RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 15 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 15 BY HALIMA K/MASHI
Da Kyar Mama ta lallashi Hajiya ta dauke shi
domin da ta ki, ta ce, ai ta ganshi a hannunsu. Duk wannan abu da su Hajiya ke yi sam Momy da ‘yan
uwanta ba su san ma arziki tana bori ba.
Shatima tamkar ya tafi da dan gudan jininsa
haka yake ji. Sun yi batun kayan suna, ya ce zai sa
Anty Momiyo ta turo mata lesissika da atamfa don ta
zaba, ya kuma tambaye ta ko nawa zai ba da game da
abincin suna?
Amna ta ce,
“Ni ban sani ba, amma bari in
tambayi Anty Amarya
Anty amarya ta ce,
“Tabdi! Gaskiya ban san ya
zan ce maka ba sha’anin gidan nan ana kashe kudi sosai, ka dai kimanta ka bada kawai
Ya ce,
“In na ba da dubu hamsin ya yi?”
Duk suka yi shiru, duk da sun san karfinshi bai
kai nasu ba, amma dai dubu hamsin bai kai ko kudin
kajin da za a dora a kan abinci ba. Ban da Sada ya
zama.ka’ida dole a yanka, ga nau ‘o’ in abinci da na sha.
Jin sun yi shiru Shatima ya ce,
“Anty abin ne da
yawa, yanzu haka Nafisa a watanta ta ke
Anty ta ce,
“Duk da haka sun yi kadan sosai”.
Ya ce, “To insha Allah zan kara”.
Amna ta ce,
“Ni ka bada dari da hamsin ko dari
biyu sai ka bar kayan da za ka sai min na fitar suma,
tunda ina da kaya ko na lefena ban taba ba, sai nadauka a ciki”
Anty amarya ta ce,
“Momy ma ta dinka miki
kayan suna tun zuwansu Dubai”
Ya kalli Amna,
“Shi kenan, in dari biyu ba ta
samu ba zan yi kokarin ko dari da hamsin ne. na gode
da karamci, in ina da kudì kin cancanci in kashe duk
abin da na mallaka a kanki da dana”
A mota Hajiya tana ta mitar abin da aka yi
musu a gidan su Amna, fadi ta ke,
“Ban da isa sai a
wani share mutane ana nuna irin wannan iko? Kai da
gudan jininka sai an wulakantaka sannan za a ba ka?
Mu ba rokonsu muka je ba, ba ruwanmu da abinsu”Mama tace
“Ke ma kina da gajen hakuri ne
Hajiya, shi fa shi’anin masu da shi din nan sai da kai zuciya nesa, don sai ka iya zama da su”
Shatima ya Ce,
“Wai me ya faru?”
Hajiya ta shiga rattafa mishi abin da take ganin an yi mata. Cikin sauri Shatima ya ce, “Laifina ne, nine na kasa ba da shi, ki yi hakuri”Daga nan ta dan saurara.
Ranar suna gidan tankam da dan Adam. Da masu masu zuri’a ne sosai, dangin Shatima da matansa sun z0, amma ban da Salma. Nafisa ma tazo ta gane wa idonta. An ci an sha kuwa komai sai da aka
barshi, ga maijego da jariri suna ta shiga suna fita.Nafisa kuwa a ranta fadi ta ke, ai gara da na zo na gane ma idona don kar in haihu ba a yi min wani abin ba.
Kyauta kuwa ta kaya da kudì har da mota yaro ya samu, babban wansu Amna ya sai mishi. Aliya kuwa tamkar “yar aiki haka ta zamar da kanta, duk wanda yazo ita ce mai zuba abinci duk da cewa akwai wasu da
aka tanada don raba abinci. Da ma neman suna take yi
a gurin dangin Amna, kuma ta samu. Don in sunata yaba mata. Da za su tafi aka hada musu kaya rigijit
Sai Karfe takwas da wani abu suka isa Zaria.
Nafisa ta ce, ita kam ba za ta tafi Kaduna a
daren nan ba, gobe a kawo ta.
Cikin wanna daren ciwon haihuwa ya taso ma
Nafisa, aka nufi asibiti da ita. Hamida ce ta kira
Shatima a waya ta sanar da shi. Ji ya yi tamkar ya yi
tsuntsu ya nufi Zaria. Ta sha wahala sai asubahi ta haifi
danta mai kyau. An yi mata dinki don sai da aka karata.
Da sassafe su Hajiya suka je asibitin da Alhaji,
sun yi murna sosai, Alhaji ya rungume yaron yana yi
masa addu’a. Ba tare da neman shawarar Shatima ko
Nafisa ba ya yi wa jaririn huduba da Musa, sunan mahaifin Nafisar, Kaninsa. Ya mika wa Hajiya shi tare da fadin,
“Karbi Musa na yi masa huduba
Hajiya ta ce,
“Alhaji ka yi shawara da iyayen
dan ne, ka san fa su
*ya yan yanzun kafin a haihu an
zabi suna
Nafisa ta yi dan murmushi tana daga kwance,
Tace A’a ba mu zabi suna ba
Alhaji ya ce,
“Ko ma dai kun zaba ta sunan dan
uwana Allah ya ci da shi”.
Sallamar Shatima ce ta sa Hajiya canza abin da za ta fada zuwa amsa sallama.
Gurin Nafisa ya
wuce kai tsaye ya kama hannunta yana yi
mata sannu.
Mama ta fito daga
bandaki tana yi musu sannu da zuwa. Suka gaggaisa, ta dubi Shatima ta ce,
“‘Har ka zo?”
Yace Eh mama
Sai lokacin ya gaida su
duka.
Hajiya ta mika mishi jariri tare da fadin,
Babanka Musa”
Mama tace
“Wa ya yi masa huduba da sunan
tsoffi? Don ita da ma sunan kakanta ne.
Alhaji ya ce,
“Su sai su ce ba sa son sunan
Baban nasu in ji
Shatima ya manna dan a Kirjinsa tare da fadin
“Wane mu? Allah ya sa ya biyo halin Baban namu Duk suka
amsa, sannan suka
koma kan
shawarar inda za a kai Nafisa gidanta ko nan Zaria.Shatima ya ce, shi dai ta koma dakinta. Hajiya ta ce,
“Wane ne zai kula da ita can?”
Mama ta ce,
“Tunda dai mijinta ya fi son ta
zauna a can a barta ta koma can”Hajiya ta ce,
“A’a in ba za ki tafi da ita ba, ni in tafi da ita”
Shatima ya ce,
‘”To duk yanda ku ka yi”.Ya dubi Nafisa,
“Ina ki ka fi so?”
Ta ce,Ni gurin Mama zan tsaya”Ya ce,
“Shi kenan. Aliya ta ce in gaida ki kafin
ta zo. Ni ma yanzun zan wuce gurin aiki ne”
Kaka ta ji dadin yanda a ka sa wa jaririn sunan
kakansa don ita tana son ake yi wa juna kara.
Kwana biyu da haihuwar Nafisa kwatsam sai ga Hadiza da Innarsu murna a gurin Salma ba a magana.
Ta yi musu girki mai dadi ta kuma hada musu abin sha.
Sun yini sun sha hira amma ko da wasa Salma ba ta sanar da su Inna rashin jituwarsu da Shatima ba. Ta dai
fada musu haihuwar Amna da kuma ta Nafisar da ta ji
a bakin Aliya, don ko shi ma ba ta samu ta yi masa barka ba.Inna ta ce, in ta koma za su je da Hadiza su yi
wa Hajiya kaka barka.
Salma ta ce, har da can gidan
Shatima duk ku je. Sai a nuna muku gidansu Nafisar tunda tana can Zaria din. Inna ta ce,
“Insha Allah za taje”
Da za su tafi, Salma ta kawo dubu’ biyar ta bai
wa Inna ta ce, ta yi jari ko na kayan miya ne don Inna ta yi kuka da rashin sana”a. Ta raka su suka tafi.
A bakin Aliya Shatima ya ji cewa Innar su
Salma tazO, ya same
“ta a dakinta tana rubutun
islamiyya, ya ce,
“Ke wato su Inna sun zo shine ba za
ki iya kirana ki ce min sunzi ba ko?”.
Ta ce,
“To ai Yaya ba ka daga wayata shi ne
dalili? Ya CE,
“Tò me ya hana ki yi min message?”
Ta yi shiru ba ta son jayayya ne kawai, amma
message nawa ta yi masa babu amsa. Ya ce,
“Kar ki sake yi min irin haka. To me ki ka ba su?”Ta dago
“ta dube shi a dan tsorace,
“Kudin
hannuna ne kawai na ba ta duka”.
Ya juya zai fita, ta ce,
“Ashe Anty Nafisa ma ta
haihu?”
Sai da ya saka Kafa a waje sannan yace”Eh”.
Gidan su Nafisa ta koma, Hajiya ta hada kayan barka ta kai. Alhajin su Shatima ya sai raguna. Ranar
barka ko in ce ranar kauri, gidan cike da dangi da yake
su ma akwai zuri’a.
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe