NAYI GUDUN GARA CHAPTER 31

NAYI GUDUN GARA

CHAPTER 31

Yarinyar mai suna hansatu Iaila ta kalla tace to zaki ringa yi mana sharar falon nan da goge shi kullum safe da yamma, sannan bangarena zaki na min wanke -wanke da sharar falona da sauran wasu abubuwa da gaba zance ki nayi. Bansaniba ko kishiyata zata sanya
ki to dai dukyana ciki.”
“To,” yarinyar ta fada tana rarraba idanuwa. Karamin Dakin da ke gefen kitchen din ladifa aka shigarda ita ta ajje kayanta ta zauna tai tagumi.
Ta dade a zaune tana ta kalle-kalle karshe ta tashi ta tura bandakin da taga kofa agefe tai
Alwala ta fito tayi sallah. Nan bacci ya dauketa awajen.
Dakin dame aikin take ladifa ta shiga ta taradda hansatun na bacci,sai ta tasheta ta tashi
da sauri tana rarraba ido, ladifa tace “kinci abinci kuwa? .” Ta yi mata alamar Aa, Sai ta koma ta zubo mata ta zauna za taci ita kuma ta fita.
Bata dade da cinye abincin ba ladifa ta dawo tace taje tai wanka, nan kuwa taje tayi wanda tana fitowa ta sanya kayanta ta kuma maida hijabin jikinta. Iaila ce ta shigo tace “ki fito ki fara aikin shashena,” ta juya hansatu ta bita abaya.Tana tunani aranta dan adan mintuna harta fahimci wadda ta bata abinci tafi kirki wato ladifa.
Nan fa ta shiga aiki baji ba gani, ba ita ta gama ba sai wajen bayan sallahr Ia’asar, ta koma public falo shima ta dada goge shi tas! duk inda ya kamata, lailar ta kunna turare abunner yana ci kadankadan.
Yarinyar dakin da aka bata ta koma ta zauna, duk yawan aikin ba wanijinsa tai ba sakamakon sabo da tai na wahala. Haka a ‘yan kwanakin nan shashen lailla ya dawo hayyacinsa,nan Iaila ta kuma bajewa sai dai kawai tai girki. Hakan ya sa ramadan ya rage
mata fadan rashin tsafta.
BAYAN SATI BIYU
Misalin karfen takwas da rabi na dare.Ramadan na zaune yana cin abinci.Laila na gefensa
tana kallo. Ladifa kuma na sama tana gyaran kayan fuad.
Kallonta yayi yace “dauko min cokali Iaila.” Sai ta kwala kiran hansatu ba taji ba,sai data kara kiranta,hansatu dake kitchen ta naiwa ladifa wanke-wanke ta fito da dan sauri ta tsugunna. Laila ta ce “biyo ta bayan kujera ki shiga ta shashena ki miko min cokali a
kitchen.” Nanta tashi da sauri, ta yi hanyar shashin Iaila. Bata dade ba ta dawo ta ajje, adaidai lokacin ladifa ke saukowa rike da fuad a kafadarta, nan tabi hansatu da ido, duk da yarinyar haryanzu da hijab take sanye, amma takan gano sassan jikinta da alama gabbanta mai girma ne. Alal hakika tunda taga yarinyar taji ba tai mata ba. Ama yanayinta rashin kulawa ya sanya bata dada budewa ba.ina ga in ta samu cima me
kyau.Dole fa sai ta sanya ido a kanta. Koba komai amanace a wurinsu.
Karasa saukowa tai ta karaso wurin da suke sanye cikin wata doguwar riga mara nauyi mai fidda shape m kasa, ta sanya hula akanta sai kamshi take ita da fuad. Ta zauna gefen da ramadan yake tai mai sannu da hutawa, ya juya ya kalleta yace “baby kin barni ina ta
missing dinki kin haye sama k0.”
Murmushitai tace “ashe! muna daya ina can hankalin naga mijina, sai zumudi nake na
sanya idona acikin naka my happiness.” “Allah ko babyna, kice kamar dai yanda abi fuad keji ne, gaskiya jazakillah.”
Lumshe ido tai ta bude su akansa. Hannunsa ya mika mata ya karbi fuad da ke ta bacci.
Laila dake cin apple ta saki tsaki aciki-ciki ‘iyayi me za a nuna mana, kallaferi kawai uwar
son iyayi da nuna bariki ta fad’a azuciyarta.
Haka suka zauna suna hira kad’an -kad’an har ya gama, da yake shi ba ma’abocin cin abinci a dining bane shiisa, yana gama ci Iaila ta kuma kiran hansatu lokacin hansatun na kwance dan da wuri take bacci, ta mike ta fita ta manta bata sanya hijab ba, tana zuwa Iaila ta ce ta kwashe kwanukan abincin, nan ta sunkuya asaitin ramadan ta shiga kwashewa, idan ramadan lokacin ya dago zai kalli tv ya sauka akan kirjin hansatu data sunkuya, sai yayi sauri ya dauke kai. Tashi tai da kayan musukur musukur tana tafiya ga rajajjiyar atamparta ta dada sanyawa jikinta na rawa. Ta gefen ido ramadan ya bita da kallo. Wani irin mamaki ne ya kamashi, danshi bai taba ma kallon yarinyar haka ba, dan kullm da hijab yake ganinta, kuma bai taba tsayawa ya kalleta ba, shi bai san ma ta kai girman haka ba. Jinjina kai yayi ‘ga yarinyar yar kauye amma akwai kayan manyan manta.Lalle wannan inta kara girma da shekaru za ai dakakkiyar mace.
Duk irin kallon da yabi ta da shi a kan idon ladifa. Nanfa jikinta yayi sanyi dama abinda take wa tsoro kenan ta san waye mijinta. Shiisa tunda aka kawota takejin ba dadi. Sai inta tuno cewar mijinta ba wai kowacce mace ma ce ke birgeshi ba, sai ta ji sanyi. Amma jikinta
na dada sanyi ne idan taga surar yarinyar. Duk da cewa mijinta ba mai bin mata bane,amma hanyar lafiya abita a shekara.
Laila ko ido na kan tv tana gatsar apple dinta tana kallo sai dariyar show din da ake a film
din take, sam! bata san wainar da ake toyawa ba.
Asanyaye ladifa ta tashi ta bi bayan hansatu da har ta kuma kwantawa. Agefen gadon ta
zauna tace “tashi muyi magana,”
Sai ta tashi, ladifa tace “daga yau karna sake ganin kin fito haka ba hijab in har me gidan na nan, kai fitowa ma bance kiyiba,idan ma fitowar ta zama dole to ki ringa sanya hijab kina
dai gani ke ba karama bace.” “To anty, yau ma mantawa nai.” “Wai ni dama ana kawo kamarki ne haryanzu?!’
Hansatu tai dariya gaskiya ba sosai ba, anty yawanci gidan da kesan manya ake kawo musu. Nima anty laila ce tace a hado da mai girma sai aka taho dani.” “Toki nutsu bana son kina yawo haka ba hijab, indai mai gidan yana nan tace kinji da wai.”
Tashi ladifar tai ta koma falo ba ramadan sai laila, nan tai mata saida safe ta wace sama
itama lalla ganin hakan ta Mik’e.
Washegari’
Karfe bakwai hansatu ta fara aikace aikacenta da hijabinta, tun jiya da ladifa ta gaya mata take muku -muku da shi,ganin yana hana ta aiki sai ta cire ta ajje gefe, dan azatonta k0 me gidan bai nan, ta shiga goge tiles din.ta Juya baya tana ta aikinta, ramadan ya sauko ladifa na binsa abaya da jakarsa a hannunta. Karasowa kasan yayi idonsa ya sauka akan ‘yar aikin,
baisan yana kallonta ba musamman yanda take dan gaba da take gugartiles hakan ke taimakawa jikinta ke motsawa. Karar takalmin ladifa ne ya ankarar da hansatu, ta juya da sauri jikinta na rawa, saita tsugunna ta shiga gaida su suka amsa. Acan kan dining ramadan ya zauna. Hakan ya sanya da sauri hansatu tazo ta wuce ta gabansa ta dau hijab dake kusa da kujera ta wuce. Gaban ladifa ne ya fadi ganin yanda ramadan ya bita da ido yau ma ta dada karewa yarinyar kallo yanayin surar hansatun mai fisga ce, musamman da yanzu yarinyar ta samu jin dadi abinci take narka na fitar kai, taci me kyau ta sha me kyau. Shi,isa tashi daya ta dad’a cika. Ga shi ta danyi haske saboda canjin waje kuma ba fita take ba. Ashe yarinyar wahala ce ta sanya fatarta ta koma baka, wanda gashi yanzu dadi ya sanya ta washe, sosai yarinyar keda manyar sura musamma daga kasanta zuwa sama, Yanayin
yarinyar kamar ba ‘yar kauye ba.
Bayan fitar ramadan Kitchen Ladifa ta shiga tana ayyana abubuwa da yawa aranta, sai taji hankalinta ya kasa kwanciya da yarinyar ba dan wai tai mata komai ba, ah sai dan girman da tai, haka kawai inta gifta sai taga kamar ramadan yana kallonta, duk da cewa ta kamashi sau biyu, Tsaki tai “ba dan waccen masifaffiyar ba wallahi daba yanda yarinyar zatai ta zauna.Kuma bata son tayar da husuma ne da sai tace dole yarinyar ta tafi a kawo
karama. Cike dajin haushi tai samanta.
10:am
Hansatu ce rike da mopper suka hau sama ita da laila, ta bude shashin ramadan suka shiga tace “hansatu kullum har nan zaki na yi,shashin me gidan ne bansan sa‘ido da tabe taben abinda bai shafeki ba, abinda ya kaiki kawai zakiyi.”
To tace mata to ta shiga aiki. lta kuma ta fice hansatu ta kusa gamawa kenan. Lad’ifa ta fito
daga nata wajen, sai taga wajensa abude har tana tunanin k0 ya dawone, sai ta doshi wurin kai tsaya, taga hansatu na gogegoge, wani irin abu taji ya tsaya mata a makoshi,
dakin maigidan nata, turakarsa, lalle!
Gyara tsaiwa tai tace “hansatu me ya kaiki zuwa nan kuma kiyi aiki?” sai ta tsugunna “anty
ce tace min nayi har nan.”
Ladifa tace “dauke ki Fita ba aikinki bane.”
Daukewa hansatu tai ta fice.
Cikin fushi ladifa ta sauka kasan tai shashen laila, tana zaune tana shan fura da nono tana duba wasu Atamfoti. ladifa ta shiga tace “laila magana nazo muyi, yanzu ya dace ace mai aiki ce zata sharewa mai gidanmu dakinsa, wannan ai bayi bane ba. ldan ba zaki iya ba ki barshi nina ringa yi kawai.” ’
“Sannu yar iyayi gadon iyayi, to ita nai niyya, kuma bance mace taimin aikina ba, ballan tana wataran aimin gori.” “Au haka kikace?.“
“E! haka na fada, yanda kikeji ke matar gidance haka nima.Kuma ba fina kishin hakan kikai ba.“
Ladifa ta juya tace “aishi kenan.”
Sallamar salma ce ta katse mata tunanin da take. da murna ta tare ta, ta karbi babyn salmar ‘yar shekara d’aya, suka zauna Iadifa tace “gaskiya salma kinyi nisan kiwo, daga tafiya ibadan kukai mukus ke da Abdallahnki.”
Dariya tai tace “Wallahi wasu abubuwa ne suka rike mu.”
Nan ladlfa ta tashi ta kawo mata kayan motsa baki. Nan fa hira ta barke atsakaninsu, tana
tambayarta fuad tace yana can yana bacci.
Kwallah kiran hansatu tai ta amsa tare da zuwa tace “gani anty” tace mata taje ta karasa mata gyaran kitchen, kamar laila naji ta fito da sauri tace “tai miki me? aikina kuma a
kaishi ina? idan ta gama nawa ta yi naki.” Hansatu bata motsa ba, ladifa tace “tashi kije ki mata.”
Nan ta mike ta tafi, laila ta kalli salma suka gaisa tabar wajen, salma tabi hansatu da kallo
tace “wannan kar dai kice ‘yar aikice,” Tace “E”
Salma tace “amma wallahi naga rashin wayon ku, ina ake irin haka yanzu?, yaushe ake d’aukan ‘yar aiki budurwa. yau ko karama ce wasu takatsantsan suke balle wannan da kayan mata yaji fal! ajikinta,ku baku da ido ne?.”
Ladifa ta tabe baki “ni kaina kullum na kalli yarinyar nan sai na ji tsoro, mu da muke da matashin miji, amma laila da yake ita ce ta samo, duk ta kakkane ta futtutuke, idan nai
magana Abi fuad yace “na bar maganar.”
“Hmm! kawai salma tace nikam me zai kaini daukan ‘yar aiki gwanda aiki ya karni, wallahi kishiyar nan taki sai aslwo.Yakamata ki magantu, dan ko gidan tsofaffi ba zasu dau wannan yarinyar ba.”
