NAYI GUDUN GARA CHAPTER 37
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 37
Lalla na shlga d’aklnta ta zauna ta shlga raira kuka, ace Ita za ai wa kishiya! Abar da take gudu gashi gaba da baya tana da ita. Kishiyar ma a b’oye. Ta tsani kishiya ko sunanta ba ta son ji, amma wai yau ita ce aka yiwa. Lad’ifa ma dan kawai ta zo ta sameta ne babu yanda
za tai ne, amma sam! tanajin ba za ta iya zama a gidan ramadan ba, musamman wulakancin da yayi mata gaban amaryarsa. Wani irin haushin ramadan ne da kishin yanda amaryarsa ke wani gantsara agabansa shi kuma ya susuce agabanta ya tokare wuyanta, dan ji take ko ganinsa ba ta son sake yi, da sauri ta shiga had’a kayanta, dan ba za ta iya ci gaba da zama agidansa ba, dan za ta iya murgud‘e kugun amaryarsa in ta shi ga gonar ta, domin abinda yake mata ya kai intaha, yayi aure bai sanar da su ba, ga kuma salon wulak’anci.
Lad’ifa kuwa na shiga shashenta ta kwanta tai rubda ciki, babu abinda ke yawo a zuciyarta sai abinda ta gani kuma ya faru, da ta runtse ido safna take hangowa ajikin ramadan da yanda ya rik’e kugun safnar. Wani irin kishi ne ya k’ume zuciyarta, kishin da ko lokacin da ya auro laila ba ta tab’ajinsa be, me mijinta ke san maida kansa ne wai? Komai aure, ramadan ya fara ba ta haushi wai meke damunsa ne? duk k’ok’arinsu, amma shi ko a
jikinsa, sai ta runtse ido zuciyarta na k’una.
Safna kuwa tana shiga d’aki ta zube a gefen gadonta, ta tallafe hab’a meye dalilin da ya sanya ramadan bai sanar da matansa zai k’ara aure ba, ita ba ta so akace sun fara ‘yar haka da matansa ba. Kawai sai ta saki tsaki. Tare da tab’e baki alamar abin bai wani dad’ata da k’asa ba.
Shi kuwa gama da fe kansa da yayi yana jin kan na ciwo sosai, Mik’ewa yayi kawai ya doshi wajen Lad‘ifa domin yasan idan ya shawo kanta yasan ya samu sauki. Tura falonta yayi babu kowa sai k’arar fltar Ac na aiki, hakan ya sanya shi yin cikin d’akin nata. Tana kwance kanta ba d’ankwali sai iska da ke kad’a gashin nata, ba bacci take ba amma tana jin shigowarsa.
“Lad’ifa tashi muyi magana,” amma ko waigowa ba tai ba. Ta saitinta ya tsaya yaga dai
baccin take, hakan ya sanya ya d’an zauna.” Lad’ifa ki tashi mi magana, ya fad’a da d’an kaushin murya.”
Runtse ido tai ta bud’e, da damararta shi dan ko babu komai mijinta ne bai dace ta
shareshi ba,duk da irin lefln da yayi mata.
A hankali ta mike ta ja baya ta zauna ta dau d’an kwali ta d’aure kanta. Ba ta kalle shi ba tace “naam.”
Tashi yayi ya dawo inda take ya zauna ya ce “baby na san na yi miki laifi am so sorry nasan
ke mai fahimta ta ce, za ki gane dalili.”
“Abu fuad.Ni mace ce mai kishi akan abinda na ke so, ina kishinka sosai, nima mutum ce fa,
kodan ka ga ba na nunawa shine kawai kake yin abinda kaga dama saboda kasan zan
hakuri na kauda kai. To wallahi Ina ga babu wacce ke kishinka kamar ni, da za ka bude zuciyata kirjina ka ga irin yanda na keji da kana sassautawa. Allah shi ya halatta maka auren mata hud’u duk mace mai hankali ba za tai ya ki da hakan ba, ba kuma wai dan ba ta
San mijinta ba ne aa sai dai biyayya ga umarnin Allah.
Sai ta girgiza kai. Banji dadin boye aurenka ba, alaokacin da zakai min kishiya na baka kwarin gwiwa ballantana kuma yanzu da muke mu biyu za kai ta uku. Kaban mamaki
gaskiya sai na kejin wani iri a duniyata.”
Wani iri ya ji a ransa ta bashi da sauri ya rike hannunta ya ce sorry habibbty afuwan nasan
nayi laifi. Ke ce farin cikina ko kinsan kika juyan baya ba zan shara ba.” Hmm! Tace kawai tai ta koma ta kwanta tace “ni bacci na keji.” “Ba ki ce komai ba.”
Ba ta kara magana ba ta kuma rufe ido.
Jin k’arar kamar ana son bud’e get ne ya tashi ya lek’a ta taga da kansa, sai ya ga laila na k‘ok’arin shiga mota,komawa ta yi dan ta d‘auko jakarta, da dan sauri ya fita ya shiga tsallake step.
Alokacin ta fito ta kulle k’ofa ta zo zata wuce ta ji ya tsaida ita, ta juyo ta ce “me zan maka,
tunda ni banda k’ima da daraja a idonka. Duk shararka akaina kakejuyeta.”
“Please laila wai meya sa ba za ki hak’uri bane. Ba dan in b’a ta ranku na yi ba, kawai dan
zaman laflya ne.”
“Da ace kasan ciwon da mace keji yayinda mijinta yayi aure ba tare da ta sani ba da bakai ba, amma da yawa-yawan maza sukan amfani da son rayukansu ne. ba sa duba rayukan da ke karkashinsu, wanda sunsan cewa dole suji ba dad’i , wallahi ya fi ace ka gaya min zakai aure akan wannan salon da kai.” Rik’eta yayi ta fusge hannunta, “ni ka rabu da ni na gama aurenka, ka je ka zauna da matar
so amaryarka.” Tana fad’a ta yi hanyar waje. “Binta ya yi, ya ce “laila ban ba ki izinin fita ba, ba da yawu na kika fita ba.”
Juyowa tai ta banka mai harara ta fad’a mota da sauri ta tasheta, ta yi hon maigadi ya fito
daga d’an d’akinsa ya bud‘e ta fita a fusace. “Matsala.”
Ya fada.” shi yana tunanin ya gujewa tashin hankali da haukan kishi na laila, to baisan wata jalalar ya tado da ita ba, gashi ta shafi har Lad’ifarsa ta yi fushi, wanda sai yanzu k’wak’walwarsa ke circulation, tabbas da ace ya sanar da su da yasan ladifa ba za ta zam! Cikin masu fushi da shi ba, tunda yasan za ta goya mai baya. Sai yanzu kuskuren da ya tafka
ya shiga jin bai dede ba.
Duk da haka ba zai bi laila ba, yanda ta fice ta dawo da kanta. Komawa d’akin Lad’ifa ya yi, ya tura k’ofar falon zai shiga yaji gam! Gam! ta rufe k’ofar.
Kamar wanda akaiwa duka ya juya ya ya sauka ya shiga shashen safna, yana ganinta yayi Murmushi ya zauna agefenta, sai ta kalleshi da lumsassun idanuwanta, ta ce “ashe ba ka gayawa matanka ba aurenmu?.”
Hannu ya d’aga mata, “babu ruwanki a ciki please.” Sai ta dan tab’e baki ta ce “kunfi kusa”
Anan shashenta ya zauna. Duk ta mantar da shi wani damuwa, da nata irin salon. Da yamma bayan ramadan ya flta, lokacin Lad’ifa ta gama baccinta ta fito ta sauko k’asa, dan ita ta ma manta da Amaryar ramadan. Kitchen dinta ta bud’e yayi d’an k’ura ta shiga gyara shi. Ta gama gogegogenta ta d’ora, girki, sai ta fita shashen laila ta ga arufe to fah! ta
fad’a. ‘kodai fita tai sai ta zauna agefen kujera.
Sallamar zainab ce k’anwar ramadan ya d’an sa ladifa ta dago kanta, da d’anta a hannunta
ta shiga ciki, murmushi ta yi ladifa ta tare ta tace “sannu da zuwa zainab ta zauna agefe.
Ruwa mai sanyi ladifa ta d’auko mata ita kuma tai mata sannu da zuwa na dawowa daga umara.
“Daman na je gidane yaul sai d’azu ina gidan yaya yaima hajiya waya kundawo shine tace
na biyo nai muku sannu da zuwa. Da ai da fuad za mu zo ya ganki.”
Murmushi Lad‘ifa tai ta ce “gaskiya na yi missing fuad.”
Zainab ta ce “aishi wasansa ya ke ma kamarya manta ki.”
Ta kalli shashen laila. “Ina kuwa maman najwa.
“Wallahi kinga shashenta arufe ya ke, bansan daliliba. Ina ga ko tafi ta.” Zainab ta ce “ina amarya Safna?.”
Ta dan kalleta ta ce “ai munyi fushi da ku shine yayanku zai amarya ko ku muji, sai da muka
dawo muka ganta.”
Rike baki zainab tai tace “ikon Allah wai! Ashe! daman yaya bai gaya muku ba? mu duk mun d’auka kun sani cabd’i lalle! yaya na wani aiki. Gaskiya yaya baiso zama laflya ba.” Hmm kawai Lad’ifa ta ce.
Alokacin safna ta fito, tana ganin bakuwa sai ta dan washe baki na bagararwa da iya siyasa,
ta zauna gefen kujera “bakuwa mukai?!‘
Ta kalli ladifa, dan ita ba ta san cewa itace ladifar ba. Kallonta ladifa tai ta ce E! Kanwar ramadan ce.”
“Ah! Ashe kanwar mu ce. To sannu da zuwa.”
Zainab ta kalleta da ya ba kirkinta ta ce “amarya ya bakunta? ta amsa tare da tashi tai ciki
ta ce “to ni ina aiki ne tai ciki.
Nan zainab tai kokarin taflya, ladifa ta ba ta tsaraba ta tafi. Zainab na fita sai ta bugawa hajiya waya ta ce “hajiya kinsan me? ashe yaya bai gayawa su maman fuad zai yi aure ba,
ashe ba su sani ba sai yau da suka dawo.”
Sallalami hajiya ta shiga yi “me ya samu yaron nan ne wai? kyaleshi zaizo ya sameni ne
wannan tab’argaza haka. Sallama sukai.
Ladifa kuwa bayan fitar zainab ta buga wayar laila tana ring lokacin tana gefen hajiya tana kuka.
Ladifa ta ce laila naga shashinki arufe bakya nan ne? Ina so baki jakar ki ne.”
Laila da idonta ya kumbura saboda kuka ta ce “ina nan gidanmu na bar auren ramadan, akan matarsa zai wulakantani bayan auren da yayi ba da saninmu ba.”
Ladifa ta ji wani iri ta ce hakuri za ki yi.” laila ta ce “ba za ki gane ba, zami waya anjima ta kashe.
Ladifa ta zauna ta ce “hmm lalle ta yarda ita mai hakuri ce sosai! Karyarta ma ta ce 2a ta je gida da sunan ya ji. Tabbas ramadan yayi musu ba daidai ba,jinjina kai kawai tai ta rashi tai kitchen.
Bayan kiran sallar magriba ladifa ta gama girki ta kaima ramadan can bangarensa. Ta ajje mai ta yi nata wuri ta kulle shashinta. Sai wajen takwas ya dawo sabida ya biya gurun hajiya tai mai fada sosai kan b’oye aurensa ga matansa. Hakan ya sanya ransa ya d’an b’aci sai sakin tsaki ya kejiya da yau suna neman dagula mai lissafi ya san su za su gayawa
hajiya.
Koda ya dawo dai saman ladifa ya yi, ya tabbatar dai ta kuma kulle d’akin sai ya girgiza kai yayi bangarensa. Anan ya ga kayan abincinsa. Ya zauna ya ci kad’an ya sauka ya yi shashin safna.
Da safe misalin k’arfe goma sha -daya na safe
Laila na zaune tana kuka. Umma ta ce “zancen kike so laila, tun jiya da kika zo kike min kuka, na gaya miki kan babanki ya dawo daga jigawa ki ta shi ki kama k’afa ki tafl gidanki,
dan kinsan yace karya kara ganin kinzo gida da sunan yaji.”
“Yanzu umma bayansa kike bi? Umma abinda yayi wallahi bai kyauta ba ni na gama aurensa”
“An san abinda mijinki yayi bai kyauta ba kokad’an. Ba kanki farau ba. Wasu mazan haka suke ,sun ruga sun san Allah ya basu damar k’araa aure, to babu ruwansu da yanda matansa za su shiga duk yanda su ka ga dama haka za su yi, musamman idan suna gujewa tashin hankali da za su fuskanta ga matansu. ‘
Wallahi laila idan kikaji mazan wasu, wallahi sai kinji na ki ashe! mijin marainiya ne, saboda na farko bai hanaki ci da sha ba, bai hanaki suttura ba, yana kyautata muku daidai gwargwado komai na jin dadin rayuwa daidai samunsa yana samar muku. To aikin ga da sauki, daman in dad’i yayi ma mutum yawa sai ya ce Allah kashe ni.
Wasu matan da mijinsu bai ba su sunci sunsha ba, komai su za su yi wa kansu, kuma ta nema ta dafa ya lo ya ci, in ba tai mai abinda ransa ke so ba ya jingeta, duk da irin wannan halinda da take ciki na talauci haka zai kuma karo aure, ba damuwarsa ba ce, kuma haka ta ke zaune da shi, wani namijin. za ki ga yana da kudi, amma matansa baya tsinana musu komai baya biya musu duk bukatunsu, kawai girman gidane, sai dai ya kashewa kadangarun bariki, akwai matanda suna nan su mu’amalar auratyya ma sai suyi wata uku bai shiga tsakaninsu da mijinsu ba, akullum korafim matan kenan, amma babu ruwansu, haka kuma zatai ta hakuri. Akwai macen kullum cikin haihuwa ta ke, ga yara ga miji, idan
mugu ne, ki ga mata na ta rama duk ta kare a tsaye.
Case kuwa na rashin ciyar da iyali ga wasu mazan ya fi yawa, miji baya ci da matarsa baya
iya ci da su amma yana iya aure. Ina gaya miki akwai namijin da inya shukawa matarsa tsiya sai ta ji kamar tabar duniyar.
Akwai mazan da ba su da aikin sai neman mata, kuma matarsu inma ta sani babu yanda za tai sai tai ta yi ta kunsar bakinciki. Tana bankar kuka har lokacin da Allah zai yaye mata. Ki
godewa Allah tunda na ki ma aure ya yi. Ina so ki gaya mini duk cikin matsalolin nan dana lissafo akwai na ki aciiki ne?.”
Ta fada tana kallonta. “Ni umma Ba mu da matsalar abinci da sutura, komai yana wadata mu dashi, matsalarsa fad’a ne da shi ka son karin aure, sannan bai fi ya ba da kud’in
kashewa ba”
Murmushi umma tai ta ce “duk d’an adam d’in da bai godewa Allah ba to kuwa yana tare da godewa azabarsa, ki godewa Allah da mijinki yana da iya rike ku, wata ma tana nan, ga talauci ga yawan auren da mijin ke yi kuma haka nan suke zaune suna hak’uri, ki karanta
da su dake waya fi matsala.? !
Wallahi laila rayuwa fad’i ne da ita ana so bawa ya kasance a kullum mutum mai godewa Allah. Shiisa na ce miki kiyi sana’a k0 ki nemi aiki. Duk wani matsalar rashin ba ku kudi zai
kau za kina yin hidimarki ba sai kin tambayeshi ba”
“Umma ai kowa matsalarsa ya sani. “Duk wannan misalan da na kawo miki kawai ina yi ne dan ki gane rayuwa ki gane cewa akwai fa matan da suka flki shiga matsala indai akan aurene. Wanda nake sojin hakan, ya sanyaya ranki, shi hakuri arayuwa baya tashi banza. Dubi kishiyarki ke ba yi mata ke akai ba, kuma ta hakura ta zauna dake, me ya cije ta, ni so nake ki koyi da kishiyarki, don inna
saude kullum yabonta take, adan zaman da tai daku lokacin da kika haihu.
To abinda nake san nusar da ke laila shine har abada shine ki na kallon na kasa dake, wallahi akwai macen da ita za ta samu irin mijinki to da ta yi alfahri, saboda tsabar irin
ukubar da take ciki a gidan aure.
Kisani acikin kundin maza marasa mutunci idan da za 3 duba list, to mijinki ne mai damadama domin ba lalle ma asanya shi cikin maza mugwaye ba. Shi mijinki yana amfani da son Zuciyarsa ne kuma yawan aure ha a kansa aka fara ba. Ke dai kawai ki zama ta gari duk iya wuya zai Alfahri da ke koda kuwa sai an d’au lokaci mai tsawo. Ya kamata ki ci maganin zama da shi. Irinsu da lallami ake bi da su.
To ina umartarki ki tashi ki koma gidanki, kinga wannan fitowarma da kikai ba da izininsa ba, laifl ne domin ba ki tambaye shi ba, wallahi tallahi laila babu ruwan Allah da cewarwai mijinki yayi miki laifl, wannan da ban a tsakaninku, hakkin aure da Allah ya shimfida daban, Allah zai tambayeki, dalilin fltarki ba tare da izininsa ba, to ki sani mai neman aljanna dole sai ya zama ya jure ya tarbi kowacce irin jarabawa, kisanya aranki cewa wannna shine irinjarabawarki, addua kawai ya kamata kiyi ma mijinki, irinsu addua kawai
ce za tai ladab da su da tsantsar biyayyama, tashin hankali da tarzoma sai dai ma ya dada
tunzura su, yanzu idan kika flta kika san wanda za ki aura? ki ka san wanne iri za ki kwasa
watak’il ma ki had’u da wanda yafi mijinki a shuka tsiya.
kuma ke ko tausayin wannan ‘yar taki, ba zaki ji ba, nidai ki hak’uri ki koma gidanki, tun kafin ita amaryarki tasan cewa ma kin fito dan an yota, inta gane kin yi yaji saboda ita ne, ko kin koma wallahi ta ga lagonki.
Laila tuni ta yi laushin bisajin maganganun ummanta sun shigeta, ga gajiyar taflya.
Share hawaye tai ta ce “Umma na ji abinda kika ce kuma zan koma yanzu.”
Umman ta ce mata ta tsaya ta tafi da najwa ta ce sai an kwana biyu.”
Tashi ta yi ta tafi, haka ta k’arasa gidan nasihohin mamanta nata yawo a ranta harta k’arasa gidan. Babu kowa afalon ta shiga ta bude shashenta.
Yau ramadan sai takwas ya shiga gidan. Babu kowacce a falon duk suna shashensu, wajen laila ya kalla ya tabbaar lalle ta dawo.
Sai ya doshi wajenta ya shiga tana zaune tana shan tea, kallo daya tai mai ta kauda kai,
zama yayi a gefenta,sai ta mik’e tai kitchen ta jje kofi ta flto ya ce “laila,”
Sai ta tsaya, ta juyar da kai. “Ka barni da tabon daka kunsa min tun aurenka da nai, wanda nake danasanin yinsa yanzu,” ta fada tare da shigewa dakinta ta rufo kofarta tai
kwanciyarta dan bacci ne a idonta na gajiya.
Ya dade azaune sannan ya fita yayi bangaren ladifa, ita already ma kofar arufe take duk sai
ya kasa gane kan matan masa.
Tsaki yayi ya tafi shashen safna tana zaune tana yanke farce, taci kwalliya da shigarda yafiso ta tare shi, nan duk ya manta da dukjidalin da matansa ke neman sanya shi. Bai tashi fitowa ba sai saflya.
Sai karfe goma suka fito, lokacin laila da ladifa na tsaye na zaune a falo suna hira,kalonsu
yayi ya d’anyi, ya shiga mamakin had’ewar kansu.
lta kuwa safna cikin nata salon. Ta ce “sannunku ina gajiya?.” Ta fada fuska awashe, ladifa
kawai ce ta amsa ta ce “yawwa sannu ya gajiya.” Laila ko tsaki tai ta dauke kai. Danji ta yi kishi na kona ranta yana tafarfasa zuciyarta.
Wani abun ma da gayya safana ke yi duk dan su ji haushi musamman laila da ta kula da
yanayinta. Zama yayi a kan tree seater. Safna ta zauna gefensa, yajuya yace “baby kuzo nan.” Da sauri safna ta juya a ranta ta ce ‘baby kuma hmm.‘
Laila ce ta je dayan gefensa ta zauna, sai ladifa da ma ba ta karaso wajen ba, cikin nutsuwa ta karasa ta zauna a wacce ke daga gefe, ya ce “ina son sanar muku cewa safna matata ce kamar ku, aurota na yi, ba na son tashin hankali, itama za a raba kwana da ita kamar yanda duk ake yi da, za a fara takanki ke ladifa tunda ke ce babba. Ya kuka gani kwana d’ai d’ai yayi ko biyu?.”
Babu wacce ta kalle shi ma ballan tana suyi magana, sai ladifa ce tace “yanda kace kawai.” I Murmushi yayi ya kalleta ido cikin ido, sai ta tabe baki tajuya. Safna ta ce “a maida kwana dayadaya dai yanda ba za a kwari kowa ba. “Yayi?.”
Juyawa yayi gefen laila ya ce maman najwa ba ki magana ba, acike take taf! Saura kad’an ta fashe, kanta na kan waya tana dan yin game. K0 kallonsa ba tai ba. K’arshe ma ta shi tai ta buga tsaki ta barwajen. Girgiza kai kawai yayi.
Safna na kula da yanda ramadan ke satar kallon ladifa, sai yace “ladifa kece da girki yau
gwanda afara a saiti.”
Dan yake tai ta ce “to madallah! to bari nai sama zan danyi aiki. ”
Mikewa yayi ya fita, safna ta rakashi ta dawo ta zauna. Laila ce ta kuma fitowa safna ta dago ta kalleta suka hada ido ta kauda kai. Dan gefen kujerar dake saitin hannun dama laila ta kalla taga tebur irin karamin nan na tsakiyar kujeru an mai dashi wani shashin, bayan tasan abangaren hagu yake, sai ta tashi ta gyara shi, safna ta ce “ya zaki maida shi nan? ai
yafi kyau anan.”
Laila ta ce “k0? to tun kan kizo anan yake dan Allah ki saurara.”
Safna ta ce hmmm! Nan laila ta ci gaba da abinda ta ke. Sai ta tashi ta haye saman ladifa.
Lad’ifa na tsaye tana rura wutar turaron wuta falonta, ta kalli laila ta dan juya sai ta tsaya bakin kofa ta ce “hmm maman fuad kiji ni da waccen matardan kinibibi, harda daukan teburta canja mai waje.”
Dariya ladifa tai dan ita ba ta Ma san ana kawo mata maganar wani ba, ta ce “ni na rasa ma me zance ma.”
Ni wallahi sam ba tai mini ba sai shegen san iyawa da shishshigi wai ita mai kirki,” nan ma
ladifa dariya tai ta ce “wallahi ni laila k0 maganar ma ba na sonyi”
Laila ta ce “dan Allah maman fuad kizo mu hade kai mu cusgunawa munafukar can,
wallahi ji nake kamar na mutu inna ganta.”
Dariya ladifa ta sanya domin ita tasan komai kishiya za ta zo ta gaya maka kan kishiya, to
kaima inta samu wuri za tai maka.
“maman najwa ke dai ki share kawai komai hakuri za ki , ki shiga harkokinki kawai. Idan ma
laifi ne ai ba ita tai miki ba mijinta ne.”
“Hmm ba za ki gane ba ladifa wai ke musuluma.” Nan ta yi kwafa ta fita tanajin ita fa ba
zata ragawa wannan mai kama da karuwan ba.
Da dare ramadan da zumudinsa ya dawo, sanin cewa ladifa ke da girki, amma abin mamaki kofarta a rufe sai kayan abincinsa da ta kai mai shashinsa. Da fe kai ya yi ya ce “yarinyar nan na son he ni wahala.” Sauka ya yi kasan. Duk d’akunan matan arufe. Wajen safna ne kawai a bud‘e hakan ya sanya ya shiga. Ya dan rage dare a wajenta, sannan Ya koma dakinsa ya zauna. Kallo ya tsiri yi, dan ya d’an rage mai lokaci sai kiran wayar ladifa ya ke, amma tana ring babu amsa. K’arshe ya ji ma wayar ta mutu d’if! Murmushi yayi kawai ya yi
kok’arin shirin kwanciya.
Haka zaman ya dawo. Ramadan a wajen safna kawai ya ke samun kulawa. Duk da cewa
itama wataran sai ta ce sai ya ajje mata kudi koda dubu biyar ne kan ta bashi hakkinsa. Shi fa ta fara ba shi mamaki sosai! ta yaya ace ya biya sadaki amma mace sai ka biya dan tsabar son kudi. Ga shi har lokacin ladifa da laila ba sa bi takan komai na sa, musamman laila ta fl dauka da zaf’l dan in ya dameta da magana kuka take sakawa.Gashi da kowacce da wuri take kulle kofa. Shi baisan mai ya sanya ba duk yafl damuwa da ladifa, amma ta ki ba da hanyar suyi magana. Duk da cewa da safe za tai mai komai da ya kamata duk abinda
take. Al’amuran sun d’an mai zafi sosai.( ramadan kenan yo ka hada matasan mata agida dole kanka ya dau zahi)
Yakan zauna ya shiga tunanin yaya Zai b’ullo musu ne? kodai shima ya fita harkarsu ne? Amma kuma da zararyanda ya ga suna zuba fasion agidan duk sai ya kasa hak’ura, domin laila kwalliya take zubawa( kunsan ita ma’abociyar kwalliya ce) kuma tasan yana so hakan ya sanya take yinta ta fito. Ko hasadun iza hasada sai ya yaba. Kar ladifa taji labari domin
itama ba a barta a baya ba.Ta yi kwalliyarta simple mai shiga rai duk su fito falo abu kadan
su yi dariya su tafa. Musamman idan sunga ramadan na nan.Anan ya dad’a ganewa cewa fa duk mace macece. Musamman idan kowacce ta fiddo da baiwar da Allah yayi mata. Sai yanzu da ya samu irin zubin macen da ya ke so ya gane hakan. Musamman idan suka hadu dukkansu har safnar.
Shi kuwa makwadaici duk sai ya ji yana san kebancewa da matan nasa amma abun ya faskara. Domin suna fa nuna mai suke koda amaryarsa ta fi su kyan sura to su ma suna da abinda bata dashi.
Safna kuwa na kallon duk abinda ke faruwa. Ita tai sai ta gama sanin kan gidan.
Yauma suna zaune da yake weekend ce misalin sha-biyu duk sun fice suna zaune a falo suna hira.Ladifa na sanye cikin wata atampha mai adon red da yellew ta yi kwalliya, sosai ta sanya redjambaki ta bazo gashinta da ta je tai sallon jiya ya sauka kafad’arta. Ga d’aurin da tai ture ka ga tsiya yayi mata bal’in kyau sosai atamparta haska farar fatarta. Ga fuskarta da ke annurin kyau sai kamshi ta ke. Laila kuma na sanye da shadda green dinkin riga da siket daidai jikinta. Ta baza kwalliya da daurinta.
Sai ga ramadan ya shigo gidan dan ya d’an fita ne. Idanuwansa ya kasa d’aukewa a garesu musamman lad’ifa. Ji yayi k’irjinsa na wani irin fat-fat. Takowa yayi ya zauna a kan dining. Ya kalli ladifa ya ce “please zoki hadan tea,”
laila kuwa sai ta kauda kai, mikewa ladifa tai ta isa har inda yake idonsa kafe kanta.sai yake ga kamar babu macen da ta kaita kyau a idonsa. Ga kamshin arabian perfume da ta sanya na tashi ahankali ajikinta. Gama had’a mai tayi ta mika mai ya amsa tare da hadawa da hannunta. Cirewa tai ta koma ta zauna.
Laila ya kalla ya ce maman najwa zo mana.” Ko motsawa ba tai ba dan ita har lokacin tana jin haushin kishiyar da yayi mata. Adaidai lokacin safna ta fito tana taflyar nan tata, ta jan
hankali, cikin shigar wani yadi mai rawa ajikinta.
Take annurin fuskar laila ya dauke. Nan fa hankalin ramadan ya koma kan safnar ta zauna tana wanijuyajiki. Wani murmushi yayi ‘kai godiya ga Allah daya bashi wadan nan mata.
Jin kansa yayi ya yi girma musamman in ya kallesu ya ga cewa duk mallakinsa ne.
Da murmushi akan fuskan safna tace “sannunku ‘yan uwa.’ Lad’ifa ta maida mata “yawwa dai , tace mata ya take, ta amsa lafiya.
Laila ko ko kallo safna ba ta isheta ba, ta kalli ladifa ta ce “kinsan me maman najwa, ina wannan film ta shiga bata labarin saboda itama ta kalla, sai suka fasa dariya harda kyakyatawa. Ladifa ta mike tana dariya ta ce “karki kashe ni da dariya Iaila, bari nai sama
zan yi aiki ne.” Cikin dariya laila tace “to.”
Dan da biyu tai hakan. Duk dan Safna ta ji haushi. Tabe baki safna tai ta ce azuciyarta’za ku
gane baku da wayo ne.‘ Jitai ma gwanda ta koma shashenta. Mikewa safnar tai ramadan ya janyota ta zube ajikinsa yace mata akunne “beautiful.” Lumshe ido tai tace “thank you sugar na.”
Wani zabgegen tsaki laila ta sanya tana jin zuciyarta na lugude da ihu. Ta flta ta yi wajen harabar gidan. Ba dan tasan inda ta dosa ba.
Safna cikin lumshe ido ta ce “nikam ban san me naiwa matanka ba, duk ba sa wani kulani, akullum yaum nakan gaishesu amma sam! Kamar wata mujiya gara ma ladifa tana amsawa
ta kulani da sakin fuska. Amma lailar nan bansan me na tsare mata ba. ! “Karki damu ba wani abu bane kinsan kowa da yanayinsa. Dan ba ku saba ba ne.”
Mikewa tai itama tai hanyarwaje ya bi ta da ido tare da d’an zamowa daga kujerar ya
lumshe ido yana tuna al’amuran matan nasa.
Safna na fita laila na shigowa suka bangajijuna. Safna ta dawo da kafadar laila ta kalleta sama da kasa ta ce “ba ki san wacece safna ba ko? to kar kafadarki ta kara gigin tabani ‘yar
rakiyar mata kawai.”
Laila tace “see you, har ke za ki kalle ni ki ce rakiyar mata, wallahi duk abinda kikeji da shi, na wuce ki, ba dai kin auri mijina ba, to wallahi sai zaman laflya ta gagareki. Sai na nuna miki ke baki da wayo ashawo kawai.”
Mari ta bawa laila tana huci ta ce “kar bakinki ya kara kirana da karuwa domin ni ba ita bace, duk abinda kika ga ina yi dan farincikin mijina ne. Da kike cewa na auri mijinki ke ba wata kika zo kika samu ba, to wallahi idan so kike a zube fefen salon kishi sai mu bud’e dan
acikinsa na tashi na girma. Dan haka ba zai gagareni ba. Kawai ina raga wane.” Kanta rufe baki itama laila ta maida mata da marin. Ta dafe kunci sosai marin ya shigeta.
Laila bata sake magana ba ta wuce za ta shiga falon, ai da sauri safna ta bita. Kafad’arsu na gogorjuna sai ta fadi a daidai kafar laila, ta ce ash! wanda wani sai ya dauka lailar ce ta tureta, ramadan ne yajuya ya ga safna ta kalli laila ta ce “me nai miki laila? daga zuwa
wucewa za ki ture ni,wai me na tsare miki ne?.”
Tabe baki laila tai ta bar wajen, safna ta mike tana d’an karkade jikinta ta kalli ramadan tai
mai fuskar tausayi sosai wanda kowa ya kalleta zai san cewa an b’ata mata.
Ramadan ya kalle ta yace “laila,” ciikin kakkausar murya.” Tsayawa tai ta kalle shi ta ce “meye,”
Ya ce “wai meye yarinyar nan ta yi miki ne? kike neman illa tamin ita.Haka kwanaki kika
dakar mata ciki. Kishi hauka ne ehe?.” “Au kai har ka yarda da abinda ya faru?.” “Na yarda dan da ido na na gani.”
To ai shi ke nan, banda lokacin tsayawa bayani,” ta wuce. Tana aiyana irin makircin safna agaban ramadan ta nuna kamar me kirki. Amma a bayan idonsa bata da shi
Ya tashi ya bita d’akin cikin huci …..
Safna tai murmushi ta ce “kad’an ma kika gani, ni nan safna wanne irin kalar kishi da makirci ne ban iyaba. Na kula bakya san zaman lafiya amma zan maganinki ne, ta fad’a kamar lailar na wajen.
Adaidai lokacin wayarta tai k’ara dake gefen kujera ta d’auka ta shige falonta mamanta ce a kan layi. Ta ce safna …….
Hmm
Ana wani abu a gidan ramadan Ga dai ramadan yabi laila ko ya zata wanye musu.
lkon Allah wai yau lalla da ladlfa ne ake shlri aka kuma gane. Hmm Allah yasa adore.
Ga kuma maman safna ta bugo mata waya ko me za su zanta! Akwai chakwakiya fan