NAYI GUDUN GARA CHAPTER 30

NAYI GUDUN GARA 


CHAPTER 30

Wani hamdala tai a zuayarta a yayinda taga sun faka a harabar filin gidan nasu,juyawa tayi ta kalleshi wanda shi hankalinsa naga kokarin kashe motar, fita tai ta shiga takawa a 
hankali ta shiga falon. Kamshi ne ya doketa sai tai murmushi tana son gidanta. 
Babu kowa afalon sai fanka da ke aiki. zama tai akan kujera alokacin ramadan ya shigo da jakun-kunanta ya ajje, sai ta mike za taja, yace “tsaya shiga kawai na shigo dasu, kina da karamin Clkin zaki d’au wannan babbar jakar. sai tai murmushi ta bude shashinta ta shiga ganin yayi dan kura ya sanya ta ajje mayafinta a gefe, ta shiga kokarin gyara wajen bayan 
ramadan ya gama kai mata jakar. 
Ladifa bata san da dawowarsu ba har saida ramadan ya hau saman ya gansu suna shakar bacci ita da fuad,juyawa yayi zai fita, sai karar kofa ta tada ladifa, da sauri ta bude ido 
“zauji” ta ambata sai ya tsaya ya juyo yace “ashe ba bacci kike ba?!’ Sai tai murmushi ta ce “wallahi shi nake yi, karar buga kofar da kai ce ta tashe ni sannu da zuwa.” 
Ya amsa tare da dawowa ya zauna gefen fuad yana shafa sumarsa ya ce “laila ta dawo fa 
inda abinci ki mika mata.” 
Duk da cewa sai da gabanta ya bada dan! Amma ta dake tai murmushi tace “kai! masha Allah amma naji dadi,” kokarin mikewa yayi itama ta mike ta bishi a baya, bayan ta sabo 
fuad a kafada dan ta ajjeshi a kasa saboda kar ya tashi bata kusa. 
Sauka kasan sukai bayan ta ajje fuad tayi shashin laila dake goge -goge. Murmuahi tai 
bayan ta tsaya a bakin kofar falon tace “Sannu da zuwa laila andawo lafiya?!‘ 
Da dan yake tace “laflya lau ya gida da fuad,” ta amsa da lafiya ta fita babu dadewa ta kawo mata abinci ta koma. 
A ranar Iaflyar Allah laila akaita gudanar da lamurra, wanda tsakaninta da ramadan dai sai ‘yar san barka. Haka komai ke gudana, suna zaman Iafiya dan laila taji fada ta daina yiwa ramadan rashin kunya, duk da cewa takan dan taba,arnma da taga ransa ya baci zata saduda. Bangarenta da ladlfa kuwa kadaran kadahan. domin lailar bata ma fiya fitowa falon ba, saboda karta ga wani abun da zai daga hankalinta, don har yanzu kishin nan na nan, sai dai ta yi alkawarin ta daina nuna shi, koda taga abinda taji kishi takan koma daki ne ta karaci jin haushinta, idan kuka ne ma tayi, idan ta fito kuma sai ta hau yaken karfi da yaji. 
Takan samu kulawa sosai awajen ramadan, saboda cikinta, hakan ya sanya kanta ke fasuwa tana jin kamar ita yafi so. Wanda da zarar taga yanda ramdan ke washewa little fuad baki, da yanda yake nuna taananin kaunarsa da kulawa sai kuma taji kishi, ta ringajin haushi, idan tana wajen sai ta hau dariyar yake tana nuna jin dad’inta kamar har ranta, idan kuwa bata kusa haka zata koma daki tana maganganu. 
Ita kanta tana damuwa da yawan kishinta, bata manta hudubar mamanta ba kan ta yawaita addua da rayuwa kishin, wanda duk da hakan abun wataran ya faskara. Amma tana kokarin ta hadiyeshi. Suna zaune a falo dukkansu har ramadan suna kallo, laila na yi musu sharhi kan wani film da suke kallo wanda ita ta ganshi complete, amma su basu gani ba sai yau, shine take gaya musu sai dariya suke sha. Sau da dama hakan na kasancewa a yanzu zasu zauna ana hira 
kamar babu wani kishi a tsakaninsu, amma ta ciki na ciki danma laila ce ke tayar da komai, 
amma tunda ta dawo sai ta canza sabida Ita tasan halin da ta shiga, kuma ta zauna tana tunani tabbas idan taci gaba da fito da shi koyaushe zata dinga samun matsala. 
Fuad ne ya tashi daga bacci yana kuka dan ya razana, addua ladifa ta shiga tofa mai amma 
yana ya kuma tashi tangararau! sai kawai suka rabu dashi har ya wartsake, hirar film dinsu kenan data tsaya, yayinda lalla dake gefe duk wani haushi ya kamata saboda indai fuad idonsa biyu to fa hankalin ramadan kansa ke komawa, sam! Sai take ga baya bata kulawa kamar irin na ladifa lokacin tana da ciki, kacokam! Hankalinsa na kan fuad ita ke da ciki amma duk hankalinta ya kasu biyu, wanda alokacin da ladifa ke da ciki ko tari tai sai yayi magana, amma ita duka gashi ya raba kulawar tata biyu ya bawa fuad rabi, sai tai yake tace “ladifa ki karbi yaron nan mana ki bashi ya sha daga bacci fa ya tashi,” tayi hakan ne 
duk dan hankalin ramadan ya bar wajen. 
Hakan kuwa akai ta karbeshi ta shiga bashi sai yayi shiru, wani numfashi taja ta shafa cikinta tana ayyanawa nan da wasu watanni itama ta haifi nata,sai tai murmushi tace “habiby nifa yau bandashe nake san ci wallahi. ta fada tana mai nuna alamar shagwaba, wai ita mai ciki. Kallonta yayi yana ayyano yanda ladifa ke tata shagwabar da bambamci sosai, yet” so yaga shagwabar wajen lad’ifa bai san daliliba watakil ko ita tafi iyawa ne. Cikin dada hilata tai magana, dan anan laila tafi kwarewa tace “shi muke bukata ni da 
babynka. Ta fada tana mai satar kallon ladifa taga yanda za tai, ita ko kanta na sunkuyo a daidai fuskar fuad tana yi mai wasa yana dariya.  
Laila kin manta yanzu dare ne, ina zan samu ne? karfe tara fa.” 
Sai ta taso ta dawo lnda yake ta kwantar da kanta gefen kafadarsa, ta shiga shafar sumar 
kansa tace “ni dai sai an sayo ba zan iya bacci ba in banci ba.“ 
Murmushi yayi yace yanzu sai dai na fita ko?.” 
Sai alokacin ladifa ta sanya musu baki tace “ahh Abi fuad yakamata a sayowa mai ciki 
abinda take so.Kasan masu ciki in suka ce suna son abu fa to kawai ai musu.” “Au! kema haka kika ce ko ladifa.” Sai tai dan fari tace “ai gaskiya ne.” Laila ta dan yi yake tace “hmm nidai asayo min karna sanya kuka.” 
A zuciyarta tana jin haushin yanda akai ladifar taga bata damu ba k0 kuma taji haushi, ganin hakan yasa ta kauda kai gefe. 
Ta shi yayi ya mike ladifa tace “a tawo mini da Iceream; yace “kuce taron dangi za kuyI min,” sai suka sanya dariya shi kuma ya fice. 
BAYAN WATA DAYA 
Laila na zaune a d’akinta tana shafa mai, sai zumbura baki gaba take kamar zata fashe,ji take kamar ta bar dakin. Alokacin ramadan ya shigo da jallabiyya ajikinsa, har sukai kokarin kwanciya, bata daina zumb’urar bakin ba. Ita har ga Allah ba ta san adan kwanakin nan yana damunta. dan haka kawai bata son yace wani zai kokarin karbar hakkinsa, haka kawai takejin ba taso sam! bata so. Batasan meya sanya ba ko yanayin cikine yajawo. Tana kwanciya shi kuma ya shiga kokarin nuna damuwarsa akan abinda yake san samu. Sai ita kuma ta noke, al’amarin da ya dugunzuma ruhinsa kenan, ya kalleta, wanda wajen sati daya in har dai ta karbi girki sai tayi wannan hali, sam! taki bashi hakkinsa, dakyar ya shawo kanta ta bashi, bayan ya sha mita. 
Wanda shi lamarin yayi matuk’ar kaishi bango, abinda ya fara ba shi matsala kenan da Iaila 
tun bayan dawowarta gidan. 
lta kuwa ko ajikinta, ga yawan kasala data koya da kazanta, ko girki ba tai sai dai ta dambashe a falonta tana kallo da daurin kirji, musamman idan ta saka film tana kallo tana kwasar dariya abinta. 
Yauma tana zaune da tsintsiya a hannu da tayi shara daya sai ta tsaya, karshe ta zauna 
tana yi a zaune, wanda haka kawai takejin bata son yin. Shiga falon yayi ya tsaya ya kalleta ya ce “laila,” Sai ta daga ido ta kalleshi “yadai habibi?.” 
Ta fada tare da kokarin tashi. “Wai meke faruwa dake ne? Laila kazantar me kika koya hakane wai? duk kin wani burkice, ji falon nan tun jiya baki share ba, ko kwalliya yanzu ba kyayi, haba ina duk kika kai tsaftarki ne? 
Tabe baki tai tace “wallahi gani nan dai kasan ciki babu abinda bai sawa, bana sha’awar yine kawai komai wahala yake min. 
Girgiza kai yayi yace “akanki aka fara ciki kenan?, kwata-kwata cikin ba watansa biyar ba? idan ma ace nauyine ke hanawa, ke ina yayi girman harda zaki yi haka? A irin haka nan dai kinsan ladifa take komai kuma bata canja ba alokacin da take dashi,da cikin take komai 
bata fasa ba. 
Bata rai tai “ai nida ita ba d’aya bane yanzu dai zanyi ayi hakuri‘. Sai ta mike ta shiga 
share falon. 
“Allah ya kyauta kawai,” yace ya fice. Yana Fita ta ajje tsintsiyar ta malale akan tile din,ta 
dau waya tana kallo aciki. 
Haka al’amura keta gudana ta bangaren laila, domin kazanta take ta fitar hankali. idan ramadan ya yi magana tace ciki neya sanya, ga tsirfa wanda tana yine kawai dan ladifa ta gani tasan cewa yes! itama ana sonta 
Ita kuwa ladifa data fahimci wani abun da gayya laila keyi sai take bata kwarin gwiwa ma, 
ganin hakan ke sanyawa ita kuma lailar taji tama sare. 
Tana son magana amma bata son ace tana tayar da fitina, ba ta son ace daga dawowarta ta fara k’orafi amma abin sam! Yana bata mamaki ta yaya ace ramadan zai daina cin abincinta. 
Agogo ta kalla ta ga daya na rana, tasan ramadan yau na gida da sauri taje tai wanka, wanda kawai ganda ta sanya taki tashi tayi da wuri,har saida ta ji ramadan na cewa ladifa tai mai girki, alhalin ayau itace da girki, cikin saurisauri ta watso wanka ta sanya turare kadai, k0 mai bata shafa ba ta fita, dan yanzu sam bata kwalliya acewarta saita haihu. Ta fito kenan ita kuma ladifa na kokarin dumfarar sama d’auke da kayan abincin data dauko na ramadan, wani tunani ne yazo ma laila, ai sai tayi sauri ta dan karasa daidai lokacin ladifa za taka kafarta, da sauri ta bangajeta ta hau saman,kayan abincin suka tarwatse sai tajuyo irin bata san komai ba, tace “Iahhh subhnallah maman fuad! wallahi sauri nake ban kula akwai abinci a hannunki ba,” ta fada tare da yin sauri ta dawo ta tsugunna tana 
kwashewa, murnushi ladifa tai tace ”babu komai fa dan ita ba ta kawo komai ba. 
Kwashe komai sukai aka kai kitchen, kafin ladifa ta hau saman laila ta hau, ta shiga falon ramadan ta zauna kusa dashi, ya kalleta ganin yanda take wani furi-furi da ido, yace “ya na 
ganki haka? kodai wani abu ne?.” 
Sai tace “babu komai,” sai ya juyar da kai. Alokacin ladifa ta shiga falon ya kalleta “kin 
gama?.” Sai tai shiru tace “wallahi na gama kawai tsautsayi ya sanya abincin ya bare.” 
Har zai fara babatun fada sai ya tuno cewa fa ba girkinta bane kawai dai ya sata tai ne, sai 
ya juya kawai yace “babu komai.” Sai tace “kona dora maka wani ne zauji?. Kallonta yayi ya saki murmushi yace “karki damu dear kije wajen fuad karya tashi.” 
Caraf! laila tayi tace “aini sai ni dafa maka, sabida dama ai girkina ne koka manta ne. 
Bai ma kamata ka sanyata ba,bayan gani me girki ta fad’a tana mai murmushi. 
Sai ya kalleta “so what? Ita na yi niyyar sanyawa. keda kike da girkin aikinsan abinda ya kamata ko?.” 
Sai ta kame baki tana kunkuni, ladifa kuma ta fita. Tana fita laila ta sanya kuka “yanzu ya 
dace ace ranar girkina ka sanyata taimaka girki bayan kullum inayi ba kaci haba.” 
Tsayawa yayi da abinda yake ya kalleta yace “kin kyauta akan maganar ki kuwa? yanzu saboda Allah haka kike yida, amma yanzu saboda Allah kullum sai jallof din taliya koyaushe, gashi kin koyi kazanta, koyaushe cikin damuwa kike.” 
“Kaima ai kasan da ba haka nake ba, Ciki ne ya sanya, Ni haka kawai bana son ma a,kuma ai kasan babu wanda zai nunan tsafta da kwalliya har abincin, kawai lalura ce ta sanya.” 
Shi bai yarda cewarwai Cikine ya sanya bata son bashi hakkokinsa ba, kawai yafi yarda sabon iskanci ta tsuro, sai ya hade rai yace “ki gyara, dan gaskiya bana son kazantar waje, nafi so naga komai neat. ldan har kinsan ba taliya za ki dafa min ba. to kije ki girka idan kuwa ita kikayi bana ci 
Ya fada tare da barin kallonta. Girgiza kai tayi ta mik’e ta bar falon tana maganar zuci ‘Ace mutum yana cikin irin halin nan komai sai yayi, gaskiya ba za ta sabuba, dame za taji 
ne da yawan rashinjin dad’in da nakeji ajikinta koda masifarsa.’ Babu yanda za tai haka ta yi mai abinda ya keso. wanda tana gamawa ta kwanta sai bacci. 
Haka lamari keta gudana, wanda tsakanin ramadan da laila sai ido, dan kullum cikin neman hakkinsa sai sunyi fada, da abin yaci tura sai ya tafi wurin wani abokinsa doctor yayi mai bayanai akan matsalar, doctor ya gayamai tabbas! akan samu wasu matan haka, 
wanda har sai wani dan lokaci su dawo normal, wasu kuma ba sa shiga wannan halin sukan so abinne ma sama da lokacin da suke da lafiya, so ba wata matsala bace. Wannan bayanin ne ya sanya ya yarda, sai kawai ya daga mata kafa ya daina nemanta ya 
komarda al’amuransa wajen ladlfa kacokam! hankali kwance. 
Ganin yanda ya daina nemanta sai kuma kishi ya darsu ga laila, ganin ramadan ya daina nemanta da komai ya sanya ta kuma damu kanta, duk da cewar dama tafl son hakan, amma akasan ranta ta kanji kishi ta keji,tasan tabbas har kwananta ya hadawa ladlfa. Sai tai kwafa. 
Da safe ko karyawa ba tai ba, taje dakin ramadan wanda lokacin ladifa bata dade da fitaba, zama tai tace “yanzu ya dace ace dan ina da ciki sai ka maida shi kacokam gun wata, 
kwana na ko baza ai komai ba ai ya dace ace kana kwana dai, kasan fa lalaura ce. 
D’an tsaki ya sanya “wai kanki aka fara ciki ne ehe? duk kinbi kin ishi jama’a abu kad’an kice dan kina da lalura ne, to na d’aga miki k’afa kuma kinzo kina wani damuna, ko so kike na takura miki wani ciwon ya kamaki. ldan baki yarda ba ki saida mini da kwanan naki ba shi kenan ba.” “ 
Dam! Gabanta yayi kuwwa ta kalleshi da hanzari cikin mamaki tace “na saida maka da 
kwana na dan kawai na nuna ba naso? cabdi” 
“Oh my god! kinga laila ban kaurace miki ba, har saida na tabbatar cewa cikinjikinki na hanaki komai,to dalilin da yasa kenan na kawo wannan magana, ni ba damuwata bane in har za ki yarda. Zan iya duk kwanaki na ban nemeki ba, to amma ina tsarin wataran kar na kasa hakuri nace miki ta dole, kizo kina cewa zan kashe ki. Ya kamata faki gane komai da muhallin da ake kaddamar da shi. 
Shiru tai na sakanni tare da shiga tunani. Allah ya sawwake ta saida kwananta, wannan ai tsabar shirme ne, sai kuma wani tunanin ya fado mata, kodai ta yarda ne ta tsira da kudin tunda ba ta son wani abu yanzu, amma wannan ai wulakanci ne ko yaya kishiyarta za ta fahimci wani abu, kash‘. Kai ba zata iya hakan ba, domin zata iya bude kofar da zata zama silar kawo wata matsalar. 
Sai ta daga kanta ta kalleshi ta ce “ban yarda ba, babu wani sai da kwana da zan yi, sai kace a bariki. Kawai na yarda kana zuwa inda hali na baka in ba hali sai hakuri sabida 
kaima fa kasan kowanne kalar ciki da yanda yake zuwa atoh. Girgiza kai yayi ya ce kima rike abinki, ya fada yana girmama maganar lailar. 
Fita tai tana magana tana cewa “wallahi ni nan laila ba zan tab’a bari na zama bora ba cab! dan rainin hankali wai ta saida kwananta dan ya kaiwa waccen sai taji wani haushi ya dada kamata. 
Wata ranar laraba laila na zaune a falo, tana cin wainar masa da miyartaushe wacce Iadifa 
ta yi ta aika mata sabida tsabar son da laila ke mata ya sanya ba tai filako ba ta amshe. 
Ladifar kuma alokacin na kitchen tana wanke -wanke, fuad kuma shima na falon kan kujera 
an kwantar da shi yana kalle -kalle. 
Sallama ramadan yayi laila ta amsa, ya shiga, tsayawa yayi ya kalli falon ba yanda ya saba ganinsa kojinsa ba, babu wani kamshi, tabbas! yasan girkin lailane yau, shiisa falon bai samu gyara ba. Zama ya yi kan kujerar ya ce “yanzu laila sabida Allah falon nan an share 
shi.” Sai ta yatsine fuska “ni ban share ba, saboda banji dadi ba wallahi”
Kiran ladifa yayi da k’arfi, ta fito da dan sauri, murmushi tai sakamakon ganinsa, sai ta sakar mai sumba a kumatu tace “wallcome oga na.” murmushin jin dadin sunan yayi ya 
rike hannunta, yace “maman fuad ya gidan?!‘ Ta amsa da lafiya lau, fuad yace ” ya dace ace falon nan an barshi haka? idan ita lalura ta sanya ta kasa ke ba zaki yi ba.” 
Da mamaki akan fuskar Iadifa ta ce “wallahi ayyuka ne sukai mini yawa, kasan inba girkina bane, ban fiya sakkowa kasa ba, sai wajen yamma, kuma dalilin da ya sanya kenan ban gyara ba.” 
“Wannan ba hujja bace,” ya juyarda kansa gefen laila yace “bana son kazanta fa, idan 
kinsan ba zaki gyara ba, toki bari a gyara.” 
Cika tai tayi fam! kamar zata fashe tace “kawai ka amince a d’auko mai aiki, danni wallahi wahala nake sha ko daki na ma ba ni wahalar shararsa nakeji, ga wankewanke dan Allah ka bari a d’auko ko wasu abubuwan za a rage mana, koya kika gani maman Fuad?.“ 
Ladifa tace “kwarai kuwa.” 
“Laila abar batun mai aikin nan, lokacin da ladifa ke da ciki ba ita ke komai ba wai meyasa 
ne ke bakya fahimta ne. ” Turo baki tai gaba, sai da tai jim! Tace “afuwan habiby zan gyara dan Allah ka taimaka.” 
Gyara zama ladifa tai tace “please Abi fuad ka amince, kallonta yayi ganin yanda take wani lumshe mai ido. Sai yaja numfashi yace “to babu komai maman fuad.” 
Sai ya juya ya cewa “laila babu komai a dauko.” 
Sai tai murmushi duk da cewa taji babu dadin ganin sai da ladlfa tai magana sannan ya amince.Tsuke baki tai ta kurawa center carpet ido. Domin ta riga ta sanya aranta cewa ta daina tada jijiyar wuya koda taji kishin. Zata hakure da sannu dai akuya zata shiga ramun kura taci ta da yaki. Tabbas tana da yakinin wataran ita za ta zam mowa. 
Sai tace “to ba matsala.” Washegari babu bata lokaci Iaila ta bugawa wata kanwar mamanta waya dake yawan yin masu aiki,take sanar mata itama tana so asamo mata ‘yar aiki, kanwar maman tace mata insha Allahu za a samo Sati daya a tsakani suna zaune a farfajiyar bayan gidan suna hira, ko babu komai yanzu sukan zauna waje daya suyi hira, duk da cewa babu ta yanda za ai wai kishiya ku zauna waje d’aya ba tare da ta ciki na ciki ba, wanda ladifa take fatan wataran su zamo daya kowacce ta kauda dukkan wanijin haushin ‘yar uwarta aranta koda ace ba duka ya ragu ba,domin babu abinda yakai zaman laflya dadi. 
K’irr! wayar Iaila ta fara ruri, da sauri ta daga tace “mama an samo? tace mata “E tace to 
“alhamdlh sai sun zo goben.” Tana gama wayar take sanar da ladlfar ita kuma tace Allah ya kaimu. 
Washegari wajen sha-biyu sai ga mata mai suna Maria taz0 da yara biyu daya za tai shekara 15 daya kuma 13, ladifa na tsaye goye da fuad yana bacci a falon tana kokarin getta falon, sai taji sallama ta amsa taje ta bud’e kofar da yake mai glass ce ta ga kuma sun kasa budewa. 
Budewa tai suka shiga, bayan sun zauna ta kawo musu ruwa. Suna cikin magana sai ga 
Iaila ta fito tace yanzu kuwa ake gaya min, ashe! kuna tafe.” ’ 
Bayan sun gaisa mari tace “to gadai yaran sai ku zab’a.” Iaila tai caraf tace “wannan me d’an girman muke so daga gani za tafi iya aiki. Mari tai dariya “ba daga nan take ba wallahi karkiyi mamaki kiga wannan karamar tafi 
iyawa. Ladlfa tace “hakane ni kuma sai nake ga ad’au karamar.” Iailatace ahh! babbar tafi kinga na fiki bukatar ai min aikin kema kin sani.” Ganin yanda Iaila ke wani ciccira ido ya sanya ladifa tace “haka dai.” 
Sai ta dan tashi tai hanyar kitchen taya fito Iaila, itama ta tashi ta bi bayan ladifar tace “yanzu ke dan Allah Iaila sai mu dau wannan babbar kamar wanda bamu da ido, akalla fa zatai shekera 15 ki duba fa, ni fa gaskiya batai min ba. 
“Kinga Iad’ifa, waike kika ce asamo maki ne, ko ni? ki barni kawai na zaba tunda nice na 
fara kawo maganar.” Wani kallo ladifa tai mata na baki da wayo ta juya tace “Allah ya kyauta” Ladifa girgiza kai kawai tai tabi lailar da ido. 
Hakan ta shaidawa mari kan babbar zata dauka. Mari tace “ai duk daya ne nan ta fadi
kudin aikin yarinyar mari ta koma da dayar. 

Hmm koya zata kaya muke dai 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE