RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY HALIMA K/MASHI
RANA DAYA BOOK 3 CHAPTER 6 BY HALIMA K/MASHI
Ta ce,”To ba za ka shiga ku gaisa da su Inna
ba?”
Ya dubi jikinshi,A,a zanzo na
musamman
Kananan kaya na saka yanzun”.Ta ce,
“Shi ke nan, amma don Allah ka kawo
min Badi’atu ta kawo min kayana
Ya ce,
“In ban samu zuwa ba sai Mustapha ya kawota Ta ce, “Duk daya ne”.
Salma ta yi murna da dinkunanta da Badi’atu ta kawo, sun yi kyau sosai da yake ita ma Salma Dankasa
kusan Kirarsu daya da Salma din. Sai dai Salma Dankasa ta fita cika idanu.
Salma ta dubi Badi”atu ta ce,
“Anty Badi’atu nawa ne kudin dinkin?”
ido A Badi’ atu ta ce, “Yaya fa ya bada
Salma ta CE Kai! Ya bada kuma shi da ba shi
da kudi? nage Badi’atu ta ce,
“Ai tun lokacin da ya kawo
kayan ina kai wa ana fadin kudin ya biya”
Sai da Salma ta yi wanka ta shirya, sannan suka
tafi tare da Badi’atu. Can gidan Hajiya Kaka suka nufa,
sun bar Inna cikin murna ganin yanda Salma ta yi kyau, ga shi ta waye abinta.
Da dare suka bar gidan Hajiya Kaka, Salma ta
dawo su Badi’atu suka wuce. Ta ciro kudin da ta zo dasu ta ba Inna dubu arba’ in a ciki, ta rike goma. Ta ce a
sai mata wani abin. Sauran da ta cire ta sa a jakarta tace gobe daurin aure zan so ace da kudi a jikina, mutum ya dan yi alheri.
Abin da ya ba Aliya mamaki, ranar daurin aure
sun hadu a gidan kaka, duk kowa ya zo ya kai
gaisuwa ana zaune, Salma ta shigo ta yi kyau sosai
cikin atamfar ankon, doguwar riga. Ga dauri ta sha abin sha’awa. Ita ma ta je gaban Kaka ta durkusa har Kasa ta gaida ita.
Kaka ta ce,Wace ce wannan?”
Aliya cikin gadara da son ganin an wulakanta
Salma ta ce,
“Salma ce kaka, matar Shatima”
Kaka ta dube ta,
“Masha Allah, to Allah ya yi
muku albarka dukkanku”.
Salma ta bude jakarta ta ciro leda baka babba,ta mika ma Kaka da hannu biyu ta ce, “Ga shi KakaTa amsa tare da tambaya,
“Me muka samu?”Salma ta zauna gefe ba ta ce komai ba. Kaka ba
ta bari ba, ta bude ledar. Turmin zani ne da turaruka sai
“yan dari biyar guda hudu. ta kalli Salma,
“Allah ya yi
miki albarka. Ina jin ke ce za ki saka ma uwar Shatima da abin da ta yi min”
Nafisa ta mike ta fice, Aliya kuma aka yi tsuru
cikin jin kuna. Dole ta shiga jerin masu cewa, “Amin”
In Kaka ta yi ma Salma addu,a, ga shi Kaka ba ta raina
abin fada, kowà ya zo a zuri’arta sai ta nuna.
“‘Kun ga abin da matar Shatima karamar ta
kawo min”
Dole Aliya daga sallah ta sulale ta gudu; Salma ko da yake kanta a waye yake, tuni ta
shige cikin sa”anninta suna ta hotuna. Karyar kowa dai
ta turanci ne, kuma ita ma yanzun ta kware gurin fesoshi. Hakan ya sa wasu daga cikin dangin Shatima
sha’awarta. Sai da aka dau amare sannan Salma ta je ta sallami Kaka, ta samu Hajiya a gabanta zaune. Ta
durkusa tana gaida Hajiya don ba ta ga zuwanta ba
Dole Hajiya ta amsa, ta kuma yi mata godiya
don Kakar ta riga ta fada matA kuma ta bukaci Hajiyar
da ta yi mata godiya a gurin Salma.
Kaka ta ce,
“Allah ya yi miki albarka, ki gaida
manyan naki, ki wa ‘yar uwar taki ban gajiya
Da yake Yaya Hadiza tazo
Tana fitowa don ba nisa ta hau hanya. Wata
mota tana ta yi mata horn tà yi banza, Kila ma irin mazan nan ne sun ga duhun dare. Motar ta yi gaba kadan ta tsaya, Salma ta fusata, ta ce, kila zan ji me motar nan. Ta zo za ta wuce, ta jikin motar ta ji an ce,
“Yammata ji mana”. Ba ta tanka ba, amma muryar da ta ji ya sa
gabanta faduwa, har ma ta waiwayo ta kalli motar,. Bata san motar ba, amma muryar irin ta Shatima ce. Ji tayi an kara cewa,
“Don ana miki magana shine za ki
share mutane?”
Ta waiwaya da sauri, tare da fadin, “Kai ina da miji? Maganar ta makale ganin Shatima. Tayi muryar shagwaba, “Haba Yaya, ka ba ni tsoro dayawa Ya ce,
“Wa ya ce ki fito titi? In wani ya taka ki
kamar yadda na yi din nan fa?”Ta ce,
“Ai na ga babu nisa ne Ya kama hannunta”Muje in kai ki gida». Baya ta shiga, sai ta ga ashe Munnir ke jan
motar. Ta gaida shi, sannan suka sauke ta kofar
gidansu. Ya miko mata leda, “Ga shi rabonki ne
Ta amsa, ko ba ta buda ba ta san kaza ce, don taga suna ci suna hirar gidan biki.
* Tana nuna wa Innarsu hotunan da suka dauka,
Inna ta ce,
“Na ga abubuwan da Hadia ta zo da su na
rabo Salma ta ce, “Sun yi rabo sosai. To auran fa yara biyu, kuma kin san Babansu ya rasu, amma an yi
musu komai. Gaskiya zuri’arsu suna da yawa, ga zumunci”
Inna ta ce, “Gaskiya sun more, don duk zuri’ar
da ke rike da zumunci ba ta tabewa” Salma bata bada wani labari da zata bata
sunan mijinta ko na danginsa ba.
Har Hajiya da su Yaya Hadiza suka dauko
zancenta, sai ta nuna ai yanzun Hajiyar ta daina nuna mata kiyayya. Inna ta juya zancen da Salma ta kawo
mata, ta ce, “Lokacin da na fita takaba ma Hadiza ta sai
min turmin zani, sai su Babarku sun hado min
zannuwa uku, har da hijabai daga kauye”
Salma ta ce, “Ai kuwa an gode. Ni ma na so
zuwa Ya Shatima ya hana, wai sai ka ce biki?”
Inna ta ce,Gara da ya hana din, tunda lokacin
duka kwananku nawa?”
Ta ce,”Mun dan jima fa Inna”Ta ce,
“Ai yanzu komai ya wuce”
Washegari za su koma gida Yaya Hadiza tazo
dan -su shawarta kan kudin Salma, ita Yaya Hadiza cewa ta yi,; a canza mata kujeru tunda guda uku ne sai a siyo mata saiti. Salma tace duk yadda aka tsara, amma wa zai
Siya nawa? Hadiza ta Ce,
“Gun Lami dillaliya aka sai naki,
kuma za ta siye su sai a cika a sai wasu
Salma ta ce,To motar da za ta kwaso wadancan fa?”Hadiza tace
“Ai tana da masu mota, illa dai
Ki kira mijinki ki tambaya, sai mu je gidan a zaba
Suna tsaka da hira da Hajiyarshi akan abin da ya shafi haihuwar matanshi, da kuma zuwan azumi da
sallah wanda ake kan shirinsu, sai ga kiran Salma ya shigo! Ya daga tare da sallama, ta amsa sannan ta gaida
shi. Ya amsa tare da cewa, “Ya ya dai Salma?”
Ta ce, “Da ma za mu je gidan wata mai saida
kaya ne za mu duba kujera”.
“Ke da wa za ku?” Ta ce,
“Yaya Hadiza” Yace
“To kar a zauna anjima za mu tafi”
iTa ce,Insha Allah
Sun je sun zaba, kuma ta amince amma da
yarjejeniyar za ta bi motar kaya don ta ga wadancan.
Sun amshi lambar juna don mai kaya ba sanin gidan tayi ba. Karfe uku tana kwance a kan tabarma a tsakar
dakin Inna, sai ta ji sallamar Yaya Auwal. Su biyu ne
suka aje buhun shinkafa karamin da buhun gero, sai
suga da kayan tea. Salma ta ce,
“Daga ina?”Sallamar Shatima ya sa ta samu amsarta. Kan
tabarmar da ta tashi daga kwance nan ya zauna kusa da
HMMM LABARI FA NATA TAFIYA SHIN KOYA ZATACI GABA DA KAYAWA KUDAI KUCI GABA DA KASANCEWA DAMU A KODA YAUSHE