NAYI GUDUN GARA CHAPTER 36
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 36
Ramadan bai samu ya kira safna ba, har sai daya fita zuwa sallahr tarawi, ya tsaya ya kira, ta dade tana ring, safna tai burus taki dauka . Sai ya hakura ya tafi. Bayan an sauko ya kuma kira, tana ring sai da tai sau uku ta dauka a cunkune,ta gaidashi, yace “kiyi hak’uri safna dazu bana kusa da wayar ne.”
Tabe baki tai dan tasan ba zai wuce matan sa ba, sai ta basar tace “ai na gode kawai, saida ya lallabata, sannan ta hakura, sukai hira suka rabu.
Haka al’amura sukai ta tafiya kwata-kwata ramadan ya canja akalar komai, ba ya taba waya agaban matansa, ko zai kira safna sai dai ya kirata idan ya fita da dare k0 wajen aiki. Hakan itama ba ta taba kiransa yana gida. Domin ba taso ta faso tun yanzu, matansa su ga lagonta. Haka watan azumi yayi ta tafiya al’amura nata tafiya, mutane nata ibada har
aka kai da an ajje azumi wato anga watan sallah. Anyi shagulgulan sallah da dama har sallahr ta wuce.
Bayan sallah da sati uku ramadan ya fara karasa ginin da ya fara tun lokacin hansatu. Sudai matansa sai ido kowacce da abinda take sakawa. Wata rana laila ta tambayeshi yake sanar mata cewar ai hajiyar sa yake tunanin zai dawo da ita, nan duk ya bagarar dasu basu kawo komai ba, amma dai Ladifa ta so fahimtar wani abu sai ta zubawa sarautar Allah ido
BRYAN WATA BIYU.
Ramadan ya gana da iyayen safna. Lokacin da hajiya ta ji labarin zai kara aure, wato lokacin da yaje ya nemi shawararta ta ce “kai yanzu ramadan wai wannan aure -auren na meye ne kake yi haka? Sai kace wanda bai da mafadi haba. Kamar wanda akai mai gorin aure aure?.
Shiru yayi yace “babu komai hajiya kawai dai.” Tsai tai tana tunani karshe tace “to Allah yasa ai a sa.”
Wannan dalilin ya sanya babu bata lokacin aka sanya a rana, nan da wata d’aya . Kwana biyu kuma duk sai ya shiga fargabar yanda zai sanar da matansa ko Lad’ifa, da yake ganinta mai dan dama -dama ya kasa gaya mata, dan baisan tashin hankalin da laila zata yi ba, karshe ya barwa cikinsa ba zai fada musu ba, har a d’aura aure.
Lokacin da abdallah abokinsa yaji ya kalleshi yace “gaskiya abokina kana ,,,,,, baka san cewa mata uku gobara ba.”
“Ahh babbaka ne ba gobara ba, akaina aka fara aure ne? Gidaje nawa ne za kaje kaga mata
hud’u ko uku, kai da wuya kaga gidan iyayenmu da kakanninu masu mata daya, daga biyu
sai uku zuwa hud’u. Dan dai nazo a d’an zamani sai a saka min ido. Allah ne fa ya horemin abin nan, ba haramun bane ba fa.” “
An san da haka, amma kai abin naka fa aida mamaki, ko shekara biyar bakai da auren fari ba, amma gashi zakai mata uku.”
Dariya ramadan yayi yace “ko za ahana ni ne
Dariya ya yi shima ya ce “ni ai dan shawara ne.”
Wata shawara ramadan ya yanke domin kuwa yana san ya shana da amaryarsa, kuma yasan da wuya a wanye lafiya da laila. Hakan ya sanya ya ware wasu kudi yayi tunanin biya musu umara.Da wannan tunanin ya tsaida matsaya.
Tarasu yayi dan yaji ta bakinsu, “Nayi tunanin biya muku umara ne,” dan kallon juna laila da ladifa sukai, suka yi murmushi saboda tsabarjin dadi.
“To ta sati uku kuke so ko biyu?!’ Ya fada yana dubansu yana addu’ar Allah yasanya suce uku, laila ta ce mudai ta ukun muke so, ko ya kika gani Lad’ifa.”
ladifa tai murmushi tace “tayi sosai ma kai, amma mungode wallahi burina kenan naje naga kabarin shugaba sayyadina rasulilllah SAW. Wallahi mun gode Allah ya kara budi da zaman lafiya.” Suka ce amin.
“lnsha Allahu gobe zamuje ai muku passport.” nan duk suka amsa aranar kwanan dadi sukai sai murna suke, da safe sukaje dan ai musu passport. Sannan kuma ya shiga nemar musu visa.
Haka al’amura sukai ta Tafiya, safna dukta kanainaye ramadan.Ba shi da wani tunani da buri sai nata.
A b’angare d’aya kuma ramadan na ta karasa gini a hankali wanda saura kad’an a gama komai.
Ana i saura sati d’aya tafiyarsu, laila ta kai najwa gidan mamanta, dan lokacin satin yarinyar biyu da yaye. duk shirin tafiya sun gama shi, Har ranar tafiyarsu tazo inda suka
daga kasa mai tsarki. Ankai kayan lefen safna lokacin da masu kaiwar suka tafi maman safna ta fito tsakar gida ta
ce “ayerrrrrrrrrri! Yarinya mai goshi, kin tafi kin barsu, kin dawo suna nan, haka za ki kuma tafiya ki barsu.” Ta fada tare da kallon shashin da matan gidan ke aikace-aikace.
Mama rukayya dake gefen rijiya tana yanka kabewa ta tab’e, baki tace “da wani auren ai gwara zaman, ai wallahi da auren da tai na wata uku an sakota gwanda yarana suyi ta zama ba mijin.“
Maman safna ta buga cinya ta ce “Aikuwa wallahi karya ne, da babbar budurwa ba gwanda
karamar bazawara ba. Yarinya mai kashin arziki, dan bakinciki sai ya mutu anajin haushi yayana nan azube fal d’aki.
A gurgun tunaninki ba, har kike ganin da babbar budurwa gwanda karamar bazawara .Wannan ai karatun ki ne. Kuma nan na godewa Allah dani na aurar kuma ‘yata na zaune lafiya lau.”
Shewa maman safna tai ta ce “yo da wannan auren na binta bansan me zan kirashi ba, kullum mace cikin duka miji ya shawo giya yayi tatul! yazo ya narka kuma ta wanke k’afa ta zauna.”
“Eh hakan ma mungode Wa Allah. Wataran sai labari. Yoke meye ba mu sani ba a auren safnar na farko, dan an mana rufa -rufa ance wai miji madoki, karyar banza da wofl muna nan komai zai fasu, ai ramun karya kurarrene, wannan ma da ake son yi Allah yasa ya dore”
“Bakinki ya sari d’anyar kuka. Duk mugun nufin ki akan auren ‘yata wallahi, saidai ya koma kanki, nan gani nan bari sadakin ‘yar mayya.”
Haka suka zauna suna ta sakin maganganu mai kama da tone-tone, saida dayar matar ta rokesu da Allah su hakura sannan.
Ramadan duk sunyi waya dasu laila suna gaya mai sun sauka lafiya suna ibadarsu. Bai gigin sanar musu ba har suka rabu. Kwanansu hud’u da tafiya aka d’aura auren ramadan da safna. Sosai ramadan ya sakar ma safna bakin aljihu, dan duk wani hidimarta shi ya bada kud’i, hakan ya sanya safna da uwarta sukai ta d’aga kai agidan nan ‘ya tayi goshi. Sunje sunyi jere a shashin da ramadan ya gama kammala ginawa, yayi kyau a ranar dai aka
kai amarya d’akinta.
Zumudin da ramadan keyi ba,a magana sanin cewa babu kowa agidan hankalinsa a kwance babu fargaba. Shiga yayi bangaren safna, tana zaune acan cikin dakinta ya shiga, idanuwa ta dago ta kalleshi tai murmushi tajuya, sai ya samu kansa da zama agefenta yana aika mata da smiling yaye mayafin yayi ya kalleta “ina miki marhabun da zuwa gidana.”
Murmuahi tai ta ce “nagode.” Nan ramadan ya mik’e domin Allah Allaha yake ya idda nufl, musamman da turarenta daya cika d’akin, da kamshi yake shigarsa ahankali, tashi sukai suka gabatarda duk abinda ya dace sallahr godiya ga Allah, suka ciyar dajunansu.
Nan kuma ramadan yajuya akalarsa kacokam! kan safna take dan tsoro ya shigeshi sakamakon tuno daren farkon laila. Sai yaji dari -dari kar itama ya kasance cewa cuko tayi. Amma a yayinda ya nutsa cikin tafkin kogin duniyarta sai yaga natural ce ba cuko, hakan ya dada d’imauta shi, musamman da yayi tozali da manyan burikansa. Cikin yanayi mai wuyar fasasaruwa suka shiga duniyar ma’aurata.
Sosai ramadan ya wadatu da abinda ya dad’e yana muradi. Sai da komai ya lafa suka dawo nutsuwa. Ramadan sai sakin murmushi yake. Sai daya kuma komawa ruwa saboda nishadin bai isheshi ba. Abubuwan da yakewa naci ya same su available musamman ita
kanta safnar data gane yana sonsu,sai ta dada karamar kwarin gwiwa.
Da safe da kansa ya zabarwa safna kayan da zata sanya, ita kuma hakan ke wani dad’a fasa kanta, yanda yake wani nan nan da ita, takejin takai macen da za a sota, riga da ya bata ta sanya irin body hug din nan, haka ta sanya ta duk inda tai idon ramadan na kanta musaman yanda take tafiya kai shi yama godewa Allah da ya sanya yayi tunanin kai su laila umara.
Aranar haka ramadan ya yini nane a shashin safna, awannan ranarta fahimci cewa ba matukar kyau jikinta kema mijin nata ba, hakan ya sata yi ta shigar kaya masu fidda sura.
Amarci yake kwasa son ransa. Duk da cewa ba fin matansa tai ba, shi kad’ai yasan bambance bambancen dake tsakanin matan nasa.Amma kasancewarta mace mai structure da yake so ga mace, ya ke samun nishadi atare da ita sosai.
Da yake idonta abude yake ta kuma gane yanda jikinta ke burge mijin nata ya sanya take shigar kananan kaya kala kala, ya lafe a falonta yana binta da kallo, wani shigar ma tayi kamar ka rufe ido saboda tayi fitsara da yawa, duk tabi ta kanainaye ramadan ko nan da can bai fita, kud’i take tatsa sosai a wajensa, musamman yanda uwarta ke mata famfom yanda zata amshi kudi wurinsa har ta gina kanta, gashi bata girki sai dai su fita aci a waje, wajen sati daya kenan, sannan ramadan ya koma aiki. Ranan da zai fita kuwa kuka ta sanya na sam bata san ya fita ita tsoro haka ya shashance awajenta baije ba.
A can saudiya kuwa, ladifa da laila ibadarsu kawai suke, masaukinsu d’aya shakuwa sosai ce ta dad’a shiga tsakaninsu, komai tare su ke yi,idan suka tafi harami tun sha-d’aya na safe sai bayan sallahr isha suke dawowa,haka za suyi tayin ibadarsu.
Aduk yayinda Lad’ifa za ta ganta gaban ka’aba sai ta ji hawaye na zubo mata, takanji tsoron Allah da girmansa na dad’a kwaranya a ruhinta. Batai k’asa agwiwa wajen kai kukanta ga Allah wajen addu’a first sune iyayenta sai mijinta da ya biya mata har tazo, sai ita kanta da danta fuad da sauran yaranta da zasu zo nan gaba, sai gidanta na karuwan zaman Lafiya da ita da mijinta da kishiyarta. Babu adduar da take yi sosai irin Allah ya dada sanya kaunana aran mijinta, ta zamo mai niema agareshi kullu idan sukaje adduar ta kenan, laila ma na adduarta sosai wanda ita har addu’ar Allah karya sanya mijinta ya karo aure take.(tofah su laila manya)
Lokacin da suka cika sati biyu a can ne suka dan samu sab’ani da laila musamman duk safiya ramadan ke bugo mata waya, sai ya fara bugo mata sannan ya bugowa laila, wannan abin shi yake dada ba ta haushi kawai sai ladifa ta ga laila ta canja mata, a ganinta ita ce ke hana shi bugo mata da farko wanda idan ita ta buga mai suna fara waya zai ce abawa Lad’ifa .
Sai ta daina tafiya tare da Lad’ifa ta samu wasu dake kusa da room na su suke tafiya, ladifa dai ba tai magana ba saboda ita ba tasan me tayi mata ba, kawai sai ta kyaleta take tafiya daban.
Sai dai ta ga laila awajen dawafl, in tai mata magana ta amsa a ciki -ciki, akwai lokacinda laila ke dawafi wani ya take hijab dinta, ga matsatsi ta rasa yanda zatai idan tace za ta sunkuya akan bi ta kanta. Ladifa da ke bayanta sai tai sauri ta dan tsarga gaban hijab din kadan, haka ya sanya ta samu ta janyoshi, ta samu ta dawo daidai.
Sai tajuya ta ga waya taimaketa, sai sukai ido biyu da Lad’ifa, ta riketa gam tana “sister nagode,” idonta har na kawo ruwa saboda tsabar matsar data sha.
Tun daga nan suka dawo daidai, anan lokacin kuma laila ke bawa ladifa hakuri akan irin sharetan da tai, murmushi kawai laila tai tace “babu komai dama rayuwa haka ta gada.”
Ramdan na zaune yana shan bakin shayi, ranar weekend ce yana gida da waya ahannunsa ya kirawo Lad’ifa ta d’auka . Sanyin muryartane ya dake shi nan yaji kamar an kwaronyomai da ruwan sanyi, yace “ya ibada baby.” ta amsa da laflya.
“gaskiya ina missing dinki sosai,” dariya tai tace “ai karshen satin nan zamu dawo..” To Allah ya kaimu. “Ina maman najwa?.”
Adaidai lokacin laila ta fito daga wanka. Ladifa ta mik’a mata. Suka gaisa take tambayarshi, najwa na kuka yace ai yaje ya ganta ta sake ba ta kuka sosai. Alokacin safna ta fito sanye da wata red din gwan irin mai jikin robber din nan, mai fito da kusfa kusfarsurar mutum, ta dososhi tana tafiyar nan tata kamar tana girgiza jiki. Murmushi ramadan yayi ya mik’a mata hannu, ta karaso ta shigejikinsa yana bin ko’ina najikinta da kallo.
Sallama sukai da laila, wanda kafin ta katse taji kamar maganar mace, saidai bata kawo komai ba suka rabu. Nan ya maida hankalinsa kacakam kan safna yana ta zuzuta irin kyan da rigar ta yi mata, murmushi kawai take musammn ganin yanda ya kasa d’auke idonsa daga jikinta.
Adan zaman da tai da shi ta kula amatansa yana ambatar ladifa sosai, hakan yasanya tunkan ta ganta takejin haushinta, taga da alama yana sonta sosai.Tabe baki tai. Bayan ta dawo daga dan karamin tunanin.
Haka kawai ramadan ya tsiri sanyata aiki, dauko min kaza, miko min kaza, dukdan ya sha kallo, ita kuma da ta fahimci hakan duk sai ta kuma canja salon tafiya.
Weekend yakan dan fita amma tunda safna tazo gidan indai weekend ce ko nan da can
bai fita, sai dai tai mai duk irin shigar da yake so yayi ta kallonta yana jin dadi . Dan dakansa yaje ya siyo mata kananun kaya kala -kala yajibgesu duk dan ta sanya. Bata fiya bude kanta ba musammam ta kula yana son gashi, ita kuma bata da shi sai dai tai style na dauri abinta.
Yau suna dakinta saboda lokacin kwanciya yayi ta sanya sleeping dress din da ita za ace gwanda babu. Lokacin da ramadan yace ta kawo mai dauke sai tajuya, yace “ya hakan?!‘
Dariya tai saboda tasan ba zai taba iya bacci ba, tare da ya dangana da abubuwan da yake mayen so ba. Lumshe lumsassun mitsi-mitsin idanta tayi tace “yau wasan na kudi ne inji dumus! Kawai.“ Ta fada tana dariya.
Bai kawo komai ba yace dan wannan, nawa kike bukata, ya fad’a yana nanikarta. Tace “20k”
A kunnenta ya fada yace “kamar ke 20k ai tayi kadan saidai 30k,” “To inji alert.”
Mirmushi yayi dan shi a tunaninsa duk wasan masoyane, saida ya tura mata alokacin ta transfer sannan ta maida hankalinta kansa shi kuma ya tsumu da muradin ransa.
Yau lahadi su laila ke dawowa tun da asuba sukai mai yawa kan zuwa lsha za su karaso 9ja. Hakan ya sanya ramadan keta karakaina. Yanda safna ta ga ramadan na rawarjiki, yasanya ta shiga tsaki tana tunanin cewa lallai da aiki a gabanta. Saida ta daidai ci d’aya ta kusa kawai ta langwabe cikinta na ciwo, nan fa hankalinsa ya tashi dan baisan abinda zai taba safna, sai ya tafi kaita asibiiti, wanda alokacin kumajirgin su Lad’ifa ya sauka, suka fito suka zauna a reception zaman jiransa.
Suna asibitin, safna duk da tasan babu abinda ke damunta, amma ta dage za taga likita, duk dan karyaje, dauko su lad’ifa ne.”
Kiran laila neya shigo wayar, sai ya tashi ya kalli safna ya ce “bari yaje ya dawo Zai d’auko su, ya ce taga likitan kan ya dawo, tsaki tai dan ya kwafsa mata ba haka taso ba amma babu komai.
Direct airport ya tafl ya d’auko su bai san yayi missing matan nasa sosai ba sai yanzu daya gansu. Yana ajje su maigadi yayi musu barka da dawowa ya shigar da jakunkuna, sudai sunga dan canji a felon kasa, sai babu wacce ta damu suka yi bangarensa .
Shi kuma ya koma asibitin safan ta ci ka tai fam! hakuri ya shiga ba ta, ta hade rai tace “muje to.”
Kamar wani mai tsoronta ya jata suka tafi
Suna zuwa ta zube a falo dan tasan matansa sun dawo. Shashinta tayi dan tai wanka dan zafi takeji.
Ramadan direct wajen Lad’ifa yayi lokacin ta fito daga wanka, wanda har kanta ta wanke ta fito yana digar ruwa a bakin kofa ya tsaya yana kallonta zama tai a bakin gado tace “ya dai zauji i missi you fa.”
Ya taka ya zauna gefenta ya ce “kinsan wani abune?ji na yi kamar wani shashina ya dawo. ” Sai tai murmushi tace “abu fuad kenan.”
Jin ankira sallah ya mike yana murmushi ya shiga b’angaren laila, ita ta riga har ta sanya kaya. Jikinsa ta fad’a tana cewa “ai fushi nake dakai,” yace “me nayi?.”
“Ai kafi ni sani, shine acan ba ka taba bugon waya da farko ba, har sai ka fara bugawa Lad’ifa matar so.”
“0h! laila, korafi itace gaba da ke a gidan a auratayya, kinga babu damuwa dan hakan ta faru.”
Sai tai danyi yake “hakane kuma fa.” Fita yayi ya haye sama dan yayi wanka, dan wani irin zafi ake bugawa na
Safna kuwa tana wajenta tana kalkale -kalkale, so take ta futowa da kishiyoyinta a karon farko su ganta a kasaitacciya.
Riga da siket ta sanya na atampha ta sanya, sun kamata sosai! dan rigar ma yanayin yanda akayita irin tabi yanda shape din west dinta yake, hakan ya dada sanyawa faffadan kugunta ya Fito sosai! ko’ina tsam tsam! saman kirjinta harta saman rigar suka samu mazauni, ta kafa d’auri ita kanta tasan ta burge ta watsa cewgum a baki tana tauna k’as k’as! ta fito babban falo.
Ba ta dade da fitowa ba, aka kawo wuta, sai ta tashi dan ta kunna kallo, daidai lokcin laila fito. Za tai sama wajen ramadan yazo yaga tsaraba.
ldonta ne ya sauka akan safna, gage idonta tai dan dai tasan wannan ba Lad’ifa bace, tasan dai su biyu ne mata a gidan, ‘to daga ina kuma wannan ta Flto? ganin yanda take kokarin kunna tv ya sanya gaban laila ya fad’i.
‘kardai karuwa ce ramadan ya shigo da ita.Na shiga uku,” ta fada.
Ai da sauri taje gefen tv ta matsar da hannun safna tace “ke daga ina kuma kika shigo
haka??
Lumsassun shanyyyun mitsi-mitsin idanuwanta ta kafawa laila, ta saki kwan cewgum tace “tamabaya kike kome?.“
Tajuya sai kace mari babban kifi tanajuwa kugu.
Tsaki laila tayi, “Ke dan Allah idan bakuwa ce ke ki fad’a, ta yaya zaki shigowa mutane cikin gida kandai kandai kina yawo haka!!
Wannan ai salon karuwanci ne.”
Murmushi safna tai ta kalli laila akaron fako tasan cewa karta san kar ne ita da laila, musamman yanda ta ga lailar ta tsare ta da ido. Sai ta juyar da kai tare da Tabe baki tace “mai gidan bai gaya muku zai amarya bane?.”
Dam! gaban laila ya fadi, ” ke Wallahi idan ke karuwa ce ma sai kin gane kurenki, sai kinyi danasanin biyo mijina gida, ki fitar mana daga kida. Tunkan na sauke fushi na akanki?.”
“Kinga dallah! yanda kikejin ke matar gidace haka nima, dan wallahi karki sake ki shiga gonata, yanda kikejin kanki a matar ramadan daya auro ki, haka nima.”
Cikinjin takaici laila tace “Ke har kin isa ki sanya kanki a macen ramadan.”
Juyi safana tai tace “kalleni sama da kasa kinsan ina da zubin da mijinki dole ya yaba dan haka sai kin koyi runtse ido.”
Cikin matsanancin fushi dajin haushin maganar safna, laila tazo za ta tunkuda safna kanta fice musu daga gida, dan ita bata yarda cewa matar ramadan bace, tafi kawowa karuwarsa ce.
Rike hannun lailar tai tace “baki da wayo na kula, kibi a hankali dan wallahi kina ganin mijinki zai iya gagararki.” Da yake safnar ce ta saitin da bene yake, ita taga alamun fitowarsa, ai da sauri ta saki hannun laila ta fasa kuka ta durkusa “wayyo cikina.”
Zaro ido laila tai na ganin makirci da rana tsaka, ai da sauri Ramadan ya sauko yace “safna meye‘Cikin muryar kuka hade da kissa ta makirci tace “matarka, ina zaman zamana afalo, tazo ta ganni sai ta shiga surfan zagi ta uwa ta uba. Wai ni karuwa ce na shigo gidan nan ka ajiyeni saina fita. Kawai dan nai mata magana me yasanya take haka. ban aune ba naji ta
kaimin duka acikina.” Ta karashe da shashshk,ar kuka.
Huci ramadan ya tsiri yi, ya kalli laila yace “kin dawo ko? to wallahi ba zan lamunta ba, yanda kike macen aure awajena haka take ,to ki shiga hankalinki.”
Adiadai lokacin Lad’ifa ta sauko ta karaso ta tsaya.
“Kuma ki saurara kiji, daga yau karna kara ganin kince zaki dakar min mata.if not zaki sha
mamaki.”. Cikin fushi mai hade da tarin takaici laila tace “yanzu irin abinda kaimana kenan.?.”
Dan ita maganganunsa sam! Ba suyi tasiri akanta ba, tafi jin ciwon kara auren da yayi a boye. Sai ta juya wajen Lad’ifa tace “maman fuad ki gani fa, ashe! aure yayi shi’isa ya turamu umara.”
Ita kanta Ladifa abin yazo mata a ba zata, sai tajuya ta kalli safna dake ta wani rangwada tana gantsara kirji gaba shi kuma duk ya wani susuce, hannunsa na bisa kugunta.
Sai ta maida kanta wajen laila ta ce “maman najwa bangane fa mai kike cewa ne”
Tabe baki safna tai ta wuce tanajuya jiki hade da girgiza ta wuce shashinta. Ramadan yabi ta da ido har ta kure
“Abinda na gaya miki kenan ladifa, aure yayi.” Ta fada tare da zama kan kujera ta dafe kai.
Wani bakinciki ne ya tokare wuyan ladifa ta kalleshi ta banka mai harara tace “yanzu zauji yaci ace kai aure baka gaya mana ba, wa zai hana ka auren.?.”
Zama yai yace ta zauna “please kuyi hakuri, nayi hakanne saboda samun zaman lafiya .”
LaiIa tace “ba wani zaman lafiya, wannan abinda kai shine babban kuskure domin gwanda ace mun sani, amma wallahi ka sani ka dauko hanyar rashin zaman lafiya dani.” Ta fada tare da barin wajen.”
Ladifa na ganin hakan ita ma ta mike tace “Aurenka na biyu ni ban hanaka ba, wanda har kwarin giwwata na baka, ace sai wanda zakai na uku, ace na kasa baka kwarin gwiwa, gwanda ace ka fada da ka boye mana, daga dawowarmu mu taradda abin mamaki. lnai maka fatan Alheri Allah ya baku zaman lafiya.”
Sai ta girgiza kai kawai ta juya, da sauri ya ruko hannunta, ta kalleshi cikin ido da wannan kallo da zarar tayi masa take sanyawa yaji duk baya jin dad’i, hannunta ta fusge tai samanta duk da tasan kamar laila akaiwa kishiyar, amma dole itama abin zai bata
ranta.Musamman ta yanda salon auren yazo
Dafe goshi yayi yace “oh god! Matsala,” nan yaji kansa na ciwo, kallon gefen laila yayi ya kalli na safna ya kalli na ladifa
Hmm lallai ramadan da alamun ya debo ruwan dafa kansa