RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 5 BY HALIMA K/MASHI
Ya ce,
“To za kiyi min rashin kunya ne ko za
Ki fada min magana ne?”
Ta yi shiru tana rike da Kugu.
Ya koma ya zauna, ya sauke ajiyar zuciya
sannan ya soma magana da Aliya, “Yi hakuri ki koma bayan” www.newspawa.com
Aliya ba ta so haka ba, amma sai ta wayance ta bude Kofar tana fadin, “Zo ki shiga ba don halinki ba,
kuma kar ki sake ki takura min yaro na fada miki”Nafisa ta shige tana zumbura baki. Salma duk
tana jinsu, ita neman layin kawarta Salma Sadik take
yi. Aliya cikin son daba ma Nafisa magana tace, “Ke baki fadan shiga gaban motar? Da yake yanzun Salma ta
Gama sanin wace ce Aliya sai ta tabe baki, tace,
“Anty ai ni gaban motar Yaya in da gundira ya kamata ya gundure ni. Kullum sai na hau zuwa makaranta”
Aliya ta tabe baki ba ta sake magana ba.
Suna hawa babban titi layin Salma ya shiga.
Kuka suka soma shirmansu, “Hi kawata ya ki ke?”Ta ce,
“Ya ki ke Kawas? Gamu za mu je Zaria din
Tace Haba ki ce yau sai City?”
Salma ta ce Ga mu a hanya, in na dawo zan
Zoin kawo miki kayanki”
Salma ta ce,
“Ke din ce zaki zo? Lallai
Salma ta ce, www.newspawa.com
“Allah zan z0. Zan roki yayana ya
barni inz0 ko ya kawo ni in maido miki style dinki dana ara kin ga mun yi hutu, kuma za a shiga azumi Salma Sadik ta ce “Ki bari dai zan z0 miki da sallah
Salma tace “Za mu sake zuwa Zaria da sallah,
amma duk da haka zan jira ki”.
Ta ce, “Shi kenan”. Suka yi sallama.
Shatima yace, “Ina za ku je yawon sallah din?”
Salma ta ce, “Uhm
Ya ce”Na san kin ji ni”,
‘Ta ce, “Zaria mana da sallah fa”
Ya ce, “A’a ba za ku z0 ba, kun je daf da azumi
sannan ku je da sallah:”
Ta yi shiru. Aliya da Nafisa har suna hada baki
gurin cewa, “Haba dai, sallah guda!”?”
Ya ce, “Au kuma kuna son zuwa ne?”
Aliya ta ce, “Haba my love, sallah lokacin
ziyara ne Ya ce,
“To ni dai ba dinkin sallah zan samu
damar yi muku ba, don akwai abubuwa a gabana”
Aliya ta ce, “My love ta ya ya ma za mu ce
maka sai ka yi mana kaya, ga’ zannuwan nan na lefenmu za mu dinka”.
Nafisa ta ce
-Ni kam zanyi da ace tun muna
gida aka yi wannan zancen da na zo da kayana na bada www.newspawa.com
dinki”.
Shatima ya ce,
«Wannan ai mai sauki ne, in zan
sake shigowa Zaria zan z0 miki da shi”
Ya kai hannunshi daya ya shafi cikin Nafisa
tare da fadin,
“Ke kuma wa yace miki kwalliya ba ta
yi miki kyau?”
Cikin shagwabar da ta san yana so, ta ce, ” In jika mana
Ya maida kanshi titi, “Kin ma san me ye? Ai
kin ma fi kyau a haka. Ina kallonki da dan yarona
‘Ta ce, “Ni nace maka yarinya ce fa”
Ya ce, “Ai ni na yarda da batun likitan, duk da
shi ba Allah ba ne. Amma Allah ya ba shi ilimi a kan haka
Aliya bakin ciki ya hana ta magana; sai da
Shatima ya ce,
“My love wannan layinku ne, hoto ya
nuna namiji amma tana musu”.
Ta yi dariyar yake, “Ai kin dai ji an ce namiji
ne to hakan ne”
Nafisa ta ce, “Ni dai Allah ya ba ni mace ba zan daina wannan addu’ar ba
Aliya ta ce, “Ki dai roki alkhair kawai”.