Haka sukai ta hira har lokacin tafiyarta yayi ta tafi.
Bayan shud’ewar wasu ‘yan kwanaki
Kaya kala biyu ladifa ta ware akayanta ta bawa hansatu tace tana sawa ta daina saka kodaddun nan. Da murna ta amsa. Abangarenta tana kyautatawa hansatun musaman yanda take son fuad take daukansa kullum! lndai ba aiki take ba yana hannunta ta nai mai wasa. Hakan ya sanya ladifa take
dan jan hansatun ajikinta take nusar da ita abubuwa da dama.
Weekend Ramadan na zaune lokacin a shasshin ladlfa yake, daga shi sai vest da gajeran wando ladlfa ma na zaune da wata yaloluwan riga mai mannewa ajiki tana jikinsa suna ciyar da
juna breakfast fuad kuma na bacci.
Kasa can kuma hansatu ce keta aiki laila na daka mata tsawa kan tai sauri kafin ramadan ya sauka.
Tsaki tai ta mike daga falon tai nata ta shiga kitchen ta duba fridge taga nono da fura ya kare, dan tunda ta samu ciki take son shansa. Saita Fito ta cewa hansatu taje sama wajen ladifa ta gaya mata zata dibi nono nata ya kare . Nan ta Ajje mopper din, tai saman shiga tai falon ladifa, sai ta dan koma tai sallama ba suji ba. Sai da tai da karfi. Dan Ladifa tace ta daina kwankasa waje ba tare da tai sallama ba, dan kwanaki haka tai. Sai da ladifar ta gaya mata cewar wannan ba dabia mai kyau bace ko yaya in kaje waje kai sallama. Kar ka
soma shiga har sai an baka izini. Shi’isa ta ki shiga saboda kar ta karya dokar Ladifar. Ladifa ta mike ta isa bakin k’ofar tace “ya dai hansatu?.” Sunkwi da kai tai tace “anty ce tace wai ki sammata nono nata ya kare.”
Ladifar tace mata taje ta diba, hansatu ta juya, alokacin ramadan ya tako zai fito daga falo. Idonsa nakan yanda yarinyar ke tsallaka matattakalar bene jikinta na rawa. Da sauri ya kauda kai.
Ladifa ta ankare da kallon, wani haushi ya kamata taji kamarta make idanuwansa, ga
haushin hansatu sai kace bata bata kaya masu kyau ba, amma ta boye ta nacewa rajajju.
Kokarin sauka daga falon yake.Lad’ifa ta Tura shi falon ta rufo kofar, domin kawai kar ma
yace zai sauka kasan, ta san bata gama aiki ba.
Tsaki tai ita dai wannan ‘yar aikin ta fara zame mata jara ba. Duk da cewa tana jin dad’in yarinyar na da biyayya amma kuma yanda mijinta ke satar kallonta abin ke bata ranta. Dole ta duba lambar mari me kawo ‘yan aikin a wayar laila tai kiran matar kan a canjo musu wata.
Agefensa ta zauna ta dora kanta akan cinyarsa, yana wasa da gashin kanta, tace “ni ko zauji agaskiya ina so na acanja ‘yar aikin nan.to bana so nai magana matarka ta tada fitina shiisa .”
“Abar maganar nan baby, saboda bana san fitina. akan wannan za ku iya samun sab’ani,
And kuma ni banga me yarinyar nan tai ba.Ta iya aiki sosai.”
Hmm kawai ta fada. sannan ta kara da cewa “na bar maganar har abada Nawan Allah yayi miki albarka.“ Tace “Amin.”
Dayan wata day
Laila ce tsaye da kudi a hannu tana gayawa hansatu abin da zata sayo mata. Hansatu sanye take da doguwar rigar abaya baka wacce ladifa ta bata kwance, ta sanya mayafln akanta. Kwata -kwata laila ba ta gane canjin da yarinyar ta samu acikin zamanta na wata biyu ba a gidan, dan data gano tabbas yanda take da kishin nan za taji kishi mijin ko sau
daya ya kalli yarinyar, dan ta dada cika dama wahala ce ta sanya kyanta ya boye, dan sau da dama idan sukai baki ba sa daukan ‘yar aiki ce.
Jaddada mata take kan kar tai mata shirme.
Hansatu ta fita, ramadan na soko hancin motarsa ta gabas da layin ya ankare da hansatu, daidai da ita ya tsaya ya tambayeta Inda zata, ta gaya mai, nan ya dauko dari biyu ya bata yace ta sayo lemon tsami, ta juya ta tafi baija ba bai gaba ba, shi alal hakika yana mamaki yarinyar kamar ba daga kauye take ba, bata da kamarsar su, gata da irin jikin da yake so, da sauri ya kauda tunanin yayi horn mai gadi ya bude ya shiga ciki.
Haka dai al’amura sukai ta tafiya wanda har yarinyartai wata hudu a gidan lokacin ya kama watan haihuwar laila.
Kwance ya ke kawai yana tunani da kwakwalwarsa, domin surorin yarinyar ke karakaina adukkan wani motsinsa, ya rasa mai yasa musamman kwanakin nan k0 rufe ido yayi
surarta yake hanga, ya dade daga bayan ya kuma kwanta da tunani kala -kala aransa.
Koda kuwa washegari tayi, sai ga ramadan da riga da siket na ‘yan kanti, har hoda da turare, da kansa ya bawa hansatun yace tana sawa ta ajje tsofaffln kayanta, wanda hansatu dadi ya kamata, dan maigidan yana burgeta yana da kirki da sakin fuska, har so take ta ganshi idan ta san zai bata wani abun. Komawa dakinta tai da sauri wanda duk da sanya hiiab dinta, hijab din bai boyejikinta ba. Binta da ido yayi yana mamaki shi dai yasan ba son yarinyar yake ba, amma kyawun jikinta ke sanyawa yana balain jin sha’awarta, runtso ido yayi ya bude. Shi dai ko da wasa ba zaice zai auri yarinyar ba saboda ba ajinsa bace
amma kuma sha’awarta tan mai katutu.Yaya zaiyi ne?
Dan ma yana samun ganin giftawarta musamman alokacin girkin laila da zatai ta kiranta dauko kaza daukowa habiby kaza zoki dauke kaza, wanda ramadan ke samun kallonta sosai. Kuma ikon Allah bata tab’a ganewa ba. Sabanin ladifa da karyar hansatu ta je shashinta
idan ramadan na wajen.
Al’amura na ta gudana, sosai wataran ramadan ke saukowa kasa da daddare yace “hansatu ta d’auko mai wani abu akitchen, shidai kawai yayi ta kallon hansatu na bazar
bazar dajiki. Wanda duk tsabagen kishin laila bata san wainar da ake toyawa ba.
Ranar da hansatu ta sanya kayan daya sayo mata, rigar ta kamajikinta haka siket, suna zaune a harabar filin gidan, ladifa ta kirawota tace “hansatu rawar kanki ta fara yawa, waya
baki kayan nan?.“
Sai ta tsuru ta sosa keya “maigidan ne ya bani yace na daina saka lalatattun can wai baya son
kazanta.”
Da sauri laila tajuyo ta narkawa hansatu zagi, nan jikin hansatun ya fara rawa, lailar tace “wato kin samu wajen da har maigida zai baki kaya ko? to kije ki ciro mun su kona farfasa jikinki.”
Ladifa tace “daya baki ba sai ki sanar ba, kice ga shi wane ya ban kaya ba shine zaman
amana, to ki kiyaye gaba.” “Ki kyaleta kawaita jeta ciromun kayan nan,“ laila ta fada tana harararta.
Adaidai lokacin ramadan ya shigo da motarsa harabar wajen, kallo daya laila taiwa motar tajuya taci gaba da surfawa hansatu masifa. Wallahi duk randa ya kuma baki abu kika amsa saina illata ki kuma Kije ki cirosu yanzu -yanzu wawiya ‘yar kauye kawai.
Da sauri ta mike ramadan lokacin ya fito daga motar yabi hansatu da ido. Ya dauke ido
da sauri dan kar matan su ganshi.
Ladlfa ko tashi tai ta wuce bayan tai mai yake wanda keda ma’anoni da dama, dariya yayi
mai cike da murmushi ya bita da ido, yasan yayi lefl inhar ya ga ladifa tai haka.
Laila k0 sai hura hanci take, ta mike da tulun cikinta, alokacin ya karaso suka jera tace “agaskiya abban fuad bai dace ka sayowa ‘yar aiki kaya ba, ba tare da mun sani ba, wannan
ai raini sai ya shiga.”
“Au! Shiisa naga kowacce acikinku fuskarta ba annuri! Kinga ba na son surutu nayi ne dan Allah saboda ganin yanda take yawo kaya kamar tsirara, idan iyayenta basu da kudin sai mata kume kuke da ba zaku bata tsoffin naku ba. Dole tunda kuka daukota aiki kuyi
mata suttura koda ba sabo ba. Saboda kuma kwa fijin dad’in ku ga mai muku aiki fes!
“Ka tambayeta kaji, kala uku Iadifa ta bata, har da doguwar rigar abaya, ni kuma na bata daya . Kawai bata sawa ne, tana so ta kai gidansu, amma ya dace ka sayo mata wadannan
kayan ina lefin atampa ka sayo a dinka mata. Gaba yayi ta bishi abaya tana mita.
Lad’ifa na kitchen hansatu na tsugunne tanai mata fada “kar na kara ganin kin ma fito falo in har me gidan mu ya dawo, idan dole sai kin saka kayan nan to karki fito mana falo,
kinji na gaya miki in har kina son ci gaba da aiki agidannan ki kiyaye. Ta fada tana maijuyawa hansatu ta mike ta fice.
Misalin karfe goma sha daya na dare lokacin kowa ya kwanta,inka dauke ramadan dake tajuye-juye saboda tuno surarjikin hansatu musamman kirjinta da in tana tafiya yake motsawa. Ashe dama akauye akwai dirarrun mata yana mamakin abin nan sosal ( hmm ramadan kenan kauyawan ma ai mutane ne)
Mikewa yayi ya sanya silifas a kafafuwansa ya sauka kasan, ahankali ya taka har kofar dakin da hansatu take ya murda ya shiga. Da yake da mukullin dakin futila a kusa da kofa yake ya kunna, wani irin kwanciya tai duk ilahirin rigarta ta yaye har saman kirji sai
sharar bacci take ko ajikinta, buga tuber dake gefe yayi yarinyar ta tashi a firgice, ta kalleshi da sauri ta gyara jikinta, ta sauko ta tsugunna “sannu akwai abinda zanyi ne Ta
fada da muryarta masu bacci. “Aa yace mata, ya zauna agefen tuburya kalleta yace “kina son na sai miki waya?
Sai ta girgiza Aa, dan tana mamakin yanayin kulawarsa agareta, kudi ya zaro ya bata “gashi gobe duk ki sayi abinda yayi miki dadi.”
Washe baki tai tace “ngd Alhaji,” Jikinta na dan rawa ganin babban mutun a dakinta.
“Ki saki jlkinki dani ba abinda zan miki.” Sai ta gyara duk kudin nan ya dauke hankalinta, hannunta ya rike yace “kina son kiyi aure
abirni ki zama mace kamar matan birni?.” “Wallahi idan na samu da wuri zan yarda duk da an sanya aurena da surajo.”
“Wato zaki so ki auri dan birni?.” Tace E ta fada tana dan kallon kofa.Dan har ga Allah tsoro takeji.
Tace“Sosai na dade ina aikatau a birni, tun ina ‘yaryarinya ba zanfi shekara goma ba lokacin,
tona saba da burni sosai.”
Mirmushi yayi yana ayyana abubuwa aransa. Shedan ne yaci gaba da kada masa ganga, wanda yasa ya dada damke hanun hansatun, wanda da farko taki yarda ta dan tsorata ainun! dan bata saba ba, sai ta kankame hannun. “To k0ni zan iya aurenki ko?.” Sai ta kalleshi da sauri gabanta na faduwa, dan abin tana ga da wuya, kuma maimaitawa
yayi. Sai ta daga mai kai alamar E! Murmushi yayi yace “karki damu.”
Hakan ya sanya ta dan sakijiki. Yana rike da hannunta, wanda takejin tsoro na kamata, dan adan karatun da take tsinta tasan babu kyau hakan.
Shi kuma wata zuciyar ta ankarar da shi cewa shi faba halinsa bane, kuma abin kunya ne ya zauna ya wani lallabo gurin ‘yar aiki kuma wacce ba muharramarsa ba, wanda a addini sabawa Allah ne. kar ya je abinda bai yana saurayi ba, yanzu yayi shi da yake da iyali, sai
jikinsa yayi sanyi, ya zame hannunsa daga nata ya mike tsaye yace “to ki kwanta kiyi barci.”
Yana fita ta shiga murmushi dan ita idan yace zai aureta ai ta tasarma sa’a ba ruwanta da
wasu matansa. Kuma nan da nan zata manta da wani surajo. Kai lalle ita mai sa a ce.
Hmmm! To ana wata sabuwa agidan Ramadan koya zata kaya t Toku dai biyoni 

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE