NAYI GUDUN GARA CHAPTER 40
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 40
Yau ramadan yasan girkin safna ne yaki dawowa da wuri har saida tai bacci yana shigowa yayi samansa ya kulle. Ya zauna ya shiga tunani ya zama dole ya sanya tsaro a dakinsa,
domin dauke dauken da ake mai yayi yawa.
Da asuba da safna ta tashi ta tuno fa ramadan a wajenta yake amma shine bai dawo da wuri ba. Tsaki tai tace “ai yana sane yayi min hakan,” wanka tai ta tafi dakinsa. Alokacin ya tafi”: masallaci, domin ladifa ce ta sanya mai alerm irin na bakin gadon nan, dan tasan baya tashi da asuba, amma da yaji alerm zai mike. Dakin ta shiga ta dade akan gado, Iokaicin bai
dawo daga masallaci ba, yana shiga dakin yaganta sai ya dan kauda kai. Ya kwanta, tace ‘shine jiya ko nema na bakai ba.‘ Ai kinyi bacci lokacin.”
Yasan abinda take rara gefe, shi fa wallahi yanzu ta isheshi, sam ma saboda damunsa da take yasa ma ya daina jin wani mararinta, abubuwan da dama ya kwallafa rai akanta duk sun fice mai arai, saboda rashin hutun da bayayi ya sanya yake jin haushinta akasan ransa amma
bai nuna mata a fuska ba.
“Kaima ka sani Please ka tashi”. Saiya mike “me kike nufi ne?.” .
‘Ai ka fini sani.” Tsaki ya yi, yace “bacci nakeji, haba ke dan Allah bakya gajiya ne ehe? ki sani komai fa sai dason abun da lafiya akeyi, ni bacci ne fall a idona.Dan haka ki rabu dani.‘
“Ba zata iyajurewa ba aduk yayinda ta sanya shi a idonta sai taji bukatarsa ya damaimaye zuciyarta, bata samun nutsuwa sai komai ya kammala.
Tashi yayi zai fita ta sauko da sauri ta sha gabansa, ta rungume shi “please taimaka.‘ ‘ki rabu dani safna.‘
Sai ta sake shi cikin fushi zata fita, ganin yanda tai fushi, shi kuma baya son fushinta, ya sanya ya janyota babu yanda ya iya haka ya hau aiki bai kara runtsawa ba, gashi har bakwai tayi sai kawai yayi wanka.
lta kuwa a lokacin ta koma bacci hankali kwance ga iska na kada ta. Haushinta ne ya damaimaye ransa. Sai kawai ya sanya kaya ya fesa su turare ya sanya agoge ya shirya ya fice. Direct shashin ladifa yayi, tana kwance tana bacci ya tashe ta, ta tashi.
Fuskarsa atamke yace “zoki hada min break yunwa nakeji.‘ ‘lna safnar ne ba itace da girki ba Lumshe ido yayi ya budesu akanta yace Ki bani kawai” Sai ta mike ta fita ta sauka kasa ta shiga kitchen. Shima ya biyota.
Wajen laila yayi itama bata tashi ba sai ya fito ya koma falon ya zauna. indomie mai hade da kwai tayi mai da shayi mai na’a na’a, sannan ta dauko mai ruwa a glass cup mai sanyi ta
ajje wanda ruwan rubutun nan ne, nan ya zauna yaci a gaggauce yana kallon dakin safna,
dan karta tashi ta fito, ladifa na kula da yanayinsa, tana mamakin hakan.
Sai ga laila ta filo, ta gaidashi ya amsa sama sama ya tashi ya fice suka bishi da kallo. Kowacce da abinda take tunani.
Dan tabe baki laila tai ta zauna tace”dan Allah maman fuad taimakamin da dan tea wallahi yau banjin dadi. Gashi da wata iriyarjin yunwa na tashi.”
Ladifa tace “eyya laila sai hakuri daman ciki inya zo da laulayi. Koma daki zan kawo miki.“
Tace “to,” ta juya ta shiga shashenta.
Ladifa ta hado mata tea da bread ta soya mata kwai, ta tafi kai mata,ta shiga falon ta duba ba ta ganta ba. Sai ta shiga kitchen din, lailar na zaune a kitchen din ta daga kai sama. Tana numfashi akai kai. Kallon kitchen din ladifa tayi ko ina kaca -kaca, ga wanke -wanke tuli, watakil har dana jiya.
“Laila ga shi ki tashi kici.”
Ta dago idanuwanta muryarta adan dashe tace “yawwa nagode,” ta tashi ladifa ta kai mata falo ta zauna tana ci.
Sannan ta shiga kitchen d’in ta ce “bari kiga na getta miki kitchen din nan. Na san yanda bakyajin dadin nan da wuya ki iya.”
Ta shiga ta fara da wankewanke, sannan ta goge kitchen din tas! tai mopping komai ya fito tas. Sai wajen tara ta gama, lokacin laila ta gama ci, shiga tai ta tsaya ta yi murmushi “wallahi na gode sosai ‘yar uwa, nagode daman wallahi na kasa tunjiya wanke-wanken nan, sabida bana jin dadi sosai! ” ladifa tai murmushi tace “babu komai fa zaman tare ya gaji haka, cudanni in cudeka.”
Laila tace “hakane wallahi da ace kowacce mace za tai dace da kishiya irinki aida ba wanda zai kita, wanda da ni da farko na shigo inai miki abinda bai dace ba, ashe ke alherice
agareni a zaman mu wallahi na gode” Ladifa tace “babu komai. Allah ya kara lafiya bari naje kitchen nawa na gyara.“
Nan laila ta koma dakinta ta kwanta sai bacci.
Ramadan na zuwa wajen aiki shugabansu ya kirawoshi ,yake tambayrsa dalilin daya sanya yake makara yanzu, duk komai nasa kwazonsa yayi baya. Hakuri ramadan ya bada kan cewa abubuwa ne suka sha mai kai. Nan dai yayi mai fada, ya tafi office nasa.
Al’amuran safna gaba suke dad’a yi, dan yanzu ta fito da kalarta sosai. Ta gallabesu duk masifar laila da fadanta ta samawa safna lafiya, dan duk abinda takeji da shi ta shafeta. Gashi sam Tama daina girki sai dai ramadan daya dawo za tace suje restuarent asiyo mata. Haka kuma zasu fita sai sukai tara basu dawo ba. Ko fita unguwa za tai shine zai kaita, koda kuwa me yake yi. Duk inda zata kuma koda goma zata kai na dare shi zaije ya daukota, abin na damunsa, sam ba haka yake tafi da komai nasa na gidansa da ba, amma ya rasa ta yaya yake kasa tankama safna.Lalle ya yarda mata suna suka tara ada Ioakacin ladifa ita kadai yana ganin kamar duk itace ke da laifl. Sai yanzu ya fahimta. Tun daga auren laila har zuwa yanzu. Ya gane mace ta gari itace mai irin halin ladifa. Duk da cewa yasan laila kishine da masifa kawai da ita. Amma safna kam duk lamarinta yana bashi tsoro. ‘
Haka maman safna ke zuwa gidan tun safe, wataran har dare da kannen safnar suci wannan su ci wancen, haka zai ta hidima da su. Safna ta dinga cewa suyowa mama
wancen, siyo wannan. Uwar taita washe baki ‘ya tayi auren kece raini.
Ladifa da laila kuwa sam! Sun maida hankulansu kan abinda ya shafesu musamman laila
dake rainon cikinta. Dan yanzu yakai wata takwas.
Ladifa kuma makarantar koyan sana’a yaya kareema ta samo mata. Me makarantar macece kawar yaya kareema ce, ana koyar da sana’u kala kala, lokacin data sanar ma ladifa yakamata ta tashi tsaye tasan me take, yanzu mace saida sana‘a idan kana sana’arka duk wasu abubuwan kishi da kishiya ba zai shamaka kai ba. Sannan za kana kaddamar da komai da kudinka, ba tare da ka tambayi mai gida ba yana cewa ka dameshi.
Wannan dalilin ne ya sanya taiwa ramadan magana, da ya basar da maganar da tai mai, sai data kuma yi mai maganar sai yace babu damuwa taje. Daga nan bai kara cewa komai ba. Shi baice yaya ne kudin shiga makarantar ba, shi kuma bai bata kudi ba, ita kuma bata
tambaya ba, kawai sai ta tafi”: wanda daman ya kareema ta rigada ta biya mata komai.
Tunda ta fara zuwa sai ta maida hankalinta can ga sabbin mutanen data sani. Hakan ya sanya inta dawo bata damuwa da lamuran gidan, shi kansa ramadan ta watsar da lamuransa na wai hakkinta, ita dai tana nan tana addu’a tana shan kuma rubutunta
wanda shima yana sha.
Safna na zaune gefen gado tana irga irin kudaden da ta wafta. Domin acewarta idan ramadan ya sanya CCTV camera dan yaga mai satar mai kudi to tana da wata hanyar, dan tunda ta gano ya sanya cctv camera a dakinsa dan ya gano, tun daga nan ta daina satar domin karya kamata wataran.
Sai taci gaba da karba awajensa tace ya bata za tai kaza da kaza, abubuwa kala -kala.
gidan ya dawo kamar dai ita kadaice matarsa sai yanda tajuya shi.
Jitai cikinta ya murda mararta ta yi kuwwa, sai ta dafe, ya dan lafa ya kuma dawowa, sai ta ajje kudin agefe. Ta dafe mararta, tunani take mai taci ne ya sanya cikinta ke ciwo. Tuno cewar ta sha wani maganin mata dazu ya sanya tai tunanin k0 shi ne ya sanyata ne, dan indai zata shashi sai cikinta ya danyi ciwo amma ita bata gane illa ne dashi ba, wani irin murdawa mararta tayi.. Da sauri ta dau waya tai kiran ramadan lokacin yana tsaka da aiki, da kuka kan take magana kan cikinta na ciwo yazo a gaggauce ya mike daga office din
nasa ya rufe yaje ya sanar yana da mara lafiya agida, ya tafi, lokacin da yaje harjini ya fara zubo mata ta kafarta, da kyar ya daga ta suka shiga bandaki ta daurayi jikinta . Suka fito suka tafi asibiti.
Suna zuwa aka karbeta aka dubata aka sanar cewa cikin da kejikinta ne yake san barewa. Nan suka shiga bata taimakon gaggawa dan kar cikin ya bare. Da yake Allah ya kaddaro sai ya bare, cikin ya kuma murdewa ya zube gaba daya, wanda har saida akai mata wankin ciki tasha wahala sosai ba kadan ba.
Sun gano cewa dalilin shan magungunan mata wanda basu da kyau. Ya sanya cikin barewa.
Kuka take wiwi, tana sambatu da ace tasan cewa ma tana da ciki, ba zata sha magungunan ba, ta yi bakinciki ga koshi ga kwanan yunwa.Sai dare aka sallamosu ta dawo gida. Duk matan babu wacce tasan mai yake faruwa. Sai bayan da suka dawo. Sukai mata ya jiki.
Ramadan ne ke mata komai duk ta narke, tace wannan tace wancen, musammmn jin cewa likita yace ta ci abubuwa masu kara jini sosai haka ta dada bude wuta.
Sai data dawo garau! sannan ramadan ya runtsa. Inka kalleshi wataran duk a hargitse duk ya canja.
Ladifa ta gama makarantar ita kanta tasan ta koyi sana’a kala -kala, gashi matar tace duk mai san ta fara sana’a kan irin abubuwan da aka koya musu. To ita zata hada shi da customer. Nan ladifa ta kudiri niyyar fara yin curry irin homemade din nan.Shima yana daga cikin sana’ar da ta koyo.
BAYAN WATA DAYA
Addua makamin mumuni, domin dagiya da addua da sukai ta yi, asirin jikin ramadan ya fara fita, domin a wani zuwa da hajiyarsa tai lokacin da ita safnar tai bari ta zo duba ta, al’amarin da ta gani ya bata mamaki wai yau ramadan da ke dajarumta, taga mace na wajigashi duk ya fice a yanayinsa. Gashi ita kanta tafi wata uku bata sanya shi a ido ba.
Haka kawai sai ta kasa yarda da al’amarin safna, nan ta koma gida ta sanya akai tayi mai
addu’a Sosai gata bangaren ladifa ma. Nan ya fara dawowa normal haryakan shiga shashinsu yakan duba lamarinsu. Sukan samu kulawarsa, shi kansa ji yake kamar an zare mai wani gungumen abu dake kansa. A hankali a hankali komai ya dawo asirin ya karye murus! ramadan ya dawo ramadan dinsa.
Inda safna ta fahimci asirin ya barjikinsa, ta gane ne yanzu duk abinda tace zai ce aa ko ya hau mata fada. Kuma gashi taga ya koma kamar da da matansa. Ta ga duk sun fara dawowa walwalarsu, gashi ya daina bari ta dibar mai kudi, musamaman da daddare idan ta kwarzabeshi indai ya gaji zaice ta kyaleshi haka, kuma komai zatai ba zai kulata ba. Wanda da adan dane jikinsa rawa yake farawa in tai fushi. Sai dai tai ta kuka amma duk da hakan takan takura mai ta wannan bangaren kadai ne take cin galaba akansa. Danya rigada ya gane halittarta ce haka. ‘
Ramadan na falonsa ladifa ta shiga ta ajje mai fura da nono da ta dama. Tace gashi murmushi yayi yace nagode. Sai ta danyi jim tace “daman kasan nayi makarantar koyan sana’u ta six week ko?.
Ya daga mata kai tace “to shine a irin sanar dana koya zan fara daya, shine na gaya maka kaban izini” Murmuahi yayi yace “masha Allah to ko na bada gudunmawa ta ne?.” Tace “yanda kace,” yace to zan bada tai murmushi tana godewa Allah azuciyarta da Allah ya sanya mijin nasu ya dawo normal, sannan ta kara da cewa “sannan dan Allah ka dage da addu’a wallahi yanzu lamarin mutane sai addu’a dan Allah.”
Cikin ido ya kalleta yana girmama kaunarta akansa, yace “na fahimta Allah ya shi miki
albarka, tabbas hali shine mutum na gasgata haka.” Murmushi tai ta mike ta fita.
Cikin ikon Allah ta fara yi kuwa ta zuba A Farar leda na gwaji, ta aika makotansu da gidan su maman rauda. Ta aikawa da ya kareema da yawa ita kuma ta kaiwa abokan arziki tace kanwarta keyi.
Cikin ikon Allah sai ga maman rauda tazo, ta shigo gidan laila ce a zaune a falon, sai tai dan dariya tace “a’a maman rauda.”
Maman rauda ta kalleta da dan mamaki dan da sam! Ba tayi mata magana ba ganin zama tai ta ce “sannu yajiki?.” Alah ya saukeki lafiya. ladifa ta sauko tace “wa nake gani kamar maman rauda?.”
Tace “hmm ai takanas nazo akan curry naki, kinga da nai miya yanda baban rauda ke santi wai kamshin yayi.”
Dariya ladifa ta sanya tace “dan Allah? kai amma naji dadi dama na farko ne na fara so nake na fara na sayarwa.”
laila tace “aiko nima yayi min dadi.” Maman rauda tace ai yanzu ma zuwa nai a bani zan kaiwa yayata taji irinsa ko tana son irinsa.” Ladifata ce to shike nan.
Cikin ikon Allah lokaci kadan kori na ladifa ya shiga da farinjini, dan an siya da dama. Nan ya kareema ta bata shawara tayi da yawa, ita kuma zata sara saboda a bangarenta ma akwai wanda yayi musu. Sati daya tsakani Laila ta tashi da nakuda sosai! ladifa ce ta kaita asibiti a mota, sabida ramadan baya kusa, safna kuwa tana falon lokacin da aka fito da ita saima harara data bisu
dasu tana taunar cewgum fus fus.
Koda suka je basu dade ba ta sauka, ba kamar haihuwar najwa ba, inda ta samu baby boy sosai sukai murna, nan taiwa ramadan waya ta sanar mai cikin farinciki yace gashi nan, haka ‘yan uwa da abokan arziki, ‘yan uwanta sun zoda hajiyar ramadan.
Zuwa dare aka sallameta da babynta mai kama a babansa sak saidai baiyi haskensa ba, yayi kalar laila mai duhu.Ladifa ce ke ta kaikawo, kowa sai yabonta yake da sanya mata albarka musamman dangin laila, umman laila nace wa, ” wallahi laila ki rike uwargidanki ku zauna lailfiya, yarinya ce ta gari mai sonki ce, dan babu kishiyarda zata karjiki tai maka haka, idan ba mai kyakkyawar zuciyaba.” Safna ko lekowa ba tai ba tana can tana kulla sharri.
So daya taje ta daukeshi, shima dan ta bagarar da nutane ne, bakin nan awashe ta shiga ta dau baby ta dade sannan ta fita. Daga nan kuma bata kara shiga ba.
Sati ya dawo aka rada suna aka sanyama yaron sunan baban laila ana kiransa da Arif
Safna ganin cewa asirin da sukai ya karye sai ta komawa makircinta. Akwai ranar da ladifa tai girki, bayan ta zuzzuba na ramaadan. Sai ta rufe kitchen din dan tai wanka. Da yake amkusa kiran sallahr dare.
Tana fita daga kitchen din safna ta fito a hankali ta bude warmer da abincin ramadan keci ta zambada yaji da gishiri a miyar, tajuya ta rufe tai sauri ta fice.
Sai lokacin da ramadan ya dawo ne ladifa ta sauko takawo mai a binci laila na daki da baby arif, safna na bangarenta, jin ya dawo ta fito tana juya jiki.
Ta zauna. Ramadan ya fara cin abuncin, da sauri ya zari tisshu dake gefen dining din ya furzar da abncin ya kalli ladifa. Yace “ya haka? kin manta ne baki dandana bane.”
Sai ta dan daburce ta dauka ta dandana da sauri ta rufe bakinta tace “kai wallahi bansan haka ta faru ba. ”
Safna ta tabe baki ta juya. Ramadan yace “gaskiya ni ba zan iyaci ba, am so sorry baby. zanje na yo mana take away nasan kema ba iya ci za kiyi ba.”
Murmushi tai tace “kwarai. Nan ta dau shinkafar takai fridge. Shi kuma Yayi shashen laila.
Safna ta mike cikin kunci tai dakinta tana jin haushi dan ba haka taso ba.Taso ace ya
zazzaga ma ladifa rashin rashin mutunci.
Ya shiga wajen laila tana zaune abakin gado tana shafawa baby farar powder a goshinsa, ya zauna gefenta ya shafi kan babyn yace “maman baby ya dai?.”
Sai tai murmushi tace “Alhajin Allah, baby na gaisuwa.” Shafa kumatun babyn yayi ya ce “na dan fita.“ Ya fita, tai murmushi itama ta shiga godewa Allah daya sanya mijin nasu ya dawo daidai. Dayan wasu makwanni.
lkon Allah sai ga ladifa da ciki, danjin yanayinta tai ya canja, kamar irin na lokacin cikin fuad ta siyo Pt strip ta gwada taga positive. Nan ta sanarma ramadan sukaje asibiti aka tabbatar da shigarsa.
Cikin nutsuwa taci gaba da rainon cikinta, dan bai zo mata da laulayi kamar na faud ba.
Agefe gashi ya kareema da yake matar dake koya sana’u kawarta ce tai mata hanyar cewa ladifa tana yin curry da yawa ta zuba a robobi yan dogwaye farare. Wanda tai mata hanyar da sukai rigister da nafdac, nan da nan da yake kareema naso kanwar tata ta karbu ga sana’ar, kuma matar ta ce zata hadata da customer nata da zasu na sarar na ladifar, ya sanya har yar takarda da ake likawa da suna dasu adreshi, suka lika a robobin, inda ladifar ke yi akalla roba hamsin takai. Kuma ba adadewa ake kawo mata uwar kudinta da riba.Wataran har roba dari tana yi. Sosai takejin dadin sana’ar.Dan tana biyawa kanta bukatu ba sai ta tambayi ramadan ba. ‘
Lokaci yaja al’amuran gidan nata tafiya, yau fari gobe baki, ta bangaren safna tana nan sai abinda ya karu.
A wata rana ne shugaban wajen aikinsu ramadan da yake yana daukan ramadan mai kwazo da sanin yakamata awajen, ya sanya ya kirawo shi kan zai aike shi yakai wasu kudade banki.
Hakan ta kasance ya aikeshi da makudan kudade na dollars. Wanda shi kansa ramadan baisan yawan kudinba tunda basu tsaya anyi ba.
Karfe shabiyu na rana ya fito da karamar jaka ahannunsa, ya sanya agaban kafarsa cikin motarya tafi maganin zazzabi ya tsaya ya saya a chemist wanda Arif ke fama da zazzabi in yaso in ya kai mata,daga baya ya koma yakai kudin.
Hakan kuwa akai ya saya yaje gida, da zai fita ya dau jakarsa ya shiga gidan ya mikawa laila maganin. Sannan ya haura samansa da jakar, safna taji lokacin da ya dawo dan taji dirin
mota, daman tana so tai mai magana kan sakonta. Shi kuma yana shiga dakin sai ya ajje jakar ya shiga wanka dan zafi yakeji, alokacin ta shiga dakin idonta ya sauka akan jakar, safna bata kawo cewar kudi bane, amma kamarjanta ake sai ta bude zif, taga dollars kal kal dasu, dafe kirji tayi, nan da nan hannunta ya shiga rawa, sam ta manta ma da CCTV camera dake dakin, dan ta kidime, take muguwar zuciyarta ta sanya ta zari wasu kudade daga ciki da yawa, ita kanta batasan ko nawa bane, tasan akalla zasu kai manyan kudi, idan aka canja da kudin nigeria, nan ta zuge jakarjikinta na rawa, ta zuba adankwalinta, ta fice
daga dakin gudu gudu sauri, ta karasa cikin dakinta ta kulle ta ajje tana haki, sai da ta
tabbatr ta ajjesu a killataccen waje, ta nutsu, shi kuwa bayan ya fito sam bai kawo komai ba.
Ya dau jakarya tafi. Bank ya je ya zuba, wanda akalla kudin a kudin nigeria za suyi miliyan bakwai. Bayan ya koma wajen aikisu shugaba yayi kiransa yace “ka kai?.”
Ya ce “E! babu dadewa alert ya shigo na dollar account dinsa. Yaga yawan kudin da sauri
ya kalleshi “ya akai hakan ramadan?.” miliyan bakwai na baka? ya haka naga an zuba hudu. Me ya samu ragowar kudin?.” Da dan mamaki ramadan yace “ai yanda kaban, haka na kai su.”
Shugaba yace “zancen banza da WOfi kenan, bance ka duba takarda agefen jakar ba, na yawan kudin?.”
Da sauri ramadan ya duba yaga daidai kudin miliyan bakwai, kuma gashi yaga hudu.”
“Banji lokacin bane oga.” Ramadan ya fada yana tunani aransa ‘daga ina matsalartake ne?.” ‘ Ya kalle shi “wallahi bansan yaya hakan ta faru ba.” Buga benci mutumin yayi yace “duk inda kudinnan ya shiga ka fito dashi.”
Nan ramadan ya mike ya fita al’amarin ya bashi mamaki.
Hakan ya koma gida duk cikin fargaba. Ita kanta safna duk sai ta kasa tsugunni saboda kar a ganota, tasan dollar ba kananan kudi bane.
Kwana biyu ramadan ya shiga dumbin damuwa ga yawan wayar da shugaba ke mai.
Bayan kwana biyu Yana zaune shugaba na cewa “haryanzu dai baka gano ba ko?.”
Ramadan yace wallahi fa.”
cikin bacin rai shugaba ya ce ban san sanda ka canja hali ba ramadan, tun watannin baya da kake makara a aiki, ba zan shaideka ba, to wallahi ka saurara kaji dole ka fito mana da kudi ka biya, domin da da hukuma ma zan hadaka, amma saboda kana da mutunci a idona na daga maka kafa dole ka biya. Mu rufe case din nan anan, ba tare da anje court ba.” Dafe kai ramadan yayi yace “to shikenan.”
Account na ramadan babu wasu kudade da yawa befi saura miliyan daya ba, saboda ya ciri kudin nasa, ya bada su zunzurutu za ai mai order kaya, kuma kayan har yanzu ba suzo ba custume sun rike kayan.
Gashi duk safna ta gama tatukeshi, ya kalli shugaba ya ce “a biyoni miliyan biyu, ko ana daukar wasu a albashi na.”
Shugaba yace “babu matsala.”
Kwana biyu damuwa taiwa ramadan yawa sai dai ya tashi da dare yana tunani. Matan sunyi magana, amma bai gaya musu ba. Sai da yaga sun damu musamman ladifa sannan ya tarasu.
Ya kallesu yace “Ina so ku tayani da addua wani matsala ne a wajen aikina, kuma gashi nayi orde kaya custume sun tsare kayan.” Jimami suka shiga yi sosai.
Acikin lokacin kankani, ramadan samunsa yayi baya, sam ba kamar daba! saboda matsalar kayan da aka rike ga wajen aikinsa albashinsa ana biyar ragowar kudin da bai cika ba, haka yasanya gidan yayi kiyau yayi dry, duk cin dadin da ake duk babu, hakan ya sanya safna duk ta shiga damuwa ta fara rashin mutunci. Idan tace ramadan ya bata kudi ya ce babu takan ce wallahi ita ba ta yarda ba. Dan ba zata zauna ace yanzu miya ma ba nama, ko lemu da kajin ma da ake siyowa babu. Sai dai suci kawai lami. Al’amarin da ya sanya safna ta tsiri cewa aiko ita ba zata iya da wannan talauci da ya kunne mai kai ba.
Kadan kadan take zarar kudin tana canjawa tana siyan abubuwan da taga dama. Dan har kayan daki ta canjawa uwar. Ta sai mata fridge. Wanda dama haka uwar ke so. Nan fa habaici ya dad’a yawaita.
Anan sana’ar ladifa tayi aiki sosai dan da ita take taimakanr ramadan awajenta yake rancen kudi. Wanda alokacin laila ma ta fara bussness tana saida takalmi da mayafai ana
bata tana kara nata akai.
Bayan wasu watanni.
Safna so take kawai ta samu hanyar da zata rabu da auren ramadan, domin dama son kudinsa yafi yawa, akan komai data aureshi, sai kuma burgeta da yake saboda kirarsa ta maza, dake sanyawa takejin sonsa. Zamu iya cewa kacokam! Auren kudinsa da sha’awarsa ne ya sanya ta aureshi. Amma yanzu tun da ya zama ba kudin yanzu takejin haushi, kuma tana tsoron ya gano wataran itace ta dibi kudin nan. Shi’isa take ta san samun hanya.
Wata rana Laila da ladifa na tsaye a wajen hanyar kitchin din ladifar suna hira. Sai ga safna nan ta dawo daga unguwa. Da gangan ta bangaje ladifa ta turata gefe “dallah malama matsa zan wuce,”
Hakan ya sanya ladifa ta kifa, saura kadan ta fada kan farar kujera dake saitin kan cikinta. Sai da laila ta rukota. Duk da haka ta bige da kugunta.
Wanda a idon ramadan dake saukowa daga sama. Da sauri ya sauko cikin fushi yayi shashin safnar, tana tsaye tana kokarin cire kaya ya daka mata tsawa ” safna baki da hankali ne wai?mai ta miki zaki tureta? yanzu data karasa faduwa kan cikinta fa.” “Dan Allah kaga ka kyale ni, idan zafin talaucin daya sameka ne to bani na kar zomanba. ”
Mari ya kaiwa bakinta sai ta dafe da sauri ta fasa kuka “wallahi tallahi ba zan yarda ba, yau na bar zama dakai ka daki aurenka, wallahi sai ka sakeni,”
“Ai saiki zo ki makureni na sakeki.”
Da sauri ta cakumi rigarsa. “Wallahi idan baka sake ni ba saina caja maka bala,i da masifa.” Cikin fushi ya kai mata mari ta shiga Allah ya isa santa.”
Nan ya kuma bata wani ta shiga kuka wiwi, dama haushin rashin mutuncin da take mai yake yi. Cikin kunar zuciya yace “kin dauka idan na rabu dake zan kasa rayuwa ne? wallahi bakya
gabana ki tafi na sakeki.Tunda haka kike bukata.Kuma ki bar min gida.”
Cikin kuka tace “tafi nono fari, mai na sama ya bawa na kasa,” sai kuma ta kuma fasa kuka, dan sai taji bata so sakin ba, ko ba komai tana son zama da shi, tunda yana iyajure jarabar bukatarta.
Hmm na tausayama ramadan don yaji jiki