Yace, “Abin da ya fi kamata ma kenan
Sun isa Zaria cikin tukin da yake na nutsuwa da
kwanciyar hankali. Kai tsaye gidan su Hajiyarshi ya
nufa da su.
Ta sa an gyara gurin bakin ta dauka har da
Amna za azo ta sa an yi girki na alfarma da kaji. Tafito da fara ‘a tana fadin, “Sannunku.
• sannunku”Ta dube su, “Ina Amna?”
Shi ma wanda ke kokarin fita ya ce,
“Sun je umra www.newspawa.com
Hajiya tace
“Masha Allah, Allah ya dawo
mana da ita lafiya
Sannan ta kalli salma
“Kowa ya nemi gidan
uwarsa in- yana da shi, tunda dai ku ba baki ba ne, dama na sa an gyara sasan ne saboda Amna, don nice
uwarta ta Zaria
Shatima yaCe,
“Naso Su zauna
anan gabadaya
Hajiya tace,
“A’a sam ba zai yiwu ba, ga dai
abinci nan su ci, kowa ta kama gabanta
Nafisa tace
“Har ni Hajiya?”
Hajiya ta ce,
“Ai ke nan gidan ubanki ne, in zaki zauna zauna mana
Salma dai hakan ya yi mata dadì, don tana
kewar Innarsu. Abincin ma ita ba ta ci na kirki ba saboda doki.
Ita da Aliya ya dauka don ya kai su gidajensu,
Nafisa ta ce, sai Alhaji ya zo sun gaisa.
Aliya ya soma saukewa, sannan ya nufi kofar
gidan su Salma. Cikin doki ta fito za ta dauki kayanta.
Ya yi saurin riko hannunta, “Kina ta sauri za ki rabu dani ko?”
A hankali ta kalli hannunsu, sannan ta dago ta
kalli fuskarshi. Babu ko digon son Salma a zuciyata Kalaman da suka dawo mata gar a zuciya kenan. A hankali ta zame hannunta,
Cikin sauri ya sake rike hannun gam!
“Fadi abin dake ranki”
Ta Kirkiro murmushi, “Ba ni da magana”
Ya ce Ba za ki yi kewata ba?”
Ta ce, www.newspawa.com
“Ko dakina zan yi kewarshi bare kai. Ina
da sabo sosai
Ta kuma janye hannunta daga nashi, tare da
Fadin, “Bari in shiga ciki’
Ya sauke ajiyar zuciya, “Ban yarda ki je ko ina
ba ba tar da kin sanar da ni ba’
Ta ce, “Ni kadai kacema haka Don Anty
Aliya ban ji kace mata haka ba”. Cikin shagwaba tayi maganar.
Shatima ya ce, “Ai ita ta san me ta ke yi”
Salma ta ce, “Humm, kai dai kana yinta da
yawa Yace Me ya sa ki ka ce haka?”
Salma ta ce Komai ita”.Ya ce,
“To shi ne ya sa ki ka ce na fi sonta?”
Tace
“To wa ka fi so a cikinsu?”
Ya ce, “Ya aka yi ki ka cire kanki?’
Ta ce,
“Yaya kenan, ai da ma ni ba na cikinsu
sam”Ta yi murmushin Karfin hali sannan ta fice daga
motar da sauri, tare da fadin, “daga min baya in Dauki
kayana Ya ce, “A bude yake, ki daga ki dauka
Tana fito da kayan shi ma yana fitowa daga
motar yana kallonta.
“‘Kin cire kanki a cikin matana saboda har
yanzu ba ki san so ba?”
Ta ce, “Humm, ka tafi abinka Yace” Duka kika kwaso kayanki?”Ta ce,
“Ba ka ce in dauka duka ba? Amma ka
cire wanda ka ce in ba ka ko?”
Ya ce,A gabanki na dauka, har kin manta?”
HMMM LABARI fa nata Tafiya shin KOYA ZATACI GABA da KAYAWA KUDAI KUCI GABA da kasancewa damu A koda Yaushe www.newspawa.com