RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 27 BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 27 BY HALIMA K/MASHI

 

 

Salma ta shiga lokacin da aka z0 daukan gadonta da

Shatima ya taba ajewa a daya daga cikin dakunan Salma.

Aliya ta ce ma matar yayanta su

yimà

Shatima magana su tafi da ita Zaria tunda shi ba ya nan, yana Abuja, babu kuma wanda zai taya ta aiki. Shatima bai musa ba domin shi ma hakan zai fi masa

sauki, don Salma ba za ta iya yi mata aiki ba, saboda aikin jini da ta yi sai da ta yi ta amai, har sai da ya amso mata magani, Don haka zuwa yamma ya kai suda wasu yan uwanta. Washegari kuma ya koma inda ya kai su

Alhajinsa, nan kuwa aka yi wa yaron huduba da sunan wani Kanin su Alhaji da ya rasu, ubansu daya, Aminu.

Shatima ya bada duk abin da ya san zai bada

duk da za su zo suna shi da Nafisa, ita ma Hajiya tayi kayan barka kamar yanda ta yi ma sauran.

Salma ta yi nasarar zama daya daga cikin

daliban da suka samu gurbin karatu a jami’ar

Ahmadu Bello ta Zaria, Shatima ya yi tsayin daka don ganin Salma ta zama daga cikin sahun farko na daliban da za su fara karatu. Ta so ya barta ta zauna Zaria ya cé, ya yarda kullum a kai ta a dawo da ita.

Ya ce, nan gaba in ta yi hankali sai ya koya mata mota take zuwa da kanta. Hakan ya Kara kunna Nafisa ta bijiré da zancen nata karatun a karshe dai ta

yarda ya sa ta makarantar koyon dinkin da ta je ta ga irin aikin da suke yi.

Safwan yana karya kwanar ya ce a ranshi,

Wannan ai layin su Anty Momiyo ne”

“Yana gangarawa sai ko ga gidan. Ya kalli gidan da murmushi, a fili ya ce, “Bari in dawo Anty zan shiga mu gaisa Kiran abokinshi ya sake shigowa, ya ce,Na shigo layin yanzun, ai na san layin, domin layin su Antyna ne, ga ma gidansu nan…. kai wane gidan ne

naka din?”Ya ce,

“Nine na karshe a layin, don layin ba

ya fita”Safwan yace

“Fito waje to”.Nan kuwa ya samu abokin nashi, aure abokin ya yi lokacin Safwan yana Chaina shine ya zo ganin amarya.

Sun shiga ya ganta sun gaisa, ya dai sha

ruwan da aka kawo, amma bai ci kayan garar ba, ya, yi wa amarya alheri ya taso. A gurin motar da abokin ya raka shi, ya ce, “Ga gidan Antyna can, zan shiga mu gaisa

Abokin ya ce,To bari na je mu gaisa tunda

makota muke”Bai shiga da motar ba a waje ya aje, suka kwankwasa. Aisha ce ta zo ta bude, cike da murna tace,

‘”‘Oyoyo Yaya Safwan”Ya ce,

“‘Anty tana ciki?”Ta ce,

“Ku shigo Ta shiga tana kiran,

*Mama ki fito ga Yaya

Safwan”

Sun zauna a falo Anty Momiyo ta fito daga

kicin tana fadin, «Batan hanya ka yi ko Safwan”?”Ya yi

*yar dariya, “Anty dai ba ni da ta cewa, don ba zan tuna rana ta karshe da na z0 gidan nan ba

‘Ta ce,Yau ma na san ba na musamman ka

zo ba Ya dubi abokin, *Ga wanda ya jawo ni,

abokina ne ya yi aure ya tare a layin nan, ba na kasar aka yi bikin shine na zo ganin amarya, yana min kwatance ina shigowa sai naga layinku Ta ce, “Ko da na ji, na san dai kazo ziyara. musamman da wahala Ta dubi abokin,Allah ya sanya alkhairi. Ko

shine aka yi wancan satin yara sun ce an kawo

amarya?”Ya ce, “Shine kuwa, amin na gode”

Aisha ta aje musu abinci da ruwa, Safwan yace, ‘Dauki abincin nän, yanzu za mu tafi”,.

Suna cikin hira wayar Aisha ta yi ringin,

wayar tana kusa da Safwan ya dauko tare da fadin,Wayar wane ne?”

Sai kiran ya yanke Yana kallon wayar

gabanshi ya fadi, hoton Aisha ne da yarinyar da yake ta nema. Ya sake kallon fuskar wayar tare da fadin,

“Wannan wayar ta wane ne?”Aisha ta ce, “Tawa ce

Ya shiga gurin hotunan yana kallo. Ya bude

tashi wayar ya tura hotunan Salma, sannan ya mika mata wayarta. Ya kalli Anty Momiyo,

‘”‘Anty bari mu tafi Ta ce, “Da wuri haka?”Yace;

“Zan zo na musamman

Ya. kalli Aisha, “Bari in ba kuna siyan kati”. Ya ciro yan dubu-dubu ya

mika mata, sannan ya mike, Anty tana taya ta godiya.

Suna fita ya sauke abokinshi, sannan ya dauki

hanya. Sai da ya yi nisa sannan ya tsaya ya ciro wayarsa ya fiddo hotunan da ya tura na Salma, ya tsura musu ido. Tunda ya rasa Badi’atu sai wannan

karon ne ya sake ganin yarinyar da yake matukar so, ya yi kwatancen duniya wa Mustapha bai gane yarinyar da yake nufi ba. Haka dai ya yi ta neman

wanda zai taya shi gano yarinyar ya rasa har

mahaifiyarshi ya yinwa zancen yarinyar, da kuma kwatancenta amma ba a gane ba. Cikin murna ya ce,

“Yau ga ta na ganta a sama, wa zan tambaya ne labarin yarinyar nan? Ina ganin bari dai in kira Anty

Momiyo Sai kuma ya fasa ya tada mota ya nufi hanyar gidanshi, zai bi a hankali har ya gano ta. Sa’ida Kanwar Safwan tana kallon hotunan da ya ce ta duba na wasu takalma da ya yi Oder , yace ta

zabi kala biyu. Ta ci karo da hotunan su Aisha, tace

Yaya Satwan ina ka samu hoton Aisha da matar Yaya Shatima?” Da sauri ya ce, “Me kika ce Sa’ida?”Tanuna mishi tare da cewa,

“Wannan

hotunan da bikin Anty Badi’atu ne Ya ce, “Ki ka ce wace ce dayar?”

Tace

“Salma ce fa matar Yaya Shatima,

amaryarshi”Ya amshi wayar, “Ita ce wannan?”

“Eh Ita ce”Safwan ya fasa shiga bandakin da zai shiga, ya zauna bakin kujera yana kallon Sa’ida. Ya sake

kallon hoton Salma zuciyarsa ta ce, Sa’idar da ba ta shiga cikin jama a ina ta santa?

Ya dube ta, “Ke da ba ki shiga mutane, ina ki

ka santa?”Ta yi dariya, “Allah yaya ita ce, sau nawa ina ganinta a gidan Hajiya?”

Ya ce,To je ki, wanka ma zan yi”Ta ce,

“Yaya ban zabi takalmin ba Na turo ta wayarki ki zaba, yanzu

sauri nike yi”Ta Ce,

«Yaya kai din fa sabga ta yi maka

yawa, kafin ka samu damar turo min.

Ya ce, “Ki je dai”.

HMmm LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE