NAYI GUDUN GARA CHAPTER 34

NAYI GUDUN GARA CHAPTER 34
A fusace ya shiga gidan, tun daga soro yake cewa “ladidi fito, rashin mutuncinki yayi yawa.” 
Fut ta fito ta tsaya tana fadin”yakuba menene ya kaika shigowa cikin gidana?.” 
“Ke ladidi hawainiyarki ta kiyayi ramata, wallahi ba damuwata bane na mangareki, ke har kina da gidane ladidi? mutuniyar da jahilci yayi miki katutu ina kika taba ganin an yi neman aure kan nema? ke mace ma kin taba ganin ta aurar da ‘ya‘ya.” 
“Ka gama? Nace ka gama, to ka saurareni kaji, wallahi idan naci, sunana ladi to ba a isah asanya yarinyar nan a lalle ba indai da surajo ne, nice nan ni ce mahaifiyarta, ni nake kula 
da ita, kuma nice nan zan aurar da ita, uban me kake yi mata na ce uban me kake yi mata?.” 
“Ba nayi mata komai, amma nine nan mahaifinta. Bayan kaita birni aikatau da kikai shekara da shekaru ban magana ba, sai yanzu za ki wani zo ki nuna rashin hankalinki, to yanda kika tufka haka za ki warware.” 
Adaidai lokacin hansatu ta shigo gidan, tana ganinsa ta tsugunna tana gaidashi, sai ya daka mata tsawa, “wato hansatu kin koyi halin uwarki ko? to wallahi indai da raina baki isa a daura miki aure da wani ba inba surajo ba, idan ku baku da ilmi ni ina dashi, kuma ayau ayau din nan zaki bar gidan nan, mazajeki hado kayanki. 
Tujewa tai da alamar babu inda zata, ladi tace “uban kuturu yai kad’an, wallahi babu wanda ya isa agarin nan ya nunan yatsa na daga mai kafa, kai ka isa kace zaka zo kaimun abinda bai dace ba, wallahi ni nan ina da yakini sai na aurar da hansatu ga dan birni.” Ta fada tana mai wulla mai mugun kallo.
“Hansatu kije ki debo kayan ki nace.” “Ni dai gaakiya wajen inna zan zauna.” 
Wani mangara ya kaiwa bakinta, wanda saida ta fasa kuka, ya juya bayansa ya wawuro danyen ice ya fara zaulawa hansatu, ta fasa ihu. 
“wayyo zan hado” 
Ladi ta tsaya agabansa tace “wallahi ba ka isa ba, itama ya zuba mata daya zwit ya shaula mata a baya ta gantsare. 
Hansatu ta fito ya nuna mata hanya “muje,” ya fada tare da daka mata tsawa, kuka ta shiga yi shabe -shabe ta bishi a baya, ladi ta bishi tana surfa mai bala‘i, ko kallonta bai kara yi ba. Har suka fice. 
Suna fita ta zube awajen ta dora hannu aka ta fara kuka “shikenan zai min katankatana, wallahi wurin mai unguwa zan kaishi kara a bi mini hakkiina,” sai ta zari mayafl ta ficee tana surutai. 
Ramadan sai wajen 10 ya shiga gidan saboda yana can hada hadan yanda komai zai tafi na aurensa, da yana tunanin ko ya kamawa hansatu haya sai hajiyarsa tace Aa ita ba tasan raba gida d’in nan, tunda Allah ya hora mai gidan nasa kafcece ne yasan yanda zai fitar 
mata, dalilin daya sanya kenan ya tsaya,washegari yana son a farayi ma gidan gyara. 
Shi bai dauka ma zai taradda matan nasa ba suyu bacci ba, sai yaga laila kam zaune a falo tana hura hanci. Lad’ifa kuwa, tun tara tai samanta, musamman da fuad ke mata rigima, sai ta haye ta kwanta bacci, sai baccin ya gagara saboda tunanin maganar da mari tai, tabbas! zama bai kama ce suba,dan Allah yace tashi in taimakeka, saboda ta nemi kariyar Allah, alwala ta dauro ta shiga yin nafilolinta, sai da tai raka’a takwas sallama hud’u, sannan ta zauna ta dingajan carbi, ta dad’e tana yi har zuwa sha -biyu, sannan bacci ya tasammata, tai kwanciyarta bayan tayi adduar Allah ya kauda duk wani sheri da makirci na dan adam a garesu, mugunji da mugun gani Allah ya kare. 
Tun a kasan ta fara zazzaga bala’i tana kuka ya yaudareta ashe shi munafiki ne, shine zai sayo mota yayi toshiyar baki to ba taso, bai bi ta kanta ba ya haye samansa. lta ma ta bishi. 
Koda suka shiga dakin saman taki barinsa ya runtsa, sai fadar maganganu take, harya kwanta ya mik’e. Sai a sannan ya kalleta ya ce: “laila ina so ki samawa kanki lafiya, ki sani 
aurena da hansatu babu fashi domin ina sonta zan aureta ne kamar yanda ke ma na auroki ki, idan da ba a aurowa ke a auro ki? shiga hankalinki.” 
Share hawaye tai ta mike cikin in.. Ina ta ce “Ba zan shiga ba ramadan, na rantse da Allah muddin ka aurota wallahi tallahi saina babbaketa, in yaso kowa ma ya rasa, na gata tsiya dan jaraba kawai mu biyu bamu isheka ba sai ka auro wata. ” 
“Idan ke kike nemar mini kudi ko isarki ta isa ta hanani bisimilla. Allah ne ya halatta mini mata hud’u dan haka ra’ayina ne nayi aure haukanki da rashin da ar ki ba zai sanya na fasa aurena ba. Kuma Ki tashi ki fita .” 
“Babu inda zan fita ai wannan zalunci ne ka rasa wacce zaka auro mana sai ‘yar aiki, na rantse da Allah sai dai ai kowacce wacce baka da kwanciyar hankali agidan nan, sai na tadar maka da hankali saina sanya kayi dana sanin aurenta.” 
Mikewa yayi, yace “get out of my room.” Ya fada mata yana mai tsananin jin zafin takura mai da tai da fadanta. 
Cikin karaji tace “ba zan fita ba wallahi.” 
“I said get out of my room ya kuma fada yana kallonta cikin ido. 
Zaman dirshen tai ta shiga raira kuka. “Wallahi tallahi ramadan ka ci amanta,ban taba 
zatan za kace za ka aureta ba.” 
Tsaki yayi ya fice ya bar mata dakin sai ta kifa kai gefen gado taci gaba da kuka.Dan ji take kamar kirjinta zai ballo saboda tsabar kishin data keji aranta. Da zuciyarta ta dan doshi hanyar da za taji sanyi sai kishin ya kuma bijirowa, ta kumajin wani dunkulallen bakin ciki na karakaina a zuciyarta. 
Shi ko Kan kujera yaje ya kwanta ya tsiri baccinsa a nan. Da asuba ladifa ta mike tai sallahrta nan ma tayi adduointa, ta d’ora da karatun Alqur’ani, tai adduarta, ldan har hansatu alheri ce ga mijinta dasu kansu baki d’aya. Allah yasa ya 
aureta, idan ba alheri bace zuwanta zai ja da musu matsala Allah ya kawo mai maslaha, ta dade tana addua K’arshe ta rufe da salatin annabi ta kwanta. a 
Da safe, tana zaune tana bawa fuad custard,ramadan ya shiga, kallo daya tai mai ta dauke kai, tun jiya bai sanyata a ido ba, sai yau wani irin fuzga zuciyarsa ta yi musamman ganin ta kalleshi ta juya gefenta, ya zauna ta gaidashi, da dan murmushi a fuskarta, daukan fuad yayi yace “my boy good morning. Dariya fuad din yasa yana mai gwaranci. 
Kallonta yayi, sai ta juyar da kai, takan burgeshi muddin tana basarwar nan bata san cewa kyau ma take karawa ba ahakan. 
Yake yayi yace “baby da kinsan cewa yanda kike min din nan kyau kike da bakiyi ba.” 
Sai ta dan juyar dakai, dan maganar ta bata dariya, kuma ba taso ya ga dariyarta, tace 
“hmm abu fuad kenan ya shirye-shiryen aure?.” “Bai magana ba, ya zauna agefenta. “To Allah ya sanya Alheri tunda ba za a amsa mini ba.“ 
Dariya ce ta so kufce mata ganin yanda yake wani kakkaucewa, sai ta mike ta shige daki, ya san cewa bata bukatar karin magana kan hakan. 
Burgeshi yaji ta kuma yi, komai nata in class take yinsa. Ba kamar laila ba. Zai so ace ya 
kuma dace da macce irin Lad’ifa. 
Al’amarin Ladi kuwa, koda ta fita afusace din nan kuwa, bata zame ko ina ba sai gidan mai unguwa, ta same shi a k’ofar gidansa. Cikin kuka ta sanar mai karya da gaskiya kan abinda yakubu yayi mata. Mai unguwa yake ce mata “washegari idan anfita fada zai musu magana. Yaji daga gare su. 
Safiyar da ta waye. K’arfe goma ladi tai mata a soron gidan mai unguwa dake d’auke da shimfida yana zaune a tsakiya, gefe ga liman. Salllamar yakubu ce ta tsaidasu ga maganarsu. Ta gefen mayafl ladi ke wulla mai harara. 
“Maimaita abinda kika zo kika sanar mini jiya ladi.” Babu tsoron Allah ta maimaita. “To Alhamdlh.” Mai unguwa ya fada tare da kallon yakuba yace “muna son ji daga gareka.” 
Gyara zama yayi yace “Allah ya ja da ranka. Wannan matar dai kasan tsohuwar mata tace, to mun rabu ta tafi da yarinyata to Allah ya gafarta malam yarinyartana da masoyinta wanda sun dade tana sonsa yana sonta. Da kanta ita ladi tazo ta shaidamini maganar komai akan surajo da yarinyar nan tace shine zabinsu ita da ‘yar har aka sanya rana. Wanda na san duk ka sani saboda kai ne ma ka jagoranci abun.” 
“Hakane ban manta ba.” 
“To yau wajen sati biyu kenan al’amari ya canja inda a wajen aikin yarinyar ta samo miji yana sonta da aure, sunzo wajena na gaya musu nai mata miji an saka aurenta saura wata d’aya. Muka rabu a haka, ashe ban sani ba matar nan taje ta karbi kudadensu, kawulle 
wanta ya jagoranci abin hannu biyu, wai har da sanyawa yarinyar ranar aure wata daya.” “Subhanallah! kwamacala kenan. Mai unguwa unguwa yace “haka akai ladi?.” “Yallabai auren dole fa zai mata fa.” 
“Mai unguwa yace “bana sonjin maganarki don nima duk na san komai kawai ina son amaimaita abinne, saboda izinah ko a addini ma ai haramun ne ga ubanta a zaune a raye 
bai mutu ba, ace wani ne zai ba da aurenta, dan hauka ma dasa ranar wani akanta. Kallon liman yayi yace “ko ba haka ba liman?!‘ 
Gyara zama yayi yace “Allah shi gafarta malam haka maganar take. Ai a sharia babu mai aurar da yarinya sai ubanta. sai dai in shi mahaifin nata ne ya umarce wani da ya zama waliiyinta ya daura mata aure. Dangin wajen uwa ba sa cikin waliyai masu d’aura aure. Waliyan yarinya na daga cikin Asibaidinta (wato da ko uba). Sannan ba a neman aure akan neman aure, ma’ana kar wani ya nemi aure bayan wani ya nema. Ma’ana kada yayi tayi akan tayin waninsa, indai an yanka sadaki ko an sallama, ma’ana an bada yarinya. To babu damar wani kuma ya fito neman aurenta. To wanan shine abinda addini ya zartar. Ladi baki da hurumin da zaki d’auki yarinya ki bada ita har a daura mata aure.Wannan 
babanta ne keda hurumin aurar da ita.” Kuka ta sanya “daman dai an shirya kitumurmura ne.” 
Tsawa mai unguwa ya daka mata ya ce “dole ki kasance cikin abinda dokar musulunci ta kafa. Dan na kula baki da cikakken ilmi. Ya kamata ki koma ki koyi hukunce-hukunce na shari’a na addinin musulunci, kuma karna karajin kin tada wata magana, saboda baki da 
hurumi aciki, uba shine a hakku, in banda jahilci ma, ta yaya an sakawa yarinya aure da wani kuma ki kawo wani, wannan ai haramci ne, to karna kara ji, idan ba haka ba zan aika birni yan hisba suzo su shiga lamarin.” 
Gyaran murya yakubu yayi yace “alfarma nake nema dan Allah, tunda yau talata ina so ranar jumaa za a d’aura auren hansatu da saurajo saboda ni nasan wacece ladi komai za ta iya.” 
Kuka ladi ta fasa babu damarta tsawaita magana saboda tana dan shayinsu mai unguwa. Yace “shikenan za ai hakan. Allah ya sanya alheri.”Nan ya sallamesu suka tafi. 
Ladi kuwa tsaida yakubu tai ta ce “wallahi indai ina raye ba za ai auren nan ba. Wanda nake so, shi zata aura, kuma ka dawo min da yarinya.” 
“Ai indai kinga kin kara ganin hansatu to ranar da aka daura mata aurene sai kizo ki d’auketa kije kuyi biki,” yana fad’a ya juya. 
Wani irin bakin ciki ya tasammata, tana ganin wankin hula yana son kaita dare. 
Koda hansatu taji batun d’aura aurenta da surajo, wanda surajon yazo yana washe mata baki yana sanar mata, sai ta saka kuka tai cikin gida, kuka take sosai ga takunkumin da mahaifinta ya sanya na ko kofar gida ba zata ba. Kuka take kamar taci babu, don ita ramadan take so shine take haukan so, shine take son taje tai zaman aure da shi. Yaya za tai ne.? Da yamma bayan fitan babanta ta silala ta fice tai gidan innarta, tana zuwa ta dinga rusa kuka, ladi tace “barni dasu wallahi tallahi karya suke, ai d’azu na je gurin boka na gangare ya sanar min cewa babu makawa za ai aurenki da ramadan ki kwantar da 
Hankalinki. Ni nasan aikin na gangare babu karya aciki komi ya fada gaskiya ne.” 
Ana e gobe daurin aure, wato ranar alhamis, hansatu ta samu damar buga wayarsa. Lokacin yana tsaka da gayawa ma‘aikatan dake gyaran gidan yanda za suyi, dan dakin da hansatu ta zauna na kusa da kicthen yake so su kara girmansa ta baya, saboda filin bayan 
akwai flli sosai, to girman dakin za a k’ara ya zama karamin falo, kuma a yi wani d’akin a gefe, sai ya zamana ta kofar dake kusa da kicthen din ladifa za a shiga shashin da zai sanya hansatu, da yake yana da kudin, nan da nan aka ajje su bulo aka fara aiki gadan -gadan. 
Wanda laila ganin hakan ya dada sanyata ajazaba, har da su zazzabi kullum kuka,ta dad’a 
burkicewa kullum fada Ita da ramadan, koda ma tai ma mamanta korafi Ita gida zata dawo ba zata iya zama da kishiya ba,kuma ‘yar aikinta ba, maman tai mata nasiha sosai ta tunatar da ita abubuwanda in har ta fito to ita da komawa sai wani ikon Allah, wannan dalilin ya sanya ta hakura kullum cikin aibata auren take ka’in da na’in. 
Lad’ifa kuwa ta komar da kanta ga Allah ta kusanta kanta kullum cikin ibada, kan Allah ya shiga ‘sakanin nagari da mugu kan duk wani sharri da za,a akulla. Da duk wani abu dake tattare da mahaifiyar hansatu na kokarin sanya asiri a lamarin. Tana yi ne kan Allah ya 
karesu, agefe guda kuma takan dinga yin adduar karya sihiri tana tofawa aruwa, musamman take yi ta tsiyaya ajarkar ruwa ta sanya afridge wanda in ramadan na bukata ruwa take ba shi. Kallon kawai laila take yanda duk ta rame ta canja kala, hakan ya sanya tai mata maganar cewa yakamata tazo su dage da addu’a kodan hatsabibancin matar da aka fadi . Kawai to lailar ta ce mata ta kauda maganar amma ita kishin dake nukurkusarta ya hanata katabus! wanda haka duk ya shafi najwa, sai dai yarinyartaita kuka wanda ta nan bangaren suke dad’a hawa sama da ramadan kan dole ta kular mai da yarinya dan rashin tausayi. 
Yana tsaye abayan gidan ta daidai ina ake kara ginin, wayarsa tai kara, yaga sunan hansatu ya d’auka, cikin kuka take sanar mai abinda ke faruwa, gabansa ne ya fadi . Sai yace mata zai zo anjima ko gobe da safe. 
Duk sai ya diririce ya koma cikin gidan yayi wanka. Wajen uku ya fita, har ya dauki hanyar garinsu hansatu, sai wayarsa tai k’ara ya d’aga ake sanar mai hajiya ba lafiya. Kan motarya juya ya tafi gidan nasu. Yana shiga gidan ya tarad da su zainab na kuka saboda hajiya batasan inda kanta yake ba sakamakon ciwon cikin da take ga amai kamar zata b’arar da kayan cikinta, wanda har suma sai da tayi. Nan ya shiga k’ok’arin kai hajiyar asibiti, aka kaita ana zuwa aka bata gado, babu inda kanta yake wannan dalilin ne ya d’auke mai hankali. 
Wanda ya manta ma da zuwa garinsu hansatu. 
Washegarin ranar juma’a ladi na zaune ko ajikinta, dan kojiya da yamma ta je boka ya shaida mata cewar fa auren nan ba zai tab’a yiwuwa ba, Saboda ya yi aiki akan lamarin. Wannan dalilin ya sanya ta shantake suna jira ramadan yazo
Acan kuwa bayan sakkowa daga masallaci mai unguwa da sauran ‘yan uwan baban hansatu da mutanen gari da ‘yan uwan surajo, aka d’aura auren hansatu da saurajo. 
Wanda lokacin da hansatu taji, sai ta saki ihu ta zube a k’asa ta shiga rusa kuka “shikenan na rasa ramadan.” 
Labari ne ya bazu a garin, nan da nan yakai kunnen ladi, kamar karamar mahaukaciya haka ta koma, tai gidan yakubu, yana kofar gida da jama’a ana gaisawa. Ta tsaya ta shiga zazzga mai bala’i, wani irin fada ne ya kaure tsakaninta da yakubu ta shiga surfa mai zagi 
tana aibatashi. Ko k’ala bai ce mata ba. Tunda dai bukatarsa ta biya. 
Dakyar da sud’in goshi aka kawar da ladi daga kofar gidan, ta tafl tana kuka tana surutu a hanya , kacokam! Sai ta d’ora lefin kan boka, “ni boka zai ha’inta, ni zai ciwa mutunci, ni zaiwa kafar baya, duk ya gama karbe kudadena, ashe shi nan yasan abin ba zai yiwuba.” 
Kamar wata mai almatsutsai haka take tafiya tana magana, babu inda ta zarce sai gidan boka, tana zuwa ta shiga cikin kuka ta ce “dama karya ka zuba min cewa auren nan ba za ai da surajo ba, amma gashi can auren an d’aura da surajo, gashi kayi min asara. Ba zan yafe maka ba, azzalumi.” 
“Ke gafalalliya, ya nuna ta da yatsa an gaya miki cewa koyaushe aikin keci ne? saboda ke butulu ce duk ayyukan da nai miki a baya kin manta ko, za ki san wa kika nuna da yatsa, saina illata rayuwarki. ” ’ 
Cikin fushi ta d’au Wani dutse ta saita ta narka a kan wata tukunya. “Sai na lalata tsafinka 
mushriki.” 
Nan fa tukunyar ta fashe, wasu irin bakaken tsuntsaye ne suka fito fuuuuuu daga ciki, boka ya kyalkyale da dariya “za ki san cewa ni mugu ne.” 
Baibayeta tauntsayen nan sukai, sukai ta cakarta afuska ta shiga ihu tana karewa da hannu, wanda hannunma sukai ta cakarsa, sai da ta galabaita sannan tsuntsayen suka bar wajen. Dak’yar ta kai kanta gida duk uban tafiya da nisan wajen.Bayan ta rufe fuskarta da 
mayafl. 
Tana zuwa gida ta shiga bandaki dan tai fusari har lokaci tana dage da fuskarta da jini ke tsatstsafowa wajen da suka caketa,jitai kamar an doka mata guduma akanta, sai ta zube ji kake tim! daga nan ba ta sake sanin inda kanta yake ba. 
Ramadan kuwa, sai wajen karfe biyu ya samu kansa, bayan hajiya ta dawo hayyacinta, cikin nata ya lafa, hakan ya sanya ya koma gida ya yi wanka ya sanya k’ananun kaya ya tafi. Sai wajen hudu ya je garin. 
Direct gidan kawulle yaje, akace kawulle baya nan. Ashe kuwa yana cikin gida kunyar Ramadan d’in ya keji, saboda bai san mai zaice mai ba. 
Daga nan ya karasa gidan baban hansatu, yana zuwa shi kuma uban na fitowa, suka gaisa, kafin yayi magana uban yace “ni mahaifin hansatu na d’aura mata aure yau, dan haka dan Allah kayi hakuri. Yau da ace babu sanya ranarwani akanta dana baka ita. Daman matar mutum kabarinsa. Allah ya hadaka da rabonka. 
Yaudararka kawai hatsabibiyar uwarta tayi tace maka auren dole zan mata, wanda sharri kawai ta yi min kuma bata samu nasara ba. Domin kaima kaso tafka babban kuskureduk 
dana san cewa kasan hanyar da kuka biyo bai yi ba. Nan sukai sallama ya shiga mota. 
Wani irin jiri ne yaji yana dibarsa kawai sai yaja motar yabar garin. 
Al’amarin ladi kuwa, sai da uwale ta shiga gidan tambayarta kan abinda ke faruwa gaske ne ko karya, dan taji an daura aure da surajo, kiran sunanta ta shiga yi ta ji shiru. Allah ne ya kaita har kofar bandaki ta kwankwasa kofa shiru, sai ta ga alamin zaninta ta kasa sai ta tura, ganin ladi ayashe ya sanya ta fasa ihu, ta fita waje tai kuwwa aka taru aka fito da ladi, wacce sai da tajima ta farfado, ga fuska tai suntum duk ciwuka, amma ba ihun ba in in kuma ta dawo kamar mahaukaciya sai fusge-fusge ta ke. 
Abinka da karamin gari. Nan da nan gari ya d’auka ai ladi ta haukace dalilin an d’aura ma hansatu aure, wasu kuma suke cewa ai mugun alkba’iran da ta yi ne arayuwa ta fara girbar su yanzu. 
Wanda sai Hansatun ce ke kulawa da ita. K’arshe kawulle ya kaita gidan mai magani wanda kan kankanin lokaci ta dada tuburewa. 
(Shi sharri dan aike ne, gun wanda ya aikeshi nan yake komawa. Karshen mara tsoron Allah kenan da take gaskiya, mai bawa mushrikai damarjuya akalar rayuwarsu. Tabbas komai dadewar karya mai karyewa ce, gaskiya kuwa yado take tai rassa. Ta tsaya da kafafunta.Haka za tai ta mamaya. Da baban hansatu da surajo suka rike gaskiya gashi sunga ribarta.
Dakyar ramadan ya kai kansa gida wajen shida ya karasa direct shashinsa ya haye yayi wanka ya zauna yana tunani, bai tab’a zaton ba zai samu hansatu ba, shi kansa yasan baban hansatu ya fisu gaskiya, amma kuma saboda tarinjin in bai mallaki hansatu ba, ba zai zauna lafia ba ya sanya ya zama makaho kurma ba ya ganin duk wasu abubuwan da yake gudana. 
Dakyar ya Fito ya tafi masallaci bayan ya dawo ya zagaya inda ake karin gini yaga sunyi nisa sosai, dan zasu iya fara flasta gobe, girgiza kai kawai yayi ya koma cikin gidan. Matan nasa kuwa sam ba su lura da canjin nasa ba saboda sun san yana busy. 
Washegari da yake ladifa ce da girki tana bangaren ramadan tana getta mai shi, filo ta 
dauka tana d’an matsa su dan su tashi, hakan yasanya taji kululu a daya, sai ta tsaya ta zuge zip ta bud’e ta sanya hannunta ta tab’o abin, ta zaro sai ta ga wata k’wandaleliyar laya,jikinta ya hau bari, ta fita da sauri ta samu wuka ta yanke zaren jiki ta bude, rubutu ne ta gani wasu da hausa wasu da ajami da larabci, baro-baro ta ga sunan ramadan har sau bakwai, ta ga sunan hansatu a kasa, jinjina kai ta yi ta fito da sauri ta yi k’asa, ta shiga kitchen ta zuba kalanzir ta ketta ashana Iayar ta kone. Ta bar wajen da al’ajabi lalle! dan adam sai abarashi, mutum na zaune bonono baisan mai yake ciki ba, tabbas sunyi sakaci sosai.Ba ta gaya wa kowa ba, ta ci gaba da addu’ion inta da take yi kullum babu fashi rana 
dare. Bayan kwana biyu. 
Ta b’angaren ramadan ji yayi kamar an cire mai kaya, tun bayan da ladifa ta kona Iayar nan. Abinda ya daure ma su laila kai shine ma ganin an tsaya da aikin da ake yi da aka faro gadan~gadan . 
Sosai ta bangaren ramadan ya bar maganar hansatu. Shi kansa akaran kansa sonta da ya keji yanai mata duk sai yaji yayi sanyi, yakan kwana biyu bai tuno taba ma. A hankali a hankali kuma ya manta. 
Ganin haka ya sanya Lad’ifa ta tambayeshi.suna breakfast tace ya “maganarka da hansatu ne?.” Sai da yayi jim! yace “wai hansatu ‘yar aikinku?.” Ai”Tayi aure kinsan dama tana da wanda za ta aura. Allah beyi dani ba.” “Ikon Allah. Allah bai yi matarka ba ce.” Tsaki yayi ya mike dan baisan maganar yace “zancen kike so.” Sunkuyawa da fuskarta tai kasa ta fasa dariya tace “ango, ango na hansatu.” Murmushi yayi yace “zan kamaki ne.” ya fice. 
Daidai lokacin laila ta shigo falon ta ce “maman fuad dariyar me kike yi ne?.” Sai ta ce “hmm ina girmama ikon Allah ne yanda abubuwa sukaita faruwa a gidan nan gadan gadan musamman auren zauji da hansatu, sai gashi wai an daura mata aure da asalin wanda dama dasa rana atsakaninsu.” 
Ai kuwa Wani guda laila ta sanya tace “Allah nawa, kai masha Allah! wannan abu yayi, shi’isa kwana biyu komai ya lafa, amma fa yau da karamin party agidan nan, bari ma kiga.” 
Sai tai wajenta da sauri. Lad’ifa ta jinjina kai tare da binta da kallo, karshe tai samanta 


HmM anya ramadan zai haqura kuwa

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE