NI DA PRINCE CHAPTER 13
NI DA PRINCE CHAPTER 13
Yau juma’a salman na kwance har wajen 10, salma tad’an tabashi ya motsa tare da bud’e ido cikin kalar bacci, yace ya? Tace skul fa? Yace bazani ba, yafad’a tare da juyawa tai ajiyar zuciya tare da mikewa,jawota yai takoma ta zauna tare da kallanshi, ya d’ago a hankali yace kishirya zamuyi tafiya bayan an sauko, takalleshi tace zuwa ina? Ya saketa tare da juya baya ta kalleshi aranta tace ko ina zamu?+ Mikewa tai ta fita falo, tana zaune tana kallo, salman ya fito, ta kalleshi har yayi wanka tace ka tashi? Yace umm tare da zama, farha ce ta shigo salma ta harareta aranta tace yau kuma? Salman ya kalli farha yace kin iso? Salma ta kalli farha kin iso? Farha ta kalleshi tace na iso yayana😊, takalli salma tace hi in law salma tace sannu, farha ta kalli salman tace yaya rakani zakai fa☹? Salman yace ina? Tace kai yaya kafa sani, salman yace yanzu? Yafad’a tare da kallan salma dataci magani ta kafeshi da ido, salman yad’auke kai yace muje, farha ta kalli salma ta saki wani murmurshi, tai gaba. Salma ta makama salman harara tai d’aki, d’aki da sauri ya kalleta yai murmushi tare dayin waje. Salma tai d’aki tare da kwanciya tad’au pillow ta d’aura akanta. Salman na fita suka karasa gun mota da farha, yad’au waya yakira wani, suna zuwa bakin mota farha taga driver takalli salman, salman yakalli driver yace habu kiranka nai zaka kai farha unguwa, dasauri farha takalleshi tace yayana😳? Salman yace inzaki fita kid’inga neman habu zai dinga kaiki, yana kainan yai gaba. Farha tabi bayanshi da kallo tana kiranshi ko kulata baiyi ba, habu yace muje hajiya? Farha cikin masifa tace bazani ba😡 tai cikin gida da sauri tana shiga tad’auko akwati ta shiga zuba kaya tana hawaye. Salman na shiga yai d’aki, a kwance yaga salman ta rufe kanta murmushi yai tare da zama kusa da ita, ya zare pillow din, ta d’ago a hankali ta kalli salman, cike da mamaki tace har ka dawo? Ya kalleta yace ina zani da? Tace ba fita zakuyi ba? Yace ahh yazanyi? Matata sai kishi? Tace bafa kishi bane☹ yace ummm to menene? Tace kawai dai…..yace hmm kinshirya mana kayan? Tace bakace sai an sako ba? Yace nafasa mutafi yanzu. Tace wai ka fad’a? Yace na sanarwa mahaifina ko akwai wanda yazama dole infad’amai bayan nan? Takalleshi sannan tai murmushi tace nibance ba, ahankali ta mike ta jawo karamar jaka, tafara zuba kaya tana gamawa yace muje, tace wai saurin nameye?yace so nake insami sallah acan, tace to. STORY CONTINUES BELOW Sunfito tasanar da hanne, nan sukai waje suka shiga mota, suka fara tafiya, sunyi tafiya mai nisa harta daina ganin gari, wudil taga ansa ta kalleshi tace wudil? Yai murmushi tare da gangararawa, sai da suka je karshen garin wani d’an karamin had’adden flat suka isa, ahankali mai gadi ya bud’e gate d’in salman ya karasa yai parking, salma ta shiga kallan gida sosai gidan ya burgeta gashi ba girma gareshi ba, sai kyau da tsari, mai gadin ya iso da sauri ya kalli salman yace yarima barka da isowa, shekaru dayawa? Salman yace ashe zaka gane? Yace ina na isa namanta dakai? Bayan nasan bamai zuwa sai kai? Salman yai murmushi ya fito,mai gadin yai saurin budewa salma kofa tare da gaisheta yace kai uban gidana masha Allah, salman ya kalli baba tsoho yace kai baba? Nan yad’au jakarsu yai ciki, salman ya kalli salma yace kishiga bari nai sallah tace to. Salma tashiga ciki tare da kallan gidan,da alama ana kula da gidan, a hankali ta karasa cikin falon mai cike da tsari, ta karasa gun wani hoto dake kusa da tv, ta d’aga,tare da gogewa da hannunta salman ne da mahaifiyarsa, tagane mahaifiyarsa ta kurama salman ido, tace suna kama,ajiye pic din tai ta d’auko tsintsiya tafara kad’e falon tagama share falon tai d’aki, sai data gama ta shiga wanka, tana wanka taji motsi, takalli kanta daga ita sai towel, tanaji salman ya murd’a kofa da alama ya fita, tai saurin fitowa, tana fitowa shikuma ya tuna yabar wayarsa a d’akin ya murda kofar, salma ta juyo a rude, salman ya kalleta daga sama har kasa, d’an karamin towel d’in dake jikinta, duk cinyoyinta a waje, ya kura mata ido,itama kallansa take da sauri ta juya baya, salman ahankali ya tako inda take, yasa hannunsa a kugunta, idanta ta runtse, salman ya kwanto ta bayanta tare da sakin ajiyar zuciya, salma tai shiru tsoro duk ya kamata, ahankali ya juyo da ita,idanunta a runtse suke kam…..kawai jin bakinsa tai anata, wani salo salman kewa salma, jitai kafarta bazata d’auketa ba ahankali yakaita gado, ganinai ya zame towel din jikinta, umm nikam ganin yanda salman ya rud’e yashiga aikama salma wasu sakonni dasu kad’ai sukasan ma’anarsa sam sun fita daga hayyacinsu as wannan shine na farko ga kowannensu, nikam ganin hankalinsu yabar jikinsu ahankali naga salman ya d’ago ya hararen yamin alama da kofa, dasauri nafita tare da ja musu kofa……..masu karatu kuyi hakuri bazan samu damar d’auko rahoto ba dan salman ya koroni😭😭 3 Salma taji jiki salman sai daya tausaya mata, waya ya d’auka yai searching nan ya tashi ya cika baho da ruwan zafi ya d’auketa kamar yar tsana yasa ta aciki, tad’anyi kara sai dai daga baya taji dadin ruwan, salman dakanshi yataimaka mata tai wanka, sannan ya d’aukota ya maida ita d’aki,sannan shima yai. Kusa da ita yazo tana kwance, zama yai, ya nuna mata cinyarsa yace kwanta my wife😊 salma ta kalleshi tare da rufe ido, yace ki kwanta, a hankali ta gyara ta kwanta, ya shafa kanta tare da cewa nagode *salmah* a hankali ta kalleshi, sannan tai murmushi yace salma kinsan ina ne nan?,ta girgiza kai yace inda nafara zama da mahaifiyata ko ince inda aka haifeni, salma ta kalleshi jikinta yai sanyi, salman yai murmushi yace munzama d’aya yanzu dan haka I can’t keep any secret 4rm u kema I hope u won’t ta kalleshi wani dadi na ratsata yace salmah? Ta d’ago ido ta kalleshi, yace can I say it? A hankali tace me? Bakinsa yakai goshinta ya sumbata yace *I LOVE YOU* Salma ta zaro ido zuciyarta ta shiga bugawa ahankali kuma hawayen dadi yashiga zubo mata.. Salman ya jingina pillow shima ya kwanta, sunyi shiru na d’an wani lokaci, salma dai banda murmushi ba abinda takeyi, can taji salman yace kinsan me? Tace a’a.+ Salman yace mahaifina da sarkin daya sauka wa da kani ne, mahaifina Alhaji Sadiq yataso cikin gidan sarauta sai dai tunda bashi zai zama sarki ba yasa zaman yafara gundurarshi, suna tsananin shiri da yayansa sai dai mutane kullum cikin gaima sarki gulmar Abba suke hakan yasa yanemi alfarma yadawo nan wudil garin mahaifiyarsa da zama, a lokacin Abba ya auri fulani dan alokacin ‘ya’yanta biyu mata, itadai bataji dadin barin gidan ba, gashi tana fama da laulayi. STORY CONTINUES BELOW Dakyar ta lalabashi yabarta a kano akan inta haihu sai ta dawo wudil, bayan tahowar Abba anan garin ya had’u da mahaifiyata suka fara soyayya mai karfi harta kaisu ga aure. Fulani taji haushin wannan aure sosai gashi sanda ake bikin ita kuma ta haihu, taji d’adin haihuwar namiji datai, d’an data haifa akasamai ishaq, nan gidan aka kawo mahaifiyata, tana tsananin san Abba, fulani kishi yasa tace sai dai tacigaba da zama a kano Abba yad’ingazuwa can, wannan dalilin yasa basu zauna tare ba. Umma shekararta 1 da aure ta samu ciki, farin ciki agun Abba ba’a magana, mun shaku da Abba sosai harnakai shekara 9 sai dai umma batasake haihuwa ba sai bari, alokacin ne sarki ya aikoma mahaifina da takarda akan yanasan ganinshi. Abba yashirya yaje sai dai yana zuwa ya taradda sarki ba lafiya sosai, cikin hawaye ya karasa yace meyasameka yaya? Ba wanda yasanar dani? Yace nasan bamai fad’ama shiyasa natura kazo, Abba yace meke damunka haka? Sarkin yace Abubakar inaji ajikina bazan wuce yau ba, cikin rudewa Abba yatambayeshi dalili? Sarkin ya mikamai takarda tare da kiran manyan mutane masu matsayin a masarautar yasanar dasu Abba yabawa mukaminsa da milki, ba Abba ba kowa yasha mamaki ganin yanada ‘ya’ya maza, sarki yace asanda mahaifinmu yabani mulkinnan saidaya sa nad’au alkawarin zan baka kafin yabani, Abba jikinsa yai sanyi yaso yaki amma ganin yayansa na rokonsa yasa ya amsa. Nida umma muna gida yau tunda umma ta tashi take kwance ba lafiya, in nace a kira Abba sai taki yarda, bayan magriba da Abba yakira sai ta d’aga ta nunamai lafiyarta kalau, nan yasanar da ita halin da ake ciki, ta tayashi murna kafin suyi sallama. Jikin umma ya tsananta ga Abba kwanansa uku kenan dan washegari daya shirya tafiya sarki yace ga garinku nan, hakan yasa aka rikeshi yazauna. Ganin umma bata ko iya mikewa yasa na d’au wayarta na fito falo na kira Abba,sai dai harta katse bai d’aga ba, nakirashi yafi sau nawa bai d’agaba, na ajiye wayar naje gun mai gadi na fad’amai, nan danan yakira driver muka wuce asibiti. Abba kam alokacin suna zaman makoki, muna isa asibiti akai emergency da umma, duk ta rame, anan muka kwana,duk yanda nake kiran Abba bai d’agaba, waahe gari uku, a ranar da yamma aka shirya nad’a mahaifina, alokacin jikin umma yai tsanani, kuka nake sosai. Wajen karfe d’aya mahaifina ya kira da sauri na d’aga yanacikin mutane, hakan yasa yace ku shirya za’azo a d’aukeku yanzu,dan da yamma za’ai nad’I,nace nad’I?cike da mamaki yace salman? Kaine? Nace Abba umma fa bata da lafiya inata kiranka, yace kuna ina? Nace asibiti yace ok bari azo yanzu a taho daku nace to. Ba’afi hour daya da rabi ba aka turo mota babba ta d’aukemu, umma kam batasan meke faruwa ba dan bata hayacinta nikuma sai kuka nake, muna isa gidan dan Abba ya ganta kafin mu wuce asibiti, ina zaune rike da hannunta, tace salman? Ahankali na kalleta nace umma kin warke? Tace salman ka kula da mahaifinka, nace naam? Sai dai kafin takara magana naga tana wani abu😰. salman na zuwa nan yai shiru, salma kam banda hawaye ba abinda take. Can salman yace na fita da sauri akan in kira wani, ganin Abba na tahowa yasa nai gunsa da gudu na fad’amai, dasauri ya karaso sai dai muna zuwa mukaga umma tace ga garinku nan. Hawaye ya zubowa salman yace kinsan me? Salma cikin tsananin tausayi da hawaye ta girgiza kai yace su fulani, da ragowar manyan mutane a gabana sukacema Abba wai abirne maganar mutuwar nan tunda sarakuna da manyan mutane suna gidan, a je kawai a mata wanka in ba haka ba mutane zasuce mahaifina da gawa ya fara a mulkinsa, salman ya rike kansa, salma ta mike da kyar ta matso inda salman ya kwanta hawaye na gudu a idonta, salman ya kalleta yace kinsan kuma me? Ta girgiza kai yace Abban ma ya yarda da maganarsu, shine daga baya ganin ina zaune sam bana magana yasa aka kaini paris gidansu farha. Yana kainan yaji kirjinsa ya fara amsawa, jawoshi jikinta tai ta rungume tana kuka tama rasa me zatace, wace irin rayuwa salman d’inta yai? Tun yana karami an gama b’ata rayuwarshi da bakin ciki? Ganin yafara numfashi sama_sama yasa ta bude jaka tad’aukomai magani ta mike dakyar ta d’auko ruwa yana sha ta koma kusa dashi itama ta kwanta tarr da rungume salman, addu’a kawai takeyi, ahankali salman yaji numfashinsa ya daidaita, baccine ya fara d’aukarsa, salma ta kalleshi tace *I LUV U TOO MY PRINCE* kuma insha Allah I will take care of u😭.Farha ce tagama had’a kaya cikin hawaye ta jawo akwatinta, fulani dake zaune tace farha ke kuma meye hakan? Farha takarasa gunta tasa kuka, fulani tace ke da salman ne? Farha ta d’ago da sauri fulani ta kalleta tace nasan komai farha amma fad’a kuka?,farha cikin kuka tace sam bai damu dani ba matarsa kawai ya sani nikuma bazan juri ganinsu tare ba, fulani tad’anyi wani dariya tace haba farha mata da mijinta? Ai dole ki gansu tare kuwa, farha ta turo baki, fulani tai ajiyar zuciya aranta tace da alama nasamu wacce zata sa salman a koreshi, a fili tace kamar bakida wayau? Keda kika taso a kasar waje har matar data taso anan zata fiki sanin yanda ake jan ra’ayin maza? Farha tace duk nayi, kinsan halinshi ai😪fulani tace nasani to ba sai kibi ta hanyar dazaki shiga tsakaninsu ba? Inta fara zarginsa ko ya fara zarginta aikinga dole su rage damuwa a juna, farha tace wow nagane, fulani tace ko kefa?…. Nikam dariya ma sukaban da alama basu san basa gidan ba😂😂 + Sunyi bacci sosai dan sai 4:30 suka tashi, salma ce tafara mikewa sai dai yanzu tafijin karfin jikinta, a hankali ta janye jikinta daga na salman ta mike da kyar tai hanyar toilet tai alwala, ta tada sallah salman ya mike, ya kura mata ido, a ranshi yace Allah nagode maka dakasa salma itace matata😊, Sannan ya mike yai alwala, salma ta dade tana rokon Allah yau kam duk addu’arta ta salman ce, bayan ta idar ta mike tai kitchen. Kitchen din ta shiga dubawa, taga ba kayan abinci sai wasu ledoji akan dinning nan takarasa ta bude, take away ne, da alama salman dazu dasu ya shigo ta bude d’ayar ledar, kaza ce da dankali, sai dayar kuma lemo. A hankali tadau ledojin takarasa kitchen ta dauko plates tafara wankewa, salman ya karaso inda take yasa hannu a kugunta tare da turo kansa ta wuyanta, yace beauty me kike? A ranta tace beauty? Ta juyo ta kalleshi da mamaki kafin tai magana ya manna mata kiss a kumatu, yace ba dream bane😉 murmushi tasaki sannan ta maida kanta gun wanke_wanken, tace andaina stubborn d’in? Kara kankameta yai yace sosai ma😊 ta turo baki ta juyo ta kalleshi tace ba wani bayan a wayarka haka aka sa? Yace oh ashe fa hakane, shan yace wait……kefa? Dasauri ta maida kanta tace umm nikam dama d’azu da abinci kataho? Baka fad’amin ba? Ya kwanta a bayanta yace inafa na tuna🤔? Ta gama wanke wanken ta goge dinning d’in sannan ta jera ta kalleshi tace abinci, yazauna tare da kallanta, itama tazo ta zauna a kujerar kusa dashi, ta zubamai abincin, nan suka fara ci,sai dai insuka had’a ido sai duk suyi murmushi, sun gama suka mike, salman ya kalli yanda take d’ingisa kafa, karasowa yai inda take kawai sai jitai ya d’agata da sauri takalleshi 😳 Ya juya kai tare da cewa tunda nina saki d’ingishi I have to take responsibility, tai murmushi tare da cewa ahh ni kunya nakeji🙈 ya fara tafiya tare da cewa toh yaza’ayi? Gashi nikima banasan mace mai kunya 🤔 dasauri ta bude ido, tace naa daina, dariya yasa tare da zama akan kujerar da ita, yakalleta yace wai daga fitata kikai duk wannan aikin? 1 Tace yayi yawa ne? Ko tayani zakai? Ya kalleta yace ahh sai dai inmiki sannu dan inaji tunda nake ban tab’a rike tsintsiya ba bare shara, salma tace na sani ai basai an kara sanar dani ba☹ ya ja kuncinta kad’an yace umm haka nakeso, tace bafa kayan abinci? Yace toko muje a siyo? Nikaina ina kwad’ayin cin abincinki, tace in kuma ba dadi fa? Yace anya kuwa? Bayan inaji ajikina ta iya? Salma ta mike daga cinyarsa tace yallabai muje? Tafad’a tare da kallansa, salman ya kalleta tare da had’e rai, tace menene kuma? Yace waye yallaban? Tace bafa suna bane☹kawai fad’a nai yanzu, yace au sannan ya mike yai gaba tabi bayanshi da kallo tace oh ni. Sun shiga mota sun zauna salman ya d’au waya tare da yin dialling sai dai salma dake zaune taji wayarta na ringing awajen radio ta ajiye wayar a tare suka kalli wayar da salman sai dai me? *My Prince* yaga ya fito a jikin wayar, kallansa tai tare da saurin d’auke wayarta, yai murmushi tare da kunna motar. STORY CONTINUES BELOW Sunyi siyayya sannan suka koma gida, a falo suka zauna salman yakalli salma yace jikin fa? Tace da sauki, salman ya sauko kasa sannan yakalli salma dake kan kujera ya miko mata hannunshi, kallansa tai sannan ta mika mai nata,tare da sauka in da yake, sunzauna daf da juna dan rabin jikinta ma a jikinsa yake, hannu yasa ya kwanto da kanta jikinsa, ta gyara kwanciyar tare da lumshe ido, salman cikin magana mai rad’a yace baza’a fad’amin sunan nawa ba? Ta kara shigewa jikinshi, yai gyaran murya yace ahh nikam bansan mace mai kunya, salma tai shiru, ahankali yaji tace my prince🙈 yai murmushi tace ahh nikam banjiba🤔 tad’ago tace Allah kaji☹kiss ya manna mata abaki yace beauty daga yanzu kid’inga kirana haka, tace naam😳? Yace me? Bakyaso? Dasauri tace a’a bafa haka nake nufi ba, yace to me kike nufi? Tace sai dai in muna mu biyu, yace banyarda ba to in muna cikin mutane sai kice salman? Tace ahh ni? Yace to me zakice? Tace to ai in a cikin mutane ne bana fad’ar suna, yace ohh sai kice kai? Tace 🙊 ni? Ban isa ba, salman ya kwantar da kansa akan kujera yace shikenan. Murmushi tai tare da sako fuskarta inda kansa yake tace zan d’inga fad’a kaifa? Yace wa? Ni? Ke kina tunanin ni zan kasa yin abinda naso? Tace ina fa? Rungumeta yai, salma tai ajiyar zuciya tace prince? Yace umm tace ban iya san abu ba, ina tsoron kar sanka yamin yawa in rasa ya zanyi? Kara kankameta yai dadi yakeji har ransa yace nabada dama kisoni harsai zuciyarki takai yanda bazaki iya rabuwa dani ba, tace I am afraid😞 ahankali ya d’agota yace of? Tace you, yace me? Tace eh, kara rungumeta yai baice komai ba, hawayen dasuka taru a idanta ne suka zubo.