RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 10 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Tana wanka ta fito don ta yi shirin bacci. Kan gado ta

samu Shatima a kishingide. Tayi mamakin ganinshi,

saboda bai cika zuwa ba, sai in zai saka kaya. Ta nufi

gurin da ta aje kayan baccin ta saka, sannan ta dube shi,

“Sannu da shigowa Ya ce,

“Ke ma sannu da wanka

Ta yi yar dariya, sannan ta fita zuwa kicin. Ya

ga tana ta jero masa tukwane dauke da nama.

Ta ce,Kalli kason da na yi

Ya ce,Kason me?”

Ta ce,Nama mana, ga naka, ga nawa, ga na su Hajiyarka, ga na kaka, ga na Innarmu

Ya yi yar dariya,

“Da ma haka ake yi?”

Ta ce,To da mu kadai za mu ci?”

– Ya ce,

“To yanaga na Inna,ba shi da yawa.

Kara musu da nawa”Ta ce,

“Ai ba su da yawa

Ya sauka ya dauki tukunyar ya zuba mata

kusan rabin nashi. Ta rike,

“Barshi hakaYa ce,

“Da kin bar su Hajiya, don nama yana

can kamar ya yi magana a gidansu •

Ta ce,Ai namu daban, tana son ta ga na

gidankaYa ce, “Salma!”Ta dago ta dube shi, ya ce,Kina da manyance ko da yake na ga kin girma. Maida naman kizo

*Sai kawai ta ji gabanta ya fadi. ni

Tana dawowa sai ya janyo ta zuwa, jikinsa.

IAbubuwan da yake mata ne suka tsorata ta. Ta ce,Yaya don Allah ka bari”Ya ce,

“Salma yau zan amshi hakKina matsayin

mijinki, domin naga kin soma girma

Ta ce,Na shiga uku Yaya, ba zan iya ba

Ya ce,

“Zan koya miki, kar ki damu’

Yana dora ta kan gado ta rarrafa zuwa karshen

gadon ta makure. Ya cire kayan sannan ya dube ta.

Daga shi sai gajeran wando, ta boye fuskarta a cinya,

tana fadin,

“Yaya don Allah ka sa kayanka. Yaya na

shiga ukuna Yana janyo ta sai suka hau kokawa. Sai kyarma take tana kuka.

Ya ji haushi har ma komai ya fice masa a rai,

ya hankade ta, sannan ya tashi ya fita zuwa falo bayan

ya saka jallabiya. Ya kwanta kan kujera cikin bakin ciki.

Tun kusan kwana uku yake a matse, Nafisa ta

Yi nauyi dole ya tausaya mata, Aliya kuma tana al’ada.

Ya kwana da takaici, ita ma dai Salma ba ta runtsa ba,

ga shi tana son ta yi masa abin da yake so, amma ta kasa don tsoro

Yana yin sallar asubahi ya nufi dakin Amna, ya

bude ya shiga. Gadonta ya hau ya kwanta cike da

kewarta, ya dauki filo ya rungume. Bacci ya dauke shi,

karar wayarshi ce ya tashe shi, ya mike zaune. Amnar

Ce, ya daga cikin jin dadi yana fadin, “Zuma ta ina cike

da kewarki, da mafarkinki”Ta ce,

“Amma ga shi sai ni na kira ka, tun ranar

jajibiri da ka kira ni?”

Ya ce,

“Yanzun haka ina Dakinki, ina kwance

kan gadonki rungume da filonki ke da yarona kawai nike son jin duminku’

‘Ta ce, “To yau zamu taso”

.”Ki ce inzo Kano in jira ki?’A’a, sai na huta

“To yau za mu je Zaria ranar da za mu

dawo sai in zo mu taho’

Tace Haka ya yi”.

A nan dakin ya yi wanka ya shirya tsaf?

Lokacin da ya koma dakin Salma ta kammala abin kari

don haka yana zama ta fito daga kicin ta aje a gabansa,

tare da yi masa zannu. Bai ko kalle ta ba bare ya amsa.

Tana kallo ya dauki wayarsa ya kira Aliya ya ce ta kawo masa abin kari dakin Salma.

Salma” ta soma sabon kuka tare da fadin,

“Yanzu Yaya ba za ka yi min hakuri ba?”

Ya daka’ mata tsawa, Tashi a nan!”

Ta tsora ta sosai cikin hanzari ta dauki tire din

kayan shayin ta maida kicin. Ta zo da gudu ta shige

daki, sannan ta banko kofa. Tana jin shigowar Aliya

saita daga labulen window tana kallonsu: Ta hada

shayi ta mika masa, ta saki labulan ta koma kan gado

ta kwanta tana kuka.

Tsaf ta gama shirin zuwa Zaria tana jiransu.

Nafisa da Aliya sun shirya tsaf, Salma ta kulle namanta

da ta kasa da cincin. Shatima ya shigo zai dauki

wayarsa, ya ga Salma ta fito da kayan tafiya. Ya dubeta cikin tsawa,

“Ko kofar gida na ji labarin kin fito sai

na yi mummunan sa6a miki Ta ce,

“Yaya don Allah, to ka z0 yanzu na

yarda ko zan mutu, Allah zan yarda kada ku bar ni, ina

son in je Zaria”

Ya ce, “Ki bar abinki bana so, na tsani duk

wani abu da ya fito daga gare ki”

Kalaman Shatima sun yi tsauri a gurin Salma

Ba ta kara magana ba, ta dauki kayan sawarta ta maida

ciki. Ta dauko kudin jiya sababbi ta Kirga dubu biyu ta

Kulle a leda ta sa a cikin Kullin Kaka. Ta sa dubu biyu a

na Innarsu, sannan ta dauka ta nufi gurin Nafisa. Ta

samu suna ta saka kaya a mota, ta kira Hamida ta ce

“Don Allah ki ba ni dama in ba ki sako”.

Hamida ta ce, “Ba za ki ba?”

Hawaye suka soma sulmiyo mata, ta ce, “Ya ce ba zan je ba. Don Allah ki ba Anty Badi atu wannan

daurin kayan za mu yi waya. Wannan kuma ki ba

Hajiya na san can za ku fara zuwa”.

Hamida ta amsa tare da cewa, “Insha Allah zan ba su. Ki yi hakuri ki daina kuka’

Ta ce, “Na gode”. Ta juya.

Aliya ma ta fito da kayanta, ta cema Salma,

“Ke ba ya ce ban da ke ba?”

Salma ba ta tanka ba ta wuce, sai ta ji Aliya ta

saki dariya kyalkyal. Ba ta waiwaya ba ta shige daki ta

banko kofar. Ta hau gado ta kwanta, sannan ta kira

Badi’atu, ta ce, “Ga sako nan ta taimaka mata da shi zata amsa a gurin Hamida.

Badi atu ta ce, “Au ba za ki zo ba!”

Ta ce, “Eh na yi laifi ne, ya ce ba zan zo ba”

Badi’atu ta ce, “Mayafin da na miki message

jiya?”Salma ta ce, “Ban gani ba wallahi, me ki kace?”

Ta ce,, “Pink din gyalanki za ki ara min”.

Tace

‘”Au, bari in kai ma Hamida ta kawo

miki, amma ba’aro-ba, na ba ki duka”

Badi’atu ta yi godiya, ta je ta ba Hamida

mayafin.Salma tana jin fitarsu ta koma ta kwanta cike da

da ta sani. Ta lumshe ido tana tuno irin rokon da yake mata a kan ta ba shi hakkinsa, amma ta kasa. Dole yayi fushi da ita, fatanta Allah ya huci zuciyarsa kafin su dawo.

Ita daya a gidan ta kwana tsoro ya ishe ta

ba ta yi baccin kirki ba.

Washegari ta ce, bari ta je gidan makociyarsu

mai gwanjo inda shi ta siya, ko ta dan yi tattaki. Tana

zuwa maigadi ya ce,

“Yata ki koma ciki;, maigida ya ce

kar a barki ki fita, kuma kar a bar kowa ya shiga har su dawo

Salma ta ce, “Tofa!”

Ta juya ta koma ciki, ita ba talabijin ba bare ta

kunna ta kalla.

Kwana hudu suka yi cif sannan suka dawo,

Salma ta leka ta windo ta ga Mustapha ne ya kawo su

da motar Shatima, sannan ta ga ya dauki motar Amna

ya fita. Ba ta kara bi ta kansu ba ta koma ciki.

Amna da Shatima sun yi matukar murna da

ganin juna. Ya dauko ta suka nufo gida. Ranar gurinta

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE