RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 31 END KARSHE BY HALIMA K/MASHI

RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 31 END KARSHE BY HALIMA K/MASHI

 

 

 

Bai tanka ba, ta dube shi bayan ta fita, ” Na

gode Nan ma bai tanka ba. Ya karasa gidansa. Nafisa da yara suka fito suka tari Shatima, sai

yanzu ta gane cewa zamanta a Abuja jin dadi ne, don tana manta cewa tana da wasu kishiyoyi. Ta taimaka

masa ya yi wanka sannan ta zauna suka shiga cin abinci, Saura sati daya bikin

Auwal, Salma tana

wanki sako ya shigo wayarta, har kashi biyu a jere. Hakan ya tabbatar mata ba

“yan gidan waya ba ne. ta

dauraye hannu sannan ta goge ta dauki wayar. Daga ganin rubutun ta san wanda ya iya’ ne ya yi shi. Da

turanci ya turo sakon kamar haka;

Salma, barka da war haka, na san cewa yau

hutu ne na karshen mako kina gida. Ina fatan kina cikin Koshin lafiya. Safwan ne, babu mamaki ba ki da lambata, don na ce ki kira in samu lambarki amma kin ki. Ban ga laifinki ba, domin kina kare aurenki ne. salma na so in hakura da tsananin sonki

da ya kama ni a ranar da muka yi karo da ke, amma inna tuna wasu kalamai da mijinki ya yi a lokacin da muka je siyan wayarki, sai in samu kwarin gwiwa

tare da yarda cewa zan iya cimma burina. Ya sanar dani ke da shi ba auran soyayya ku ka yi ba, kuma ya ce shine dalilin da ya sa bai kuma tunkararki da huldar auratayya ba tun sau daya da ya gwada ki kaKi yarda. Kuma ya tabbalar min da rashin son da ki ke masa ne ya sa ki Kinsa, amma ba rashin wayon da

ki ka nuna masa a lokacin ba tunda yara ma wadanda ba su kai ki shekaru ba sun san rayuwar aure, kuma in na tuna yanda ya nuna ba zai takura miki ba in kin

fidda wani mijin zai barki, sai ince tattala min ke yayi. Kuma ban da Allah ya hukunta cewa ba shi da rabo ya za a yi ya zuba wa mace kamarki ido? Salma cike da karfin gwiwa nike fadin ina sonki, so na hakika, kuma na shirya daukan duk wani kalubale

da zai taso a dangi in ma da shi. Sannan zan nuna miki soyayya irin wadda ba a taba nuna ma wata ba a duniya ba cika baki ba. Fatan za ki yi nazarin zancena sosai, kuma kar ki damu kanki da cewa sai kin ba ni amsa, na fi son ki yi nazari. Na barki lafiya

abar kaunata

Salma ta jike sharkaf da rufa, ta maimaita

karanta dogon sakon ya kai sau goma sha biyu, sannan tuni ta manta da batun wanki ta hau gado don

son yin nazari. Duk da ta yi bakin ciki da sakon Safwan, amma ba ta ji haushinsa kamar yanda take jin na Shatima ba. A fili take fadin,

“Lallai Yaya Shatima ya kai makura a rashin sona. Na zaci tuni ya bar Wannan zancen?”

Ta tashi ta je gaban madubi.

“Mene ne laifina? Duk da ban kasance kyakkyawa ba, amma

ban zama mai munin da za a guje ni ba Gaskiyar Safwan ne Shatima ba ya ra’ayina, da ko bai sona zai bukace ni. Na yi ta yin tunani a lokuta da dama ina

neman dalilin da tun tayin farko Yaya bai sake kula ni ba, ashe Kaunata ce ba ya yi”

Ta ja numfashi, sannan ta saki kuka. Ta yi

kuka sosai domin tana tuna lokacin da ya fada a gaban kishiyoyinta da iyayenshi. Lallai ya kaita babbar hujja, kuma daga yau ta ja layi da Shatima, ta shirya yaki da tallarta da yake yi. Ta sake fadawa kan gado, ta ce,

“Ban san adadin mutanen da ya fadamawa ba ya sona ba. Gara ma ya sauwake min

‘in huta, matanshi ma duk a banza suke kallona’Yar karamar hauka dai Salma ta yi ta a ranar, kuma ta lashi takobin nuna wa Shatima cewa ta gaji da zama da shi, wanna satin in ya zo sai ya sake ta.

Ranar dai wanki bai gamu ba, sai washegari.

Ta kwana cikin fushi da ko abincin dare ba ta ci ba.Ta zuba idon ganinshi a washegari lahadi, amma bai zo ba, kila wanna satin ba zai zo ba, don ya kan yi haka yanzu.

Ranar litinin ta dawo makaranta da dare tana

kwance, duk ta gaji har ranar ba ta da walwala. Ta dauki wayarta tana kara karanta sakon Safwan. Ta samu kanta da rubuta mishi amsa duk da yace ba ya bukata.

*Yaya Safwan ban ji haushinka ba, da na zaci

ko kana son yin hulda da nine a munafunce lokacin da ka sa min katinka cikin laptop din da ka sai min. In ka shirya za ka aure ni zan yi yaki in bar wanda ba ya sona, in koma ga wanda yake sona. Da ma ni ban

damu da so ba bare in ji haushi, ina nufin ban san so ba. Sai dai na yi imani in na zauna da mai sona Zan koyi so, tunda ance zama da madaukin kanwa. Na gode sai dai ba za mu sake magana ba har sai na zama bazawara ko in ce sakin wawa Ta tura a layin Safwan.

Salma me take shirin yi? Domin yau talata

kwanaki uku-kenan ba ta daga kiran Shatima, sakon dubu biyar din da ta gani a account dinta ba ta gansuba ta gani ba. Ranar talatar ba ta je makaranta ba,

don ba za su yi komai ba tunda sun gama jarabawa.Tana yin tuwonta tana kallon kiran Shatima yana shigowa yana tsinkewa har kashi uku.A gefen Shatima, ya shiga damuwa da rashin samun Salma. A iya saninshi ko missed calls dinsa in Salma ta gani za ta mishi filashin ko sako. Ya fi

tunanin ba ta da lafiya ne, amma Aliya ta ce masa lafiyarta lau kuma tana zuwa makaranta. To me yake faruwa? Ya kuma kiran Aliya, ya ce,Salma tana gida?” Ta ce,

“Eh, don yau ba ta je makaranta ba

Shatima ya ce,

“Ki je ki gani lafiya? Sannan ki ce nace ta daga wayata yanzun nan

Aliya ta sabi danta wanda suke kira

da Abulkhairi ta nufi akin Salma. Ta same ta zaune

tana. cin tuwo, ta yi sallama, Salma ta dube ta a wulakance, sannan ta amsa. Aliya cikin mamaki ta kalli Salma, ta daure tace

‘”Baban Abulkhairi yace

ki daga waya yana ta kiranki, ko kin yar da wayar ne’?”

Salma ta dube ta cikin son jin Karin bayani,

“Waye kuma Baban Abulkhairi?”

Aliya tace, “Tofa! Yau kuma har mijin naki

ba ki. sanshi ba?”

Salma ta saki *yar dariya irin ta rainin wayo,

sannan ta ce,

“Baban Jafar, Baban Ashraf, Baban

Abdul wa kikace ma?”

Aliya ta ce,Kai yau wata rashin kunya ki ke

ji ne haka? To ko Baban wa aka ce an ce don ya haifa ne. kuma ke ma da kin haifa na san sai kin ce

baban wane. Tunda kuwa ba a da da sai a bari masu ya’ ya matansa mu yi”Salma taCe,

Tofa! Har dasu gorin haihuwa?”

Ta saki dariya, har da “yar shewa. Aliya ta ce,

“An yi miki, in fitsari banza ne

kaza ta yi mana”

Salma cikin fusata tace, “Ni don Allah ki je

kin sa tuwona ya huce ina surutu”.

Aliya tace

“To da ma mijinki ya ja min wanna rashin kunyar da ki ka yi min, don shi ya

turo ni” Salma tace

“Ki fada masa ba ni da lokacin

daga wayarsa” Ta dago wayarta daidai lokacin da kiran ya Kara shigowa,

“Gashi nan ya sake kira banji dagawa ba

Ta maida wayar ta aje. Aliya ta zaro ido tana

kallon Salma, ta mike ta dauki robar tuwon ta nufi kicin tana cewa, “Ki je ki fada masa sakona, don nasan ko ban ce ki fada ba kai tsegumi aikinki ne Aliya ta juya cikin tsananin mamaki, jiki har Bari yake, ta kira Shatima tana fada mishi wai Salma

ta zage ta tas! Har da kuka, kuma ta ce ba ta da lokacin daga wayarsa.Shatima ya cika da mamaki, ba don Aliya ta

fada mishi da, ba zai yarda ba. Duk da haka sai yana tantama, don haka sai ya tura mata sako kamar haka.Kin ce ba za ki daga sakona ba a kan me?Sai Salma ta tura masa amsa kamar haka.

Haka na fada’. Ta tura mishi.

Mamaki da tsoro suka dirar ma Shatima, ji

yake tamkar ya kulle ido ya bude ya ganshi a

Kaduna. Ya soma lissafin ranaku, kwana uku ya yi masa nisa. da ya zo gida bai iya daurewa ba yana fada ma Nafisa wai Salma ce ta yi kaza da kaza.Dariya Nafisa ta saki tare da cewa,Ai dama

_karshen alewa Kasa, kuma dama tunda kace ta je jami’a ai dole idonta ya bude” yace ni kuma nafi tunanin ko aljanu ne suka shigeta nafisa tace aljanun iskanci ba Ranar juma’a Salma ba ta je makaranta ba ta

bari ne sai in ta koma Zaria. Kayanta ta ke ta linki tana. loda su cikin akwati, ta kalli lodin kananan kayanta wadanda ta dinga siya tana sakawa lokula da dama in Shatima yana dakinta. Ashe ita aikin banza take yi? Ta girgiza kai tare da fadin, “Humm Allah

Ya dawo da mutumin nan lafiya ya sha

mamakina Takwas da mintuna na safiyar juma’ a Safwan

yana kwance kan gadonsa kamar ba shi ne zaibi jirgin karfe tara zuwa Abuja ba. Din yanada sabgogi da yawa kuma yanason ya ga Shatima.

Ya kai hannu ya dauki wayarshi da nufin ya sanar da Shatiman cewa, yau fa zai shigo Abuja, kuma yana

son in zai zo a kan son ganinshi da Shatima ya ce yana yi, sai dai kuma yana dauko wayar bai dire ko ina ba, sai kan rubutun Salma. Duk kwanakin nan matsawar ya dauki wannan

wayar, tofa sai

karanta rubutun Salma kafin ya yi abin da zai yi. kuma fa ba wai yana farin ciki da zantukan nata bane, domin ya gama nazarinsu kaf babu so a zantukan illa haushin mijinta da ta ji sakamakon abin da ya ce

a kanta. Kuma hanyar da ta biyo don yin bore ga mijinta ba za ta bayar da masalahar da ake so ba, illa ma a samu matsala in ba a yi sa’a ba rikicin ya shafi

dangi. In ya yi tunanin rubuta mata sakon dakatar da ita ta bari har sai lokacin da ta gama karatun kamar

yanda yä ce, sai kuma ya fasa in ya tuna da gargadin da ta masa cewa ba zasu sake ji daga juna ba har sai

ta zama ba matar Shatima ba.

Agogon dakin ya buga tara, da sauri Safwan

ya danna kiran Shatima. Ya dauka sun gaisa, sannan Safwan ya fada masa cewa zai shigo Abuja, kuma zai zo don ya ji neman da yake yi masa. “Ya ce, to shi ma dai yau zai tafi Kaduna don wancan satin bai je ba. Safwan ya ce, to ya jira shi

sai su dawo tare.

Karfe uku da rabi daidai Safwan suka isa

gidan Shatima, inda Shatiman ya je ya dauko shi.Nan suka ci abinci har ya yi wa su Ashraf kyautar

kudi. Suna cin abinci Shatima ke fada

masa bukatarsa ta son gwada kasuwanci.

Safwan yace,

“Gaskiya kayi tunani.

kasuwanci yana sama da duk wani aiki a gurina, ko don da shi na bude ido?”

Shatima ya ce,

“Haka ne, ba wai don ka

bude ido da shi ba, haka batun yake. A rana sai ka ci ribar albashin wani na wata daya

Safwan ya sa dariya, ya ce,

“‘Na wata kadai. na shekaru ma

Sun tattauna sosai. inda Safwan ya ba

‘Shatima shawarar ya shiga harkar man fetur, ya ce,amma jarin naira miliyan goma sun yi kadan sai

dai ya zuba kar ya waiwaye su yanzu a yi kamar shekara. Shatima ya gamsu da duk shawarwarin da

Safwan ya ba shi Sun nufo Kaduna tare shi da Shatima,

zuciyar Shatima tam da tambayoyi a kan Salma.Ita kuwa Salma zaman jiran zuwan Shatima take yi, don ta hada kayan sawarta gaba daya

gadonta ta jingine, ta tattara kujerunta gefe guda ta

Zuba kayan kicin dinta a buhu ta daure, ta tara komai a falo, sannan ta ci uban kuka idanunta sun

kumbura suntum! Muryarta ta dashe, sai dai ita baza ta ce ga dalilin kukan nata ba. * Shatima bai san dalili ba, yana shigowa

gidan ya ji wata mummunar faduwar gaba.

Idanunsa suka dira kan dakin Salma, dakin a bude yake a wangame. Kai tsaye can ya nufa da kayan

da yake dauke da su a hannuwanshi. Baki ya saki ganin babu labulan a kofar, ya karasa falon nan ya

yi turus! Ya zube kayan da ke hannuwanshi ya

shiga cikin falon tsibi-tsibin kayan yake bi da

kallo.Ya yi karfin halin  kwala mata kira,

“Salma! Salma!!”

Ba ta amsa ba, sai dai ta fito daga cikin

dakin tana rataye da jaka da kuma akwatin da za ta iya dauka tana janshi. Ya kalle ta tare da fadin,Lafiya?”

Harara ta watso mishi da jajayen idanunta,

“Lafiya ka ke tambaya? To ita ta kawo haka, ba don ina jiran takardar saki ba da babu abin da zai saka tarar dani a gidan nan yanzu kam ka bani takarda ta don bazan sake kwana a cikinshi ba

Ta daga murya shatima ka sakeniiiii

Hmmm bari mu danja numfashi anan

Mu hadu a littafi na hudu

Related Articles

Leave a Reply

Back to top button

You cannot copy content of this page

Adblock Detected

YOU ARE USING ADBLOCK TURN IT OFF TO COUNTIUE BROWSING OUR WEBSITE