RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
RANA DAYA BOOK 2 CHAPTER 2 BY HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Mun tsaya
Munnir ya ce, “Wai don Allah Shatima lafiya ka ke tsaki?” Ya ce, “Ina tunani ne, yarinyar nan Salma tana can cikin damuwa, koma ayi mata wani abin tun da na san ba a sonta
Munnir ya zabga ma Shatima wata harara, sai ka ce irin yara kanana din nan, sannan ya ja dogon tsaki ya ce, “Ka san Allah har na soma tsanar wannan Salmar, duk ka bi ka zama wani soko a kanta.”
Ya ce, “Munnir ba zaka gane ba ne, da dai na sani da na ce ma Anty Momiyo a hada ta da Aliya nasan zata kula min da ita.”
Ya ce, “To ka kira mana ba ga waya a hannunka ba, ka dame mu da tsaki.” Shatima ya fita ya kira layin Anty Momiyo, sai a kira na uku sannan ta daga.
Ya ce, “Haba Anty, kin ki daga wayata.” Ta ce, “Wallahi na gaji ne, na fara bacci.” Ya ce, “Anty don Allah Salma ita da wanene?” Ta ce, “Oho ban duba ba, ‘yan uwanta dai sun fito sun tafi.”
Ya ce, “Ya ya za’ayi don Allah ki hada ta da Aliya.” Anty Momiyo ta ce, “Babu ruwana da Hajiyarku. Kowace Amarya an barta ita da kawayenta da danginta. Sai in je in ce tazo ta hadu da wata! Babu ruwana.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Ya ce, “To don Allah dan leka min ita Anty ba wai na raina ki ba ne.” Ta ce, “Sai dai in saci idon Hajiyar ka in duba don gaskiya ba da wasa take yi ba a kan wannan Salmar, zata saka kafar wando daya da duk wanda ya ce zai ko kalli inda Salmar take.”
Ya ce, “A taimaka mini zan jira kiranki.” Kamar minti goma ta kira shi, da sauri ya daga ko ringing bata yi ba, har ya bata ‘yar dariya. Ta ce, “Dama zaman jirana ka ke yi?”
Ya ce, “Wallahi.” Ta ce, “To ita daya ce a dakin, kuma sai kuka take, wallahi har ta bani tausayi.” Ya ce, “Anty ba ki bata hakuri ba?”
Ta ce, “Au, ba ka ga kokarina ba, so ka ke sai na
ja ma kaina matsala da ita kaga ni sai da safe.” Shatima ya zauna ya zabga tagumi suna ta hirarsu.
Haushi ya hana Munnir magana. Sha daya saura, Munnir ya ce bari yaje gida. Ya zubawa Shatima makullan motocinsa guda biyu, tare da fadin “Ga wadannan ka rike zan tafi da dayar motar.” Www.bankinhausanovels.com.ng
Shatima bai tanka ba. Munnir ya ja tsaki, “Duk ka damu mutane da zancen wata tsuntsuwar yarinya,
ka dauki jarabar so ka dora mata. Shatima ya ce, “Kai ka ki saurarona ne bare ka gane dalilina, kaje kawai.” Munnir ya wuce.
Shatima dai ya rasa sukuni, sai tunanin yanda zai fidda Salma a matsala. Har kusan sha biyu bai samu mafitar da ta wuce yaje gidan ba, duk da su Hajiyar sun nuna cewa zuwan shi gurin Amaran a yanzun ba tare da an yi budar kai ba kamar wani haramun ne bisa al’ada.
Sha biyu da mintuna ya shigo da mota harabar gidan, ya kalli gefen baki inda Aliya take, sannan ya taka ya nufi falo. Babu mutane sai yara da suka yi bacci a kan kujerun falon. Amma yana jiyo magana daga gefen Hajiya, cikin sanda ya nufi samanshi. Salma wadda ta sha kuka fuskarta ta kumbura suntum! Kukanta da yawa, ta tuna Mahaifinta, ga rabuwa da Innarsu, da Yaya Hadiza, da Yaya Auwal, da Umar kaninta. Sannan gashi da a lamun bata samu karbuwa a wannan dangin ba, sannan gashi ba ita kadai gurin miji ba.
Tana jin lokacin da Anty Momiyo ta bude kofa, cikin sauri ta dago ta dube ta, sai taga matar ta tabe baki ta juya. Hakan yasa ta sabon kuka ga makogwaronta ya bushe, tana bukatar ruwa.
Sake bude kofar taji anyi, cikin sauri ta sake dago da kai suka yi ido hudu da Shatima. Wasu sabbin hawaye taji sun zubo mata, da sauri ya iso ya tsugunna a gabanta.
“Salma, mene ne? An yi miki wani abu ne?”
Yasa hannu ya dago fuskarta. “Subhanallahi! Haka
fuskarki tayi? An dake ki ko?” Muryarta a dishe, tace “Ba a bige ni ba.”
Ya ce, “Kukan me ki ke yi to, saboda ba ki sona?” Ta zuba mishi ido kawai tana kallonshi. Ya ce, “To share hawayenki, na tuna ke ba ki ma san so ba ko?”
Ta daga kai alamun ‘eh’. “Na gano kukan da ki ke yi na rabuwa da Inna ne ko?” Ta daga kai. Ya ce, “To kada ki damu, zan dinga kawo ki a kai-akai kin ji?” Ta ce, “To.” Ya ce, “To yi murmushi.” Ta dan kirkiro shi tayi.
Ya mike ya soma kwashe kayan shi da ke zube a kan gadon, duk sabbin da ya yi ta canji ne, sai kamshi suke. Ya ce, “Bari in rage miki kayan nan Www.bankinhausanovels.com.ng
ko? Za ki ma iya kwana ke daya? Me yasa ba a bar miki kowa ba? kuma ke wai ba ki da kawaye ne?” Ta ce, “Su Yaya Hadiza sun ce an yi musu wulakanci ba za su zauna ba, ni kuma ban gayyaci
kowa ba saboda Babanmu bai dade da mutuwa ba.”
Ya dan yi jim! Don bai so abin da aka yi musu ba, amma sai ya kauda zancan da cewa, “Kina jin yunwa ko?” Sai lokacin ta tuna duk yinin ranar ba ta ci komai
ba. ya matso “An baki abinci?” Ta ce, “A’a, yau ma bana zaton na ci wani abu.”
Ya ce, “To ina zuwa.” Ya fita, ta sauke ajiyar zuciya. Taji dadin lallashin da ya yi mata.
Mota ya zara ya nufi gurin saida kayan kwalam. Ya siyo Kaza da madara zalla mai sanyi da ruwa. Ya sake wucewa cikin sauri ya nufi samanshi.
Sai dai wani tsautsayi, katsam! Hajiya ta fito da nufin zuwa saman don yin gargadi da barazana ga Salman da danginta in tare suke, sai kawai taga Shatiman yana bin kafar bene.
Sororo ta tsaya tana kallonshi har ya wuce. Ranta yayi mugun baci, ban da gidan cike yake da baki ga su Amna da danginta, da sai ta yi tijara a cikin daren nan Ta gama yarda dari-bisa-dari cewa wadannan talakawan sun asirce mata da.
Shatima bai san Hajiya ta ganshi ba, yana shiga ya same ta kwance ya ce, “Tashi Salma.” Ta mike zaune. Shi ne ya cire mata tsokar yana aje mata, ita kuma tana dauka tana ci tamkar irin dai yanda za ka yi wa karamin yaron da ka ke son ya ci abinci.
Ya zuba mata tatacciyar madarar a kofi ta dauka tana sha. Sai da ta koshi tam! Sannan ta sha ruwa, lokacin ne ya duba agogonshi biyu saura minti shida. Ya ce, “Kai! Har dare ya yi haka? Bari in je in Www.bankinhausanovels.com.ng
kwanta nima.” Ta ce, “Amma a cikin gidan nan za
ka kwanta ko?” Ya ce, “A’a in da abokaina suke.”
Ta ce, “Kada fa wani abu ya faru da kai…” Kwankwasa kofar suka ji an yi, gaban Shatima ya fadi, ya isa gurin kofar ya ce, “Wane ne?” Muryar Hajiyarshi ya ji ta ce, “Ka bude ka gani.” A fili ya ce, “Ya salam!”
Ya bude a cikin tsoro. Ciki ta shigo sannan ta maida kofar ta rufe. Tana juyowa bai ankara ba sai jin saukar mari yayi dau!! Salma ta mike a tsakiyar gadon duk ilahirin
jikinta ɓari yake. Hajiya ta wuce shi ta iso gurin
Salma, cikin sauri ya nufo ya tsaya tamkar zai kare
ta. Hajiya ta nuna ta “Ke! Kalli cikin idona kin ga
alamar wasa?” Salma ta durkusa gwiwa biyu a kan gadon. Hajiya ta ce, “Ba ki da gurin zama a gidan dana, ki fada min ina ku ka je ku ka asirce min da?” Salma ta soma kuka, tare da fadin “Wallahi
Hajiya ba ma zuwa gurin asiri.” Shatima ya ce,
“Haba Hajiya!..” Ta dora yatsanta a kan lebe
“Ka min shiru.” Ya ce, “Hajiya ina mamakin wannan fa ba halinki ba ne, ni na sani kina da tausayi.” Ta ce, “Na ce ka rufe min baki.
Ta sake kallon Salma, “Zan sa a kama duk danginki a rufe min har sai sun karya asirin da suka yi wa dana. Kuma sai ya sake ki, sa’arki daya gidan nan yau da bakin alkairi bakin kunya, da sai na sa yai miki sakin wulakanci.
Ina son ki sani zan zo har Kadunar kuma zan sa ya sake ki, kar ma kije da tunanin za ki shantake wai kin samu gurin zama. Sannan gobe ne bikina na nan gidan, da wasa kar ki sake ki fito bare ki bata min biki, na fada miki.”
Salma bakinta na rawa ta ce, “Ba zan fito ba Allah, kiyi hakuri don Allah!” Tsaki Hajiyar taja “Ki ma fito ki gani.” Sannan ta juya kan Shatima.”Kai kuma fita muje, abin da ya sa ni ke raga maka don nasan ba yin kanka ba ne.” Ya ce, “Hajiya ni fa babu abin da aka yi min.
Ta ce, “Ai ko anyi maka kai ba za ka sani ba. Da haka ka ke? Kai da ka ke tsayayyen namiji mai ji da kansa, gashi kan wannan duk ka zama soko, wuce muje.”Haka ta tasa shi a gaba har cikin dakin Mustapha Www.bankinhausanovels.com.ng
kaninshi da ke can cikin harabar gidan, ta ce “Shiga
nan ka kwanta.” Yana shiga Mustapha tuni sun yi bacci da shi da wani dan uwansu da suka zo biki, kan kujera ya zauna cikin tashin hankali da tunanin Salma.
Ita kuwa Salma tana tasa shi gaba suna fita, ta
sauko daga kan gadon tana kuka, ta samu can kusa
da wata durowa ta shige sakon ta zauna. Kanta ya sake kullewa, lallai gaskiyar Inna ne da ta ke ta jinjina al’amarin auran nan, tabbas akwai dinbin da na sani a cikin duk abin da aka yi gaggawar shi, domin wata gaggawar daga shaidan take.
Yanda Salma ta kwana zaune, haka shima Shatima zaune ya kwana, kowannansu cikin takaici tare kuma da rasa wane irin tunani ya kamata suyi.Da Asubahi Salma tana jin kiraye-kirayen sallah, har a ka shiga Masallaci. Ta yunkura ta tashi, tana rangaji ta nufi ko far da take zaton bandaki ne.
Tayi alwala, ta kalli fuskarta a madubi, har yanzun a kumbure take. Ta zo ta yafa gyalenta da aka rufo mata, tayi sallah tana addu’a tana jin sanyi yana ratsa ta, kasancewar lokacin sanyi ne.
Ga wani irin bacci da take ji tamkar na mutuwa. Kan gadon ta hau ta ja bargo ta kudundune, nan kuwa bacci me nauyi yayi awon gaba da ita.
Shi kuwa Ango bayan sun fito Masallaci, yana son zuwa dakin abokansa inda suka yi masauki. Amma kuma yana son sanin halin da Salma take ciki.
Ya nufi falo lokacin gari ya soma yin haske. Ya samu Hajiya ta saka ‘yan aiki suna ta gyaran falo da gida. Tayi kicin-kicin da fuska, kuma da kyar ta amsa gaisuwarshi.
Ta ce, “Ina za ka nan?” Ya ce, “Badi’atu zan kira.” Ta ce, “Tana dakina tare da su Nafisa.” Ya tsaya. Ta ce, “Shiga mana ko ni zan kira maka ita?” Ya wuce falon Hajiyar kai tsaye. Duk ‘yanmatan
Nafisa ‘ya’yan dangi ne nan suka kama gaida shi. “Sannu da zuwa Yaya.” Ya ce, “Ina Badi’atu?” Suka ce, “Tana cikin dakin Hajiya tare da Amarya Nafisa.” Yayi kamar ya ce su kira ta, sai kuma yasa kai ya shige dakin. Www.bankinhausanovels.com.ng
Nafisar tana kudundune a gadon Hajiya cikin bargo, tana danna waya. Su Badi’atu suna kan gadon a gefen duk hira suke. Nafisa tayi maza ta tashi zaune jin muryar Shatima.
Ya ce, “Badi’atu zo nan.” Suka kalli juna na lokaci. Rabon da su hadu tun ranar da yaje ba ta kati ta ki amsa. Shi ne ya fara dauke idanu daga kai, sannan ya ce, “Kina lafiya?”
Ta sauke ajiyar zuciya tare da fadin “Lafiya.” Sannan ta koma ta kwanta rigingine tare da jan bargon zuwa kirjinta. Ya fita tare da fadin “Zo Badi’atu.”
Suka tsaya a babban falo. Ya ce, “Hau dakin
nasa ki kwaso min wayoyina.” Hajiya da ke kallonsu
ta windown waje, ta hangi Badi’atu tayi sama, ta ce,
“Ke! Ina za ki nan?” Shatima ya ce, “Wayoyina zata kawo min.” Ta ce, “Oho!.” Ya ce, “Badi’atu zo.” Ta dawo, muryar shi kasa ya ce, “Don Allah Salma tana ciki ki duba min wane hali take ciki? In kin dawo ki same ni a dakin Mustapha.”
Kusan minti tara, sannan ta shigo. Tana ba shi wayoyin shi kuma yana tambayar ta ganta? Badi’atu ta ce, “Na ganta tana bacci a kan gadon ka ta rufa.”
Ya amshi wayoyin tare da fadin “Alhamdulillah.” Ya kama hannunta “Zo kiji Badi’atu. Don Allah ki min wani taimako.” Ta kalle shi cikin mamaki,
Yayanta mai izza da isa yau kuma ita yake roko. Ta cè, “To mene ne zan yi maka Yaya?” Ya ce, “Ina son ki ke kula da Salma, in ta tashi don Allah ki dan debi abinci ki bata, duk abin da ya dace ki taimaka mata, ni kuma duk abin da ki ke so in an gama bikin nan ki fada min zan miki shi.”
Badi’atu ta ce, “Ba sai ka bani komai ba Yaya, zan kula da ita insha Allah.” Ya ce, “Na gode kanwata.” Da ta tafi ya ji sanyi a ranshi, sannan ya kira
layin Aliya, suka gaisa. Ya tambayi lafiyarta da ta
mutananta. Ta ce, “Duk suna lafiya.” Ta ce, “Jiya
ina daga window naga ka shigo, ka kuma fita ka
dawo. Ka ban tausayi sai naga duk ka fada.”
Ya ce”Ai naso in zo in da ki ke lokacin, Salma ce bata ci abinci ba, na fita na siyo mata.” Gaban Aliya ya fadi. Ta dake ta ce, “Ai da ka kira ni nan ga Www.bankinhausanovels.com.ng
abinci sai yanzu ma na kwashe kayan.” Ya ce, “Tana dakina ita daya ce, ta bani tausayi,
har kusan karfe biyu ina gurinta. Aliya ta sake danne kishinta tace, “Allah Sarki!
Da ka rako ta nan sai mu kwana. Ya ce, “Babu
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE WWW.BANKINHAUSANOVELS.COM.NG