NOOR ALBI CHAPTER 2 BY MAMUGEE

Ajiyar zuciya anty Sa’adah ta sauke lokacinda taga laylan na aje plate din gefe daya alamar ta koshi
Ta dauki ruwan dake da sanyi sosai
Saikuma ta maida ta aje Dan batashan ruwa Mai sanyi sosai sbd lafiyarta na daya daga cikin abubuwan datake kiyayewa badan kantaba sai Dan kula da Abban da gidan gabaki daya Dan kuwa idan ta kwanta ciwo komai cak yake tsayawa a gidan duk da ba wani babban gida bane ko gidan taro su kadaine agidan Wanda yakeda iya nasa girman na masu rufin asiri.

Miqewa tsaye tayi batareda ta kalli Anty Sa’adah ba ta nufi kofa daukeda plate din da ruwan cikin sanyi tana cewa”

Zanje nafara aikin abincin Rana
Lokaci yafara ja.

Ficewa tayi tabar Anty Sa’adah na bin bayanta da kallon Kamar koyaushe cikin jin qauna irin ta jini dakuma tsantsar burgewa da laylan ke Bata akoda yaushe Dan kuwa Babu abinda Layla ta baro mahaifiyarta tun daga kalar fatar,da jikin,da tafiyar dama sanyi da nutsuwa Wanda hakan kesa Koda mugun kallo Momy Bata kaunar kallon fuskarta sai da dalili Wanda kallo daya take Mata ta dauke Kai,
Ita kanta anty Sa’adah so daya taga fuskar mahaifiyar Laylah
Shine lokacinda sukaje asibiti tareda momyn da aka Kira cewan Abban yasamu hadari aka kaisu har gadon mahaifiyar Laylah alokacinda ta haifeta,
Kallon mintuna masu tsayi Momy tayiwa ZAINAB da jaririyarta kafin suka juya suka fice Bata sake ganin fuskarba har yau saidai Akan fuskar Laylah.

Wayarta ta dauko ta Danna Kiran umma Jamila yayar Momy Wanda ke ji da Sa’adah din itama Kamar itace ta haifeta sbd ita Bata taba haihuwaba.

Dan madaidaicin kicin dinsu ta Isa ta ajiye plate din hannunta tareda Dora ruwan data dawo dasu akan fridge su huce kafin tasha
Ta tattara kayan da akai amfani dasu tafara wankewa cikin Dan sauri sbd lokaci yaja Mata sosai.
Tana gamawa ta goge kayan ta saka a kwando ta dauko tukunya ta kunna lafiyayyan risho dinsu babba ta Dora abincin Rana ta fito ta nufi palon gidan Wanda yake daukeda dakin Momy a gefe saina anty Sa’adah a gefensa sai nata daga can gurin hanyar fitowa palon.

Tsaf tagyare palon ta nufi dakin Momy ta gyaro takoma dakin anty Sa’adah ta gyara kafin ta fito ta nufi palon abbansu Dake dayan gefen tashiga da sallama duk da tasan suna daga kurya Momy na magana dashi Wanda sai babban al’amarine kesa Momy magana dashi Dan haryanxu babu Wanda yasani akan akwai aure tsakaninsu haryanxu kokuwa zaman rufawa Kai asiri suke? itadai abinda tasani a gidan shine zaman alfarma take.

Gyaran palon takeyi cikin nutsuwa saiga momyn ta fito ta fice har lokacin Bata dagoba Saida tagama gyarawa kafin ta nufi dakin Abban da sallama idanuwanta akansa ta qaraso tafara gyaran dakin duk da Babu inda dauda ko rashin tsafta yake a dakin kullum tana gyarawa hakama kullum sai Abdullahi yazo yayiwa Abban wanka da wasu abubuwan tareda wankin kayansa.

Daga zaunen dayake kansa a langabe gefe ya zuba Mata ido cikin yanayin Mai tsananin ‘daci da damuwa tareda tausayinta Mai tsanani,
Akan idonsa ‘yarsa da zainab ta taso cikin bauta da rashin walwala,
Ta taso cikin kadaici da maraici,
Badan Sa’adah ta tallafi rayuwarta ba da zuciyarsa bazata iya kawo yanzu tana daukan tsananin baqin ciki da damuwarta ba
Shiyasa har abada bazai daina godewa Sa’adah da momyn ba ko Yayane dai sun tallafa rayuwarta alokacinda baya iya tsinana Mata komai amatsayinsa na mahaifinta…

Saidai babbar gagarumar damuwarsa shine shin wane Hali zata shiga idan babusa?
Tayaya zatai rayuwa Kamar kowa tasamu farin ciki?
Ya tabbatarda rashinsa zai qarasa juyarda duniyartane gabaki daya sbd har abada zata qare a bauta da wahalar gidan Dan kuwa kowane lokaci Sa’adah Dake tallafarta zatai aure ta tafi tabarta.

Hawayene suke bin gefen fuskarsa suna gangarowa zuwa kan kafadarsa da kayansa
Zuciyarsa na tsananin quna cikeda damuwa.

Ajikinta taji kukan mahaifin nata
Ta waiwayo ahankali a natse ta kallesa da idanuwanta da ako yaushe suke hasko Masa mahaifiyarta ya rintse ido hawayensa na tsananta gudu alamar kukane Mai tsanani yakeyi na zuciya Dan baida lafiyar fitar sautin kukan ne.

Qarasowa tayi gabansa a natse cikin sanyi ta zauna tareda Dan sauke kanta qasa tsawon mintuna batareda tace komaiba,
Tissue dage gefe ta zaro guda uku ta dago fararen idanuwanta dasukai ja take batareda hawaye sun taru cikinsu ba kokuma suka gangaro ta zubawa Abban takai hannu ahankali tafara share hawayensa Wanda hakan yasa hawayen nasa Suka sake barkewa ba kakkautawa,

Yanajin radadi da zafin Zuciya ba damar furtawa kokuma bayyanawa,
So yake ya bude Baki yasaka Mata albarka tareda Bata hakurin yanda quruciyarta da yarintarta take neman qarewa agurin dawainiya dashi.

Batace komaiba sai share hawayensa datakeyi ahankali tana kallonsa
Yasan bazatai maganaba sbd Yana iya hango tsananin dacin da zuciyarta ke cikk a ganinsa hakan
Dan Haka yafara kokarin danne kukansa Yana Dan sauke kansa daqyar sbd wani lokacin kasa kallonta yakeyi sbd nauyi duk da Yana matsayi na uba.

Ahankali ahankali take qarasa goge hawayensa har zuwa Kan rigarsa Sama sama cikin nutsuwa.

Damqe tissue din tayi a tafin hannunta bayan ta Gama goge Masa ta sake dagowa ahankali cikin sanyi da nutsuwa ta kallesa tsananin qaunarsa na bayyanuwa akan fuskarta ta bude Baki a natse tace”

Har abada bazan daina sake fada maka ba laifinka bane,
Qaddararmu ce mu duka ahaka,
Allah Bai dauki ran mahaifiyataba sbd wannan al’amarin
Ya karba ranta ne sbd lokacinta yayi,
Kadaina kallon kanka a matsayin uba daya Gaza,
Kallonka ko ahaka Yana bani nutsuwa da qarin qarfin tawakkali ga ubangiji.
Ka cire damuwar yanayin zamana da rayuwata sbd ban taba ganin laifin kowaba agame da hakan,
Idan Dole anason ganin laifin wani
Nice Mai laifin,
Sbd rabon haihuwata ne,
Rabon zuwana duniyane yaxo ta hanyar tarwatsa rayuwarku ku duka,
Ahakan har abada bazan taba daina yiwa Momy addu’a ba sbd koma yayane Bata barni nayi rayuwar titi ba ta barni Ina rayuwa a qarqashin inuwarta data ‘yarta
Hakan ma ya isa ka godewa Allah.

Rintse idanuwa yayi Yana Dan daga Mata hannu kadan akan ta Kama.

Kama hannun nasa tayi ta damqe Suka sauke ajiyar zuciya atare kowanne Yana kallon Dan uwansa.

Saidataga yadan kawar da damuwar kafin ta saki hannunsa ta qarasa gyara dakin tadawo gabansa ta dauki ruwa ta zuba a cup takai bakinsa tana basa
Wasu na shigewa wasu na zubowa tana gogewa da tissue.

Tana Gama basa ruwan tasake goge Masa jiki kafin ta fice daga dakin ta koma kicin gurin aikin abincin data Dora.

Qarfe daya da rabi tagama komai tasake gyara koina kafin ta nufi dakinta Dake da Dan qaramin toilet aciki tayi wanka tareda alwalar sallar azahar ta fito tafara yin sallah kafin ta shirya cikin doguwar rigar atampa Wanda anty Sa’adah ta Bata Dan kuwa kaf suturarta kayan anty Sa’adah ne,
Bata taba saka sabon Kaya a rayuwartaba sai kayanda anty Sa’adah tasaka tacire tabata
Duk da bayan kusan shekaru takwas zuwa Tara da anty Sa’adah ta Bata akwai banbancin jiki Dan anty Sa’adah ba ramammiya bace hakama bawani qibane da itaba saidai batada tsayi
Sabanin itakuma datake da Dan tsayi daidai
Hakama batada jiki Amma tafi anty Sa’adah nonuwa sbd anty Sa’adah jikinne kawai da ita batada nono ko kadan,
Wasu kayan idan anty Sa’adah din ta Bata tana kaita gurin wata tela Dake anguwar a rage Mata wasu Kuma hakanan take yawo cikinsu harta tsufa.

Fitowa tayi ta nufi kicin ta dauko abincinsu Momy da anty Sa’adah tafara kawo palo Dan Nan sukecin abincin.
Kicin Takoma acan taci nata sama sama tana gamawa ta nufi palon abbansu sbd ganin lokacin Shan maganinsa yayi.

Da sallama tashiga palon Kai tsaye
Saitaga baqi
Bakuma kowa bane face Dr Abbakar wanda yake babban Orthopedic likitane yasan Abban ne shiyasa har lokacin shine yake riqe da ragamar kula da Abban dakyau hakama da kansa yake Dan duddubasa ata bangaren paralyze dinsa daya saka gefen jikinsa baya Aiki sosai duk da dayan gefen ba laifi Yana aiki
Kuma ahakan danma ya tsaya tsayin dakane akan nemawa Abban lafiya shiyasa ba wani sosaineba rashin aikin gefen dan wani zubin ba’a ganewama.

Tareda Abdullahi babban Yaron Abban Wanda har lokacin halacci yasa yake tareda dashi Yana taimakawa gurin hidamar kulawa dashi,
Kusan duk wasu hidimar asibiti madai shine yake jagoran saidai Laylah tabisa abaya.

Ganinsu kowanne fuska ba wani walwala yasata juyawa Takoma ahankali bayan tagaida Dr Abbakar din cikin nustuwa.

Bayanta dukkaninsu sukabi da kallo har Dr Abbakar din Wanda yariga yasan damuwar Abba ba akan rashin kyawun results dinsa dasuka fito na asibiti akan yarsa ne wadda yakejin ko yayane idan Yana Raye tana abun kallo da dogaro Koda Baida wata moriya agareta dagashi har ita suna debewa juna kewa da baqin ciki.

Ajiyar zuciya Dr Abbakar yayi shima cikeda tausayin Abban dama laylan
Ya dago ya kalli abdullahi ya miqa Masa wasu takardu yace”

Malam Abdullahi karba wannan Dan Allah kaimun mota Ina fitowa.

Karba yayi cikin girmamawa jiki a sanyaye ya fice.

Bayan fitar Abdullahi sake sauke numfashi Dr Abbakar yayi tareda kallon Abba da yayi nisa cikin tunani fuskarsa Babu wani alama dayake bayyanarda yanayin da zuciyarsa take ciki,
Zuwa yanzu zuciyarsa tafara riqewa da tawakkalin tabbas komai kaddarowar ubangijine,
Duk kaunar dayakewa ‘yarsa yasan idan lokacinsa yayi Allah bazai barsaba,
Hakama Babu wata qaddarar da Allah ya sauko Mata dazai iya sauya Mata,

Results dinsa sun nuna infection daya shiga qashinsa tun farko farkon hadarin da ba’a yanke qafafunba sunyi yawanda harsun fara shiga jininsa,
Tabbas yasan yanda yakeji ajikinsa lokacinsa yakusa zuwa
Saidai duk ya kalli Layla da rayuwarda zai barta aciki hankalinsa tashi yakeyi yabar jikinsa,
Tsoro da fargaba tareda kukane suke lullubesa aduk lokacinda yayi tunanin hakan.

Alhaji MAHMOUD tabbas rikicewar lafiyarka a Yan lokutan Nan sunada babbar nasaba da damuwa da kuncin dakake Tarawa aranka,
Da zaga sassauta damuwa da tunani kasamu hutun zuciya Dana qwaqwalwa ko yayane za’a ringa samun sauki ko yayane.

Sunkuyar da Kai Abban yayi ahankali cikin irin yanayinsa na masu ciwo irin nasa batareda ya iya ko dago idanuwansa ya kalli Dr Abbakar din ba.

Shiru sukai tsawon mintuna kafin Dr Abbakar din ya miqe tsaye Yana kallon abban cikin kulawa yace”

Zan tafi gobe zandawo zamu sake dibar sample ajikinka Inshallah saimu gwada wani awon mugani,
Allah yaqaro lfy.

Juyawa yayi ya fice daga dakin har lokacin Abban Bai motsaba Yana yanda yake.
Ahankali idanuwansa suka sauya zuwa ja jikinsa na daukan zafi na wani irin zazzabi Mai qarfi daya saukar Masa atake saidai zuciyarsa ta riqe yakasa tunanin komai saina Mutum daya daya fado Masa a Rai wato babban Amininsa Wanda shikadaine zai iya magance babban abunda yazo ya tokare ransa tsawon shekaru wato damuwar Laylah.

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE