NOOR ALBI CHAPTER 5 BY MAMUGEE
Guraren la’asar Rana ta Dan bude kadan daga hadari da ruwan da aka tashi dasu
Tana ganin ranar ta Dan bullo ta kwaso kayan wankin jiyan datai Wanda iska ya lalata tasake wankewa sama sama ta shanya
Tana gamawa ta sakarwa abbanta labulan palonsa sbd magriba datai danma yau Bata fito dashiba Shan iska tsakar gida kamar yanda tasaba kullum take fitowa dashi yasha iskan yamma sai magriba ta turasa ciki
To yau sanyi sanyin ruwan da akai yahanata fitowa dashi Dan ita kanta dannewa tayi Amma zazzabin dukan ruwan datashane yake cinta sosai Amma ba amfanin kwantawar Dan haka ta danne sai idanuwanta ne dasuka ja
Sai Wanda yakeda zurfin ganewane zai gane zazzabi ne ajikinta.
Alwala tayi bayan tasake share tsakar gidan tas ta shigarda komai kicin tarufe kicin din Dan dama abinci daya sukeyi har dare basa abinci biyu matuqar ba baqi Momy tayiba aka cinye abincin Amma abinci daya akeyi har dare sbd lallabawa da neman da take.
Dakinta ta Isa ta tayarda sallah cikin dauriya tayi sallar tazauna tana adhkar har tsawon lokaci saidataji zazzabin na neman fin qarfinta ta miqe batareda ta cire hijabin sallartaba ta nufa kofa tafice zuwa gurin Abba Dan bashi abincinsa da magani kafin ta kwanta jikin ya hanata tashi.
Cikin qarfin hali tagama bawa Abban abinci tabasa magani ta maida kayan kafin tadawo ta zauna tana goge Masa fuska sai alokacin Abban yaji tsananin zafin hannuwanta da har wani siracin zafi sukeyi
Ya zuba Mata idanuwansa kafin ya Dan motsa hannunsa alamar mgn
Ta kallesa tana kawarda abunda ta fahimci yaji Wato zafin jikinta.
Cigaba da gage Masa fuska tayi tana qin Bari ya kalla idanuwanta dasukai laushi
Tana gamawa ta miqe tana Masa addua Tai Masa Saida safe ta fito takoma daki Kai tsaye Tai sallar ishai ta kwanata take baccin wahala ya dauketa a gefen katifarta ko rufar arzki bataiba.
Washe gari sbd zazzabin data dauka zai sauka kafin safiyar yasa tayi lattin tashi jikinta a matuqar zafafe da zafi Amma hakanan ta tashi taje tayo alwala tazo tayi sallah
Tana gamawa ta miqe ta fice Dan ayyukanta data Saba dasuke gabanta.
Kunun abbanta tafara damawa kafin ta soya doya tadafa ruwan Lipton ta juye a qaramin flask ta Kai Palo tadawo ta dauki na abbanta takai masa.
Cikin dauriya tayi aikin gyaran koina ta zauna tana bawa Abban abinci,
Daga fuskarsa Yana iya Jin hucin zafin jikinta dake hurowa
Take jikinsa yayi matuqar sanyi zuciyarsa ta narke da tausayin kansu dagashi har itan
Ya zuba Mata idonuwansa dasuka sauya Yana danne hawayen Dake kokarin gangaro Masa Dan karya qara Mata damuwa akan wannan halin datake cikin.
Tana Gama basa ta gyarasa ta fice zuwa gyaran palon Momy da dakunansu,
Daqyar tagama gyaran ta dauki kasko ta fita tasamo garwashi maqota tadawo ta zuba turaren wutar kadan ta aje palon Saida ya Kama koina har dakunansu kafin ta dauka takaiwa abbanta shima ya samu tadawo da kaskon tsakar gida ta aje.
Kicin taje ta zaunda Kan kujera ta janyo abincinta tafara ci taji Bata iyacin ta dauki Kofi taje ta debo kunun babanta kadan ta zauna acan tasaka kanta Sha Dole sbd Kar ciwon yafi qarfin hakan.
Tana gamawa cikin magunan abbanta ta dudduba tasamo paracetamol Wanda Yaya abdullahi ke ajewa Dan kansa shima ta balla biyu Tasha ta fito Abban na binta da kallo zuciyarsa na sake shiga hali na damuwa.
Shanyar Momy ta kashe tayi ciki dasu ta aje gefen kujera ta zauna qasa Dan tana lumshe fararen idanuwanta dasukai duhu ga jiri datake Dan gani.
Mintuna biyar ta dauka zaune agurin kafin ta miqe ta Kashi kayan ta dauko dutsan guga daga dakin anty Sa’adah tayi palon Abba sbd acan take guga Dan palon Momy tanada center carpet bayan tayils din dake qasan batason a Kona Mata carpet shikuma palon abban tayils dinne kawai Dan Haka acan take gugar duk zafi kuwa ahaka take gugar ita zufa Abban zufa.
Qatuwar daddumar baqin Abban ta shimfida tazauna akai tafara gugar.
Har Saida Suka tashi daga barci suka fito gurin Sha daya kafin tagama gugar ta kwaso ta fito suna Palo zaune Momy tagama cin abinci tana waya da umma Jamila hamshaqiyar yayarta Mai abun duniya Kamar yanda take fada.
Anty Sa’adah dake Shan ruwan Lipton har lokacin tafara kalla cikin kulawa tace”
Anty Sa’adah antashi lfy?
Lfy kalau Laylah,
Gama abunda kike wani guri Zaki rakani
Yau umma Jamila nanan zuwa inason binta daga can yafimun kusa da hanyar makaranta sbd exams din zamu fara kinsanni da yawan bacci anan duk exam sainayi latti.
Ahankali ta gyada Kai tana sakewa anty Sa’adahn murmushi tace”
Allah yabaki sa’a Anty Sa’adah.
Satar kallon gefen Momy tayi kafin ta qarasa kadan gefenta cikin nutsuwa da girmamawa tace”
Barka da fitowa Momy.
Hannu kawai momyn ta iya amsa Mata dashi kafin tasaki murmushi ta juya ta shige dakin momyn da kayan gugar
tana shiga ta ajiye Kan gado ta bude Yar qaramar wardrobe din momyn ta jere Mata kayan tas ta cire na Anty Sa’adah ta aje gefe tafara gyaran gadon da momyn ta tashi
tana gamawa ta nufi toilet din dakin shima ta wanke kafin ta dauki kayan Anty Sa’adah din tafito dasu takai Mata nata dakin.
Ganin alamar yau momyn Bata fita yasa ta nufi dakinta takoma ta Dan kwanta Dan kanta Kamar zai tsage ga zazzabi.
Baccin wahalane ya dauketa har batasan yayi nisa ba Saida taji Ana tasata da qarfi
Bude idanuwanta tayi tana kallon anty Sa’adah dake tsaye kanta shirye cikin Riga da skirt na embellished atampa dark brown da gyale Sai qamshi takeyi abunta tace”
Laylah maza tashi muje
Yi sauri na tare Mana Mai napep a kofar gida yanzu zamu dawo ba jimawa.
Tashi Laylan tayi tana miqewa tsaye tace”
Bari na fadawa Momy to.
Aa muje kawai tasani.
Jan hannun laylan tayi suka fito dama da Dan hijabinta a jikinta
Sam anty Sa’adah Bata wani damu data bari ta Dan gyaggyaraba kafin fitar itadai tunda ba tube Laylan takeba bata damuba.
Suna fitowa palon Momy na zaune har lokacin tanata wayoyinta anty Sa’adah tajata suka fice har lokacin Bata saki hannuntaba.
Napep suka Shiga Saida suka hau titi ta kalli Sa’adah din tace”
Anty Sa’adah Ina zamuje ne?
Dariya anty Sa’adah tayi tana Ciro wayarta daga handbag dinta da ake Kira taga Kiran Nasir ne Mai nemanta taqi dauka ta maida wayar jakar tana cewa”
Umma Jamila zatazo muje na karbo dinki kafin mudawo tagama yininta muna dawowa wucewa kawai zamuyi nida ita.
Ahankali ta dauke kallonta daga kan anty Sa’adah din tana maidawa Kan Hanya tareda sauke boyayyan numfashi.
Anty Sa’adah da Baki daukoni munfitoba ai sbd aikin abinci da wasu ayyukan duk gasucan nabari,
Umma Jamila ma banajin komai Akan yanda takemun ba komai bane tunda ta haifeni nesa ma
Dan Allah mu koma gidan Anty Sa’adah.
Wani kallo anty Sa’adah din Tai Mata tana sakin tsokin mamaki tace”
Bazamu koma din ba saina karbo abunda muka fito karbowa.
Shiru kawai Laylan tayi tana sauraren fadan anty Sa’adah din akanta duk da dai tasan duk yanda takeda tauri da danne Abu tareda boyewa duk umma Jamila tazo gidan sai idanuwanta sunyi kwanan rashin bacci da wani Hali ranar sbd tsanar da umma Jamila din take Mata itada abbanta Dan kuwa da dama shi kansa idan tazo gidan sai ya zubda hawayen boye akan ‘yarsa Laylah Dan kuwa bayyananniyar tsana tayiwa Laylah da Abban duk da shi kullum maganarta ya girbi cin amanarsa gashinan yagani.
Suna isowa shagon Mai dinkin yacewa anty Sa’adah Bai kammala ba
Dama hakan takeson ji Dan Haka ta nema guri Suka zauna tace ya kammala zata jirasa.
Kallonta Laylah tayi tana kallon agogon shagon cikin nutsuwa tace”
Anty Sa’adah karfe daya saura
Ni Zan koma gida
Kinga ban Dora abinci ba Kuma kada Momy tanason wani aikin bana Nan ga Abb….
quiet please Laylah,
Bazan barki ki komaba Zaki jira nagama tunda Nina fito Dake zamu koma tare so just sit quietly muyi zaman jira,
Fushin Momy na rashin aikinki yafi Miki zuwan umma Jamila so dubu.
Shiru tayi sbd Bata iya hayaniya ba bare tayita magiya saidai hankalinta gabaki daya Yana Kan abbanta da momyn,
Dan kuwa har cikin ranta qaunar uwa takewa momyn shiyasa Bata qaunar ta Bata Mata Rai.
ga zazzabin dake cinta har lokacin.
Zama yayi zama sune har la’asar Basu koma gidaba sai qarfe biyar Adaidaita sahu ta ajesu kofar gida
Anty Sa’adah ce agaba taba bayanta riqeda ledar kayan anty Sa’adah din suka shigo da sallama tun daga tsakar tasan Bata kyautaba qin dawowa da wuri sbd Yar dattin da gidan yayi na iska da aka danyi kamar za’ai ruwa.
Kallon inda su momyn suke zaune tsakar gida Kan babbar daddumar baqin girman momyn sun Gama cin abincin da aka kawo musu daga gidan umma Jamila din tunda yau baai abinciba Nan gidan suna magana hankali kwanci saidai shigowarsu yasa bacin ran da umma Jamilan ke dannewa tasowa ta kalli Laylah bayan ta amsa gaisuwar Sa’adah data zauna gefenta tana daukan ruwan robar swan Dake gurin ta bude tana sha
Tace”
Zainab haryanzu kin kasa gane illar jini,
Shi Abu idan akace a jininka yake to saifa iko na ubangiji,
Kinada ‘ya mace budurwa a gabanki da kikewa fatar samun miji na hutawa da Jin Dadi kike Bari suna fita tare da yarinyar nan?
Ta Yaya kike tunanin namiji daya zai kallesu idanuwansa su kasa tsolewa da wannan kodaddiyar fatar ta jinin gado,
Mahaifiyarta da mahaifinta akwai wani gadon dasuka bar Mata bayan na jinin cin Amana ne,
Magana daya itace na soke fitar Sa’adah da laylan daga yau karna ji ko a labari wannan umarni nane,
Shine kina zaune zata saka qafa ta fice ko aikin abinci Babu idanma kinyi baqin kunya Dole kece da tsufanki Zaki shiga kicin girka abinci
Ke kenan Haka rayuwarki zata qare a bautar Mahmud da ‘yarsa bakya tunanin Taki Yar?
To Allah ya kyauta,
Sa’adah ma Inshallah saiki fara shiri ki fadawa Mahmud din babban ‘dan Alhaji Sadiqu commissioner Dake aikin Lawyer a Lagos munyi mgna da alhajin zasuzo neman aurenta
Allah yayi Kinga tasamu miji gidan Jin Dadi da arziki Kar aja wani lokaci ayi Mata auren tasamu ta tafi gidanta inda zatai irin rayuwar da kike Mata fatar samu
Kema Kinga kin samu nutsuwa shikenan Babu Wanda zakiwa wahalar nema saiki zauna abinda yazo kibasu Wanda baizoba saisu dangana shida ‘yarsa.
Idanma bazaki iyaba Ni bayan auren Sa’adah din kiban laylan Dan masu aikina duk sun isheni wlh
Saina ringa biyanki kudin aikinta Kuna dawainiyar dashi kin huta ya komaima.
Momyn dai batace komaiba sai kayan wayarta datake dubawa tana hada Kan wani lissafi
Saidai fuskarta sosai ya bayyanarda farin cikin zancen mijin Sa’adah din da akai takumayi na’am da maganar auren saidai maganar Laylah batace kala ba duk da tariga tasan cewa tabbas Sa’adah tayi aure zamanta daga ita saisu Laylah din bazai musu dadiba su dukan Dan tasan zamanta a gidan zai iya karanci Dan kuwa zata saka kanta busy ne da yawon kasuwanci ta ringa Hana kanta zaman gidan sosai.
Itadai Laylah sallah tayo tazo tanata ayyukanta batareda ta dago Kai ta iya kallonsu ba bare ta nuna damuwar zance ko daya acikin zantukan sai kaida kawonta take tana aiki.
Anty Sa’adah ma shigowar zancen aurenta cikin maganar ya hanata saka Baki ta kare Laylah tareda sanar dasu burinta dataci alwashin duk ranarda tayi aure zata tafi da Laylah Dan inganta rayuwarta da ilimi Mai zurfi na boko.
Har akai magriba Bata Gama aikin abincin data doraba
su Kuma tuni Suka shige ciki suka bar wajen ta sake share tsakar gidan kafin ta sauke abincin ta zuba a kuloli takai musu tadawo ta gyara gurin,
Bataci nata abincin ba Saida tayi wanka tayi sallah ta dawo kicin din ta Dan ci kadan ta fito ta nufi gurin abbanta.
Zaune yake Kamar kullum Kan kujerarsa zugum Yana sauraron duk abinda yake faruwa a tsakar gidan
Maganganun Umma Jamila sun tabasa sosai sbd bayajin har abada idan ba aureba zai iya bawa wani Laylah,
Yasan a yanda yake dinnan tabbas yanaji Yana gani umma Jamila zata iya daukan Laylah kamar yanda tafada Wanda yasan tabbas duk juriya da hakuri irin na Laylah taje gidan umma Jamila rayuwarta tagama Shiga hawula’i Dan Haka bazai taba Bari hakan ta faru ba
Matuqar zasuwa Sa’adah aure yasan Laylah bazata qara Jin dadiba ko sassauci Dan Haka itama auren zai Mata a inda zata ingantu Koda Babu soyayya yasan zatai daraja.
Tana qarasawo gabansa ta zauna tareda abincin data debo zata basa ya kalleta da idanuwansa dasukai ja ya Mata alamar ta matso da hannu
Ta kallesa cikin sanyin jiki kafin ta matso din batareda tace komaiba takai kunnenta bakinsa
Cikin rawar muryar Dake tafe da kakari daqyar can qasa yace”
Zan Miki aure kafin auren Sa’adah zakije inda zakiyi rayuwa kema
Allah zai Baki farin cikinda sai sunyi Miki kukan Dadi da godiya su umma Jamila……..
Wani irin faduwa gabanta yayi tsananin mamaki zancensa yasata bama firgici ba sbd tasan Babu wani maganar aure a rayuwarta yanzu,
Tayi aure tabarwa wayeshi Abban.
Kallonsa takeyi cikin nisa a tunani Dan batamasan Mai zatace Masa ba kafin daga baya ta miqe ta fice ganin dare yayi.
Tana fita abdullahi na shigowa yayi Masa alamar Kira tareda fadar sunan AB TURAKI daqyar alamar shiyakeson Akira masa
Take abdullahin ya fidda wayar Abban Dake drwer wadda aka aje sbd Kiran mutanensa da basa daukan sabuwar number Amma suna daukan me sunansa ya lalubo Numbern qasar AMERICA.