RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 21 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 21 BY HALIMA K/MASHI
Salma ta firgita matuka gani take ma magana
ma idan ta yi wa wannan mutumin alhaki ne, amma
dole ta tanka ko don ta roke shi. Ta dube shi, sannan
ta -waiwaya baya ta kalli gefe da gefe, sannan tace
“Ina da miji bawan Allah, ni matar aure ce
Ya yi dariya,. ‘
“Ta ya ya zan yarda da ke? Ba
kiyi kama da matar aure ba. Ni sunana Yusuf
Bashir, muna zaune a Malali, dalibi ne a jami’ar
Ahmadu Bello dake Zaria, kuma yanzu ina shekara
ta karshe, ina karantar.
Salma ta daga mishi hannu, “Malam, don
Allah ka tashi a nan! In kuma ba za ka tashi ba ni bari ka ga”. Ta mike da sauri ta koma filin, ta rike hannun Salma Dankasa, tace Salma zan tafi gida, ku zo ku raka ni”
Salma Dankasa ta dube ta, “Haba don Allah,
yanzu fa aka fara, kuma ko abinci ba ki ci ba”.
Ta ce, “Kin san da ya yaya aka bar ni? Don
Allah ni dai zan tafi, ga shi gurinmu da nisa, zan iya rasa abin hawa fa”
Salma ta ce, “Ki bari komai yayi dai dole a
kai ki har gida”
Salma ta hakura ta ci gaba da zama, amma a
darare. Ko da aka soma ciye-ciye Salma kawai ta yi ta ajiye. Ta kalli agogonta, tara saura ta
mike da sauri ta nufi gurin Salma inda suke
ta daukan hotuna. Tace
“Salma ko ba za ku raka ni ba
Nina wuce dare ya yi Salma ta cE
je ki sallami amarya in raka ki, tunda kinki bari a tashi Sukayi bankwana har da sauran kawayen
suka fito don raka ta, Salma tana rike da jakar da aka
raba ta biki, suna fita hall din sai ko saurayin da abokansa guda biyu ya tsaida su. Salma ta kalle shi ta ja tsaki, ta ce,
“Don Allah ku zo mu je”
Ya dubi Salma Dankasa, ya ce,
“Don Allah ki shiga, maganata da kawarki. Ina sonta na fada mata, amma ta ki ta saurare ni
Salma tace Ba kada matsala, ZanYi magana da ita, kuma za ka ji sakamako Ya ce,
“Za ku tafi ne in kai ku?”Salma Dankasa ta ce,
“Yauwa gida za ta ka kai ta Salma cikin daga murya, tace
Dankasa kina hauka ne? Ya kai ni ina?”
Cikin fushi ta wuce fuu ta barsu tsaye. Duk
suka saka dariya Kawayen Jamila Umar ta ce,
“Na rasà mai yasa Salma ba ta so ace ana sonta sam Dankasa tace
“Yayanta take tsoron. Amma ku zo mu je”.
Ta dubi saurayin,
“Yusuf mu raka ta ka kai ta mu dawo tare kafin a tashi. Amma bari ka ga dabarar da da za a yi a wace mota ce?”Ya nuna motar, tace
“Jamila bita ki lallashe ta, ku shiga motar, don ni yanzun ina je fada za muyi
Da Kyar Jamila ta sha kanta suka shiga motar.
duk baya suka zauna ta nuna ma Salma motar
saurayinta ce Fatima ma ta zo ta shiga, Dankasa ta shiga gaba. Sam Salma ba ta san wake jan motar ba,
sai da suka hau babban titi. Ta ji haushin ganin
Yusuf amma sai tà yi shiru don yanzun ba ta da burin da ya wuce ta ganta a gida.
Kafin su Karasa gidansu ta ce, “Ku aje ni nan
in karasa’ Yusuf yace
“Bari dai mu karasa ina ne gidan?”
Dan Kasa ta nuna mishi da hannu, “Ga gidan
Can Salma tace
“Subhanallahi, kada ki ja min
matsala. Salma wallahi kar fa ya zo gidanmu
Salma tace
“Eh ba zai zo ba, ku ke yin waya
Salma cikin gadara ta
ce, “To ki ba da lambata?”
Ta bude motar ta fita, Salma ta saki dariya,
“Na tuna ba ta da waya Ita dai ba ta waiwayo ba, burinta ta shige
gida.Allah ya sa lokacin Shatima ba ya gida, goma saura ya shigo sasan Salma. Tuni ta cire kayanta tayi sallar isha tare da shirin bacci ya juya ya fita.
Bikin Badiatu ya kusanto, Aliya kuma an shiga
watan haihuwa, in tana tafe ta dafe kugu, Salma takan sha dariya domin dai tana ganin masu ciki kala-kala, amma ba ta ga mai gwadare irin na Aliya ba. Ko su Amna dai iyayen son jiki ba ta ga tana irin
wannan yatsinar ba. Salma dai ta yi sabbin dinkuna
ban da wanda Shatima ya yi musu, kudinta da ta ke dan makalewa ta ba Salma Dankasa ta sai mata ya diddika irin nata masu kyau ta bada aka dinko mata
su, sun yi kyau sosai kayan. Salma ta zaci Shatima zai barta tun ana saura
sati daya bikin, sai ya daure fuska ya ce, ba ya
son shirme. Da kyar da rokon da Badi’atu ta yi ta masa ya barta ana sauran kwana uku biki, cikin kawaye Salma ta saje suka sha lalle ana ta shirye-shirye. Bikinsu uku ya tara mutane sosai, Salma ta yi
aron kudi dubu goma gurin Yaya Hadiza da ta
kwashi adashe za ta canza gado, Salma ta ce,
“Don Allah ta ara mata ta yi wa Badi’atu gudunmuwa ta
kashe kudinta duka ne, amma da zarar an gama bikin
za ta tara ta biya ta. Wani saitin agogo ta sai mata mai guda uku dubu goma sha daya. Sun yi kyau
sosai kowa ya gani sai ya yaba, Nafisa da Salma dama rana daya suka zo. Amna cewa, ta yi ita sai ranar biki. Aliya kuma shida kanshi ya ce ta bari sai
ranar biki. Salma gidan Hajiya Kaka ta sauka gidan Kaka don za ta fi sakewa, can jama’a tayi yawa,Amna gidan Anty Momiyo suke da Badi’atun da kuma kawayenta.
Duk shagulgula tare aka hada da nasu
Hamida kamar kamu, sisters day da sauransu. Dinner ce wadda abokan ango
suka shirya ita ce ta
Badi”atun kadai, wadda aka yi ana gobe daurin aure da zasu wuce zuwa Katsina inda mijin Badi’atu yake
aiki, domin Costom ne babba.
Amarya ta yi kyau har ta gaji a gurin Dinner,
su Salma an sha gayu babu yanda za a yi ka ce tana da miji. Sai faman kashe hotuna suke yi da sauran
kawaye da ‘yan uwansu Shatima sa’anninta, lokacin da aka zo soma rawa su Salma mazari nan suka shige tare da amarya ana ta rawa,
“yan uwa da abokan
arziki suna ta yi wa amarya liki. Kallo sai ya koma sama lokacin da wani ya zo yana yi wa amarya ruwan “yan dubu-dubu. Gurin ya Dauki ihu, Salma ta tsura masa ido cikin mamakin ko wane ne wannan,
ga shi ita kadai yake wa likin ban da ango. Da ya gama kuma ta ga ya nufi kujerar da su Anty Momiyo suke zaune, Salma ta taba Aishan Anty Momiyo tace,
*Wai wane ne wannan?”
Aisha ta ce, “Yaran yayansu mamanmu ne. ya
so Anty Badi’ atu sosai ta ki yarda”.
Salma ta ce,
“Shi ma yana da mata?”
Aisha ta ce,
*A’a, ita dai ya so ya aura, ga shi
yana da kudi sosai, kasuwanci yake yi komai suna yi
irin su shinkafa, taliya da dai sauransu’
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe