NOOR ALBI CHAPTER 8 BY MAMUGEE
Yini sukai a asibitin sai dare suka koma gida suka Bar Abdullahi
Koda suka Isa gida Momy na kwance a daki zazzabi Mai qarfi ya kwantar da ita Dan Haka cikin daren Laylah tahau wani aikin ta Dora Mata ruwan tea da maganinta na Hausa data fiye Sha takawo Mata lokacin Sa’adah na zaune gefen gadon tana Mata sannu cikin kulawa ita ta karba maganin da tea din Laylah ta juya ta fice taje ta rufe gida tadawo tayi sallar ishai da basuyiba acan asibiti tayi dakinta ta kwanta tareda rufe idanuwanta kawai.
Washe gari tunda safe tayi dukkanin ayyukanta tayi wanka ta zauna ko anty Sa’adah zatace suje asibiti sai gashi batace din ba
Momy ce kawai ta shirya ta fice zuwa asibitin Dan ji daga likitoci dake jiranta.
Lokacinda Dr Abbakar yagama yimata bayanin Abban yariga yashiga coma sai ranarda Allah yayi ikon tashinsa shiru tayi tareda qurawa Abban idanuwanta dasukai jajir
gabaki daya kamanninsa sun sauya
Oxygen ne a bakinsa Wanda yake Dan taimakawa rayuwarsa datake hannun ubangiji Dan Jan numfashin duniya,
Fuskarsa tayi haske fayau kamar Wanda babu digon jini a jikinsa
Ta sauke Kai tana Jin inama zata iya dawo da baya gaba data dawo musu da bayarsu dasuke su kadai daga ita saishi
Tabasa dukkanin kaunarta da kulawarta data Saba basa,
Bata buqatan Yan uwanta ko nasa su kadai takeson suyi rayuwa
Idanma zaiyi aure saiya fada Mata ta rarrashi zuciyarta ta dauka
Amma duk wannan bazai yiyuba sbd wannan shine asalin hukuncinta sakamakonta na bujirewa iyaye.
Duk yanda taso kasa daurewa tayi bayan fitar Dr Abbakar Saida wasu irin hawaye masu tsananin zafi da Daci suka kubuce Mata ta Sunkuyar dakai sunata gangarowa Kan fuskarta zuwa kirjinta ta rintse ido kukanta yafara fitarda sauti ahankali Mai tsima zuciya.
Ta Jima cikin wannan halin tana kuka Mai quna da radadin zuciya kafin ta danne ta share hawayenta tareda goge fuskarta ta miqe ta fice batareda tambayar kudin lalurar asibitinba sbd sanin asibitin da likitocin asibitin duk na Turaki ne Wanda takanas sbd qarin lalurar Abban ya budeta Dan Haka komai na Abban a asibitin na musamman ne ko sisi basa biya.
Gida tadawo tashige daki tashige ta lalubo nata maganin Hawan jinin tana kokarin fitowa neman ruwa saiga Laylah tashigo dakin daukeda ruwa a jug takawo Mata masu Dan sanyi ganin tadawo cikin zafin Rana da ake kwadawa.
Qurawa jug din idanuwanta dasukai jajir tayi Momy tayi tanajin idanuwan na kokarin sake cikowa da hawaye ta miqa hannu ta karba jug din da cup ta aje tana zubawa tasha maganinta batareda ta dago ta kalli fuskar Laylah dinba wadda itama tuni ta sauke Kai tareda juyawa zuciyarta na sake karyarwa da yanayin data ga momyn aciki wadda itama ta tabbatarda rayuwar kawai takeyi ba acikin Jin dadiba sbd damuwar dukkanin komai da komai ma.
Bayan fitar Laylah komawa Momy tayi ta kwanta bakin gado tareda rufe idanuwanta dasukai ja da nauyi tanajin yanda zuciyarta ke azabtar da ita.
Itama laylah kasa komawa dakinta tayi ta zauna tsakar gidan sbd rashin sanin mezatai,ga Anty Sa’adah na daki sbd yauma wani irin habo tayi Mai yawa Wanda yasata kwantawa ko zata samu damarsa Wanda take ganin zafin da ake zubawa yau dinne yasata habon jinin ta hanci duk da Bata taba yinsaba sai jiya dakuma yau dinma dayazo Mata.
Yini tayi Babu kowa daya fito daga momyn har Anty Sa’adah din
Kowa da halinda yake ciki
Itama daurewa kawai takeyi Amma tana cikin tsananin pressure da wani irin yanayi datake ji Wanda ake Kira da asalin depression Dan kuwa ko numfashi tayi Jin takeyi kamar mutuwa zatafi Mata sauki akansa,
Batada Wanda zatai magana dashi kokuma muamala dashi dazai rage Mata tsananin nauyi da zuciyarta take ciki akan halinda Abbanta take ciki.
Haka aka kwana gidan Babu motsin kowa
Washe gari ma Haka suka wuni sbd ciwon Kai Mai qarfi sosai ya kwantarda Momy
Anty Sa’adah ma da ciwon gabobi ta tashi yau din sbd kwanciyar data wuni jiyan akan nosebleed din datai Dan Haka yau gabaki daya hankalinta a juye yake Haka ta juye da aikin kulawa dasu ga tunanin abbanta Dan Haka itama sai ciwon yashigeta na zazzabi Mai qarfi sbd kasa ko cin abinci datai
Koda akai kwana biyu ahakan gabaki daya ta birkice depression yayi Mata tsanani Dan kuwa ko kalma daya Bata samu Wanda ta furtawaba
Dan kuwa anty Sa’adah sosai zazzabin ciwon gabobi ya kamata har Saida Momy taga tsananin al’amarin ta tilasatawa kanta danne nata ciwon ta tashi takai Anty Sa’adah asibitin sukabar Laylah ita kadai a gidan sai alokacin ta zauna tsakiyar dakinta tareda cusa kanta cikin qafafunta wasu hawaye datafi shekara nawa Bata zubda ba suka gangaro da idanuwanta dasukai jajir Dan kuwa ko taso kuka da dama Bata iyayi Dan baya zuwa Amma yau gabaki daya Tama rasa Yaya take,
Wane yanayi takeji,
Menene amfanin wannan rayuwar tata da Babu kowa aciki sai ita kadai da zuciyarta da tunaninta tareda quncinta.
Hawayen na gangarowa daga cikin idanuwan nata wani irin kuka yazo Mata Mara sauti ko kadan Dan ko qarfin kukan batada Dan Haka ta sulale ta kwanta agurin tana rintse idanuwanta.
A asibiti Saida suka Bata layi kafin suka samu ganin likita Dan Dan sunyi lattin zuwa,
Dunata likita yayi tareda rubuta Mata magani akan Tasha idan kwana biyu Bata warware ba zasu Mata wasu test saisu gani idan wata matsalarce babba.
Cikin ikon Allah kwana biyu tanashan maganin saigashi ta warware sosai Takoma walwalarta sai Alokacin ta lura da Sosai Laylan ta firgice kamar wadda tafara samun damuwar qwaqwalwa sai Kuma hankalinta ya tashi Dan Haka saita qi cigaba da zuwa makaranta tafara kokarin ganin ta dawo da Laylan daidai.
Asibiti ta ringa kaita gurin Abban kullum suna dubosa ko hakan zaisa tadawo daidai Amma sai hakan yake qara dagula Mata komai sbd duk ta kalla Mahaifinta ahalinda yake ciki komai sake rikice Mata yake musamman da Dr Abbakar ya tabbatar musu da Abban Yana Nan ahakan sai abunda Allah yayi kodai ya tashi kokuma daga hakan shikenan Allah ne kawai yasan abunda ya yanke akansa.
Ranar da akai musu wannan bayanin duk da anty Sa’adah tashiga wani halin itama Amma ganin halinda Laylan tashiga duk da Bata cewa kala sai hakan yayi mummunan daga Mata hankali da kuwa a bayyane tafara fahimtar depression ne yake neman juya kwakwalwar Laylah din
Haka tashiga mayuyacin halin neman mafitar tallafawa rayuwar Laylah din Dan kuwa alqawarine ta dauka zata cikawa Abba burin bawa Laylah kyakkyawar rayuwa Inshallah.
Ta bangaren Momy ganin yanda kowa yake cikin mummanan Hali na rayuwa yasa ta Amincewa umma Jamila Akan buqatar ayi auren Sa’adah ko ita zata samu ta fita daga wannan qaddarar rayuwar tasu taje gidanta tasamu rayuwar kwanciyar hankali da nutsuwarda su suka rasa ahaka suka share kusan wata biyu.
*****
Zaune suke a palon gidan Momy na zaune shiru ta zubawa Sa’adah da duk ta lalace sbd rashin kwanciyar hankali ido tanaji tsananin tausayinta Dan kuwa a yanzune ta tabbatarda son da Sa’adah kewa Laylan Mai qarfi ne Dan kuwa wani irin so taga tanai Mata tamkar Wanda uwa kewa danta,
Ta tattara karatu ta daina zuwa tsawon watan biyu ta tattara rayuwarta gurin kokarin dawo da Laylan daidai wadda yanzu bayan idanuwa datake zubawa kowa ko magana Bata iyayi Dan kamar qwaqwalwarta ta tabu gashi basuda wani kudi ko arzikin nema Mata magani sai momyn ta zubawa sarautar Allah idanuwa Dan kaf Yan uwanta tasan bazasu bada taimakonda za’a nemawa laylan lafiya ba sai itama yanayin laylan yafara tabata sbd Sa’adah da al’amarin ya taba sosai Dan hatta ayyukan gidan sun dawo Kan Sa’adah da kula da laylah wadda ba jinyar kwanciya takeba jinyar qwaqwalwa take.
Cikin ‘dan zafi umma Jamila ta kalli Momy kafin ta maida kallonta Kan Sa’adah dake zaune gabansu tace”
Yanzu Zainab kina kallo Sa’adah zata lalata rayuwarta da kanta gurin kulada Mai ciwon qwaqwalwa bayan tanada rayuwa Mai kyau datake jiranta Amma ta kafe akan bazatai auren ba matuqar baza’a barta ta tafi da wannan Mai Kama da Marmaid din ba,
Ta Yaya kike tunanin za’a Kai budurwar Amarya dakinta ace anhadata tafiya da wata budurwar?
Waye mijin zai kalla a tsakaninsu?
Waye Zaifi Shiga ransa tunda kinsan ko a kyau da sigarsu ba daya ba
Waccar din kinaga daukan idone da ita duk da batada lafiya ga maza yanzu baka Basu Amana,
Gskia nidai ban amince ba
Babu inda za’a tafi da wannan yarinyar musamman yanzu datake kamar Mai ciwon qwaqwalwa..
Numfashi Momy ta sauke tana rintse idanuwanta cikin yanayi na gajiya da komai da komai na rayuwa ta bude Baki ahankali tace”
Sa’adah banida wani sanyin idaniya a yanzu bayan ke Dan Haka fatana da burina ganin kinyi aure kin samu ingantacciyar rayuwa,
Naga qaunar da kikewa Laylah nayi Miki alqawarin har abada bazan rabaku ba saidai aure Dole zai rabaku
Idan inganta rayuwarta kikeson Yi Dan ki rabata da zama Dani bayan tafiyarki namiki alqawarin barin ta tafi tayi tata rayuwar gidan nata auren Dan kuwa Abbanku ranarda ciwon Nan zai kwantar dashi Aurenta yaso badawa Dan dauketa daga gareni sbd kuna ganin nice ukubarta….
Shiru tayi wani Daci da qunci na sake mamaye zuciyarta sbd ita kadai tasan radadin datake ciki na duk abubuwan dake faruwa.
Da mamaki umma Jamila take kallonta da cewa”
Aure Kuma?
Hala dai Abdullahi zai bawa aurenta?
Amma kuwa za’a tauyesa da yawa yaron Nan
Yana fama da jinyar uban Kuma yanzu sai a basa wata kayan lalurar.
Girgiza Kai Momy tayi jiki amace da damuwa tace”
Ko a hali na ciwo Mahaifinta ya bayyanarda cewa nida ‘yata mune daga baya,
Dan kuwa inda ya bayarda aurenta guri ne daba gurin wasan kowaba Dan kuwa ko yayane sarakuna suka samu wannan matsayin sai anmusu barka bare anan….
Mamakine yakama umma Jamila ta kalli Sa’adah wadda duk ta yamutse gwanin tausayi tace”
Tashi kije idan nagama da momynki Zan dawo kanki Dan kuwa aure Babu fashi Kuma Babu inda Zaki tafi da ita.
Miqewa Sa’adah tayi ta juya ta nufi hanyar dakinta da tuni ta maida Laylah dakin nata tashige
Momyn tabita da idanuwanta dasukai laushi cikin sabon tausayin ‘yarta da hakanan takejin sabon son yarta akowane safiya Yana qara qarfi aranta
Gashi duk ta rame tasawa ranta damuwa da Jin Kamar tanada hannu acikin kowane Hali Laylah tashiga.
Kallon tsaf umma Jamila tayiwa Momy Kai tsaye tana Shirin magana Momy ta datasan tambayar dazatai Mata ta katseta da cewa”
_*ABU TURAB TURAKI*_ ……..
Da wani irin mamakin kasa gasgatawa ta kalli momyn ba tsayawa komai ta Dora tata tambayar da cewa”
AB TURAKI dai wannan Dana sani?
Aminin Mahmoud din?
Wannan dai Mai yiwa masu kudinma wuyar gani?…..
Kasa magana Momy tayi ta gyadawa umma Jamilan Kai tana maida bayanta jikin kujera ta jingina.