RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 20 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 20 BY HALIMA K/MASHI

 

 

 

Ta ce, “Zan ba ta, ba za kisai na dinner ba?”

Salma ta ce, “Dinner kuma?”

Ta kalli Shatima, “Kuma karfe nawa ce dinner

Din Habiba ta ce, “Karfe tara dai za a tafi”.

Salma ta ce, “Wai! Ba za a bar ni ba. Ki dai ba

ta atamfar sai ki z0 ki amshi kudin”.

Ya ce, “Ko ta turo account dinta”

Salma ta ce, “To ki turo account dinki zan tura

da kudin dinki don Allah ki ba Salma”

Ta ce, “Zan ba ta”.” Suka yi sallama, Shatima ya kalle ta, “To me za

ki je mata tunda Dinner ta yi dare?”

Ta ce,Kamu za ni”

Ya ce,Har da maza?”

“A’a ban da maza”.

“Shi kenan”Har za ta mike, sai ta ce,

“Ina son ma nayi

magana da Anty Badi’atu”

Ya kalle ta, “Kina son cinye kudin cikin wayata

ko?”Ta girgiza kai, tare da yunkurin mikewa.

Ya ce, Kira ta dai minti biyu za ku yi”.

Salma ta yi murmushi, sannan ta soma saka

Lambar Badi atu. Sai sunanta ya fito ya saka mata sister. Ta daga tare da fadin,

Yaya Salma ta ce, “Na’am Badi”atu tayi dariya,Salma ya ki ke?”

Ta ce, Lafiya lau, da ma kwana biyu ba mu

gaisa ba. Bikinki saura kwana sha tara ko?”

Badi’ atu ta ce,Au kina ma tambaya ne?” Nan

Salma ta sa dariya,

“Ina dai son in kara tabbatarwa ne”

Badi’ atu ta ce,

“To saura sati biki za ki z0?”

Salma ta ce, “Sosai ma tun saura sati daya zan zo Zaria tare za mu raba kati”

Hira ta yi wa Salma dadi har da zama dirshan kamar

ma ta manta cewa a waya take magana, kuma ta manta

da aron wayar ta yi, ta manta da mai wayar a kusa da

ita, suna ta tsara yanda shagalin zai kayatar.

Shatima shiru ya yi yana kallon Salma komai in

tana yi burge shi take yi. Bai taba ganin tana hira haka cikin sakin jiki ba, ya kasa katse ta sai kallonta kawai

yake yi. Har sai da ta ji daga ciki an soma gargadin saura minti daya kudin su Kare. Da sauri ta dube shi

tare da ciro wayar a kunnenta ta katse, sannan ta ce,

“Yi hakuri Yaya Sai ta ga ya yi murmushi,

“Kin manta kina

waya ne ko? Kati fa na zuba ba wai bonanza ba ce” Da hannu biyu ta mika mishi wayar tare da sake maimaita,”

“Yi hakuri”

Ya dubi gefen katifarsa, ta gane nufinsa ta aje

masa a gurin, don haka ta aje ta mike cikin sauri ta fita.

Ya bi ta da kallo.

Ranar kamu ta kama alhamis, karfe biyar aka

rubuta a jikin katin. Salma ta so bari sai karfe shida

saboda sanin wannan mummunar al’adar ta African time, amma kuma ta san in ta kai shidan nan Shatima

zai iya dawowa, kuma zai iya hanata tunda ya san ya bata kudin motarta dubu daya, kuma yana zaton tunda

rana za ta tafi biyar da rabi ta gama kwalliyarta,

ta yi kyau cikin anko, dauri mai hawa-hawa ta yi don yanzun ta kware sosai grin tsantsara kwalliya da

kuma daurin dankwali. Takalmi mai tsini ta saka,mayafi da ‘yar poss dinta mai igiyar chain. Sun dace da

atamfar, _ tana kulle kofar dakinta, Shatima yana

shigowa. Har zai wuce-sai kuma ya tsaya, ta nufo shi

– bayan ta gama rufe Kofar ta rusuna,

“Yaya sannu da dawowa › Ya daure fuska,

*”Kina nufin cewa yanzu za ki tafi?» Gabanta ya fadì, ta ce,Ai Yaya da yamma ake

Yin kamu fa”.Kina nufin titi za ki tafi yanzu

a haka ki hau mota?”

Ta ce, “Ai dole mota sai a titi”

sai Ya je ya yi baya da mota ya juya, daidai ita ya tsaya sannan ya ce, “Shigo in kai ki”

Ya kalli fuskarta bayan ya miki layin nasu don

zuwa titin, yace Da haka za ki biyo ta nan da wannan shafe-shafen? Dubi maza cike a nan

Ta yi shiru. Suna shiga sabon Kawo ya ce,

“To inane gidan?”Ta zaro ido,

“Lah na manta in z0 da katin saboda duba adress . Ya rage tafiya yace

“Au da ma haka za ki zo

Kiyita garari a layi Ta ce, “Wallahi yaya na manta katin ne

Ya nuna wayarshi a caji,

“To dauki waya ki

Ta ciro wayar cikin murnar ta samu madita

sai kuma ta yi turus da ta tuna ai a bayan katin na rubuta lambar Habiba. Shatima ya ja tsaki tare da fadin,

“Ki hakura da bikin bari mu juya gida .Cikin

sauri ta CE, Bari in kira Salma

Dankasa, har ta sare saboda Salmar ba ta daga ba,

domin wannan ne kashi na biyar da ta kira Salma

amma ba ta daga ba. Gab da tsinkewar kira na shida,

sannan Salma ta daga, Salma cikin fushi ta ce ma Dankasa,

“Banza kawai mara aji, ina ki ka aje

wayar?”Ta ce,

“Salma Bash, Allah ban san ke ba ce.

Wayar tana hannuna na zaci wani ne da yake ta

damuna, naqi dagawa a zatona shine ya canza lamba”Salma ta ce,

‘Kuna ina ne yanzu mun shigo

Sabon Kawo, ga shi ba mu san adireshin ba”

Salma tace,

“Ga amarya ta yi muku

‘kwatancen inda muke tare za mu tafi da ita’

Habiba ta yi musu kwatance, ashe ma suna

kusa da gidan, ta ce, “To Salma Dankasa ta fito mu ganta a waje

Daidai gate din suka samu Salma, ita ma ta yi

kyau cikin anko, ta sha kwalliya. Ta zo da sauri ta gaida yaya, Salma za ta fita ya ce,

“Kar ki kai magriba Ta ce,

“Yaya yanzun fa karfe shida, kuma Karfe bakwai saura ake yin magariba, ga shi kuma ko ramarya ba a dauka ba”.

Ya ce, “To yanzu karfe nawa ki ke nufin za ki

dawo?”Tace Sai dai mun je ko ba a tashi ba ni sai in dawo Wannan shi ne karo na farko da za kiJe biki. To ki sani ana wanke tukunya don gobe ne” Salma tace

“Insha, Allahu zan dawo da wuri”.

Ihu suka saki lokacin da suka hadu da sauran

Kawayensu. Amarya kuwa ta ci gayu sosai ana kan shirya ta. Sai kusan magriba suka isa hall din, inda suka dafa wa amaryarsu zuwa gurin zamanta. Da

yake har da kanwar Habiban ita ma da nata Kawayen.Ango sun shigo da abokansa, sannan aka yi kamu kawayen amarya da amarya sun shiga rawa

ana ta ruwan kudi. Salma duk ta tsorata da wani saurayi cikin abokan ango da ya zo yana yi mata liki. ta canza guri ya bi ta, har dai ta fita a filin ta samu

guri ta zauna. Sam ba ta ji zuwansa ba, sai magana ta jita bayanta, “Yammata kin gaji da rawar ne?”

A tsorace ta kalli gurin da yake, sannan ta

kauda kai. Ya ja kujera ya zauna,

“Ki fada min

sunanki da kwatancen gidanku”

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE