RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 15
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 15
Ta nufi cikin gidan jiki a sanyaye, kasa bude
fofarta tayi. Tabi motar da kallo har ta tsaya a
cikin jerin motocin Amna da Shatima. Ta bude
kofar ta ta shiga. Kasa cire kayan Makarantar
tayi, haka kuma ta kasa dora girki, duk ga kayan
Cefanen a gabanta. Ta dai yi ta maza ta kunna
Risho ta dora tafasasshen nama.
“*Lokacin da su Hajiya suka shiga gurin Nafisa
tana wanka. Hamida ta yiwa Mama da Hajiya
oyoyo. Aliya ta ga shigar mota, kuma ta leko taga http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
bakin Nafisa ne, don haka ta yafa mayafi ta fita
zata je da sigar duba jiki.
Tana shiga taga su Hajiya, gabanta ya fadì don
tasan Hajiya ba kalar wasa ba ce Amma duk da
haka ta cije ta isa ta zube gwiwa biyu a gaban su
tana gaishe su, yanda kasan zata yi musu sujjada
don girmamawa.
Hamida ta aje musu ruwa da lemo. Aliya ta ce
“‘Hamida ya jikin Nafisar? Yau da dadì jikin ko?”
Hamida ta CE
“Eh, gata can ciki tana wanka.”
Cikin kissa ta ce
“‘Masha Allah, kai naji dadi,
amma ta sha magungunanta ko?”
Ta ce,
“Kin san sai kin zo zata sha, don nayi-
nayi ta ki sha.
Aliya ta Ce
“Bari ta fito sai in
lallabeta ta sha. Naso in yi mata faten tsaki yau
ban san inda zan samu tsakin ba ne, amma ga
Rama can Maigadi ya siyo min.
Duk zubar da take yi su Hajiya suma jin ta,
kuma sun yaba mata musamman Mahaifiyar
Nafisa, don an ce me da wawa. Maman ta ce,
“Allah http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Sarki, kina ta dawainiya ko, kullum
Hamida tana fada min komai dare sai kin fito kin
dubata.
Hajiya ta ce, “Ai haka ake so shine zaman tare,
bare dama haka ake son babba. Ina ita “‘yar uwarku
fa?”Aliya ta ce,
‘”Amna, tana gurinta. Ita kuma da
sauki, sai bacci amma bari in dubota nasan yanzu
ta tashi.”
Mama ta ce,
“Allah Sarki, kiyi dawainiya da
wannan kiyi da waccan, Allah yayi miki albarka.
Aliya ta ce,
“Amin Mama.”
Ta fita cikin jin dadì
ta nufi sashen Amna ita dama burinta ta shiga
gurin kowa a yarda da ita, haka zai bata damar
kunna duk irin wutar da ta so.
Ta samu Amna zaune tana kallon TV, me
aikinta kuma tana bare mata Kwai guda biyu a kan
plate. Ta ce
“Sannu da hutawa.
.” Kallo daya Amna
tayi mata, sannan ta ce,
“Yauwa.
.” Ta maida kanta
gurin TV
Aliya ta ce “Hajiyar Shatima ta z0 tana dakin
Nafisa, ta ce in zo in kira ki.
Amna ta ce.
“Ina zuWa.
Aliya ta fita. Amna taja tsaki, “Ban da
Hajiya ce babu dakin wadda zan je. Itama Hajiyar
ta sauka can ne don ta nuna cewa tafi son
“Yar uwarsu, kowa Nafisa! Nafisa!!”
Aliya tana fita dakin Salma ta nufa, ta same ta
tana jajjage. Ta ce
“Ga su Hajiyar Shatima can
kije ki gaida su da Maman Shatima.
Salma tayi http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
rau-rau cikin tsoro, ta ce “Anty wallahi tsoro nikeji.”
“Tsoran wa?” Salma ta ce,
“Hajiya, wallahi,
Aliya ta ce, “Sai ka ce wata Mayya! Ta haifa miki
mijin ga shi nan yana ta uban kashe miki kudi
amma ki ce kina jin tsoronta?”
Salma ta ce,
“Ba haka ba ne Anty, ta taba yi
min fada ne, kuma ni tsoron fada gare ni.
Tayi
murmushin mugunta, a ranta ta ce,
*Yanzun ma
wani fadan zan sake ja miki.
* Ta dubi Salman.
“Wuce kije ki gaida ta.
Salma ta CE
“Bari in canza kaya, in cire na
Makaranta.
Aliya ta yatsina fuska jin cewa Salma
Zata cire kaya, in ta cire ai ta rage mata saukin da
ta samu na tseguntawa Hajiyar irin kudin da
Shatima ke kashewa Salma, wanda
abin ke
damunta kullum.
Salma ta dauki dan mayafin jallabiyarta ta
yafa, tunda kanta babu dankwali. Ta fita cikin
fargaba ta nufi sashen Nafisa. Aliya ta shiga
dakinta, dama ranar ita ce da Shatima, kuma ta
shirya masa farfesun kaza, yana wuta ma bata
gama ba.
Sannan tayi dafa-dukan kus-kus da hanta, nan
ta jero ma su Hajiya katon tire. Ta shigo dakin
Nafisa. Ta samu Salma tana rabe ta kasa karasawa ciki. Har da tsawarta “Mu je mana kin wani rabe.
Hajiya ta ce, “Wace ce?”
Aliya cikin sigar son
tura Kiyayyar Salma ga surukar tasu ta ce,
“Salma ce uwar shashanci.
Hajiya ta gimtse fuska har
Amna da Mama dake zaune. Salma ta tsugunna a
gabansu, kana kallonta ka san a firgice take.
Aliya ta dire tiren a gabansu nan kamshi ya
cika dakin. Ta kalli Hamida
“Kawo plate da http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
cokula.
Salma cikin raunanniyar murya ta ce,
“Sannunku da zuwa Hajiya.
Mama ce ta amsa
“Yauwa sannu yarinya.” Ta kalli Nafisa wadda ke
Taune kan kujera ta ce,
“Sannu Anty, ya jiki?”
Itama fuska tam! Ta ce
“Da sauki.
Ita kowa ya saka ma ido. Hajiya ta kalli Salma
cike da tsana. Ta ce, “Haka ne? kudin makarantar
dubu saba’ in da biyar?”
Salma cikin rawar jiki ta
ce, “Yanzun sun cike tamanin.
Hajiya ta mike cikin sauri,
“Kice ke ya ke yi
ma aikin kenan? Kullum ta Allah dubu da dari
biyar a wata nawa kenan? Jama”a kuyi min
lissafi.
Amna ta cE
“Dubu arba’ in da biyar.
* Nafisa taCE
“Kan uba! Muna zaune?”
Hajiya ta ce,
“To al
ko ni da na haife shi ya min haka nasan ya kai da.”
Maman Nafisa ta ce
“To shi me ya kai shi wannan
batan basira? Wai rokon Allah da goge.”
Hajiya ta soma kiran layin shi ya daga. Ta ce,
“Ina gidanka, Allah Yasa ka kusa tashi?” Ya ce,
“‘Insha Allah nan da awa daya zan dawo.”
Ta cE
“To sai ka iso.
Ya ce Ke da wane ne?” Ta ce,
“Ni da Mamanku ne, Mustapha ya kawo mu
Salma wadda sautin kukanta ya soma fitowa tace, “Don Allah Hajiya kuyi ha…
‘ Jifan da Hajiyar
tayi mata da dan karamin filon kan kujerar ne ya
hanata karasa maganar. Hajiyar taci gaba da cewa,
“‘Ban son jin komai daga gare ki ‘yar dangin masu asiri
Ai tun daga kan yanda yaron nan ya zo tamkar
ya yi hauka a kan wannan kazamar nasan aikin
sihiri ne.” Ta kalli Maman su Nafisa.
“Ki tuna fa http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
bai taba kwanciyar asibiti ba sai a silanta, dan na ce
ba za ya aure ta ba, ranar ya tashi a sankare idanu
kakkafe muka nufi asibiti.
Duk matan suka kalli Salma cikin mamaki,
musamman Amna wadda take da matukar tsoron
asiri. Na fisa ta ce,
“Wai dama ciwon nan saboda
ita ya yi?”
“Hajiya ta ce,
“‘In kin je gaba ma ki fada.
Da naga abin nashi yayi yawa, sai nasa a yo min
tambaya gurin Malamai, can suka fada min uwarta
tasa an yi asiri da sunan Shatima, kuma an hada da
naman bakar Akuya da miyon bakinta da ruwan
hawayenta an ba shi ya ci. Daf da bikin fa har gida
ya sai musu.
Cikin sauri ta dago tana fadin “Wallahi haya
ce.
Hajiyar ta sake jifanta da wayarta da ke
hannunta.
“‘Karya zan yi miki don ubanki?”
Aliya cikin sauti ta dauki wayar tar da fadin,
“Hajiya wayarki kar tayi lahani.
” Hamida wadda
tausayin Salma ya cikata, haka kawai taji ba
gaskiya ba ne abin da Hajiyar ta fada. Don haka ta
saci wayar Nafisa tayi cikin daki, ta kuma fada
bandaki.
Aliya ta kalli Hajiya “Kiyi hakuri bari in zuba
muku abincin.
** Ta ce,
“Saka wa Mamanku dai, ni
ai abincin nan ba zai ciwu ba sai an yi ta ta Kare a
yau din nan.
Nafisa ta ce, “Ai gara ayi, don ko da a ce kowa
ya yarda ni ba zan amince ba.
Son kai kiri-kiri. http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
Aliya tace
“Ai ba yin kansa ba ne, ba ki ji abin da
Hajiya ta ce ba?”
Amna wadda ta yarda da zancen dari-bisa-dari
ta kalli Salma cikin tsana. “In dai tana gidan nan ni
kam ba zan zauna ba, don gaskiya bana son asirce-
asirce din nan.
Hamida ta kira sau uku kafin ya daga. Ya ce,
“Ya ya ne?”
Ta ce,
“Yaya don Allah ka zo gida
yanzun domin ga Salma din nan an tsare ta su
Hajiya.”
Gaban Shatima ya fadi, sam ya manta da tsanar
da Hajiya tayi ma Salma. Ya ce,
“Na gode
Hamida, gani nan zuwa.”
Lokacin tashi bai yi ba yaga cewa dole ne fa
yaje gidan don kashe waccan wutar da shaidan ya
rura a cikinsa. Ya dauki uzurin gaggawa ya fita.
Bai san irin gudun da ya yi ba, ya dai ganshi a
layinsu.
Yayi fakin lokacin ne Mustapha ya fito daga
falon Aliya, Shatima ya nufi gurinshi. “Ina su
Hajiyar?”
Mustapha ya ce,
“‘Suna falon Nafisa,
Ya Ce,
“To bari in je mu gaisa.
Mustapha ma ya
biyo shi don ya gama cin nashi abincin.
Tun daga Barandar yake jin muryoyinsu daya-
bayan-daya. Hajiya tana fadin
“Ba bakin dan
Akuya ba, ko da bakar Jaka ku ke asiri yau sai kin http://WWW.DAILYNOVELS.COM.NG
bar gidan nan
Amna cikin kuka tana fadin,
“Yanzun zan kira
Dad dina a zo a dauke ni, ina tsoron asiri.
” Nafisa
tana fadin “Jiyan nan sai da nayi mafarki da ita, ba
zan iya tuna me ya faru a cikin mafarkin ba, amma
tabbas na ganta.
Ni kaina in tana gidan nan Mama da ku zan bar
shi yau don ba za ku bar ni ba.
• Mustapha ne ya
fara shiga, hakan ya hana Aliya yin maganar da
taso yi, don ta hange shi tsaye.
Cikin tashin hankali ya shiga dakin inda gaba
daya suka maida kallonsu gare shi. Sannan
kowacce ta.shiga nanata abin da dama ya ji suna
fada.
Hajiyà ta ce,
“Duk kuyi shirunku, yanzun dai
ka zaba ko ni da na haife ka da iyalanka, ko
kuma wannan yarinyar ita kadai.
.” Ta nuno mishi
Salma wadda ke durkushe tana cikin firgici da
matsanancin tashin hankali.
Itama kallonshi take cikin tsananin bukatar
taimakonshi. Idanunta suna nuna shine kadai na
Karshe da ta ke sa rai zai yi wani abu a kan
wannan halin da take ciki.
Hajiya ta katse shi da fadin,
“Zan la’ance ka in
“ka sake kallonta. Kuma na baka minti daya rak!
Ka yanke hukunci.
Mu hadu a littafi na uku
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.DAILYNOVELS.COM.NG