RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 19 BY HALIMA K/MASHI
Ta Ce “A’a.
‘yan dai ajinmu ne mafiyawa an
biya musu za su fitan; shine ni ma nace bari in fada
maka ko kana da halin biya min
Ya yi shiru yana kallonta yanda take kaduwa
kanta a Kasa ya san sanyin A.C dinshi ne, sai ya dauki remote ya kashe, sanan ya canza harshe daga Hausa zuwa Turanci.
“Ba ni da tabbacin kin san me ki ke yi a
makaranta har da zan biya miki ki yi jarabawar fita”Ita ma cikin harshen Turanci ta ce,
“Yaya bari
in debo maka dukkan sakamakon jarabawa ta ka gani,
har ma da kyauttukan da na yi ta samu a lokaci daban-
daban in za mu yi hutun canjin aji”.
Ya daga hannu,
“Barsu, kar ki kawo min me ya
sa ba ki nuna min ba, tun a lokutan da ki ka same su?”Ta ce,
“Yaya ina tsoro ne kar in maka magana
ka.Ya katse ta,
“In cinye ki? Ko ba haka ba ne?
kina tsorona kar ki fada min in cinye ki mana!”
Cikin däga murya ya ce,
“Bari in fada miki
wani abu. Zan biya miki kudi ki yi jarabawa Amma
ina son ki sani matsawar ki ka fadi jarabawar ko ki ka
rasa darasi daya aciki, to fa kin gama karatun boko. Baza ki je jami a ta
Cikin sauri ta ce,
, “Na yarda Yaya”.YaCe.
“Shi kenan, ki je zan je makarantar
taku Tace
“Na gode sosai da yawa Yaya”
Bai ce komai ba, ta tashi ta fita.
Suna cikin aji a zaune suna rubutu, sai ga wata ta z0 tace
“Salma A Bashir ta zo”
Tana zuwa ofishin shugaban makarantar sai ta
ga Shatima. Sun tabbatar masa zata ci jarabawar domin
duk ajin an san Kwazonta. Shatima ya biya aka ba shi
takardar shaida, ita kuma aka ce ta koma aji in an tashi tazo za a yi mata hoto da sauran abin da ya rage.
Kwanci tashi lokacin jarabawa ya yi, Salma
suka zana suka koma gida jiran sakamako da kuma lokacin zana jamb. Cikin wannan hutun ne bikin su Anty Badi atu da su hamida, Don haka ta tattara
dukkan kokarinta ta bada shi a islamiyya da hadda.
Balle yanzun da ta ke ajin sauka.
Wata juma’a Salma tana tsaka da muraja’a sai
ta ji sallamar Salma Dankasa, da murna ta tare ta suka rungume juna. Ta kalli Habiba Sulaiman ta ce,Yau
wace rana ga ki a gidanmu?”
Habiba tace ccccccccc
Duk suka sa dariya.Sun zauna ta ba su abinci da na sha, suka ba ta
katin biki da anko na bikin Habibar ne. Salma tana juya katin ta ce,
“Ku saka ni a addu’a a bar ni zuwa wannan
biki ko da rana daya ne”
Salma Dankasa ta zaro ido,Har yanzu bai
daina takurawa a kan fita ba yayan nan naki?”Salma tace
“Har yanzu baya bari. Sai dai wani
lokacin ba na ganin laifinshi in na ga yanda
‘yammata
ke lalacewa a wannan zamanin namu. Bugu da Kari ina
karanta littattafai ina Kara samun wayewar kai”Habiba ta ce,
“Dalilin Babanmu kenan da ya
tattara mu yace aure. Har da Fatinmu wadda ko
sakandire ba ta gama ba. Sai dai ya lura tana da janye
janyen kawaye
Salma Dankasa ta ce,’
“Mu ko Babanmu yana
da son karatu, kuma ba ya kawo komai a cikin ransa
game da mu. Sai dai mu ma fa muna karance-karance
mun san abin da zai cuce mu, don haka waye zai kai
kanshi?”
Sun yini sannan suka tafi.
An kusa sati Salma tana tufka da warwara kafin
ta iya tunkarar Shatima da katin biki, cingam da kuma
anko. Ranar yana dakinta
tuwon shinkafa ta yi da miyar ganye Shatima yana cin duk abin
da ta girka yanzun, musamman in ta yi abincin
gargajiya. Domin ta koyi kalolin girki a cikin littattafan
Hausa da take karantawa.
Ranar dai ta yi karambanin gyara masa dakinsa,
don kullum tana son ta gyara, amma tana jin tsoro.
Wani lokacin ma kulle dakinsa yake yi. Ta goge kayan
wutar ta sa turare, sannan ta jera masa abincin. Tun
kafin ya dawo sallar isha ta gama komai,
Da ya shiga dakin ya yi ta kallon ko’ina dakin
yana ta kamshi da kyalli, babu kura. Ya yi wanka ya
saka jallabiya ya zauna kan katifar yana cin tuwon
cikin nishadi, har yana zance da zuciyarshi cewa,
akwai kuwa abin da ya kai tuwo dadi? Ga labarai yana
kallo abinshi.
Salma ta yi sallama tare da dan tura kofar. Ya
amsa idanunsa na kan wayarsa da ke ringin. Ya daga
yana waya, ta kwashe kwanukan don ya gama ci. Ta dawo ta tsuguna tana jiran ya kare wayar da Hajiyarshi
suke magana a kan bikin Badi’ atu.
Da ya gama ya dube ta, “Mene ne kuma, don na san ke ba a ganinki sai kina da bukata’
Fadin hakan yasa ta kasa magana. “
Yace Ina jinki”
Ta Ce,
“Da ma yaya zan tambayi zuwa bikin
‘yar ajinmu ne”.
• Ta kai karshen zancen cikin faduwar
gaba da zullumi.
Ya tsura mata ido kamar mai tuhumarta, yace,
“Wace ce ” yar makarantarku?”
Ta zazzage ledar hannunta, ya bi cingam da
katin da kuma kyallen da kallo. Ya sa hannu ya dauki
katin ya karanta, sannan ya aje ya dauki kyallen,
“Wannan kuma fa?”
Ta ce,
“Kyallen anko ne’.?
Ya Ce,
“‘Maimakon a sako zanin sai a sako
kyalle?”Ta ce,Sun saka ne in mutum ba zai saya a hannunsu ba sai ya yi amfani da wannan kyallen’
Ya ce,Nawa suke saidawa?”Ta ce,
“Dubu uku ne yace
“Ina ne ake saidawa
‘ Ta ce,
“A sabon Kawo ne gidan su amaryar
Ya ce, “To su kawo miki amma a cikin bashi da
kike bina zan sai miki”Ta tsura mishi ido, “Wane bashi?”
Ya ce, “Dubunki hamsin da na ara, ai ban
manta ba Salma ta CE,
“Yaya tun a ranar na fada maka ba
bashi ba ne, baka fa na yi”
Ya ce,
“Ni ma tun a ranar na fada miki cewa ba
shine. ki kira su kawo miki zanin
Ta ce, “Ba ni da waya, ta lalace
Ya tura mata karamar wayarsa,
“In kina da lambarta kira
Salma tana ta mamakin yayan nata a yau. Ta
juya bayan katin inda ta sa Habibar ta rubuta mata lambarta, ta ce,Yauwa, ga lambar
Ta sa lambobin ta kira, babu kati, ta dube shi,
“Babu kati a wanna layin Ya turo mata katuwar,Kira da wannan
Ta dauki wayar cikin tsoro tana juya ta, ba ta
san ina za ta shafa ta kawo ba.
Ya kalle ta,Shafa tsakiyar”
Tana shafawa wayar ta kawo. Hoton Ashraf da
Junior da Shahid ne. Ta tsura ma yaran ido. Ba ta san a fili ta ce,
“Suna kama”. Ba sai da ta ji ya ce, “Duk ni
suka biyo Ta yin murmushi, sannan ta soma
saka lambobin.
– Habiba ta daga, Salma ta ce, “Ni ce Salma
Bash”Habiba ta ce, “Oho, ya ki ke?”
Suka gaisa, ta ce,
“Ina son anko guda daya, su
Salma Dan kasa sun amshi nasu?”
Ta ce,
“Gobe da safe, za ta zo ta amsa”.
Salma ta ce,
“Ki bata nawa ki ce ta bada a yi mana dinki iri daya da nata
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe