RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 25 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 25 BY HALIMA K/MASHI
Yusuf yace gurin biki na ganta ranka ya dade a taimaka min
Shatima ya sake furzar da wani huci mai zafi sannan yace kanasin kace min kunyi hira da ita kuma ita ta kwatanta maka nan gidan ?
Yusuf yace magana daya kawai tayi min wai in barta wai tanada miji
Daidai lokacin salma ta turo kafar gidan sanye da kayan islamiya zata tafi turus ta tsaya tana kallon shatima da yusuf shatima cikin tsawa yace ke zonan jikin salma ya dau rawa tazo ta taugunna tace gani yaya
Ya nuna yusuf kinsan wannan?
Tace eh
Yace meke tsakaninku?
Babu komai don inma zai fadi gaskia aina fada masa inada miji
Shatima ya zabga mata harara yaya akayi yasan gidannan?
Hawaye suka soma zubowa daga idanunta tace ni bani na nuna musu ba yace to waya nina muku? Ya tambaya tare da kallon yusuf
Yace kawarta ce ta nuna min
Shatima ya kalli salma fada masa ko wanene mijin naki don ya sani
Salma ta dubi yusuf cike da jin haushinsa sannan ta nuna shatima wannan shine yayana kuma shine mijina
Shatima ya kalli yusuf to kaji kuma ina fatan ka gamsu sannan kuma ka fita hanyarta
Ya dubi salma ke kuma koma ciki ina zuwa
Cikin tsoron kar ya hana ta karatu; tace
-Wallahi ni.
Ya daka mata tsawa, “Na ce ki wuce ko?”
Salma ta nufi ciki. tare da fadin, “Na shiga
ukuna Ya bi bayan Salma ba tare da ya kara kallon gurin su Yusuf ba. Tana Kokarin bude dakinta da makulli ya iso kusa da ila, makullin ya fadi don tsoro. Gani take yi dukanta zai yi.
Yace Ke tsaya ki amsa min, kuma ki fada
min gaskiya Salma ta tsuguna jiki yana Bari, ya ce,Kina son yaron?”
Ta zaro ido da fadin,Haba Yaya, ina da
miji kuma zan so wani kamar jahila?”
Ta fada mishi duk yanda abin ya faru
Ta ce,Kuma Kawayena ba su san cewa ina
da miji ba Ya ce,
“To daga yau ina son duk Kawayenki
su san cewa ni mijinki ne, sannan daga yau kin gama saka mayafi sai hijabai”
Tace
*To ai banida hijabai, sai wanda aka
kawo kwanaki kasai mana
Ya ce. “To a kara kawowa in sai muku. Tashi
ki tafi islamiyya
Salma ta wuce tana gode wa Allah da ya tsare
ta.
Amna cikin motarta ta nufi gidan Maman
Afra, sun Kulle da Maman afra ne saboda yawan yin
siyayya da takeyi a shagonta, mijinta sojan samane
babban soja. Maman Afra jininsu ya hadu sosai da
Amna, don suna zuwa gidan juna tare da bai wa juna
shawara. Ta kofar kicin ta shiga bayan tayi fakin
Ta samu Maman Afra tana saka danwake, ta
ce A’a yau kuma ke da kanki a kicin?!”
Ta ce. “Ke dai bari duk na saka su aiki, ga shi
yunwa ta ishe ni, kuma danwake nake son ci”
Amna ta ce Dole ki ji yunwa sha biyu fa ta
gota Maman Afra tace, “Kin san mai house ya
dawo jiya da yamma yanzun na dawo daga kai shi filin jirgi ya wuce Lagos”
Amna ta zaro ido,
“Kwana daya rak?” Maman Afra tace
“Don ni kadai ya zo,
kuma na samar masa da nutsuwa ya tafi yana
kewata Suka sa dariya, tace
“Maman Jafar a wannan
zamanin mu fa ba a sanya, mata suna nan a waje birjik suna jiran wanda za su dafe mawa. Ke da mijinki kina kallo wata a waje tana mulkinsa.Domin
yanzu mata ba sa jira a taya su,
Ta dauki danwaken tana fadin, “Mu je ciki
Maman Jafar, game da miji bana sanya, ban hada shi
da kowa ba wallahi. Duk lokacin da ya z0 sai na bar masa wata alama wadda za ta sa in kasance a zuciyarsa kowane lokaci®
Amna ta isa ta dafa kafadarta, *Tsaya Maman
Afra, wace alama ce wannan? Ni fa dama matsala ce da ni
Ta dube ta, “Wace irin matsala ce? Kodayake
mu karasa dakina
Ta kwala wa ‘yar aikinta kira, “Haula!”
Yarinyar ta z0 da sauri, ta ce,
“Kawo min
fulas din shayi da dafaffen kwai*
Kan gado Amna ta haye, don tace ba ra ta ci
dan waken ba. Maman Afra ta zube kan kafet din Wai Maman Jafar wace matsala haka dake Amna tace
“Humm, mijinmu ne in muna
tare kowane lokaci a hira da lokacin sirri sai ya dinga kira min sunan kishiya. Ko fa magana zai min sai kiji ya ce Nafisa, sannan yace au Amna? Maman Afra
abin yana damuna wallahi’
Maman Afra ta zaro ido,
“To ke kuma ki ka ce me?
HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe