NAYI GUDUN GARA CHAPTER 4

NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 4
Yau da son zuwa gidan yayarta karima ta tashi don tajima ba taji duriyarta ba, hakan ya sanya bayan gama aikinta, ta tafi d’akin mijin nata dake danna system yana wani aiki ta zauna, so take tai magana amma tanajin tsoron karya gwasaleta,dan mijin nata tamkar hawainiya haka yake. Koda yaushe cikin canjin halayya zaka same shi. 
Cikin kwantar da murya ta ce “Zauji na” Bai kalleta ba yace “yeah” Murmushi tai da alama za su sha drama ta fad’a aranta. “Dama so nake anjima kamar sha biyu zani gidan yaya karima, najima banje ba.” 
“Me ake da za ki.” Tace”Kawai zumunci.” 
Tab’e baki ya yi. Yace”Bana son yawon nan,idan zumunci ne ba ga waya ba, ki buga mata ku gaisa mana.” “Zauji!.” 
Ta ambaci sunansa da mamaki. “Ko ban fad’i daidai ba ne? kika wani zaro ido.” 
Gyara zama ta yi. “Aa zauji, kawai nai mamaki ne ya karima fa! ‘yar uwata ce fa, kwanaki fa da tai rashin lafiya k‘in hanani zuwa ka yi, yaci ace na je, yanda ya karima ke nuna kulawa agareni.” 
“Nuna min zakiyi kenan banyi daidai ba ko? Ke kullum ta Allah ba a gaya miki kiji farat d’aya,sai kin kawo k’aulu da ba’adi ko? To na ce ba zaki ba.” Ta san tun da ya harzuk‘a d’innan ba zai barta ba, narainarai tai da fuska, ‘yaya za tai ne?‘ ta fad’a aranta. Nan ta runtse idonta, tabbas! tana buk’atar ganawa da yayarta,amma 
maganar miji ta wuce ta komai,ta ke ta sallama ta bawa kanta hak’uri. Murmushi tayi wanda aka ce ya fi kuka ciwo,nan ta kwanta a gefen kafad’unsa, ta ce, “to shi kenan zauji na hak‘ura.” Ta fad’i maganar asanyaye tare da cusa hannunta cikin 
k’irjinsa, tana shafawa ahankali idonta a lumshe. Kallonta ya yi k‘asa k’asa, yanayin yanda take mai yana matuk‘ar shigarsa, hakan ya sa ya dad’a bud’awa yanda za taci gaba. ‘ Murmushi ta yi kawai, ya kalleta “lad’ifa ya dai? na ji kinyi shiru.” 
Kyawawan idanta ta kafa mai. “To mai zance zaujina?.” Ta fad’a tana mai lumshe idonta tare da ci gaba da shafar kirjin nasa. “Ai zaujina dole na bi maganarka, muddin ina san ganin daidai.” A hankali ta mik’e. “Bari naje nai bacci ko na awa ne.” Nan ta juya, taji ya kirawota ta juyo ta kalleshi. “Ki shirya ki je.” Bata wani nuna zumudinta ba, sai tace “da gaske?.” 
Yace “E!” “To nagode zaujina, bari na je na shirya.” “To adawo lafiya.” “Kai amma naji dad’i, da na d’auka ba za ka barni ba.” “Magana kike so kenan.” “Aa, kawai” ta fad’a da murmushi. “To kai za ka kaini a mota ko?.” “Aa, ki hau adaidaita sahu ina da abinyi .” “Haba zauji, kafison naci kwalliya nai titi ana kallona, bayan kana da mota kuma ka na da lokaci.” 
“Banyi niyya ba,ko dolene?.” Ya fad’a tare da kafeta da ido. Nan ya zaro 2k ya ya ajje mata. “Idan ki na san zuwa ga kud’in mota nan, ni aiki ne a gabana.” Girgiza kai kawai ta yi, dan inda sabo ta saba da wofantarda itan da yake, ita sai ta ce tun bayan da tai wata biyu agidansa, ta fara ganin canji agareshi, sam! ba ta wani ganin yana maida al’amuranta da muhimmanci,gabanta ne ya fad’i. ‘Ko dai ni ce me matsala ne?‘ Zuciyarta ta shiga raya mata, za ta iya k’aryata zuciyarta dangane da hakan, dan ita dai tasan cewa kota’ina tana iyakar k’ok’arinta wajen faranta ransa, da duk gujewa b‘acin ransa,nan zuciyarta ta kuma raya mata, kodai dan bata da cikar kirji mai girma ne, wanda ta kula yana matuk’arjin haushin hakan. Anan za ta yarda da hakan,domin tasan yana mata wulak’anci ta b’angaren. “Tunanin me kike ne wai?.” “Murmushi ta yi mai,tare da godiya kan kud’in da ya bata.” Nan ta fice dan shiryawa. Shirin tafiya ta hauyi ta flto das da ita ,ta saka atamfa kalarja da fari ta yafa burkid’ed’en farin mayafinta Masha Allah ita kanta ta ga kyanta. 
Fitowa ta yi ta shiga d’akin nasa,har lokacin da agogo ya buga sha biyu saura ,yana wajen yana aiki. “Zauji ni zan wuce.” Ya d’ago da kansa ya kafeta da ido ya ce. “Da ace akwai ki da cikar gaba da baya, ai da kin fi kyau, amma ke dai ko yaushe a shafe Rau rau tai da ido. “Haba zauji, bai kamata kana tankani ba, ni kaina da na san inda ake k’arawa aida na kara, kuma na gode da yanda Allah ke san ganina” Murmushi ya yi, “akwai mana, ke ce dai ba ki san farin-cikina, shi’isa ba ki damu daki nemi maganin k’ara girmansu ba.” Cikin fushi tajuya, “ni na taf‘l.” Don ta kula ba zai gane abinda take nufi ba. Tab’e baki ya yi “to adawo lafiya.” Tace “Tam, amma sai dare zan dawo” bai magana ba harta fice. Da k’arfl ya k’wala mata kira. Ta dawo ya ce “ki saka nik’af.” Mamakinsa ne ya kamata, sai kawai ta yi dariya, lamarin Ramadan sai shi.Wataran ya nuna kamar ya damu da ita, wataran kuma ya maisheta abar wulak’antawa. “Amma zauji, ai in dai kana kishin aga kwalliyata, bai kamata ka barni na doshi titi ba, kawai kazo ka kaini hankali kwance, tunda Allah ya hore maka kana da abin hawan nan, da dai baka da shi ne to da uzuri, dan ni banda nik’af.” 
“Sai aka ce miki bana kishinki ko? banda lokacin kai ki ne kawai, mata ma nawa ne ke shiga motar hayar, Finsu ki kai? wa su ma kota’ina sun zarce ki,amma suke shiga ta hayar.” Hawaye ne suka biyo fuskarta. ‘Har yaushene mijin nata zai san darajarta ne? wai me ya maisheta ne? Agabanta yana cewa wai wasu matan sunfi ta, kuma tana a matsayin matarsa.’ Bata san wa zai bata amsa ba,dan in tama tambaye shi dalili wani jidalin ne.” Shi ko ganin yanda ta ke hawaye sai jikinsa ya yi sanyi, nan ya tashi ya janyota jikinsa. “Sorry lad’ifata, maganarta miki zafi ko?.” D’aga kai ta yi kawai. Yace “ki sa nik’af.””Nace banda Shi. ” “To shi ke nan.Ba tai aune ba ta ji ya sanya bakinsa a nata, ya shanye jambakin da ta saka tas! yace “kuma kije ki wanke fuskarki.” Ya fad’a yana mai d’aga mata gira.” Sakatoto ta tsaya tana kallonsa,murmushi ta yi kawai, wataran mijin nata kan burgeta in ya yi wani abun, wataran kuma in ya yi ta kanji kamarta bar duniyar.“ Kamar dai a yanzu da ya saka ta a hali biyu. Dariya tai tace,” I love you zaujina, Allah ya dai ya shirya min kai.” 
Zaro ido ya yi. Yace. “Lad’ifa!” Ya fad’a da mamaki. Ganin yanda ya yi ne,ya sanya da sauri ta fice tana dariya, dan karya zubar da fushinsa akanta.” . Murmushi ya yi ya koma ya zauna. Sai da ta wanke fuskar, sannan ta fice, tana tafe tana tunanin halayyar mijin nata, ta rasa gane inda ya sanya gaba.” Tana zuwa bakin titi kuwa, ta samu adaidaita sahu. Tin K’arfe d’aya tana k’ofar gidan yayar ta ta, harabar get ta taradda ya karimar na sallamar d’an almajirinta, da murna ta kalleta. “Aa Lad’ifarmu ke ce yau?.” Da sauri ta rungume yayartata tace, “wallahi missing naki nake yaya.” Ai kece yanzu tun da kikai aure bakyason shiga jama‘a, dan ko fa sunan mabruka bakije ba.” 
“Ba laifl na bane wallahi yaya. Ramadan ne bai san fita, ba irin na cin da ban mai ba amma yace wai Aa daga baya naje barka, kuma a haka abin ya shashance.” 
“To Allah ya kyauta.” Cewar karima tare da jan hannun lad’ifar su ka shiga gidan. Bayan almajirin ya flta. 
Bayan ta huta, sai hira ta b’alle a tsakaninsu, yayar tace. “Kai autar mama, kinga kyan da ki kai kuwa? aure ya karb‘eki.” “Hmm! kawai lad’ifa ta ce. ” A hakan wai nai kyau?.” “Wallahi kinyi kyau, fatarki ta murje, sai dai har yanzu ba ki k’iba ba.” “Yauwwa yaya, dama wallahi abinda ma ke tafe dani kenan, ina zan samu maganin girman k’irji da k’iba ne ya karima? amma na gargajiya fa, wallahi abin yana damu na.” Rik’e hab’a yaya karima tayi, “ke kuwa Lad‘ifa me zakiyi da k’iba, ana zaune k’alau?.” “Hmm! yaya karima, wallahi Ramadan kullum k’oraflnsa akan sirantaka ta ne, komai fa na sanya, sai ya ce bai mini kyau ba, wallahi karki ga yanda yake kusheni, wai yafi son mace 
dimurmur.” “Cab! Shi ana gudunta, amma so ya ke, yo mazan yanzu ai basu fiye san mace mai k’iba ba.” Ai yaya shi fa bawai duka na zamo mai k’iba ba, wai fa shi yafl son yaga mace gaba a cike, baya a cike, ni kuma gani yanda nake.” Dariya ya karima ta sanya. “Sabon salo mijin nan naki ma fa d’an yi ne, kodayake, ba yau na sabajin case irin wannan ba, akan mazan dake yiwa matansu d’iban albarka kan ba su da manyan k’irji,dan ko sati ban ba, naji mak’ociyata na fad’ar irin d’iban albarkar da mijin k’awarta ke wa k’awartata, wai wallahi ya ce aure zai k’ara, in har bata san yanda za tai ba.” Dafe k’irji Lad’ifa tai tace “kishiya! Akan d’an wannan abun.” . 
“Ke dai rabu da maza Iad’ifa, ke kike ganin d’an wannan abun, amma awajen wani namijin babban abu ne,wasu mazan akwai su da san ransu. Ke Jibi irin yanda Ramadan ya so ki kan ai auren nan, kuma a hakan ya ganki yana so bai ga makusarki ba sai yanzu. “Dan Allah yaya ki taimaka min.” “Ai dole ne, idan na gyara aurenki, ai kamar na taimaki kaina da hajiya ne,Saurareni ki nutsu, in tambayeki, bayan wannan babu wata matsalar k0? ki na dai zaune laflya ko?!‘ Lad’ifa tace. “E yaya, kawai dai wannan matsalar ce, kuma ita ma dan na rasa mafita ne.” Haka kawai taji gwanda tai shiru,ba sai ta fad’awa yayartata dukkan matsalarta ba, kawai a ganinta sirrinta ne. “Yawwa ki ta hak’uri kinji, ki dad’a dauk’e ki kuma kara haquri  daman shi zaman aure ya gaji haka, kowanne aure da kalar tasa jarrabawar, ke in kika ji ta wani ta ki ai nafila ce.” 
“Nagode yaya.” Ta fad’a tana mai jin dad’i, domin tana ganin fa’idar duk abinda yayartata ke gwada mata. Bayan sun ci abinci su kai sallah. Anan tana zaune ya karima ta nemi wata k’awarta kan samar da kayan k’arin k’ibar, da na k’irjin. Haka suka sha hirarsu, tana dad’a gaya mata hanyoyin da zata bi wajen faranta ran maigidan nata. Misalin k’arfe uku wata budurwa ta shiga gidan.Karima na ganinta ta ce “Yawwa sahura 
kinzo adaidai,zo ki wa k’anwata lalle da k’unshi, ni na d’auka ma kin fasa zuwa yi min ne?.” Budurwar ta ce mata aikine ya rik’eta. Dariya Lad’ifa ta yi, amma naji dad’i wallahi. “Aiko zai mata kyau tunda fara ce, maman affan k’anwarki ce ko?.” Sahura ta fad’a tana mai hada‘ lallen.” “K’anwatace ita ce autarmu.” “Ga kama nan, amma ta fiki kyau.” “Haba dai wannan lange-langen ce ta fini kyau.” Suka saka dariya dukkansu. 
Nan me k’unshi tai matajan lalle me kyau,sai da yayi awa biyu ta cire, da ya ke ba ta da cin lalle ya yijajawur! Gwanin sha’awa, nan ta d’ora mata da zanen bak’in k’unshi k’afa da hannaye. 
Ya karima sai zuzuta kyan da tai ta ke yi. 
“Ai da ace ma mun shirya hakan, aida na kaiki bayan layin nan an miki gyaran jiki.” “Gaskiya yaya “kinaji dani.” “Yo in banji da ke ba, to da wa zan ji Autar hajiyarmu.” Bayan anga mawa yaya,me k’unshi ta tafl wajen shida. “Yaya tace “yawwa lad’ifa,bud’e ledar can ga zuma ki d’auko,” ta nuna mata kan tebur, zuma ta d’auko ajarka. “Fara Shanta tun daga yanzu,wannan had’in zumar me kyau ne, ki sha za ki bani labari yau, sannan bud’e firiji ki d’auki wani bowl.” Kankana ce hadadd’iya da taji had’i da madara, kaninfari, da sauransu, tace. “Ki shanyeta dukka,kinga tawa ce na yi d’azu, to abban affan ma sai gobe zai dawo, maza maza 
shanyeta.” Dariya lad’ifa tai tace,”wallahi yaya shi’isa nake sanki, ina son zuwa gidanki .” “To ya za,ai, d’an uwa rabin jiki, idan na gyara aurenki. Auta ai na taimaka miki damu kanmu ‘yan uwanki, ballantana hajiya.” “Cike da sanyin jiki Lad’ifa tace wallahi da wuya na karb‘u, da wuya na yi abu a yaba mini,idan banci sa,a ba ma a gwasale ni.” Dariya yaya ta sa ki. “Yo sai me? kefa duk matar da kika ganta tana zaune lafiya agidanta wallahi hak’uri ta yi, sau da dama mata na kukan rashin yabawa ga mazajensu, Ke dai yi dan Allah, komi zakiyi, to ki yi shi dan Allah, kuma dan farin-cikin mijinki, koda bai yaba miki a fuskaba, idan har yaji dad’i aransa, to Allah zai ba ki lada, idan har kika sanya cewar aure ibada ne shi kenan, kin sallama,Sannan komai za ki, ki dage ki yi dan inganta zamantakewarki. In dai bai sab’awa mahaliccinki ba, sannan kuma ba zai cutar da lafiyar ki ba, to kiyi. Mace ai da kissa aka santa.Ki faranta ran mijinki da zuciya d’aya, dan idan ya yarda dake. Allah ma ya yarda dake, Sannan ki dad’a hak’uri da duk cin fuskarsa, wata rana sai labari. Masu iya magana dai na cewa ba a b’ari a kwashe daidai.” Sosai yayartata taita nuna mata hanya mai b’ullewa. Saboda ta kula koda lad’ifar ba ta fad‘a ba, tana da sauran wasu matsalar to da yake ita babba ce ta ganota. Sai k’arfe bakwai na dare, bayan ta ci ta sha, yaya karima ta sanya driver ya tafi kaita da guzurin abinci dan ta bawa Ramadan. Domin tasan tayi daren girki. 
Hmm

Related Articles

Leave a Reply

Check Also
Close
Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE