NAYI GUDUN GARA CHAPTER 33

NAYI GUDUN GARA 


CHAPTER 33
Al’amarin duk ya sanya zuciyarta ta shiga wasi-wasi,anya kuwa ba ta d’aukowa kanta dala ba 
gwambo ba. Ganin babu sarki sai 
Allah ta share hawayen fuskarta 
ta mik’e da sauri ta shige gidan, 
innarta na tsaye ta kasa tsuguun! sai farin-cikki take tana wassafa yanda za ta tsakuri abubuwan dan ta mikawa mak’ota, dan su san cewa fa ‘yar tata ba tai zuwan birni a banza ba. 
Hansatu ta zauna gefen d’akinsu tace “inna ni abinda nake san ki gane kinki fahimta. Maganar surajo fa, kina gani ko jiya yazo fa.” 
“Ke dallah can matsa wawiya, wa ya ke ta wani surajo? ni ce dai nan ke d’awainiya da ke, dan haka babu wanda zai d’aga min hankali. ” 
Hansatu ba ta k’ara cewa komai ba ta shiga d’aki. 

***** 
Yana tafe a motarsa yana jin kira’a, tunani kawai ya ke yanda zai tunkari hajiya amma yasan babu ja tunda ta san dai ba haramun ba ne. 
Wajen 3 ya karasa gida. Babu kowa a felon haka ya sanya ya yi b’angarensa dan ya huta, yasan yanzu laila za ta zo ta dameshi. 
Wayarsa ce tai k’ara, ya duba sunan wani abokinsane harisu ya gani. Yana d’auka yake gaya 
mai an samu k’aramar motar da ya ke so ya duba ya turo mai da hotonta. 
Dubawa yayi motar ta yi kyau 
sosai black colour ce, kuma za ta dace da lad’ifa sosai. Nan ya bugawa harisu ya ce “motar ta yi haris.” 
Haris ya ce “akwwai wata irinta amma blue ce, yakamata ka sayawa dayar matar taka.” 
Dariya ramadan ya yi ya ce “ahhh a barta ba yanzu ba, dan bani da kud’in sayan biyu, amma zan ma magana idan zan kara d’aya nan gaba.” 
Haris yace “ba matsala.” 
Kit ya kashe wayar, shi kansa yasan zai had’a fad’a dan laila ba yarda za tai ba, shi kuma yanzu yana ganin wahalar ya wani kaisu unguwa, wanda da can ma ba wani damuwa yayi da ya kaisu unguwa ba. Dalilin 
auren laila ne ma hajiyarsa ta ce lallai ya ringa kai su unguwa da kansa amotarsa, in babu abinda yake alokacin, shi kuma takura yake. Hakan ya sanya shi tunanin sayan mota a matsayin ta ladifa suna zuwa unguwa, wala Allah in ya samu wasu kudad’en ya saiwa laila. ***** Yau sati d’aya kenan inda ya had‘a da neman yardar mahaifiyarsa kan aurensa ta amince mai. 
Da kuma arbain d’in laila, wanda har baba saude ta koma gidanta. Sai su kad’ai a gidan, al’amarin da ya damu laila kenan. Ita abubuwa yawa suke mata. Sai yanzu take jinjinawa ladifa ganin yanda take jajircewa. Da tsafta da kulawa, kullum shashnenta k’al-k’al. Ita kam ta rasa mai 
yasa yanzu duk ta ke jin kiwar ayyuka. Gashi kuma ta rantse ita da d’aukan ‘yar aiki haihata haihata.Gwanda aikin ya kacame mata. Wanda dalilin ne yasa ta zama wata kazamar karfi da ya ji, kwalliyar nan duk da take yanzu dak’yar take yinta sau d’aya asati. Abu kad’an ta ce jego -jego d’akinta duk kayan baby ne birjik. Ko ina kaya. 
Alokacin ramadan ya dad’a gane kalar laila. Har gori yake mata cewar ashe kwalliyar tata duk ta d’an lokaci ce daga haihuwa 
d’aya ta daina, shi kam baya son k’azanta. Sai ta sha kunu ta ce 
to yaya kake so nayi ne. Sai dai kawai ya basar ya shareta. 
Yau itace da girki. Da safe tana kitchen tana girki Ramadan ya leka kitchen din kaca -kaca sai 
yayi tsaki ya ce “Lokacin da kike da ciki cewa kike ciki ne ya sanya ki k’azanta da kin haihu za ki dawo kamar da, amman yanzu ga shi kin haihu sai abinda ya yi gaba. 
Cuno baki tai gaba ta ce “kana dai ganin yanda Najwa ke da yawan kuka wallahi rikitani ta ke, sannan ai duk kazantar da kake ikrari ina yi jikina fes ya ke ina kamshi na, kwalliyar fuskace dai kawai yanzu na daina.” 
Tab’e baki ya yi, ni nafl so naga waje yayi kal, bana son na zo na ga waje da kura k0 kaya k0 
datti, hakan zai sa muna sabawa da ke laila ba naso. Kwalliyar jiki kuma in dai za ki na zama 
Da turare koda da datti da sauki amman dai na fiso a koma yanda ake tsantsara min kwalliya ada 
zan nafi so.” 
“Au ashe kana bida, so nawa zan kwalliyar ba ka yabawa sai dai kama juyar da kai, ashe dai ana 
son.” Tsaki ya yi ya ce “ni ban mukulli na tafi.” “Au ba za ka ci ba.” 
“Akoshe na ke zanci a office ki gyara min shashinki kafin na dawo. Na dai gaya miki ba na son kazanta. 
Ya fice sai taja numfashi tace “namji yaji dad’insa, namiji dan gata, shi wani baruwansa gani ya ke kamar mace sassakota akai,lallai ta dad’a yarda cewa aure dukansa babu wani dauwamammen jin dadi, jin dad’in ragggene. 
Ramadan lokacin da yaje aiki ya karb’i excuse ya je gidan abdallah ya d’auke shi suka tafl kauyensu hansatu. Abdallah dake mamakisa yace “wai ni dagaske aure za ka kara wai me ka zama ne bawan Allah.” 
Dariya ramadan ya yi ya ce “ba za ka gane ba. Ina fa da dalilina, kowa arayuwa fa da zabinsa. Ba ka san yaya yarinyar ta ke ba ne.” Tsaki abdallah ya yi yace “wai har yanzu kana da son matanka. Wallahi na d’auka ka canja hali musaamn ganin matanka masha Allah! ai sai ka godewa Allah.” 
“Meye dalilin da ya sanya Allah ya halatta mana mata hud’u? saboda ayanda Allah ya halicci 
halittar namiji wani sam! Mace 
d’aya bata isarsa. Wani ya kanso 
canji. Koda kuwa na gidan sunai mai duk wani abunda yake da 
bukata .Tofa idan a halittarsa Ya zo a irin haka sai ya aura, da naje ina bin matan waje, ba gwanda nai auren ba. 
Kaima kasan muna da abokan da ga su nan duk da mata daidai, amma kuma awaje bin matan banza suke, to mai gari ya waya? meye amfanin halatta maka mata da yawa.” 
Dariya abdallah ya sanya ya ce “hakane maganarka abokina, amma karka manta akwai ma mazan da suke da mata da yawan kuma ka gansu suna bin matan wajen, kawai na kula abin ra ayi ne. Ka ga ni da mace d’aya nake jin zan iya zama 
Sai dai idan a kundin kaddarata Allah ya halatto mini su da yawa ne to babu yanda zan sai na aure su, k0 anan ina bayanka gwanda kai auren. Amma kuma hanzari ba gudu ba, ‘yar aiki fa yarinyar da tai zama da matanka matsayim mai musu hidima, baka ganin kamar ka sayar mata takitin rashin zaman lafiya ne in ta shigo a gidanka, kasan mata fa ga ni za suyi ka rage musu farashi.” 
Dariya yayi bayan ya karya kwana ya hau kan titi street yana sharar gudu ya ce “su mata haka 
suke kishi ne da su kamar me, amma abin nan ha haram ha ne kawai idan ka biye ta tasu ha zakai komai ba.” 
Shi dai abdallah kawai jinsa ya ke har suka karasa garin. Da yake 
sun gama magana da hansatu sai ta had’asu da wani yaro ya rakasu wajen mahaifmta. Sunje suka tsaya daidai bakin bishiya suka firfito wajen da iska Sosai 
Abdallah ya ce ba laifi yarinyar 
ta yi gaskiya,amma kamar akwai 
mu’amalar kauyawa atattare da itahar yanzu.” 
Dakatar da shi ramadan yayi yace “dan Allah kabar maganar na san abinda za kace.Ni babu ruwana da wani yanayinta.” 
Dariya abdallah ya sanya kawai domin yasan da rigima aharkar nan. Baban hansatu ne ya fito suka gaisa bayani sukai mai dangane da buk’atar da suka zo da ita, shi kuma ya jinjina kai yace “to to masha Allah.” 
Agaskiya na ji dad’in maganar ku, amma ita yarinyar ba ta shaida muku cewar an tsayar da ranar aurenta ba?.” Ramadan yace “E” 
Shiru mahaifin yayi yace “to dan samari abinda nake so ka sani shine yarinyar nan ni nan mahaifinta na ba da aurenta ga wani wanda da sunkai shekara uku yana sonta. Yanzu saura 
wata daya bikin.Kuyi hakuri k’warya ta bi kwarya.” 
Ramadan kasa ya yi da kai, hankalinsa a tashe, sai abdallah ne ya yi magana yace “ce to to madallah mungode,” ya ja Ramadan suka bar kofar gidan, a k’ofar gidan su hansatu suka faka. 
Ramadan ya shafi gemunsa yace 
“ba na jin wannan dalilin zai sanya na hakura da hafsa.” 
“Anya kana cikin hankalinka kuwa? Kana son kace min baka san cewa neman aure akan neman aure ba haramun ne ba?nasan ka manta saboda giyar so ta d’auke maka hankali, to ka farka in ba haka ba wallahi k0 auren ka yi matsala za ka fuskanta, saboda kun kaucewa sharia.” 
Ramadan bai ce k’ala ba sai shafar sajensa kawai yake.” 
Adaidai lokacin innar hansatu dakanta ta fito ramadan yayi mata bayanin abinda ya faru ta ce “karka damu fa, kuma duk yanda za ai ka aureta zanyi, buyagin mahaifinta ne kawai, auren dole ya ke san yi mata.” 
Sai alokacin ya d’an ji dad’i aransa suka tafi. 
Suna tafiya surajo na zuwa gidan ya aika aka kirawo hansatu, bayan ta fitO ta tsaya, leda ya mik’a mata ya ce “gashi mutuminki ne na sayo miki,? wani banzan kallo taimai tace “ashe ba ka san cewa na fasa aurenka ba, ba zan aureka ba.” 
“Karki min rashin kunya, alkur’an zan babb’allaki, ko kin d’auka banji labari bane? to ayanzu har labari ya je min wai samarin birni na biyoki yanzu ya dace kimin haka? kin manta soyayyar da mukai? “Ni fa d’an birni zan aura.” 
Inna tun lokacin da yazo tana bakin k’ofa tana jin mai suke 
fad’a. Afusace inna a fita ta d’au ledar kilishin ta wulla mai, ta ce “kai matsiyaci me zatai da wannan abin? Yanzu tafi k’arfinsa, ji yayi hawaye sun sararo mai, yace “inna nine fa surajo, karkiyi min haka wallahi ni hansatu ce zabina zan iya rasa tunani na akanta..” 
“Ka rasa kwak’walwarka ma ba tunani ba, ‘yata ta zama ‘yar gayu na fada maka, kaje can ka dauki irinka,” ta fad’a tare da kuma wulla mai ledar kilishin taja hannun hansatu suka bar wajen. 
Ya dade a tsugunne, kamar ya fadi ya mutu, saboda takaici be taba sanin zatai mai haka ba. Jikinsa har rawa yake ya d’au ledar ya fita. Allah ya sani ba zai iya rayuwa ba hansatu ba ya ci 
buri akanta.Dole ya san mai zai yi. 

**** 

Innace ke zuba sauri kamar ta ci kafar kare, ba ta wanzu a ko’ina ba sai k’ofar gidan kawulle wato yayanta. Ta shige gidan alokacin yana nan Allah ya so ta, Da ke yamma ce yana zaune akan karauni yana cin d’umamen abinci, “ke ce a tafe da yamman nan ladidi.” 
“Ni ce mana, ai in ka ganni ai samuwa ce, ina kandala ne?.” 
“ta fita makota barka.” 
Gyara zama tai ta ce “yaya kasan dai ni kad’ai gareka, kwarai kuma kasan duk wani abu da ya faru nida mijina muka rabu.” 
“Ina kuwa zan manta, to a yanzu auren dole ya ke san yiwa hansatu, saboda kasan sanya ranar da a kai kwanaki nata, kawai fin k’arfinta ya yi, to yarinyar nan yanzu ta samo d’an birni, kasanta da farinjini da kashin arziki sosai yake da abin hannu, kar kaga irin kayan abinci da ya kawo mana to shine nake san ka shige min gaba ka zama me daura mata aure, so nake ka shige mata gaba, dan ba zan bari a kwareta ba.” 
Kawulle yace “yo wannan ai ba wani abun azo a tada jijiyar wuya ba ne, ki k’yale komai, karma ki tada hankalinki duk randa yaron ya komo sai ki turo shi wajena. 
Gud’a ta sanya ta ce “godiya na ke yaya, Ai naka sai naka dad’in zama sai bare. Nan ta ta tashi ta 
tafi. ** 
Al’amuran gidan ramadan sun fara daidaita ganin cewa ramadan din ya bar musu maganar hansatu a gidan. Hakan yasa laila ta sarara da fad’a, ta fuskanci kanta take dan getta kanta. Amma duk da haka dai tsaftartata ba kamar da ba. Ladifa kuwa hankalinta akwance yake har d’an kumatu ta yi saboda bata sanya komai a ranta ba. 
Misalin k‘arfe takwas na dare duk suna zaune afalon gidan na kasa, ana hira ana kallo. Hannun ramadan rik’e da babyn laila najawa yana mata wasa yana cewa mamana.Ga fuad na gefe yana gwaranci yana tab’a kan babyn. D’an gyaran murya yayi yace ladifa laila duk suka juyo ya ce “Na sa yi mota wacce za ku na 
hawa amma da sunan ladifa. 
Da sauri lailata juyo ta ma kasa furta magana. Can tace “Cabdi! Adalci kenan?.” 
Ladifa kuwa tasan maganar sai ta basar saboda ita ta rigada ta gama magana sai randa ya sayowa laila zata karb’a. 
“Ke ta ki laila sai an d’an kwana biyi zan sayo miki. Sai wani kayana sunzo dan nai order zan sai miki, da yake ramadan bayan aikin da yake yana hadawa da business. 
Lad’ifa tace “nikam zauji ai kawai ka barta sai ansiyo watan. Sai ka hada ka bamu.” 
Laila tace “hmm” kawai ta juyar da kai. 
Nan ta shiga tunanin mai yasanya ita bai fara sayo mata ba sai ladifa.Daman yafi son lad’ifar 
shiisa ya fara sayo mata sai ta juya zuciyarta ta suya. Mik’ewa tai zata bar wajen cikin fushi. 
Ramadan ya kalleta fuska atamke yace “dawo ki zauna.” 
Dawowa tai ta zauna. “Har abada dai sai an nuna ladifa ce mowa afili ma ba a boye ba” 
“Wai mai yasa kike haka ne laila, sai ki tsaya ki ji abinda zan ce gaba ko?.” 
“Hmm nikam zaujina ka barta kawai sai an sayo watan k0 kuma ita ka fara bata ba komai ba ne.” 
“Abinda na tsara agidana dole shi za abi, nayi hakan ne fa kawai 
dan arage mun wasu abubuwan, tunda ina da halin sayan. Kuna da kara yawa dole na san abinda ya fissheku, bawai laila naki sai miki bane, ahh dan itace babba shiisa na fara da ita, idan kikai hakuri ai zan sayo miki k0. Kuma ayanzun ma na saye ta ne kan cewa duk inda za ku kuna amfani da ita amma da sunan ladifa.Yanzu haka jiya na bada kashi uku na cikin kudin motar taki laila, idan Allah ya hore mun sai na cika.” 
Ladifa tace da dai ka dauko driver yana kaimu kawai, d’ayar ma ta isah Saboda halin yau, ka cire motar daga sunana kawai kabarta ta zamo ta gida kawai.” 
Da sauri laila ta kalleta ta banka mata harara. ” korafu bai karfu ba ladifa.” 
Murmushi tai ganin yanda lailar ta yi. Sai ta kalli ramadan daya kafa mata ido sai ta juyar da kai, tasan kallon yabawa maganarta ya ke mata sai kawai tace “ka 
amince?.” “Murmushi yayi ya ce “maganarki na amsheta.Amma a 
bar ta ayanda na tsara tun farko. Duk dai yanda ta yiwu.” 
Hakan yasa laila ta dan sakko, ba ta san sanda ta rungumeshi ba, tana murna, tabbas tasan kafin lokacin a kawo tatan ma ta ladifar ta fara tsufa, tunda zata na hawa ta lad’ifar ai da sauki.” 
Ladifa tace “shi kenan k’albina nagode maigidana Allah ya kara bud’i. Suka ce amin. 
**** 
Ranar lahadi da ta zagayo shine ranar da ramadan abdallah da kanin baban Ramadan suka tafi can garin su hansatu. Direct gidan kawulle suka zarce. Nan babu b’ata lokaci aka sanya Rana sati biyu saboda ladi tace gwanda ayi a kare.Lokacin da hansatu da innarta sukaji labari sai ta kuma sakin guda. “Sai ni ladidi ina jinjinawa kaina kan cewa duk abinda na sa agaba saina cimma shi, boka na gangare ba ya bani kunya nina sani.( wa’iyazubillah) 

**** 

Zarar mayafi tai ta fice gidan Uwale ta zarce suka tasamma gidan boka. Mugun nufi sukai ta rattabo mai kan auren Hansatu da ramadan kan a dada mallake 
ramadan ya zamo a tafin hannun hansatun, sannan kishiyoyin 
asanya musu rashin zaman lafiya Ya tsane su. 
Boka yace”Ba ki da kyau ladidi. Kin haukatar kin gurguntan ya kamata ki zama karamar boka,” sai ta fasa dariya. Nan yace musu aranar da aka daura auren suzo zai basu abubuwan da zai had’a. 
Nan suka ta shi suka tafi.Bayan shigewar ladi gida, uwale ta yi gaba ta k’ofar gidan Mari ta wuce sai ta tsaya. Dan kishirwa ta dameta. Ta shiga gidan mari na tankade ta zauna agefe mari tace “ke kuwa uwale daga ina?.” 
Baki ta ta rike “ina muka ga ta zama ‘yar ladi ta kwaso dan birni wai wanda tai aiki agidan za ta auri me gidan yanzu haka har an saka rana.Kinsan uwale da sharri yanzu haka daga gidan 
boka muke ba irin shirin da ba tai ba.” Gaban mari me ya fad’i ta ce “subhanallah anya an taki gaskiya ba da surajo za ai ba ne? Ina ce har sanya rana anyi?.” 
“Yo k0 nice naga daula zan tashi 
tsaye kuwa. Haka sukai ta hira. **** 
Tana fita mari ta ce “ba za ai cuta dani ba dole na sanarwa matan gidan cab. Waya ta d’au ta kirawo laila. Lokacin laila za ta tada sallah ta tsaya ta d’auka. 
Mari suka gaisa take cewa “kinsa kuwa mijinki aure zai yi? Da hansatu har an saka rana.” 
Dafe kirji laila ta yi tace “me kike ce?.” Cikin tashin hankali ta ce “wallahi ban sani ba bai gaya 
mana ba.” 
Duk bama wannan ba “ina so ku ta shi tsaye da addua mahaifiyar yarinyar nan bata da kyau. Na tabbata sun asirce mijinku ne shiiisa kullum yana tafe a kauyen nan, hatsabibiya ce ta karshe zamaninda take gidan aure kishiyoyinta sunsha wahala. Wallahi akwai wacce ta haukatar ta tsiri hauka tuburan. Sauran kuma tai asirin da miji ya tsane su karshe ya sake su.” 
Fuzge dankwalin kanta laila ta yi ta wullar tace “mun shiga tara.” 
Mari tace “ni dai shawarata ku dage da addua ba dare ba rana karta cuceku. Domin wallahi matar nan ba tada imani.” 
“To na gode mari Allah ya bar 
zumunci.” 
Laila tana kashewa jikinta har rawa ya ke ga masifa na cinta. Dak’yar tayi sallah. Tana idarwa ta hau shahin Lad’ifa duk ta sanar da ita abinda ke wakana itama ta shiga rudani.Sun dade suna zanta maganar har ma suka gaji. 
Lad’ifa kuwa maganar asirin da ta ji an fadi ne ya dameta duk da ta san cewa sai abinda Allah ya kadartowa bawa zai same shi, amma kuma mutum ba zai sameshi amma Dole ta san abinyi ta mik’e da addua. 
Laila kuwa duk ta burkice so take kawai Ramadan ya dawo. motar ma daya siya ta toshiyar baki ce ba don Allah ba. Lalle za 
a yi wacce wacce. 

**** 

Mari kuwa ba tai k’asa agwiwa ba da daren rananar ta dangana da gidan mahaifin hansatu. Ta samu mahaifinta duk ta sanar mai abubuwan dake wakana. Maganar Yaji bagatatan, “ashe! ba abar maganar ba duk da na fada lalle zai nunawa ladi cewar nine mahaifin hansatu.Kuma bata isa ta daurawa yarinyata aure bada wanda ni na sanya mata rana ba.” 
Godiya yayiwa Mari ta tashi ta tafi. K0 abincin da ya d’auko zai ci ya ma kasa, sai kawai ya tashi afusace ya fita yayi 
gidan ladi.Dole ya fitowa ladi da karlinsa. Dan ya kula bata da cikakken hankali. 
Hmm nanfa ake yinta

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE