NAYI GUDUN GARA CHAPTER 7
NAYI GUDUN GARA
CHAPTER 7
Bayan sati day:
12:pm
Ranar weekend ce, wanda aranar duk wani magidanci ke zama cikin iyalansa. Hakan ta kasance da Ramadan. Yana zaune akan doguwar kujera yana wasu rubuce-rubuce a wani file.Yana sanye da T shart blue,jins tree quater. Yayinda Lad’ifa baby, ke kitchen tana kiciniyar yin waina/masa, wadda Ramadan katsahan ya ce yana da buk’atarta, ba a dad’e da kawo markad’en shinkafar ba. Tana tsaye cikin kwalliyar swiss lace black da ratsin blue ajiki, an mata riga da siket daidai jikinta, kalarta dace da fatarjikinta mai haske, ta kafa d’aurin da ya fito da shape d’in kyakkyawar fuskarta, da ke d’auke da makeup mai sanyi, sai fldda k‘amshi ta ke mai sanyaya zuciya. Tana tsaye aiki ya kacame mata, ga shi ya ce yana buk’atar tai mai zob’o drink mai abarba. Alayyahu take yankawa, tana yi tana duba wainar, Idan ta kwashe, sai ta kuma zuba k’ullun wainar, a haka har ta gama ta zuba a warmer, ta kuma gama yankan alayyahun ta wanke ta zuba a had’in taushe mai d’auke da naman kaza, sai tashin k’amshin girkin ya ke, wanda
duk ya bud’ad’e gidan. Tana cikin yanka abarba taji ya kwad’o mata kira. Da sauri ta fita ta shiga falon fuskarta d’auka da tattausan murmushi tace
“zaujina har yanzu aikin ne?.”
Kallonta ya yi, ya ce “wallahi kuwa ladi’fa,je ki d’aukon waya ta, tana kan drawer.” Nan ta tafi da sauri saboda girkinta. Bayan ta d‘auko sai wayar ta fara ihun kuka, wato ana kira, da sauri ta k’ara sauri dan kar ta katse, kanta k’arasa har ta katse, sake bugowa akai idonta ya sauka a kan sunan da ke kan screen d’in, ta ga an saka habibty, dam! gabanta ya bada k’uwwa.
Cike da sanyin jiki ta k’arasa gabansa, ta ce “ga shi.” Ya sanya hannu ya karb’a, nan ta tsaya tana son ganin yanda zai amsa wayar. bai d’au kiran ba, harta katse, ya kalleta. “Wai ba kin d’ora girki ba ne?.”
“Oh! na tuna.” Ta fad’a da sauri ta koma kitchen d’in zuciyarta na karakaina, sam! ta gaza ci gaba da aikin yanda ta faro da farko, dan duk sai taji wani irin gajiyawa ta mamayeta.Kawai sunan Habibty ke kaikawo a zuciyarta. ‘ Lumshe ido tai tana karanto duk adduar da ta zo bakinta, a haka har ta d’ora ruwan zobo ta zuba abarbar da citta, ta rufe suka hau tafasa.
Nan ta maida hankalinta kan miyar, harta gama ta kwashe ta zuba a warmer, zob’on ne ta gama had‘a shi daga baya. Ta barshi zafin ya d’an huce na wasu mintuna, sannan ta saka a Firiza dan yayi sanyi
Ta d’auki warmers ta kai dining ta jera. Kallon agogo tai taga har 1:30 ta ce. “My love life, food is ready.” Murmushi ya yi, “okey amaryata.” Ta kalleshi da d’an murmushi ganin yanda ya amsa mata da kulawa. “Ko nazo na tayaka kwashe takardun.ne “No ban gama ba zan ci gaba, yanzu sallah zanje nai, sai nazo na kwashi my fovourite food d’ina.” Ya fad’a yana mai mata murmushin da ke sanyata ta susuce. Harya fice daga falon tana mai kallon bayansa. Wani dad’i ne ya ziyarci ilahirin gangarjikinta,ta kalleshi cike da k’auna, tana mamakin canjawarsa yau, lalle ta yarda babu wani yanayi mai d’orewa kullum, dole wataran kai kuka wataran akasin haka, Addua take azuciyarta kan Allah ya sa wannan canjin data gani yau
ya d’ore. Nan ita ma taje tai alwalar ta tada sallahr, bata dad’e da idarwa ba, ya dawo gidan. Ta sauko ta iske shi yana k’ok’arin Tafiya dining, tana k‘arasawa taja mai kujerar dining d’in ya zauna, ya kalleta ya yi murmushi lad’ifa ta kenan. ‘ ‘Wayyo my real Ramadan is back,‘ ta fad’a azuciyarta, tana maijin wani irin dad’i, sai sakin murmushi ta ke. Nan ta zuba musu a flate d’aya. ta kalleshi cike da kallon soyayya ta ce “zobo drink yana flrji dan ya k’arasa sanyi.” “Okey Lad’ifa ta.” Matsowa tai ta zauna kan cinyarsa, ya saki murmushi. “Ya dai lad’ifata?.” Ta ce “ka manta ne, ai hannuna ne zai ciyar da kai.” Janyota ya yi, ta d’an kwanto jikinsa yana shakar k’amshinta. “Lad’ifa baby kenan.”Murmushi tai tanajin wani irin dad’i aranta, dan abinda ta ke buk’ata ga mijin nata kenan,
wato kulawa da soyayya, domin ita Allah ya halicci zuciyarta da san wad’annan abubuwa guda biyun, shi’isa ta ke bashi kulawa shima dan ta samu, amma ta kula ba ta cikin mata masu wannna sa’ar , sai dai kadaran kadahan, yau fari gobe bak’i, duk da cewa dama zaman tare ya gaji hakan.Kuma akowanne gidan aure.
Kallonsa tai cikin lumshe idanuwanta, ta sanya hannu ta gutsuro wainar da miyar ta kai mai bakinsa, ya kalleta ya tauna yana d’an sakin fuskarsa, alamar dad‘in girkin na shigarsa, jira ta ke ta ji ya ce girkin ya yi sweat, amma shiru kakeji, sai ba shi ta ke yana karb’ewa itama tana ci, da alama ba za ta samu wannan yabon na lafazin baki ba. Yanayin da suke ciki yana shigar kowanne ba kad’an ba, suna jin dad’in yanayin sosai, shi da kansa yana jinjina yanda take tafi da shi, amma girmankai ya hana ya nuna mata cewar fa abin ya yi mai, saima wani basarwa da yake, yana jin cewa yes, dole ne ai mai tun da shine shugaba. Labarin zuciya akace atambayi fuska ,yau da gobe tak’i wasa, tabbas! ta kuma gane yanayin mijin nata a yau, ta gano yanayin da yake yi in abu ya yi masa dad’i, tana kallon idonsa ta san santin yanayin da suke ya keji, kawai dai ba zai nuna bane, ko hakan ma sai taji ya bata farin-ciki, wasu ma basu samu kamar hakan ba.
Sai da su ka yi nak! sannan ta harhad’a komai ta maida kitchen, shi kuma ya d’auki cup, cike da zobo drink yana kurba yana lumshe ido.
D’an farin-cikin da ya sanyata ne a yanzu, ya sanya taji wani kuzari ya shigeta, ba tai k’iwa ba wajen wanke kwanunkan da ta b’ata ba, sai da ta gyare kitchen d’in tas! sannan ta koma falo tana maida numfashin gajiya. ‘ ldanuwansu na kan Tv suna kallo, lokaci-lokaci ya kan duba wayarsa, k’asa»k’asa ta ke kallonsa, babu kallo d‘ayan da za tai ma Ramadan, ba tare da sabuwar soyayyarsa ta d’arsu aranta ba, tana son mijinta so mai yawa, shi,isa ta ke tunanin,shan wahala akomai nasa, abinda ta gane kenan Mik’ewa tai cikin salon tafiyarta, ta isa gare shi, Kanta ta d’ora a saman cinyarsa, tana shafar sumarsa cikin salon kauna yanajinta amma bai motsa ya kula taba. Ganin yanda ta ke mai, ya sanya shima ya shiga shafar gashin kanta, nan ta sauke hannunta tare da lumshe ido, suna hira jefi-jefu har bacci ya kwashe lad’ifa. Misalin k’arfe hud’u kiran sallah ya tashe ta, ta ganta mik’e akan kujerar, murmushi ta yi, dubawa tai bata ganshi ba, hakan ya nuna mata da ya fita, sai wayoyinsa da ke zube a wajen. Mik’a tai, ta tashi da addua a bakinta, ta yi hanyar sama, dan ji take jikinta ya yi wani iri. Tana zuwa d’akinta ta fad’a wanka, bayan ta fitO ta yi sallah tare da adduoi ta shafa, sannan ta yi gaban mudubi, tai shafe -shafenta, ta sanya man baki, tare da mulka powder, ta saka doguwar riga k’irar k’asar turkey daidaijikinta, kalar pink and red, ta feshejikinta da kayan k’amshi, ta yi kyau ta sauka k’asa. Dan goge-goge ta hau yiwa falon, duk da cewa tas yake, tana gamawa ta sanya turaren wuta, ta zauna ta d’au hisrul muslim tana karantawa. Tana nan zaune, zaujin nata ya shigo, shima ya canja shiga, ya kalleta yace, “ladifa baby kin sha barci.” Murmushi tai, “E wallahi zauji na.”
Za ma yayi suna hira, ta shi tai ta koma kusa da shi ta shige jikinsa.
‘Ta fiya sanjiki ita dai, ya ayyana aransa.’ Kallonta ya yi ” Ke fa san jiki ne dake kamar mage.”Dariya tayi “haka nan na ke wallahi, indai da makusanci a wurina, to ba ni da haufl, kuma hajiyata nafi wa haka, yanzu ka ga kuma kaine madadinta.” “Good,” ya ce yana murmusawa. K’aramar wayarsa ta d’auka ta shiga game. “Zauji har yanzu fa wayar ba ka sayo min ba, ga shi ina missing mutane.” “Kin manta abinda na fad’a miki kenan ko?.” Shiru tai ba ta sake magana ba.” Sun dad’e a haka kamar kurame, daga bisani ya tashi ya haye sama. Wayarsa ta kalla, nan wata zuciyar ta ingiza ta da ta d’auka. Ai da sauri ta d’auka, sakon msg ne ya shigo ta whatsap, nan ta samu kanta da afkawa ciki. Ba wasu tarin sak’onni bane gareshi . Sunan da ta gani ne ya doki k’irjinta, taga an sa ka habibty. Da sauri ta danna kan sunan, sai ga tarin maganar da ta gabata wacce su kai, tiryan -turyan ta shiga karantawa zuciyarta ta tsinke wasu kalaman ma duk basu dace ba, har dasu
maganar batsa, runtse ido tayi tana jin kamar ta sume. Maganar k’arshe ta bata haushi inda ya ce, wato habibty kina da kyau kamar balarabiya, wallahi ban ga macen dake gabanki ba adai idona.”
lta kuma ta ce “Ai ban kaika kyau ba, kafa flini kyau.” Wane ni na kaiki . “So nake kawai na bude ido na ganki d’akina, gani ga ki, ai bansan farin cikin da zan ba.
Ta sanya dariya. Wani wawan kishi ne ya bugu kirjin lad’ifa ta runtse ido. Bayan gama karantawar. Kuka ta shiga rairawa ahankali. Kamar ya san ya bar b‘arna, ya dawo da d’an sauri, ganin tana hawaye ya sanya ya tsaya turus! “Mai ya faru ne ladifa, meya sanya ki kuka?.“
Cikin fushi ta mik’e tsaye, cikin d’aga murya.” Zauji mai nayi maka arayuwa ne kake min haka? me na rageka ne ka ke mini irin haka? Yanzu dama kana da budurwa.? Ta fad’a da kaushin murya.
Kallonta kawai ya tsaya yana yi, duk sai ya ji wani iri, bai so hakan ta faru ba.
“Wato ni ban isa ka ce mini kinyi kyau ba. Kina da kyau. Amma ga shi kana gaya wa wata a waje. Yanzu bankai ka dinga ce mini habibbty ba? Sai wata banza can awajen. Mai take maka wanda yafi nawa. wallahi ba za ta tab’ai maka abinda ya kai nawa ba..” “Ka yi magana zauji,” ta fad’a da k‘arfi kanajin maganar, kasan cikin kishi take. “Baka tab’a fad’a mini suna mai dad’i ba ,sai sunana na yanka, a matsayinmu na masoya.Ka gaya min nai maka?,” ta fad’a cikin kuka. Shafa k’eyarsa ya yi ya ce , ” Rigima,” ahanakli. “Saurara kiji Lad’ifa, me ya kaiki bincika min waya?.” Ya fad’a cike da borin kunya. Bata bashi amsaba, sai ma kuka data kuma fasawa. “Wallahi saika gayan wacece ita.” Ta fad’a tare da doka wayar da k’asa. “Ba zan fad’a ba ladifa, ina lallab’aki ma sai wani botsarewa kike, to kar Allah ya sanya ki tsaya, kuma ki sani budurwatace, kuma aurenta nake sanyi, dan haka ki zauna da shiri.” “Wallahi baka isa kai min haka ba. Yanzu na cancanci kishiya? zauji nice fa Lad’ifa.” “Yas Kece lad’ifa. Allah ne ya umarcemu da mu yi, dan haka duk haukan kishinki ki adana shi.” Hadiye kukan ta yi. “Okey, okey,” take fad’a kamar wata zautacciya. Cikin kuka ta ce naji “abinda ka ce, amma ya ci ace kana gaya mata kalaman dani baka min? domin nice tafi dacewa da hakan.” Tsaki ya yi, ya d‘au wayarsa dake yashe a k’asa. “Ya kalleta cikin had’e rai, ban san shirme? idan kin gaji kya hak’ura.” Shan gabansa ta yi tana hucin kuka. “Wallahi Ramadan ba ka isa ka fita ba, dan na san wajenta zakaje.” Fincike ta yayi yamatsar da ita gefe. Ya fice yana huci. Zubewa ta yi awajen ta shiga raira kuka mai tsuma zuciya. Ta dad’e tana yi, k‘arshe ta Tashi tana share hawaye. Da tunanin yanda suka kasance cikin farin ciki tun safe amma ga shi duk komai ya gushe. Sallama ce ta katse mata abinda take da niyar fad’a, ido hudu su kai da karima, yasa ta
rutse ido, bata so ta ganta acikin wannan yanayin ba Da hanzari ta shigejikin yayartata tana kuka. “Subhanallah! menene wai Lad’ifa? Share hawaye tai. “Babu komai ya karima, kece tafe da yamman nan?!‘ “E nice, fad’amin.” “Babu komai fa yaya, kawai kaina ke ciwo.”
Ni za ki mayar yarinya k’arama kamar yanda ki ke? ai ko makaho ya tab’aki,ya sam kina cikina cikin matsala..” “Babu fa.”
Rik’e baki tai ta ce ” Ki na da wanda ki ke dashi bayan ni, ne idan ba ki gayan ba, to we zaki gayawa, meye anfanin ‘yan uwantakan? idan kuma ba zaki gayan ba, yanzu na kira hajiya.” “Aa ba sai kin kira ta ba, zan gaya miki,” ta fad’a tana hawaye. Nan ta kwashe duk abinda ya faru ta fad’a mata. Cike da jimami tare da takaici, ya karima ta ce. A gaskiya lad’ifa zan fad‘amiki, gaskiya kece duk me laifl. “Ni kuma.” “Ko kinsan cewa, waya a zamanin nan na kashe aure, ko kinsan binciken wayar miji, in har kikai karo da wani abin da bai miki daidai ba, tamkar bud’e shafln bak’in-ciki ne a rayuwarki, domin wasu mazan wallahi akwai tarin rashin gaskiya a wayoyinsu, to ayanzu binciken wayar miji ba ya haifar da komai sai matsala,ko a cikin addini ma bincike baida kyau.
Kinyi wauta da ki ka binciki wayarsa, k’azantar da ba ka gani ba ai tsafta ce, yau da ace ba ki duba ba, da tuni kina cikin farin-ciki, amma gashi kinjanyo wa kanki matsala,kin je kin gano abinda zaki dad’e kinajin haushi, Ai a zamamin nan wasu mazan auren wallahi ba ka rabasu da ‘yan mata, ke abin ai ya zama ruwan dare, wani yana yin budurwa ne ba wai dan ya aureta ba, Aa sai dan kawai yana san ya ganshi da ita, Wani kuma aure ya ke san k’arawa,to duk tsiyarki wallahi idan auren ya so yi sai ya k’ara, ba gwanda ki d’auke idonki ga duk abinda zai d’aga hankalinki ba, to daga yau na hane ki da binciken wayar miji.” Sannan abu na gaba, kinga abinda ya sa mijinki ba yajin kunyar nuna miki yana da wata a waje, yake waya da ita a gida, to abin daga wajenki ne, ke kika bashi k’ofa. Wallahi da baki bashi ba, da sai dai ya yi ta b’oye-b‘oye.” “Kamar ya, yaya karima?.”
“Ta ya ya za ace da kinga yana waya, ko kinga alamar da mace ne, duk sai ki birkice, ki hau zargi, babu irin kawai cin nan, to kin fito mai muraran wuki-wuki, kin nuna kamar kin gano shi, to shi kuma aganinshi shine gaba dake, ta yaya ba zai nuna miki Eh hakane ba, komai ta fanjama-fanjam! ai irin wannan abun da salo ake yi yanda shi kanshi zaina d’ari
d’ari.” Kuka ta saka, tqce”yaya baki san waye Ramadan ba..” Dariya tai “aurene k’anwata, kowanne da yanayin jarabawarda Allah ke saukarwa Ma’auratan, kuma a zamanin nan da tsohon aure da sabon wallahi duk kowanne da nasa matsalar, ki k’ara hak’uri, kuma kibi abinda na gaya miki, Sannan abu na gaba, ta yaya zaki wage baki kina rusa ihu gaban miji, shi kanshi kukan da kissa ya kamata kiyi shi, yo kina abu cikin rashin nutsuwa hauka-hauka kina ihu, ai sai ya samu logonki, wannan shine abinda ya sanya ma mijinki bai fiya nuna damuwa ga kukanki ba, to koyaushe bud’e baki kike kina kuka,ci ke da k’arfi da rashin nuna lumana, Sannan da ace daki kaga komai na wayar, da baki haukace da kuka ba kina fad’ar maganganu, ai a yanda yazo miki, yanda ki ka kula jikinsa yayi sanyi yana borin kunya, sai ki bishi cikin kissa da salama ki magantu,ki nuna kalar tausayi, ki gaya mai kalaman da zaiji shi kanshi bai kyauta ba,idan ma kukan za ki yi, to kiyi shi cikin kissa irin wadda Allah ya baki, Domin kishi ba dad’i, wata in batai kukan ba bata jin dad’i, wasu kishi kan sanya su manta hankulansu, ki kula.””Yanzu ya ya, ko haihuwar fari ban ba,ace yana neman zai aure, ce wafa za,ai ni ce bana kulawa da shi.” Kin ga auren ya tabbata ne? K0 ma ya tabbata ai ba a kanki zata zauna ba. Ki yi ta addua, dan ba ta fad’uwa k’asa banza, addua makamin mumince, ke da sauk’i ma da baki da matsala da ‘yan uwan miji, da ace wasu ne da tuni sun sako ki a gaba, ganin wata wajen goma ba alamar ciki.”
Hmm! tai yaya, hajiyar Ramadan ba ruwanta, amma kin ga k’anwarta da yayar Ramadan, in dai muka had’u sai sun goranta min, dad‘inta ma abin bai tsamari ba, saboda hajiyar na tsawata wa.” “To kin ji, ki godewa Allah da hakan ma.” “To nagode yaya.” “Yauwa kinga dama kayanki na kawo,” ta zaro bokiti fari, “wannan garin k’arin girman kirji ne, dama shi zaki nayi, wannan shi kuma na hips ne. Kinga duk had’in masu kyaune, duk abinda ake cine aka had’a, ba masu cuta ga laflya bane saima su kara inganta,lafiyar Sannan ki samu dankalin turawa ki dafa shi ya dahu, ki dama shi ki zuba madara, shi ma yana k’ara hips sosai! Allah ya sa a dace, kin dai rik’e abubuwan dana gaya miki ko?.” “Ta d‘aga kai. “Insha Allahu zan samu lokaci na zauna saina dad’a sanya ki a hanya.” Dariya tai yaya kenan.” Haka su kai ta hira har zuwa magariba, ta taya ta sukai girki, daga baya driver gidanta yazo ta tafi da ita.. Har k’arfe 9 Ramadan bai shigo gidan ba, duk ta damu sai kallon hanya ta ke kamar mara lafiya, ga haushin sa da takeji aranta, ga kuma san saka shi a ido, dan gidan ya fara bata tsoro, dan ma ta najin b‘uruntun maigadi, ga shi basu kawo wuta ba, kuma ita ba iya tada inji za tai ba.
Ba shi ya dawo ba, sai goma da rabi na dare, tanajin dirin motarsa ta saki numfashi, saboda tasan yanzu tsoron zai ragu, da ya shigo, sai ta kau da kai ta mik’e tai mai sannu da zuwa ya amsa acikiciki. Akan kujera ya zauna,sai kuma ya tashi yaje ya kunna inji ya dawo, haske ya gauraye. Firji taje ta bud’e ta d’auko ruwa da kofi ta ajje mai, ta zuba ta mik’a mai ya sanya hannu ya karb’a. Haka kawai takejin sanyi aranta, domin tun bayan tafiyar ya karima ta ke adduar Allah ya sanyaya zuciyarta. So take ta nuna mai babu komai, amma ta kula sai basarwa ya ke. “Zauji abinci fa na dauko?.” Hannu ya d’aga mata,”ba naci.” Ya tashi ya bar wajen.
Binsa da kallo ta yi, “lalle adake ka a hanaka kuka,” ta fad’a tare da tallafe hab’a, dole itace a k’asa, ba zata bari shaid’an ya rab’eta ba, domin aljannarta ta ke nema, neman aljanna kuwa da wuya. Saman ta hau ta shiga d’akinsa, yana wanka, nan ta flddo mai da jallabiyya ta feshe ta da turare.Ta zauna ya fito d’aure da tawul yana goge kansa, ya d’ora idonsa a kanta, ya yi kicin -kicin da fuska, “me kike anan? Ko yanzun ma zuwa kikai ki d’agan murya da ihu?.” Raurau tai da ido.
“Amma Zauji kasan kaine ka b’atan rai k0, kai min abinda bai dace ba.“ Dagatar da ita ya yi. “ban tambyeki ba.
Kawai ina gargad’inki da next time, kar hannunki ya k’ara bincika min waya na gaya miki.” “To amma ta yaya za ka ce ba zan tab’a wayarka ba?.” “Ban hana ki tab’awa ba, bincike ne bana so na gaya miki.” “Naji insha Allahu.‘Magana za ta kuma yi, ya kalleta “dan Allah bana san ganinki, yau kin b’atan rai.Ki futa kawai.”
Haushi ne ta kamata ta tashi ta flce zuciyarta na tafasa, d’akinta ta koma ta kwanta ko barci ta kasa. Ahankali kuka ke zuwar mata, ‘wacce irin zuciya gare ni? mai yasa zuciyata ba ta jure fushinsa, mai yasa bana iya tsawaita fushi da shi?
Kai min lefl, na kawo kaina na hak’urce abinda kai min, amma kuma kai da ya kamata ka lallashe ni sai kuma ka hau sama. Ya rabbi.” Ta fad’a idonta na tsiyayar hawaye. Ganin baccin ya k’i zuwa, sakamakon bakin-cikin da ya taru ya mamaye zuciyarta, na farko kishi, na biyu fushin da ya ke da ita, na uku abinda ya yi mata yanzu duk su ka had’u suka tokare mata k‘irji,nishii take kamar zuciyarta za ta faso. Alwala ta d’auro, ta yi kyawawan sallolinta, ta yi raka’a yayi wajen goma,k’arshe ta sallame, ta zauna tana zubawa annabi salati, tare da istigfari tana adduar samun salama a aurenta, ta dad‘e tana yi, har bacci ya yi awon gaba da ita.
Gyara hularsa ya ke, ya ciwo wankansa cikin brown shadda mai k‘aramin kud’i, sai kamshin turare ya ke daidai iya wadatarsa, yana tsaye tun wajen biyar da rabi na yamma a kofar gudansu laila , yana jiranta ta shanya shi.Sai kawai ya tsiri goge adaidaita sahunsa yana yan wak’e-wak’e.
Sai da ya kuma buga wayarta, sannan ta ma tuna da shi, tana zaune sai dariya ta ke tana ganin wani comedy a wayarta, tsaki tai. “Ni ka takuramin, nama manta da kai,” ta sake sakin tsaki
ta mik’e ta d’au mayafinta ta fita, tana tura k’irji gaba tana taku d’aid’ai, sai yatsine fuska take. Yana ganinta ya saki murmushi. Ya zagayo ta daidai inda take “kedai koyaushe me kyauce.” “Allah ko?.”
“Ya kalleta wallahi kuwa.” To ya dai? naga sai kira na kake .” “Hira nazo kuma da muhimmiyar magana..” Dan tsaki ta saki aranta “inajinka.” Maganar aurenmu ce mana, wallahi kullum mama sai ta min maganar aure.” A hakan? Ta sanya dariya.
Da sauri ya kalketa, me kike nufi?.”
“Ina nufin kana da kud‘in aurena kenan ka shirya.?.” “Sosaima ki amince kawai, wallahi ni ba yaro bane jikinne dai kawai k’arami, ko yau ma sai da maman tai min magana, wallahi kuma ni babu budurwar da nake ganin zan iya kasancewa da ita a inuwar aure sai ke, wallahi ina matsanancin sonki so mara musaltuwa.” ‘
“Hmmm murabus kenan, kana da gaggawa, to nikam ka dad’a hak‘uri, ba muna tare ba, idan ni rabonka ce aidole ka aureni.” Allah k0, to ki ba ni dama azo ai magana dan asan dani.” Wani k’ask’antaccen kallo tayi mai, “zancen kake so.” “To ni zan koma ciki.“ “To kinga yau da munshari zan kwanta.” Nan ya burga mashin d’in ya wuce.” Tsaki tai ta shige gida, tana cewa “mara aikinyi kawai.”
Yau kwana biyu kenan yana fushi da ita duk ta damu, ko abincinta ya daina ci kullum sai ta ajje, amma haka za ta tarar baici ba, sai dai ta bawa maigadi.
In yana zaune awaje, ta zauna sai ya bar gun kuma baya dawowa sai k’arfe tara ko goma. A d‘an kwanankin duk ta rame tayi dana-sanin tab’awayar, bata san zai zame mata matsala ba, tana zaune misalin k’arfe tara na dare, cikin kwalliya ta daukan hankali, ba wani kaya mai nauyi ta sanya, ba riga ce top pink iya gwiwa, sai wando fari,tayi kyau sosai. Sai tashin k’amshi ta ke, cikin turaren da yaya karima ta bata, wanda ya kasance na daban. Ta ci alwashin kota yaya sai mijin nata ya kulata sun daidaita. Shigowa ya yi, bai ko kalli inda take ba, bai ma tsaya ba, direct sama yayi. Jikinta ya kuma yin sanyi. Kallo take, amma bata ma gane me take kalla, ba k’arfe goma ta mik’e ta haye saman a hankali, ta ka k‘afafuwanta take,jikinta na dan tsuma,ta tura k’yauren d’akin nasa, yana zaune ya fito daga wanka sai goge jikinsa yake.Bai kalleta ba, kuma bai amsa sallamar ba. Mai ta d’auka ta shiga mulka mai abaya ya dakatar da ita cewar ,”Ke
Matsa na lce.” “Please zauji,” ta fad’a cikin sanyin murya mai jan hankali. Ci gaba da shafamai take cikin salo,har ta gama, tajuyo ta tsugunna gabansa zauji. Bai amsa ba sai k’ok’arin fesa body spray ya ke, ‘yar k’ara ta saka. “Wash! idona.”
Ya kalleta ya dai?.” “Idona turare ya shiga.”
Sai hawaye sharr! dama akusa take, plsesae hure min idon.” Nan ya shiga hure mata, ta fad’a jikinta tana kuka, wayyo zafl da yawa.” “Ke meye haka.” Ya fad’a fuska atamke, ta shi ki bar dakin nan.” Kuka ta sanya, “zauji ba zan iya taflya ba sai ka yafemin, nasan na yi kuskure.” Ta fad’a tana dad’a shigewa jikinsa. “kayafemin mijina.” K’amshin turarenta ne ke dad’a shigarsa, wani dad’in turaren ya keji gashi yanda take kukan cikin kissa duk ta gama birkita shi. Ga kuma haushinta da ke dank’are aransa. Mik’ewa ya yi, ya nuna mata k’ofa ya juya. Kukan kissa ta sanya cikin raunannar murya, ta rungume shi ta baya “I‘m so sorry dear na,take ahankali tana nuna nadamarta, duk ta gama yamutsa tunanisa, shi kuma hakan sai ya ke dad’a sanya shi, a wani hali. Daga K’arshe sai da ta sanya suka raya sunna, cike da kewarjuna,wanda adaren suka shirya kamar ba abinda ya faru. Suna kwance bayan komai ya lafa. Ta kalleshi tace”ka yafemin?.” “Sosai Lad’ifata, ki kula next time ba na son hakan ta kuma faruwa, ya fad’a yana shafar sumarta. Nan ya ke sanar da ita zuwan abokinsa da madan dinsa gobe.”
Hmm