RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 4 BY HALIMA K/MASHI
shirya za ta tafi Kano don yin tatiyarsu, Shatima ya yita maza ya ce,
“Allah ya tsare hanya”. Ya kuma kawo
dubu goma ya ba ta.
Kanwar su Alhaji Hajiya Sauda ita ce ta fito da
anko, ta kira Shatima tana sanar da shi cewa, ga na” matanshi kala bibbiyu, kudinsa naira dubu arba” in.
Ya ce, “Anty na mutum uku za a cire, Amna ba
ta nan anty tace To zan barsu gurin Kaka”
Ya ce, “*Shi kenan, ki turo account in tura miki
kudin Da ya sanar da su batun anko, Nafisa ta ce za ta
sa Hamida ta je ta amshi nata a gurin Kaka din. Aliya ma cewa ta yi za a zo daga gidansu a karba mata.
‘ Salma kuwa cewa ta yi, nata a bai wa Anty Badi ‘atu ta
bai wa mai mata dinki. NEWSPAWA.COM
Ya ce, “To telan ya sanki ne?”
Ta ce, “Ta yi masa kwatance na kawai
Salma Bash shine sunan da *yan makarantar su Salma ke kiranta da shi. Kawarta Salma Sadik Dankasa
ita ce ta rada mata shi. Zuwa wannan lokacin Salma ta
waye, ta goge, ga turanci tana gane karatu sosai. Haka
nan in ka ganta tana tsalle-tsallenta sam ba za ka ce tana da aure ba. Salma da ma yarinya ce, sannan ga ta
da son wasa, shi ya sa kawancensu ya dace da Salma Sadik. Suna cikin group din Kwallon tebur da kuma rawa irin ta makaranta. Wani lokacin ma wayarta ta
kan kunna a gida tana cashe rawarta.
Yau Shatima a akin Salma yake. Dafadukan
taliya ta yi, ta zubo masa don ta lura yanzun yana cin
abincinta, tunda aka yi wannan hayaniyar.
Ta aje a gefensa yana zaune kan kujera yana aiki da laptop. Ta
koma ciki tana atisayen rawar da za su yi gobe in sun je
makaranta. Ya {walla kiranta.
Ta fito ta durkusawa a gabanshi, ya ce,
“Wai ke duk lokacin da zan shigo sai in ji kina jin wannan sautin, ina ki ka samo shi?”
Ta ce, “Muna amfani da shine a club dinmu na
rawa”NEWSPAWA.COM
Ya kware da abincin da ke bakinshi, nan ya
shiga tari.
Salma ta ce, “Ya salam!”
Ta tsiyaya ruwa a kofi ta mika masa. Ya amsa
ya shanye, ya ajiye kofin sannan ta dube ta murya a shake ya ce, “Rawa? A wane club kuma?”Ta ce,
“Yaya na makaranta ne, an ce mutum ya
zaba ko rawa ko waka Ya ce,
“Kina manta cewa kina da aure ko?”
Ta ce,
“Ban manta ba”. Ta sunkuyar da kai.
Ya ce,Gaban maza ku ke rawa ko?” Ta ce,
‘A’a Ya ce,
“To kar dai ki sake in ji an ce kin shiga
gasar rawa, balle a zo ana yinta a gaban mutane
Ta ce, “Ba zan yi ba, jibi ma za a yi mana
hutu’ Ya ce,Shi kenan.
. Yauwa Badi’atu ke ta
damuna wai dinkin anko wane kala za a yi miki? Na ce
in na dawo zan neme ta. Bari in kira miki ita”
Salma ta ce,
“Mun yi waya dazun Yaya, da ma
wai ba ta same ni ba ne ta kira ka. Nida zaka barni inje Zaria din da na kai wadansu kayan
Ya ce,
“A’a sai biki za ki je gaskiya
Ta ce,Allah sarki Yaya, kayana sun sha ruwa
wadanda aka dinka min”
Ya ce,Yau saura kwana goma sha daya bikin,
zan je ranar asabar sai ki ba ni sako Ta ce,
*Badi’atu za a bai wa, zan amshi wasu
style a hannun Salma Sadik”
Ya dago ya dube ta,
“To wa zai biya kudin inkin?”NEWSPAWA.COM
Ta yi murmushi,
“Ni zan biya kayana
Ya tattara hankalinsa a kanta,
“Ina ki ka samu kudi?”Ta ce,
“Wanda nike tarawa.Ya yi murmushi, “Kawo su mu gani, sun kai) dubu goma?”
Ta yi dariya tare da nufar daki. Ledar da ake
saka zanin gado ta dauko ta zo gabanshi, ta juye kudin a Kasa. Mamaki ya kama shi, ya ce, “Wannan duk sune?”Ta ce, “Sune mana”
Ya ce,Lallai kudi wawaye ne, sun, kai nawa
Yanzu tace
, “Sai dai a kirga a gani”.
Ya dauki
yan dari biyar, bari in hada wadannan, ke kuma ki hada sauran
“Bari in hada
Ta soma hadawa tana cewa,
Kila su kai irin dubu talatin din nan
Sun gama lissafi abin da yaba su mamaki, sai
ga kudi dubu dari da biyar har da naira sittin. Salma tace, “Kudina ne kadai kuwa?”
Ya ce, “Ana ba ki ajiya ne?”
Ta ce, “A’a, ni dai to ko aljanu suna saka
BY Mistake?
Ya yi dariya, “Kin dauki watanni kina tara su’
Ya dube ta, “Ni ma za ki ba ni aron dubu
hamsin”NEWSPAWA.COM
Ta ce, “a,a dai a raba zan dai ba ka kyauta.
Toni ban ma san ya zan yi da su ba. Ka amsa duka
mana?”Ya ce, “A’a ba zan amsa ba, ai kudinki ne”Yà Kirgi hamsin, “Wannan ma na ara ne, zan baki insha Allah”.
Tace Ni dai bar maka na yi gaskiya
Shi ma ya sake cewa,
“A’a zan ba ki su.
wadannan kuma in kin je gida sai ku yi shawara da su
Inna, ki yi yanda ki ke so”
Ran’- da za su tafi Zaria ita ce ranar farko da
dukkansu za su je gidansu, don haka duk suna cikin murma da doki sunje wajen shiga mota nan ne akadanyi wasan kwaikwayo nafisa da aliya duk sunata harin gaban mota salma tana ganin haka sai tayima kanta mazauni a baya
Aliya da yake ta fi Nafisar lafiya sai ta yi maza ta fada gaban. Nafisa ta kama kugu ciki
ya yo gaba, ta ce, “Ni ce zan zauna a gaban mota, don nice da girki”
Aliya ta kalle ta, da dan murmushi,
“Ai gaba
mazaunin babba ne”
Shatima ya riske su cikin wannan musun, don
ya je gurin Baba maigadi ya sallame shi da abin da zai
– rike kansa kafin su dawo. Ya kalli Nafisa da ke tsaye,ya ce,
“Kina nufin sai na zo za ki shiga?”Cikin dan wasa ya yi maganar. NEWSPAWA.COM
Ta ce, “Ni gaba zan zauna .
Ya kalli gahan, Aliya ce a ciki, ya ce, “To ki
shiga baya tunda ta riga ta zauna”
Nafisa ta ce,
“Oho, da ma kai ne ka ce gaban
mota na uwargida ne?”
Aliyar ta yi *yar dariyar kissa,
“Da ke sai ki bar babba a baya?”
Shatima ya ja tsaki, wai har shiga motar ma sai an yi masa wata ka’ida? Aliya ta ce, “Shi ne na gani”
“. Cikin ‘yar dariya ta yi maganar.?
“Maimakon ki shiga baya ga ciki inda za ki
sake abinki” Nafisa ta koma baya ta coge, tare da dafe ciki,
ta ce, “Sai dai ko a bude but din a fito min da kayana,don kuwa babu dole sai na je a cikin motarsa’
Kar in sake in ji kin bi motar haya. Inba za ki shigo ba, to ki koma ciki ki bude dakinki ki
shiga e Ta tura baki, “Ai dai ka san wanna bikin dole in je shi. Domin yanda ka ke jin cewa ‘yan uwanka ne za su yi aure, haka ni ma ‘yan uwana ne”
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE NEWSPAWA.COM