mata cewar lallai sunan wata taji mijinta ya kirawo, nan ta kauda abin. Amma ta k’i aminta, nan ta kuma saka kuka zuciyarta sai suya ta ke, lamarin mijinta ya farai mata yawa, abubuwa kala-kala, ko daren farkonsu dad’i bai sa ya wani kira sunanta ba, ballan tana yanzu. Haka taita ruzgar kukanta harta fawwalawa Allah. Don in gaske ne wataran za taji.
“Murabus, ba zaka bawa maryam k’anwar taka kud’in cikon ankon nata ba.” “Wallahi Mama ba ni da kudi.” Maryam da ke hura wuta tace “haba yaya! kaifa kaimin alk’awari za ka bani.” “To da nai miki alk’awari cewa akai dole sai na cika miki? yanzu bana samun ciniki da adaidaita sahun, saide naita bin titi.” “Adai dinga godewa Allah murabus, wani irin itaka yake nema bai samu bA sannan maryam kuma ba bak‘uwar zafl bace,jeka, duk randa ka samu ka cika mata..” Yawwa mama nagode.” Nan ya flta yana cilla hular sanyi a hannunsa. Bai zame ko’ina ba, sai kiran da Laila ta yi mai kan zai kaita sabongari, yana dira a k’ofar gidansu, ya yi mata waya, ‘yan matana gani fa ak’ofar gidan.” To ka jirani.” Ta fad’a daga can. 
Da yake ashirye take , yau hijab ne ta sa ka, nan taiwa hajiya sallama ta fice. Murmushi ta sa ki, murabus yayi sak’ale yana kallonta, itace kad’ai budurwar da ke sarrafa shi kota’ina, yana bala’in sonta, bai san b’acin ranta ko kad’an, duk aikin da ya ke ciki, har idan ta ce yakaita wani wajen to zai hak’ura ya taf’l kaita. Murmushi tayi tace.”Mura na, mu tafl.” Ja yayi ya ce. “Allah yaja da ran gimbiya, saifa yau kud’in ankon na ki suka had’u.” Murushin yaudara tai. “Allah ko! amma fa nagode ka cika masoyina na hak’ik’a.” “Ki amince na turo manya na neman aurenki.” Dariyar rainin hankali ta saki ta ce “mai ka keci na baka na zuba ne mura na? Mu jira lokaci Wani dad’i ne ke kwasarsa idan tace mura na, hira suke irinta masoya, wanda shikad’ai ke jin dad’in hirar, ita k0 a zuciyrta haushi ya ke ma  bata, dan kawai ta ga yana da mamora ne, dan duk inda za ta bata da hauf’l, zai kaita kuma ko k’wandala, buk’atunta kuwa koji yayi sai ya yi yanda ya yi ya kawar mata, amma bacin haka a gara ma ta d’aukeshi, don saving din number na sama a gara ta saka sunansa. 
Shi ko sai wuce tituna ya ke, ko an tsaida shi, bai tsayawa, saboda indai ya d’aukota to baya d’aukan kowa, haka suka je ta gama siyayyarta ya maidoda ita, ya kuma dank’a mata dubu goma sha -biyar kud’in ankon da sai da yayi sati biyu yana had’asu. ‘ 
Wannnan kenan. 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE