NAYI GUDUN GARA CHAPTER 31
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 31
Da karfi yarinyar ke aikinta, yayinda da ta tuno maganarta da maigidan sai tai murmushi, duk sai ta dada kamewa saboda ta kauda duk wani zargi agun matansa har burinta ya cika. Shi’isa tama daina fitowa idan har ramadan yana nan, hakan ya sanya lad’ifa hankalinta ya dan kwanta. Wanda ita laila takanta take dan cikin na dan bata wahala, shi,isa duk ta ma kasa ankarewa da wasu abubuwan.
Wanda basu san cewa ramadan ya kanbi yarinyar da daddare ba yayi hire da ita duk da baya taba ta, duk da cewa tarin sha’awar yarinyar yakai mai intaha. Wanda yakeji kamar ya afkawa yarinyar musamman da shedan ke gefe yana dada kawata masa hansatu, amma kuma yakanji tsoron yin hakan , duk da cewa Allah ya halitto shi acikin mazaje masu yawan bukata sosai! Sai kuma ya tsani zina, masu yima addua yake musu. Ya gwammace ace yayi ta aure akan yayi zina. Sosai yake kokari a wajen nan. Musamman yakan tuno wani zamani daya wuce. Tun yana mai farkon shekaru.
Hajiyarsa kan bashi labari kala-kala akan illolin zina da dangoginta. Wanda ita bibiya take, idan kayi sai anwa naka, kullum nasiharta ya nisanci zina ya katange idanuwansa da kallon haram! Yaji tsoron Allah aduk yanayin daya samu kansa. Koda ace shaidan na rinjayarsa ya yawaita ambaton Allah a zuciyarsa aduk yayinda yaga wani abunda yake
rinjayarsa. Wanda wannan nasihar ce yake yawan tunowa, saboda hajiyarsa bata gushewa
wajen tunatar da shi a kullum, sai kuma Allah ya halicce shi cikin maza mabukata . bai sani
ba ko mahaifiyar tasa ta gano irin halittar tasa, ya sanya take mai yawan nasihar. Shi dai bai
sani ba. Yasan dai yana amfani da nasihar sosai. Yasha wahala sosai akan hakan. Tabbas ya san adduar mahaifiyarsa ke bibiyarsa da shi kansa da yake yi, kan Allah ya kare shi da aikata zina, ba zai so yayi abinda za azo aiwa yaransa ba, sannan uwa uba mahaliccinsa da yayi hani da haka.
Amma muddin yaga yarinyar sha’awarta ke damaimaye shi, bai san sanda yake rike hannunta akullum idan ya silala dakinta ba. Har alokacin bai taba cewa yana sonta ba, sai dai yakance zata aure shi,Wanda alokacin ita tai zurfin cikin kaunar Abu fuad.
(to fah ayi dai mu gani hansatu) Al’amura haka sukai ta gudana suna tafiya ciki harda fara nakudar laila atsaitsaye.
Wanda alokacin kuma maria tazo tafiya da hansatu, dan za ai bikin dan uwan hansatun na dangi. Babu wanda yakai ladifa jin dad’i, saboda tasan ko babu komai ramadan zai daina wannan satar kallon, dan ita gwanda ace ya aureta daya dinga wannan kalar kallon, ta bangaren laila kuwa ba taso Haka ba, saboda yanzu ayyuka zai dada tarar mata, ramadan ma bai soba ,haka ta bukataci a bata kudin aikin ita hansatun na iya watan da tai, nan aka bata suka tafi kauyensu.
Tafiyar hansatu da kwana uku laila ta fara nakuda. Zaune ladifa ta ke a falon kasa misalin sha-biyu Na rana tana bawa Fuad custard yana sha, sai ga laila ta fito tana dafe baya. Lad’ifa tace da sauri “jikinne?.”
Laila ta kasa amsawa sai matse fuska take. Ganin hakan ya sanya taiwa ramadan waya kan laila bata da lafiya.
Babu dadewa yazo Ladifa ta goya fuad suka tafi asibitin. Haka aka sha gurmuzu, da
kamar lailar ma ba zata iya haifuwa da kanta ba, ana shirin yi mata aiiki sai kuma gashi ta
haihu inda ta samu baby girl.
Murna suke sosai. Ba a salllameta ba sai washegari suka tafi gida, inda ita iyayenta sukace ta zauna agidanta tai wanka.
Ramadan sai hidima yake, sosai yake farin cikin samun babyn wadda suke dan yanayi da
fuad saboda kamanin Ramadan d’in data dauko. Sai dai fuad ya fita kyau sosai da haske.
Sai wata ‘yar uwar baban laila tazo ta zauna mata wankan jego. Suna zaune a dakinta tanaiwa baby wanka, ladifa ta shiga ta zauna tace “kai wai wannan babyn dawa take kama ne?.”
Baba saude kanwar ‘yar uwar mahaifin lailar tace tafi kama da mahaifinta, dandai tafi laila kyau wannan, sai duhun fatar uwar da ta dauko da gashi kawai na lailar. Dariya lailar tai tace “kai baba wato sai aka ce bama kama. Ai inta biyoni tayi gidan kyau.
“Ke tafi can ba dan hanci ba, ai ba zaki ganu ba. Lad’ifa ta sanya dariya tace “atoh abu fuad ya cire tuta”
Haka dai akaita hidima harzuwa ranar suna ta zagayo aka yi suna tare da radinsa, aka sanyawa yarinyar sunan hajiyar ramadan, sai laila ta sanya mata Najwa.
Bayan sunan najwa da sati daya aka kwantarda yayar ladifa a asibiti anty hadiza dake
can garin kaduna. Haka ladifa suka shirya zuwa kadunan ita da yaya karema. Sai gidan yayi fayau.Kwanan su biyu suka dawo
buga wayar maria zan ta dawo da ‘yar aikin nan, saboda hidimar akwai yawa. ” Rike baki tai “to idan ke baki wa kanki hidima da ‘yarki ba wa zai yi kinji shakiyanci.”
“Inna saude wallahi yarinyar bata barina nai bacci fa da dare, duk sai kiji da rana na gaji, gashi inna da sassafe fa kike cewa sai na fito wanka.“
Dariya tai tace “to banda abinki ai gata nake miki. Kuma ma dai ai megidanki na zuwa ya rike miki ita.”
“Ni k0 dan saboda wankin babyn nan na keso hansatu ta dawo, ta iya aiki sosai wallahi, kullum fa sai an wanke kayan babyn nan ga hidimar gida dan ma ladifa na ragewa. “Ai shikenan sai ki buga duk da cewa mataimaki akwai dadi. Sai dai ‘yar aikin naku ai tai girma na ganta randa kukaje gidana. Kuda ita ai ba bambamci. Ina lefin karama.” “Kananan nan fa basa wani aiki Allah inna saude.”
Wayarta ta dauka bayan ta shimnde najwa, tai kiran maria ta dade tana ring ta dauka, take tambayarta yaushene hansatu zata dawo, mari take ce mata nan da kwana uku, sai tace dan Allah ta dawo.
Bangaren ramadan kuwa sam! ya ma manta da wata hansatu, duk da cewa tana fado mai arai, amma ba kamar sanda take gidan ba.
Kauyen samaru
Can kauyen samaru wato garinsu hansatu zaune mahafiyar hansatun take kan turmi, acikin madaidaicin gida ginin kasa me d’akuna biyu, tanaiwa hansatu hira.
Uwar tace “hansatu tunda dai an gama bikin sai ki koma wajen neman na kanki.”
Dariya ta sanya nan take gaya mata duk irin abubuwa da suke gudana a gidan aikinta, sai dai ba tace mata megidan na taba ta ba. Sai dai tace yace zai aureta.
Takarkarewa uwar tayi ta rannnnngada guda. “Kai farar haihuwa hansatu, ga sadin wa zai ci kaya, ai insha Allahu abinnan zai tabbatu, yo me za ai da surajo, gwanda kema afara ta kanki, yanda kika dade kina aiki abirni to gashi Allah ya baki miji acan.”
“Inna to yaya za ai da surajo ne?.”
“Ke shareshi nace miki ga sadin wazai ci kaya. Yanda kike dambasheshiyar yarinyar nan, ai yanzu kima farajin kinfi karfin surajo.”
Dariya hansatu ta sanya har dasu tafa hannu. Dan taji dadin maganar uwar.
“Kuma megidan dada damke shi zamuyi a hannu, zanje wajen boka na cikin gangare. Da dan irin kudin aikinki dana tara, muje a dadajanyo hankalin megidan ya kara sonki kinga dole ya aureki.”
Tashi hansat tai tana rawa tanajin dadi “wallahi inna karki ga girman gidan nan, sassa sassa, yo idan aka je ganin gidana, wallahi inna sai su ladingo sun sume.”
dariya uwar ta sanya “ai tun haihuwarki hansatu nasan ke mai kashin arziki na haiho.”
“Inna sai dai fa wallahi uwar gidan naban tausayi,ji nake ba zan iya auren mijin ba, tana da kirki da kulawa, amma dayar akwai mugunta ga zagi. Ni fa wallahi saboda itama na yarda mtws mata sai masifa. Ga sanya aiki.”
Tabe baki uwartai tace “yo me aKai akai ita, ai indai kin dauko halina ba kihiyar da zata daga miki dan kwali. Ki manta kuma da dayar matarme kirkin, kiyi abinda ya kamata atoh! ki canja tahiyar ki, har idan kika koma.Kihito da abubuwan da zan gaya miki.”
Nan tai mata Rada a kunne sai hansatu ta zaro ido. ” Kai! inna, nifa ba zan iya ba, haka
kawai suje su jibgeni.”
Takalmi uwar ta dauka ta jefe mata, “matan birni wasa ne har da zaki sanya Lalaci.”
Shiru hansatu tai daga bisani ta tashi ta fara shara. Uwarvta mike tare da zaro mayafi ta fice tana gayawa ‘yar ta tafi gidan uwale.
Mahaifin hansatu da mahaifiyarta basa tare, sun dade da rabuwa, tun tana ‘yar shekara goma. Mahafiyar hansatu irinjarababun nan ne, kishiya kuwa saidai taganta ta kyale, dai dai har so biyar mijinta na auren mata tana koran matan gidan da asiri, duk wani ‘yan tsummokaranta agun bokaye suke karewa, duk kauyen babu wanda bai santa ba, ga masifa idonta a bude yake saboda takan shiga birni ta sari kaya ta kai kauyen tana sayarwa, zuwa wirin boka ba abakin komai bane a wurin maman hansatu, akarshe da dukkan asirin da taiwa baban hansatu ya karye, ya saketa shine ta dawo da hansatu gabanta. Saboda tsabagen gasa da san kud’i ta tura hansatu tun tana shekara goma aiki birni, haka yarinyar ta taso cikin wahala da aiki, uban yaso amsar ‘yar taki bashi, wata uku ke nan da aka sanya ranar Auren hansatu da surajo, wanda ayanzu duk burin uwar da ‘yar ya canja.
Sai wajen goshin magriba ta dawo. Ta zube tana mai da numfashi. Hansatu ke tambayarta. Tace ai taje neman taimako ne kan maganar hansatun da megidan da take aiki. Washe ba
ki hansatu tai. Nan uwar ta baje wa ‘yar dukkan wani bayani, tare da bata laya tace mata. Tabbas inta koma tasan yanda za tai ta sanya layar a karkashin filon megidan, sannan ta bata garin magani, shi kuma ta sanya a abincinsa indai komai yayi daidai tabbas za taci galaba zai sota har suyi aure.
Murna kawai hansatu keyi Allah Allah take ta koma gidan, wanda a ranar laila ta bugo waya tana son hansatun ta koma, nan tai shirin komawa uwar tanai mata huduba kala kala.
Washegari Hansatu ta dawo, da karfinta ta dawo saboda samun dauri gindi daga wajen babarta. Ta yi murna ganin laila ta haihu haka ta shiga hidima a bangren laila baji ba gani.
Ita ce wanke wanke shara mopping wankin kayan baby kullum, rainon yarinyar wanda hakan ya sanya laila ta kumajin yarinyarta shiga ranta saboda Tana sakinjiki tayi duk abinda lailar ke sanyata.
Wani sabon salon da hansatu tazo da shi shine. Ba tayin wanka sai da yamma ta daidaici ramadan ya kusa dawo wa. To asannan ne zata tsaya da duk aikin da take tai wanka tayo kwalliya. Musamman da bata yin irin kwalliyar yan kauye ta dige -digen nan, saboda dadewa tana aiki a birni ya sanya tun da dadewa ta daina dige digen kwalliya. Akallah tayi aiki a abuja tayi a kaduna ta yi a jigawa gata kano kuma bata san adadin gidajen da tai aiki ba Shi,isa ta dan goge da sanin abubuwa.
Bata goge su dining ba har sai daita gama komai, sai bayan taje tayo wanka sai tazo tana gogewa. Wanda dole idan ramadan ya shigo sai ya ganta. Da sauri zata sunkuya ta gaidashi tana murmushi har dasu fari.
Sha’awar hansatu data tafi, ta dawo mai sabuwa fill.
Yauma suna zaune laila da inna saude agefe suna hira. Laila ta kwala kiran hansatu ta fito bakin nan yasha jambaki radau. Ta tsugunna “gani anty.”
Ja da baya laila tai tace “me zan gani haka? ke hansatu meye haka ke da kika zo aiki meye naki na sanya jambaki rabadau abaki, lalle ma! mu sanyajambaki keki sanya ko? To maza -maza kije ki goge shi idan ba haka ba wallahi kiji ajinki.” Hade rai tayi fuska atamke ta mike Dakinta ta koma tana zagin laila azuci tace “wallahi saina auri mijiki k0 ba kya so,” budejakarta tai saiga laya da magungunan da aka bata sai ta fasa dariya, “kai na manta fa dasu taf! da sauri ta goge jambakin ta dau jambakin ta boye asiket dinta. Dan tasan ramadan na bayan gida yana hutawa kuma tasan yanzu ne lokacin wanke kayan baby dan haka abayan zata je dan su hadu. Nan ta fita tana tunani dole yau ta sanyanda za ai ta zuba mai magani a binci, wala Allah gobe tasan yanda za ai ta saka layar.
ilai kuwa tana fita laila ta hado mata kayan baby da bargo ta wanke. Sai ta dauka ta fita tana zuwa waje ta fito da jambakin nan ta dadira abaki ta kalli fuskarta a wani karamin mudubi dan goma.
bayan ta isa Ramadan bai ankara da ita ba sai da taje zata wuce ta tsugunna ta gaida shi yace “hansatu ya aiki? Lfy ta fada tana wani sunne kai sai ta tashi ta bar wajen. Da gangan ta ke tsalle dan ta tsinko mangwaro daya fara fitowa wanda ramadan ya tsiri kallon abinda take. A hankali ta juyo taga yana kallonta sai ta sunkuyar da kai tana dariya, ashe dabarar innana me kyau ce lalle ita ko ta tsinci dami a akala.
Hmm
Bayan kwana biyu hansatu ta rasa inda zata samu damar zuba maganin na domin ladifa ke yima ramadan girki kuma sama take kaiwa. Gashi ita kuma haka kawai ladifa ke mata kwarjini,kuma tana jin tsoronta sai dai ta sanya ido idan taga galala ta zuba. Cikin sa a yau ladifa ta gama girki da wajen karfe shida sai ta hau sama tai wanka. Hakan ya bawa hansatu damar ta lekawa kitchen d’in, da sauri ta bude flask na miya ta barbada ta juya da cilokali ta wanke cokalin ta kai inda yake, da sauri ta bar kitchen din ta yi bangaren laila, gabanta na faduwa.
Sai ta dau dosta ta tsiri goge gefen Tv da speaker ta gefe da gefe. Tana jin dirim motar ramadan ta saki murmushi. Yana shigowa ya yayi arba da ita, sai ta tsugunna “barka da zuwa.”
Kallonta yayi yace “yawwa,” yana ayyna abubuwa da dama aransa. Daidai lokacin ladifa ta sauko daga samanta, laila kuma ta fito itama Kallon hamsatu ladifa tai, sai hansatun ta mike da sauri. Ta gefen ido ramadan ya bita da ido azuciyrsa yana cewa Allah yayi halitta. Ladifa ta amshi jakarsa tanaimai sannu da zuwa ya kalleta yace “my baby ya my fuad?.” tace yana gurin inna saude. ” Ta juya ta dan taka zuwa kan dining dan ta ajje ledar daya shigo da ita. Sai yajuya gefen laila yace maman baby ya dai? Sai ta yi dan rangwada gata nan abaya. Sai ya ce “kin faragoyata ne?.” Ta ce rigima gareta fa gwanda ta saba da bayan.”
Hansatu na bakin kofar falon laila tana leko kai, dan sun burgeta kai ita fa tana san rayuwar gidan, kai za taso a dama da ita itama.Musamman anty ladifa na burgeta tana son yanda take aiwatar da komai nata.
Karar kukan fuad ne ya maido da ita hankalinta,jikinta na rawa dan tunaninta k0 an ganta, sai taga inna saude, innan ta kalleta “ke kuma leken me kike haka?.”
Sai tai tsiri sosa kai “ahh dama… dama ..” Tsaki innan tai tace “halinki ne ai dama, ni ungo mika fuad gun uwarsa.”
Da sauri ta amshe shi ta fita lokacin ramadan na zaune a kujera yana kora ruwa ladifa agefe
“Ahh kuka yake ne?.” Lad’ifa ta fada tana mika hannu.”
E tace mata. ta kalleshi tace “Mv cute boy kiwarta tashi ne.
Ramadan ya karbe shi suka mike ya yace saura wata birthday nasa na shekara daya ko?.” Ladifa ta amsa da E.
Sumar kan babyn najwa ya shafa ya fita dauke da fuad din a hannunsa.
Hansatu ce zaune gefen katifa tana ta tunanin yanda zai ta sanya layar nan, yau sati daya da dawowarta amma ta kasa, saboda ba dama, ladifa ke komai a saman. Ta san da ace laila tayi arbain ne to da sai ta samu damar sawar tunda ita take sawa tai sharar. Dan ma Babarta tace layar bata da kaidar sanyawa.Koyau aka sanya aikin zai yi.
Yau tana kwance da wajen karfe goma ya shiga dakin ta gaidashi ya mika mata waya akwali kirar Aitel karama, wacce kira ake kawai, da ita murna kamar me taji. Tana jin kome ma yace tai mai zatai, nan yace mata ta boye idan yana son ganinta zai ringa kiranta.haka ta kwana tana jin dadin wayar nan.
Da safe fuad ya tashi da zazzabi sosai! Suka tafl kaishi asibiti, hakan ya sanya ramadan yace laila ta gyara mai dakinsa, ita kuma ta sanya hansatu wadda laila na gaya mata dama ta samu sai ta juya da sauri ta fara aikinta inda ta makke layar a gafen siket d’inta, tana zuwa saman ta shiga dakin ramadan, ta bude cikin rigar pillo din ta saka aciki, tana yi tana kallon kofa sai data gama, sannan ta fito tana hamdala lallai ta taki sa’a.
Sai wajen azahar ladifa suka dawo lokacin fuad ya samu bacci. Nan ta sauko ta aiki hansatu gidan maman rauda, ta fice koda ta shiga maman rauda na tsakar gida, nan ta gaida ita. Ta nuna alamar rashin sani tace “daga ina?.”
Tace mata daga gidan nan na kusa damu, dama anty ladifa ce tace ki bata zogale nata an sare shi, kuma kanana ne wanda suka fito.
Murmushi tai tace Allah sarki maman fuad, na dade bamu gaisa ba, hala ke ‘yar uwar watace a gidan? sai hansatu ta girgiza kai tace “aiki nake agidan.”
Wani kallo sama da kasa tabi hansatu da shi ta girgiza kai, tace “bari na tsinko miki,” bayan ta bada ta tafi ita kuma ta tsaya rike da hannu “lalle su maman na son debowa kansu jangwam! wannan gansamemiyar yarinyar ace ‘yar aiki! tabdi jam, “yoni ba gwanda aiki ya kashe ni ba dana dau wannan matsayin ‘yar aiki,” jinjina kai tayi tana tunani za taiwa ladifa magana.
Tsafigaskiyar mai shi.
Nan da nan asirin da akai ya kama ramadan, wani irin wutarson hansatu ne ta dadaya rufe shi, ji yake dole yama aureta. Sai dai duk abinda yake aboye yake, bai bari matan su gani saboda jarfa.
Haka zai siyowa hansatu kayan dadi ya tsaya awaje, yayi mata waya ya kirawota ya bata ta shigo ciki, wanda sautari takanji dadi musamman idan ladifa na samanta laila na shashinta .
Inna saude ce ta fara ankarewa da yarinyar, sam! bata yarda da takunta ba. Haka ta zauna
tana nusar da laila, tace “laila kina kuwa sanya ido akan ‘yar aikin ki dan bana ce ‘yar
aikinku ba, dan kishiyarki bata morar ta kamar ke, kuma ita na ga tafi sanya ido akan hansatu. Duk da ita ma lad’ifar nasan ba tasan abinda yanzu yake wakana ba.”
“Kai inna wallahi niba na tunanin abu fuad zai kalli wata mace ma anan kusa, macen kuma wai ‘yar aiki.” Baki da wayo, toke in banda abinki ai duk mace mace ce, ki bar raina Allura karfe ce, ki kalli yarinyar sosai, ai wallahi na dade ban ga yarinya ‘yar aiki me kyan jiki irinta ba, duba da yanayin yaran masu aikin duk a kandare zaki gansu. Ki dubeta kar ta fiki komai da komai na mata. Ke baki da ido ne? babu namijin da wannan yarinya zata zauna a inda yake ba tare da shaidan ya raya masa abubuwa ba akanta ba, musamman mazan zamanin nan da soye ~soyen zuciya yayi musu yawa, sannan kuma ni ba wai ina cewa haka mijinki yake ba, kawai yarinyar na duba nasha kamata tana lekansa idan zai wuce. Har dakon dawowarsa take. Duk wankan da take kinyi da safe sai da yamma, ba duk dan shi take ba. Amma duk cikinku babu wacce ta gane. Musamman ke laila. Kishinki laila ya zama na shirme ma, ku kula dai hanyar lafiya abi tada shekara.”
Jikin laila ne yayi sanyi tace “hmm inna saude zan sanya ido to.”
Bayan kwana biyu. Karfe sha daya na dare ramadan ya kasa runtsawa, daya rufe ido hansatu ke mai yawo aciki, sai ya mike ya sauka kasan, ya shiga dakinta, tana jin bude kofa ta tashi ta mike da sauri kikinta na rawa dan ita har ga Allah bata son yana shigo mata daki da dare dan
ta najin tsoro. Yace “hafsa.” Sai ta sunkwi da kai, dan kunyar sa taji tanaji, hannunta ya rike yace “zaki aureni?.” Sai ta daga kai alamar E!
Wanda adaidai lokacin laila ta fito zata dauki madara ta ruwa akan dining zata sha da shayi, dan yunwa takeji, ganin kofar dakin hansatu kamar da haske, kuma ga yanayin kofar abude, sai ta taka ahankali, gabanta na faduwa, kanta ta zura ta kofar ta leka dakin, wani irin duka kirjinki yayi, ganin hannun ramadan rike dana hansatu, ba taji me yake fada ba, taga dai hansatu tayi dariya ta sunkwi da kai, shi kuma sai ya dago da fuskar hansatun yana mata magana, ta kuma sunkwi da kan.
Ji laila tai fitsari yana neman zubo mata, da sauri ta koma daga baya ta shiga shashinta ta fada bandaki, sai da tayi fitsarin, sannan ta dawo falo taja ta tsaya tace ‘Dankari‘. ‘
Shi kuwa ramadan karar kofar da yaji ne, ya ankarar da shi, duk da bai kawo wai an ganshi ba, ya saki hannun hansatu ya fita bayan yace ta rufe kofar ta kwanta.
Laila kuwa wata shafceciyar bulala ta zaro wacce acikin kitchen dinta ta ganta tun zuwanta gidan, ta dauka har zata fita sai tai tunani dare ne bata san kuma mai zai faru ba, gwanda ta bari da safe ta narki hansatu iya son ranta .Amma sai data leka ta tabbatar yabar dakin dan
taga an kashe fitila.
Dabas! ta koma tazauna akan kujera tace “lallai nayi sake, nafi uwar wawaye ma, ashe’.
da gaske inna saude take? take wani irin mahaukacin kishi ya turniketa, ta shiga kada, kafa danjira take kawai safiya tayi dan gobe-goben nan hansatu zata bar musu gida . “Cabdi ” ta kuma ambata.
Jin kukan jaririyarta,ya sanya tai tsaki ta mike tai ciki, jikinta har wani rawa yake saboda tsabar bala,in daya ke cinta Hmm.
Ina so na dan kara fahimtar da wasu game da Iabarin. To indai me karatu bai manta ba ramadan yayi gudun gara ya tadda zago.Ko kun manta Iokacin da yake wulakanta Iadifa? Dan kawai bata da irin suffar daya keso, yana ganin ka wai mafitarsa ya auri laila wacce yake ganin itace mai irin suffar da yake wa mayen so, sai bayan da ya aureta kuma ya tarardda ba yanda ya zata ba, saiya gama ai gwanda surar ladifarsa sau dubu kan lailar, kunga to aiyayi gudun gara ita ce ladifa, ya tadda zago, zagon itace IaiIa. Ta saka shi a matsala kala kala bayan ya sameta ba a yanda ya zata ba ya saketa ta dawo, aka zo akai matsalar murabus taje gida ta dawo bayan tasha ukuba to kunga zagon da yake ganin da tafi garar saigashi itace ta sanyashi a matsaloli wanda har saida yayi dana sanin aurenta. Ya Inda kuma garar ce ta zame mai sanyin idaniyarsa.
Ayanzu zance laila ta zame mai kaddara zama da ita dole. Har fa yanzu ramadan a bangarensa haryanzu bai samu irin suffar macen da yake soba, wanda kuna ganin namji me kudi kuma yana da buri kuna ganin zai hakura ne, musamman idan Allah ya jarabceshi da son mata . Sai fa randa ya malIaki irin macen daya kwallafa rai akai zai dawo hayyacinsa. To kuna ganin ayanda yake son me irinjikin hansatu kuma ya ganta abagas agidansa, kuma ba Ciko ahh.’ Natural ba dole ya rikice ba. Akwai maza da dama irin hakafa nasan ko a haka na barku wanda basu gane ba sun fahimta